ENGLISH DESCRIPTION
⚜️ ANOTHER TOWN ⚜️
Hidden away from the modern world lies Garuk, a mysterious town where ancient magic rules, outsiders are forbidden, and every soul lives under laws older than time itself.
At the center of it all is Waira, a breathtaking young girl destined to inherit the throne of the kingdom's powerful mystics. Gifted with supernatural abilities and burdened by terrifying prophecies, she has been warned that the day she leaves Garuk will be the day she loses everything.
Far away from her world lives Maleek, a wealthy young man haunted by a strange curse. He despises women with a hatred he cannot explain, a darkness that has isolated him from everyone around him.
Then there is Ameer, handsome, arrogant, and powerful. A man who believes money can buy anything and whose growing conflict with Maleek threatens to explode into a war of pride, revenge, and destruction.
But fate is already weaving a dangerous path between them.
What secret is hidden within Garuk?
Why is Waira forbidden from leaving her homeland?
What mysterious connection links the enchanted flute, the kingdom of Garuk, and Maleek's troubled destiny?
As love, power, ancient magic, betrayal, family secrets, and destiny collide, shocking truths will emerge that could change their lives forever.
ANOTHER TOWN is a thrilling Hausa fantasy romance filled with mystery, suspense, forbidden love, traditional magic, royal secrets, powerful characters, and unforgettable twists.
If you love captivating Hausa novels packed with romance, suspense, mystery, magic, emotional drama, and breathtaking adventures, this is one story you will not be able to put down.
HAUSA DESCRIPTION
⚜️ WANI GARI ⚜️
A wani boyayyen gari mai suna Garuk, inda tsafi ya fi jini daraja, inda soyayya da baki suke haramun, kuma inda rayuwar mutane ke gudana bisa dokokin da suka fi karfin tunanin duniya, wata kyakkyawar yarinya mai suna Waira tana jiran ranar da za ta zama Sarauniyar Matsafa.
Waira tana dauke da sirrikan da ba kowa ya sani ba. Tana iya karanta abubuwan da suka faru a rayuwar mutum, tana da baiwar da ta bambanta da kowa, kuma an gargade ta cewa ranar da ta bar Garuk ba za ta sake dawowa ba har abada.
A wani bangaren kuma akwai Maleek, saurayin da ya tsani mata fiye da komai a rayuwarsa. Kyamar da ba shi da dalilinta, kyamar da ta mayar da rayuwarsa cikin duhu da kadaici. Duk da dukiyar da yake da ita, zuciyarsa na dauke da wani sirri mai firgitarwa.
Sai kuma Ameer, attajirin saurayi mai girman kai, mai tsananin son tsabta da kamshi, wanda yake ganin babu wanda ya isa ya tsaya masa. Rikici tsakaninsa da Maleek ya kai matakin da zai iya zubar da jini.
Me zai faru idan kaddara ta hada rayuwar Waira da wadannan samarin biyu?
Shin sirrin Garuk zai ci gaba da boyuwa?
Me yasa aka haramtawa Waira fita daga garinsu?
Wace alaka ce ke tsakanin busar sarewar tsafi, Garuk, da rayuwar Maleek?
A lokacin da soyayya, tsafi, iko, hassada, da kaddara suka hade wuri guda, za a bankado sirrikan da za su girgiza rayuwar kowa.
WANI GARI labari ne mai cike da tsafi, soyayya mai sarkakiya, rikicin iyali, sirrin sarauta, kaddara, da abubuwan da ba za ka taba tsammani ba.
Idan kana neman Hausa novel mai ban tsoro, mai cike da suspense, soyayya, al'adu, matsafa, sirri, da manyan jarumai masu kayatarwa, to WANI GARI shi ne labarin da ba za ka iya ajiyewa ba sai ka kai karshensa.