Showing 210001 words to 213000 words out of 268471 words
cause he don't get why Mami is making issues
complicated, Aunty Maryam tace "Yau saura kwana ashirin da daya cif cif, ita Nihad
din ta sani??" Ya daga kai ya kalleta ya girgiza kai yace "Ban gaya mata ba
gaskiya" Aunty Maryam tace "Aa ya kamata ka gaya mata, tun farko ma ya kamata ace
ka sanar mata kana da yarinya da kayi ma alkawarin aure kaga zata san da maganar a
kasa ba yanzu kawai taji sa kamar daga sama ba" Ya sauke ajiyar zuciya yace "Ko za
ki mata maganan da kanki Aunty?" Aunty Maryam ta rike haɓa tace "Ehh lallai, wato
ni ce ma zan gaya mata za a mata kishiya salon dai baiwar Allahn tayi ta kallona da
shi, kai dai zaka sameta kasan yanda zaka gaya mata cikin lallami, akan dai taji a
wani waje baka gaya mata ba, ba don Mami baxata fahimce mu ba da auren ma dagawa
kawai aka yi sai zuwa nan da wata uku tunda ai an kai kudi, ita kuma kaga bazata yi
tunanin don ba a sonta bane zaka sake aure, amma kuma naga bata da matsala, yarinya
ce, kaga bazata wani damu da kishi ba sai nan gaba" Murmushi kawai Khalil yayi bai
dai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Allah kuwa bazata daga hankalinta ba yanda
babban mace zata yi, she is too young for that" Khalil yace "Toh Aunty nan gidan
zata yi ta zama kenan?" Aunty Maryam tace "Toh nayi ma Mami magana ka dauketa yau
ku tafi kawai tace ai duk rana daya za su shiga gidan da Nadeeyah, kaga sai nan da
sati uku kenan, to ya zan mata??" Da mamaki Khalil ya dinga kallonta, Aunty Maryam
tace "Kasan idan Mami ta ce ga yanda take son abu to fa kawai ayi hakuri a bi ta da
yanda take son din, that's just it" Aunty Maryam tace "Ni dai zaka kai ni airport
zuwa la'asar, kar kayi nisa" Yace "Toh yanzu idan kika tafi sai yaushe za ki dawo
Aunty?" Aunty Maryam tace "2 days before the wedding in sha Allah" Yace "Toh Allah
ya kai mu" Aunty Maryam tace "Ameen"
Mami na zaune parlonta da Aunty Maryam da dake rufe trolly dinta don la'asar din
ya kusa Hajiya Amina ta shigo parlon, Ta zauna da fara'a, bayan sun gaisa tace "Ina
amaryar, shiru shiru ni dai ban ganta ba tun da suka iso jiya, shine nace to ni
bari in biyota" Mami tace "Ayya, ai ko nace Mimi ta kai ta ta gaisheku ke da Aunty
Hassana tun dazu, ban san bata kai ta ba" Hajiya Amina tace "Allah sarki, ai ko
bata kai ta ba, ita ma Aunty Hassanar dazu ta dawo ai" Aunty Maryam ta dago kai jin
sai yau Aunty Hassana ta dawo daga Kanon, Mami tace "Allah sarki" Hajiya Amina tace
"Ya muka ji da shirye shiryen biki kuma?" Mami tace "Alhamdulillah" Hajiya Amina ta
mike tace "Toh Allah ya kai mu lokaci, dama dai cewa nayi bari in leko amarya" daga
haka ta fita daga parlon, Aunty Maryam ta taɓe baki ta ci gaba da abinda take tana
girgiza kai tace "Munafurcinsu dai zai kare masu idan kin bibiya Hassanar ce ta
turo ta, in sha Allahu sai mun ji su kaca kaca a rana nan ba da dadewa ba kuwa"
Mami dai ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, ta dau wayarta ta shiga kiran
Mimi, Mimi na dagawa Mami tace "Dama baki kai ta bangaren Amina da Hassana ta
gaishesu ba kamar yanda nace maki Mimi?" Mimi ta zaro ido tace "Ohh da na shiga
dakin dazu na tarar bacci take, bari in duba yanxu Mami" Mami ta katse wayarta,
Aunty Maryam tace "Shi kuma Khalil daga cewa ba jimawa zai yi ba ya bar ni shanye a
nan gashi har lokaci ya kusa..." Mami tace "Ba ga driver ba sai ya kai ki mana,
dole sai shi Khalil din" Aunty Maryam dai bata ce komai ba.
