Showing 1 words to 3000 words out of 328222 words

Chapter 1 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

Murfin Jallo Dan Uwa,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
1
1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



Hayaniya irin na babban gida shine ya tayar da mama daga barcin data dan samu ta
runtsa na safe ,bayan idar da zikirin safe data sabayi a duk safiya .
Wanan dabi,an kusan ya zama mata jiki akullum idan ta idar da sallah zata zauna
tayi zikiri har sai rana ya foto sosai kafin ta dan kwanta ta ba ido hakkinsa.
Daga inda take kwance din tana jin yadda yaran gidan nasu da manya ke kara,kaina
a tsakar gidan kusan hayaniyar babban gidan nasune ma ya tayar da ita a lokacin.
Salati tayi tana dagawa a kasa inda take kwance saman sallayanta ta dan jima a
zaune don gargadin likitoci dake fadin.
Idan ka tashi tsaye barci kada kayi saurin mikewa tsaye a lokacin don min a
daidai lokacin jinin dake kwaranya a zuciya bata gama sauka ba yana yuyuwa ka mike
hakan ya ja maka matsala a rayuwanka a cewarsu.
Ana son Sai ka dan bada yan mintuna a zaune kafin ka mike tsaye don kariya ga
lafiyan ka a lokacin wanan dokan da mama taji illanshi.
Baga yaro ba baga babba ba dokace da likitoci suka bayar don gujewa fitinan
lafiyan jikin bawa daka iya haifarwa mutum ciwarwutan zamanin nan .
Hakan yasa wanan boyar Allah ta rike wanan akidan ta dan bada lokaci a wajen
zaune daidai lokacin da aka turo kofan dakin nata tare da daga labulen dakin aka
shigo ciki da sallama muryan danta na ukkune yake sallaman tare da fadin ashema
baki tashi ba mama ?.
Daidai lokacin ta dago kai tana sauke mai kallo tare da fadin na tashi Habu
badai har rana tayi hakaba kuna shirin fita ?
Rana tayi mama yanzu kusan karfe takwas da rabi ake nema zuwa nayi muyi sallama
don yau balaguro zamuyi har wani kasan ba lalai bane mu dawo a yau ko gobe saidai
kun ganmu dai zance.
Kallon mamaki take binsa dashi tana fadin haba Habu wai sau nawa zan maka fadan
irin haka don Allah ?
Mutum zaiyi tafiya mai nisa irin haka bazai fada a gida ai masa addua ba ka
raina da dan adduan da muke binku dashi ko yaushe ke nan ?
Zaune yakai saman kujeran dake gefe ciki da kaya yayiwa kansa wajen zama a gefe
yana fadin mama muko muka san amfanin adduan ku akan mu don duk abinda muka dafa
muna ganin alheri a cikinsa.
Murmushi matar tayi tana fadin yanzu dai ina kuka dosa Habu ko kudun zaku kuma
yau dinma ?
a,a mama wajajen Camero muka dosa wajen wani taron gargajiya da za,ayi a can
kinsan aikin mu ya kumshi hakan sai munje don dauko rahoto.
Shine zamu dauko rahoto akai da zamu yadawa al,umma su gani ikon Allah yanzu
habu har camaro zaka hankalinka kuma a kwance ?
Batare daka sanar da mu ba sai yanzu ka shirya tafiya kazo kana fada min Habu ?
Wai meyasa kudai maza baku mayar da tafiya a bakin komai bane wai ?
Kako san nisan dake tsakanin zaria zuwa camero ? camero din nan da kake ji kawai
a baki tafiyace mai nisa fa daga nan .
Ya amsa da fadin kuma tafiyan mota zamuyi mama saboda kayan aikin mu dole mubi
mota zuwa wajen taron wanan yasa zamu tashi tun yau ai a dai muna addua muje lafiya
mu dawo lafiya.
Insha Allahu lafiya zakuje ku dawo lafiya Abubakar alherin dake cikinsa ubangiji
Allah ya sadaku dashi sherin dake cikin tafiyan kuma Allah ya nisantashi daku
alfarman Annabi da alkur,ani ya amsa da amin cikin jin dadin adduan mahaifiyar tasu
a gareshi.
Sallamu Alaikum ga nakiyar baby muryan wata dattijuwa dauke da kwala a kai data
shigo babban gidan Alh talle din ta tsaya daga kofane ya karade gaba daya gidan.
Daga can dakin mama din inda take bankwana da danta taji muryan wanan matar
cikin mamaki take sake zancen da sukeyi da dan nata.
Cikin mamaki take fadin nakiya kuma da safen nan ?
Har yakai a fara tallan nakiya gida gida haka me mutane ke nema da bindan kudine
wai nakiya dai a sanina sai bukin aure ake nakiya don ango.
