ENGLISH DESCRIPTION
THE EVIL CONFESSION: The Secret That Destroyed Lives
One sentence spoken in anger was enough to change countless lives forever.
Habeeb falls deeply in love with Salma, but his love is met with nothing but hatred and rejection. As heartbreak slowly destroys his health, he refuses to let go of the woman who has sworn she will never love him.
Desperate to save his son's life, his father, Alhaji Muhammad, utters a terrible threat he never imagined would haunt him. That single confession becomes the beginning of a devastating chain of events involving a tragic accident, political rivalry, revenge, betrayal, and a courtroom battle that will forever change two families.
But the greatest shock is yet to come.
What happens when the son of the man who made that evil confession becomes the lawyer defending the father of the very girl whose life was threatened?
Will justice prevail?
Will love survive hatred and revenge?
Can the truth heal hearts already shattered by betrayal?
Or will one reckless confession destroy every hope of happiness?
THE EVIL CONFESSION is a gripping emotional thriller filled with forbidden love, family secrets, political intrigue, courtroom drama, revenge, unexpected twists, and heartbreaking sacrifices that will keep you turning pages until the very end.
If you enjoy Hausa romance novels, emotional family drama, legal suspense, enemies-to-lovers stories, shocking plot twists, and unforgettable love stories, this is a novel you cannot afford to miss.
HAUSA DESCRIPTION
MUGUN FURUCI: Sirrin Da Ya Ruguza Rayuwa
Wata kalma guda ce ta fito daga bakin mutum cikin fushi, amma ta sauya rayuwar mutane har abada.
Habeeb ya kamu da tsananin son Salma, amma soyayyarsa ta gamu da ƙiyayya mai zafi. Duk da rashin lafiyarsa da ke ƙara tsananta saboda baƙin cikin soyayya, zuciyarsa ta ƙi daina ƙaunar wadda ta rantse ba za ta taɓa sonsa ba.
A yunƙurin ceto rayuwar ɗansa, mahaifinsa Alhaji Muhammad ya aikata abin da bai taɓa tsammanin zai aikata ba. Wata mummunar furuci ta fito daga bakinsa, furucin da ya zama farkon bala'in da ya girgiza iyalai biyu, ya haifar da haɗari, makirci, ƙiyayya, da shari'ar da za ta canja rayuwar kowa.
Amma abin mamaki bai tsaya nan ba.
Me zai faru idan ɗan mutumin da ya yi wannan mugun furuci ya zama lauyan mahaifin yarinyar da aka yi wa wannan barazanar?
Wa zai tsaya a gefen gaskiya?
Wa zai ci amanar zuciyarsa?
Shin soyayya za ta iya rayuwa bayan zubar da jini, ƙarya, da ramuwar gayya?
Ko kuwa mugun furuci ne zai binne ƙauna har abada?
MUGUN FURUCI labari ne mai cike da soyayya mai raɗaɗi, sirrika masu firgita, siyasa, makirce makirce, kotu, ramuwar gayya, da juyin al'amuran da za su sa ka kasa ajiye littafin har sai ka kai ƙarshensa.
Idan kana neman Hausa novel mai cike da soyayya, tashin hankali, sirrin iyali, shari'a, ramuwar gayya, da labari mai cike da suspense, to MUGUN FURUCI shi ne labarin da bai kamata ka bari ya wuce ka ba.