Mimi na shiga dakinta ta tarar da Nihad kwance amma ba bacci take ba, Mimi tace "Ki
dau gyalenki mu je ku gaisa da stepmom dita Neehad" Nihad ta mike zaune, gaba daya
bata da walwala tun dazu, Mimi na kallonta ta mike ta dau Mayafinta sannan Mimi ta
fita dakin ta bi ta a baya, babu wani banbanci bangaren Mami da na Hajiya Amina sai
dai Hajiya Amina parlor daya ne babba, tun da suka shigo Hajiya Amina ke kallon
Nihad don ita fa duk zaman Nihad a gidan ba wai ta san ta bane, Nihad ta zauna kasa
ta gaisheta da ladabi, Hajiya Amina ta amsa faram faram tana mata sannu da zuwa,
Nihad dai bata dago kanta ba, bayan few minutes Mimi tace "Aunty Hassana ta dawo ko
Mum?" Hajiya Amina tace "Bata dade ma da fita nan ba, ku je tana can bangarenta"
Mimi ta mike tace "Toh bari mu je ta gaisheta" Hajiya Amina tace "Toh madallah"
Nihad ta mike suka fita daga parlon, da sauri Hajiya Amina ta dau waya tayi dialing
din number Aunty Hassana ta sanar mata ga su Mimi za su taho bangaren nata... Mimi
na isa ta bude kofar parlorn a hankali, ɗan matsakaicin parlor ne shi ma dai ya
hadu iya haduwa, amma bai kai na su Mami girma ba, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin
Aliyu zaune parlon saman kujera daga kusa da bakin kofar parlon yana sanye da 3
quarter da polo, suna hada ido ta sunkuyar da kai, Mimi na ganinsa tace "Hi" Daga
haka ta karasa can cikin parlon zuwa kofar bedroom din Aunty Hassana tayi sallama,
Aunty Hassana tace "Waye?" Mimi tace "Mu ne, an zo za a gaisheki ne Aunty" Aunty
Hassana tace "Ina zuwa" Dawowa cikin parlon tayi tana kallon Nihad da ta rakube
waje daya a cikin parlon, duk ta ki sakin jiki, lokaci lokaci Aliyu dake danna waya
yake mata kallon kasa kasa, Sai ga Aunty Hassana ta fito tana kallon Mimi tace "Sai
kin wani rakota kamar za a cinyeta?" Mimi tace "Aa ai bata san hanyar ba" Aunty
Hassana tace "Toh ai yanzu ta ga hanyar ko?" Mimi tayi shiru bata ce mata komai ba,
can ta mike, sosai gaban Nihad ya fadi, ta dinga kallonta har ta nufi kofa ta fita,
Aunty Hassana tana kallon Nihad tace "Sannu ko, bari a kawo maki ruwa" Daga haka ta
nufi kofar parlon ta fita, Nihad da gabanta ke faduwa sosai ta kalli Aliyu taga
still wani irin kallo yake mata, mikewa tayi da niyyar ficewa daga parlon, taga ya
mike ya kulle kofar ya nufo ta yace "Munafuka, macuciya er cin amana.... Dama ashe
duk yaudarata kika dinga yi a baya ban sani ba? Ki rasa wanda zaki aura a karshe
sai makiyi na? And you are trying to make it look as if baki san hakan ba?" Nihad
dake kallonsa zuciyarta na bugawa tace "Kai ban kiraka da munafuki ba sai nice zaka
ce ma munafaka? Naga ai ban taɓa amfani da sunan mahaifin wasu a matsayin mahaifina
ba, i never lied to you about who my dad is, hasalima har gidanmu na kai....." Bata
kai karshe ba ya sauke mata mari, ta dafe kuncinta da mamaki tana kallonsa babu ko
kiftawa, yace "Sai kinyi da kin sanin sanina a rayuwarki, kuma duk sai na fanshe
bata min lokaci da kika yi ta hanyar da baki taɓa zato ba wallahi, i am promising u
this" Dai dai nan aka bude kofar parlon Aunty Hassana ta shigo rike da tray me
dauke da kwalin lemo da glass cup, tana kallon Aliyu da sauri ta ajiye tray din
hannunta tace "Me ke faruwa Daddy?" Kofa Nihad ta nufa da sauri hawaye na sauka
idonta, Aunty Hassana ta gwalo ido ganin haka ta bi ta tana kiranta amma tuni Nihad
tayi nisa, Aunty Hassana ta dawo parlon cike da masifa rai bace tace "Kai wani irin
shashasha ne mara lissafi Daddy? Kai me yasa baka jin magana ne? Nace maka a sannu
za a bi komai amma sai da ka yi mata magana? Toh yanzu ina kake son in bi ta in