Murmushi Abubakar yayi yana fadin barin inje mama kada in makara abokan
tafiyana suna kirana tun dazun.
Nan uwar ta dago tana fadin kaje kuyi sallama dasu hjy kafin ka tafi bana son
irin korafin su na baka sallamesu ba din nan.
Insha Allahu ya fada yana mikewa tsaye barin dubasu in dawo mama ya fada yana
mai barin dakin cikin kuzarinshi irin ta namiji mai jin lokacinsa.
Dakin hjy babba ya nufa ya gaida ita tare da fada fada mata inda suka dosa a
ranan ba yabo ba fallasa tayi mai Allah ya kiyayye hanya.
Ya fito yana kokarin shiga wajen hjy Nana ya hangosu gaban wanan matan dake
faman kwada sallama suna leken wani abu a cikin kwalan da matar ta shigo dashi.
Hakan yasa ya doshi wajen saura kiris ya karasa yaga yara da manya sun watse wasu
harda faduwa kasa don tsoro ga ihun da sukeyi suna neman inda zasu shiga saboda
firgici .
Wanan ihun ya dakatar dashi yaja ya tsaya yana binsu da kallo fuska daure kafin
ya mayar da hankalinshi wajen matar da sai murmushi take a fuskanta.
Lafiya boyar Allah tace nakiyar babyce na kawo masu gashi kuma sun watse sun
barni dashi .
Kallon matar yayi cikin mamaki murmushin yagani a fuskanta yasa ya karasa wajen
yana kokarin kallon kwallan dake gabata bude.
Ido ya runtse lokaci guda don wani katon maciji kalan da sai a cikin film yake
ganinsa.
Ya nade a waje daya ya cika kwallan har baki sai kansa daya dora a saman jikinshi
yana kiu kiu da idanuwansa dake bude.
ALLAHU LAH ILLAHA ILLAH ANTA SUBBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZULLUMIN ya ambata a
fili .
Muryan matar yaji tana fadin kada kaji tsoro kai namijine kuma sadauki ba asan
maza da razana ba sadauki.
Daga can bayanshi yaji muryan dayan kanwarsa tana fadin yaya Habu kada kaje
kusa don Allah macijene a cikin kwallan nan babba.
Jin sunansa da aka ambata yasa matar fadin Garba sadauki garba gagare kai
sadaukine ko a fagen fama kafiran makka sun buga sun barka sarki rikon amana mai
alkawari ya cika har bayan rai,,,,,,,,,,
Dubu biyu ya zaro a cikin aljihunsa ya mikawa matar takai gwiwa biyu tana zabga
mashi addua da neman tsarin ubangiji gaba da bayanshi.
Ya juya da niyar komawa dakin muryan hjy Nana yaji tana fadin boyar Allah aida
kin fada kwai a miko maki abinda Allah ya hore ki tafi .
Yayin da matar tacigaba da fadin da yardan Allah kayi gaba saudaki sara da
sassaka bai taba cima a rayuwa insha Allahu sai dai makiya su buga su barka.
Mama data samu ta mike don ganin abinda ke faruwa a wajen taji yadda matar kewa
danta Abubakar addu,a ta fahinci kudine ya bata yasa ta dauki dari biyu ta fita ta
mikawa matar nan ta dasa sabon addua kuma tanawa mama jam,i ga duk zurianta.
Ta dauki kwallan ta tafi don taga sauran iyalin gidan basu da niyar fitowa balle
su sallameta saida sukaji fitanta suka fito suna mayar da ba,asin zancen a
tsakaninsu kowa na fadan abinda yagani a cikin kwallan hankali tashe.
Mama dai bata gani ba amma ta mikawa matar sadaka don tasan wanan matar banza
ba zai fito da ita gidanta haka basai neman rufin asiri da taga wanan hanyarce mai
sauki a gareta.
Zancen mai nakiyar ya hana su mayar da hankalinsu ga Habu da zaiyi tafiya don da
tsegumin tafiyan shi za,a fara sai Allah ya fabeshi a ranan dan shigowan wanan
matar mai yawo da macijin maisa a cikin kwala tana cewa ga Nakiyar baby.
Idan kuma tasan sunan wani gida a gidan zata ambaci sunan maishi tace ga nakiyar
wani sai wanan abin tashin hankalin da mamaki ya tsaya masu a rai har mahaifiyarshi
ta fito rakiyarshi da iya kofa ta tsaya tanawa danta fatan Narsara da Allah ya
tsare ya kare wamda sai lokacin hankalin hjy babba ya dawo garesu.
Daga kofanta take tambayan yau Habu kuma ina za a haka tunda safe ni yazo muna
gaisawa hankalina yana gun wanan bakar matar data tayar muna da hankali da safen
nan.
