ENGLISH DESCRIPTION
FADILA was the only girl in the family, and from childhood she was deeply loved by AMAAN and AHAAD. Everyone surrounded her with care and affection, especially AHAAD who often prayed for a daughter just like her. After years of waiting, joy finally returned to the family when UMMU gave birth to beautiful twin girls, NAJWA and NAJMA.
Their naming ceremony became the talk of the town, filled with happiness and celebration. But behind that joy, fate was already preparing a painful storm. The tragic death of SHA’AWA’s parents in a devastating plane crash shook the entire city of Katsina. Before the family could recover from the grief, another heartbreaking tragedy struck again.
From that moment, love, pain, destiny and hidden secrets began to shape the lives of NAJWA and NAJMA. Though they looked exactly alike, their personalities were completely different. NAJMA grew up fearless, cheerful and trusting, while NAJWA became calm, quiet and full of patience. But a dangerous secret hidden within the family threatens to destroy everything they know.
AHAAD rose to become a respected military captain, admired for his courage and charm, yet his heart carried a mystery no one could understand. Love slowly turns into confusion, trust becomes betrayal, and the happiness built over the years begins to fall apart.
What will happen when long buried secrets are finally revealed?
What destiny awaits NAJWA and NAJMA?
Will love survive, or will tragedy tear their world apart forever?
RUHIN FANSA is an emotional Hausa romance novel filled with family drama, suspense, heartbreak, destiny, mystery and unforgettable twists that will keep readers addicted from beginning to end.
HAUSA DESCRIPTION
FADILA ita ce mace guda daya a gidan, kuma tun tana karama AMAAN da AHAAD suka zuba mata tsantsar so da kulawa tamkar sarauniya. Kowa a gidan ya mikawa FADILA zuciyarsa, har AHAAD yake addu’ar Allah ya ba shi ‘ya mace kamar ita. Bayan shekaru na jiran samun karin haihuwa, farin ciki ya sake mamaye gidan lokacin da UMMU ta haifi tagwaye masu tsananin kyau, NAJWA da NAJMA.
Tun daga ranar suna gidan ya rikide zuwa aljannar murna da soyayya. Amma cikin wannan farin cikin ne rayuwa ta fara juyawa zuwa bakin ciki da hawaye. Mutuwar iyayen SHA’AWA a hatsarin jirgin sama ta girgiza dukkan Katsina, kuma kafin iyalin su farfado daga wannan tashin hankali sai wata sabuwar masifa ta sake fadawa gidan.
Asiri, soyayya, kaddara da bakin cikin rayuwa suka fara cakudewa a rayuwar NAJMA da NAJWA. Duk da kasancewarsu tagwaye masu kama da juna, halayensu sun sha bamban. NAJMA yarinya ce mai rashin tsoro, fara’a da son mutane, yayin da NAJWA take da sanyin hali da hakuri. Amma akwai wani sirri mai nauyi da ke boye a cikin rayuwarsu wanda zai sauya komai.
AHAAD ya zama babban soja mai kwarjini da cike da jarumtaka, amma zuciyarsa tana boye wani abu mai hadari. Soyayya ta rikide zuwa rudani, aminci ya koma zargi, kuma farin cikin da aka gina cikin shekaru yana dab da rushewa.
Shin me zai faru idan sirrin da aka dade ana boyewa ya bayyana?
Wace irin kaddara ce ke jiran NAJMA da NAJWA?
Soyayya ce zata yi nasara ko kuma bakin cikin rayuwa zai raba zukata?
RUHIN FANSA wani sabon shirin Hausa novel ne mai cike da soyayya, family drama, rikici, tausayi, suspense, kaddara, sirrin iyali da tashin hankali wanda zai sa ka kasa daina karantawa tun daga farko har karshe.