Daga kofa mama din take bata amsa da camero suka nufa lokaci guda matan da yara
dake wajen suka amsa da fadin camero kuma ?
Wasu na Allah ya tsare wasu kuma sunyi gun suna zancen zuci inda sabo ta saba da
hakan zaman gidan yawane duk yadda kayi sai wani yaga bakai masa daidai ba irin
wanan zaman.
Ya fito daga cikin gidan yana kallon agogon hannunsa saboda ymshi kansa yasan da
ya makara saidai dole su jirashi sai yaje wajen aiki inda zasu hadu.
Kamar daga sama yayi ido biyu da wanan matar ta sauke kwallan macijinta sai faman
murmushi take zabga mai a fuskanta kai ya kawar da sauri yana barin kallonta.
Habu bakari don ka na tsaya nan duk da dai shigan tsugula zan ma tunda na kula
sauri kakeyi ka kula da addua don kai din kana tare da tsarin Allah ga kuma tarin
mahassada a tare dakai.
Nagode mama ya fada yana kokarin wuce ya sake jin muryanta tana fadin ka kula
sosai don alherin ka da nasara yana inda ka dosa .
Kudi dai wanan matar keso gareshi ya nasa hakan a zuciyarshi ya sake cusa hannu
a aljihu yana dauko dubu daya ya mika mata.
Murmushi tayi tana fadin wanda kabani dakai da mahaifiyarka nagode maku Sarkin
da akaiwa ya sani.
Naso magana da mahaifiyar ka saidai gidan ku gidan yawane dana fada mata wani
magana amma ba laifi idan tana son ji ko kai ina can gidan hjy indo mai kosai a nan
na sauka.
Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin yana aje mata dubu dayan da taki karba a
hannunta saman kwallan yasa kai ya tafi don ya dauka zancen shirme take masa a
lokacin don kawai ta yaudareshi yasan halin mutanen yau da yaudara.

[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f


MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Tafiyace ta mota da zai dauki dogon zango haka suka fara tafiya tun suna dan hira a
tsakaninsu har abin yakai da anyi shiru kowa na tunane a kansan zuciyanshi.
Dosan mabila da sukayine yasa su fara bayana mamakinsu a fili kowa na fadan
albarkacin bakinsa ga albarkan kasan yankin mabila din.
Abin sha,awane da daukan hankali ga bakon zuwa wajen harma wanda ya saba sai yabi
dabbobinsu da kallon shawa yadda suke daban da wanda aka saba gani.
Lokacin da suka zo wajen wanan hawan kusan kowansu hannushi a gaba yake yana
ganin kamar ba zasu iya hawan nan ba don yadda sukaga wajen.
Sai gashi cikin yardan ubangiji sun hau lafiya sun gangara kuma lafiya a sannu
suka fara barin cikin nahiyar kasan Najeriya zuwa cikin kasan camero dake da iyaka
da Nageria.
Abin sha,awa don basai ka tambaya ba alakansu da addinin musulunci don har yan
wani addinin shigarsu shigen na musulmaine su a kasan sukeyi.
Tafiya dai tayi tafiya don shi driver yasan yankin da za ayi wanan taron wanan
yasa basu damu da yada zango ba sai tsatsaya ko ina ba.
Saidai idan lokacin sallah ya riskesu sai kuma shan man a hanya sukama hanya
amma sam basu tsaya kwana a hanya basu kamar yadda wasu da yawa suka yada zango.
Hakan yasa sukai wa wanan yankin shigar safiya duk da alokacin wurin sha dayan
ranane a lokacin duk wani mai lalura ya fito a lokacin.
Sai wanda ke gida baida abinyi sannu a hankali yake bin garin da kallo daga
bayan motan yayin da driver ke aikin kutsawa acikin garin zuwa babban filin da
za,ayi taron gwajin na gargajiyan shekara.
Suna wanan al,adanne bayan ko wani shekara goma idan ya shige in rayuwa ya
kewayo ake haduwa wajen wanan shagalin nuna amfanin gona da sauran al,adun
gargajiya.
Abaya kasan Nageria tana irin bukukuwan nan na nuna amfanin gona da sauran
al,adun gargajiya wanda yake kawo dankon zumunci da habbaka sana,an mutane da
cigaban kasuwanci harma da zumunci a tsakanin yan garuruwa na nisa dana kusa.
Sai a yanzune da abubuwan kasan suka tabarbare wanan al,adan ya mutu mutus a
arewancin Nageriaa sai dan abinda ba,a rasa ba dai kawai da akeyi yanzu.
Sai dai al,adan kamun kifi da wasan ruwa da sauran al,adun har yau har gobe
mutanen kasan kebbi a garin Argungu kabawan asali basu daina hakan basu a wajensu.
Don suna raya garinsu basu bar al,adansu da suka gada tun kakanin farko ba da
kakani baya, don manyansu sun rike da wanan abin sosai tare da kawo cigaban nahiyar
tasu ta Argungu din har gobe.
Wanan kadai za ace an saurayi a yanzu cikin arewancin Najeriya da har wasu kashe
duniya suke zuwa kallon irin al,adunmu na hausawa tare da fasahan malam bahaushe
dake tafiya da al,adanmu na Nageria.
Bayan shishi din a gaskiya yana da wuya ace an saura wanan habbaka al,adan da
sauran kasashen africa dake kewayen nageria irin su Niger, ghana, camero kwatano da
benin da sauransu su basu yarda sun bar al,adunsu ba kamar mu.
Zama ya gyara daga bayan motan yana sauraren Sahabi mai daukan photonsu dake
wanan sharfin akan nahiyar ta arewacin Nageria da yanzu abubuwa suke ta kara
lalacewa a kasan saboda sanyi da rashin sanin ciwon kan malam bahaushe a yanzu.
Ai baka sani ba malam Sahabi zance dakai wanan abin tun lokacin da aka ragewa
gidan Redio Kaduna karfi da power abubuwan da dama duk suka shiga tabarbaremuna kai
in maka na mahaukaci kamar anyi wanan abin da manuface zance dakai.
Don wallahi ba karamin koma baya haka ya mayar da Arewa baya akayi ba da hakan
hakan ya taba kima da mutuncin arewa sosai a kasan nan.
Dama sune masu haskawa suna yadawa amma tunda wanan ya faru sai sannu a hankali
kaga abubuwan sun fara ci baya.
Hakane kwarai malam ibrahim maganan ka dutse wallahi wanan abin ya taba arewa
sosai don kashe wanan gidan redio da sauran waje irin masakan kaduna su gidan kada
da wajen fata wanan abin ya kawo muna cibaya sosai a arewa yanzu don da suna raye
matasa zasu samu aikin yi a kasa.
Salatin Abubakar ne daga bayan motan ya dawo da hankalin driver ya maida
hankalinshi sosai ga a saman dan wani tsukaken haya da suka biyo inda wasu yan mata
ke gara amalanken shanu.
Wanda saura kiris su gwauro da juna Allah dai ya gyara ya takaita masu wahala
dole sukaja burki suka tsaya suna maida numfashi.
Malam ibrahim ne ya soma fitowa daga cikin motar yana fadin kaga min almuran
yarinya kawai Allah ya kawomu lafiya saida mukaga mun shigo gari muna murna zaki ja
muna tsiya.
Allah dai ya gyara malam ibrahim barta ta tafi kawai itama kauyancine bata sanda
mota a bayanta ba sun dauka sai masu kafa kawai suke tafe a hanyar.
A daidai lokacin da hakan ya faru uwa mai kulawa da yawan addu,a ga yayanta
takanji wani yanayi na daban aduk lokacin da wani mumunan abu zai samu danta.
Irin wanan yanayin ne ya ziyarci mama a lokacin sai ta shiga maimaita innalillahi
a kasan zuciyanta da sauran addu,oin da zasu aikawa yayan ta dake cikin duniya dama
wa yanda ke kusa da ita kariya.
Kasa hankalinta gida biyu tayi tana tunanen Abubakar ko Jafar mai yawan tafiye
tafiye don shi ko yaushe a hanya yake dan kasuwane bai tsaya ga aikin gwaunati ba
ya aje ya soma kasuwanci da yake ganin yafi mai aikin gwaunati a rayuwansa.
Alhamdullahi kuma an samu cigaba sosai a wanan harkan da yanzu har yakai
lamarinsa ya fara tsone idon makiya.
Su ukkune diyanta maza da Allah ya bata da marigayi din sai mata ukku shidda ke
nan matan biyu kananane koda mahaifisu ya kwanta dama autar ta ko yayeta batayi ba
a lokacin.
Wanan yanayin daya bakunceta yasa ta fita da sauri ta yafa hijjab dinta dauke da
kwalin sugar a hannunta wanda ta saya a cikin hijjab dinta.
Kofan gida ta nufa akwai tsangaya gaba dasu kadan can takai a rabawa yara sadaka
shi kuma malam ta bashi naira dubu sadaka.
Tun kan tayi nisa take jin an fara raba sadakan sugar tana tafe da dan saurin
don ba fita sukeyi haka ba don wai mijinsu ya rasu suna cikin gida ko yaushe zakice
mijin nasu yana rayene.
Don komai da akeyi gidan ba a fasa ba don ko wani daki na gidan yayansu suna
rike da uwayensu da kannensu da wa yanda basuyi aure ba.
Rayuwan gidan marigayi Alh Sanda rayuwace ta ba yabo ba fallasa ga iyalinsa
daya bari duniya don ko yabar masu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login