bata lemon nan fisabilillahi? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, baka kyauta min
ba Daddy" Aliyu yace "Ke kika ga haka mum" Daga haka ya fice daga parlon kamar zai
tashi sama, Hankali tashe Aunty Hassana ta kira wata long time frnd dinta Maimuna
da ta hadu da ita zuwansu kano ta shige daki da sauri. Direct Nihad dakin Mimi ta
koma ta zauna gefen gado hawaye na sauka idonta sai kuma ta fashe da kuka sosai, ko
minti biyar bata yi da shigowa ba aka bude kofar dakin, Khalil ya shigo, da mamaki
yake kallonta ganin kukan da take, sai kuma ya nufeta da sauri yana kallonta yace
"What happened?" Hade kai tayi da gwiwa tana kuka sosai, ya zauna gefenta ya dagota
hankali tashe yace "Talk to me plss an maki wani abu ne?" Tana shesshekan kuka tace
"Aliyu slapped me" Khalil ya dinga kallonta ba ko kiftawa, as if counting his words
yace "Aliyu slapped you?" Nihad ta gyada kai cikin rawan murya tace "Mimi ta kai ni
mu gaisa da yan gidan shine muka hadu da shi a parlon warce muka je kano tare da
ita" Khalil bai jira ya gama sauraronta ba ya mike ya fice daga dakin kamar zai
tashi sama, direct dakin Aliyu ya nufa that is almost 5 minutes walk daga dakinsu
Mimi, a hanya ya ga wani vase din flower ya dauka yana ci gaba da tafiya kamar zai
tashi sama, bai kuma hadu da kowa ba har ya isa part din Aliyu, dai dai nan shi
kuma ya fito daga dakin sa babu wata wata khalil ya fasa vase din jikin bango ya
caka masa da karfi a kafarsa, Aliyu yayi wani kara ya dafe bango da sauri yana zaro
ido, kan kace me sai ga jini kamar an bude pampo, hakan bai sa Khalil ya fasa
shakesa ba yana huci yace "Stay away from my wife, idan kuwa ba haka ba, ni ne doom
dinka, i promise you" Yana gama gaya masa haka ya turasa da karfi ya juya ya bar
wajen kamar wani soja.... Mimi ta fita da trolly din Aunty Maryam zuwa mota ta dawo
kenan ta hadu da khalil tace "Yayanmu Aunty Maryam tana ta nemanka fa" Bai ce mata
komai ba ya fice daga parlon, Mimi ta tafi ta gaya ma Aunty Maryam yana parking
space yana jiranta..... Khalil na kai Aunty Maryam Airport ya dawo sai bai shiga
gidan ba, yayi parking kofar gida yayi dialing number Mimi, Mimi na dagawa yace
"Are you with me?" Tace "Yeah ina ji" Yace "I want you to come out now with Nihad
but kar ki gaya ma Mami, zata siya abu ne a Supermarket" Mimi tace "Alright" Daga
haka ta katse wayar, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta fito da Nihad, tun daga nesa
yake kallonsu har suka karaso, yana kallon Mimi yace "Thank you" cike da damuwa
Mimi tace "Yayanmu they just rushed Aliyu to the hospital now, i think ko kwalba ne
ya fadi a kafarsa i don't just understand, he is bleeding seriously" Khalil yace
"Ohh really" Bai jira me zata ce ba ya bude gefensa yana kallon Nihad yace "Shiga
mu je ki siyo abun" Nihad ta shiga motar, ya kalli Mimi yace "Za mu dawo yanzu but
don't say anything to Mami" Tace "Ohk" Yace "Noor fa?" Mimi tace "Noor na gidansu
Nadeeyah" Yace "Ohk" Daga haka ta kulle motar ta koma cikin gida shi kuma ya bar
layin, sai a sannan Nihad ta kallesa da damuwa tace "Me yasa zaka yi injure dinsa
haka?" Yace "Saboda ya taɓa Nihad" Tayi shiru tana kallonsa, can ya girgiza kai
yace "Dama i have been targeting him for so long, so this is just an opportunity
that comes but once" Nihad da hankalinta ya tashi tace "Mimi said he is bleeding
heavily" Khalil yace "Serves him right" ta daga kai da sauri ta kallesa ganin
gidansa ya kawota, deep down her she felt happy saboda bata jin dadin zaman gidan
nan nasu, bata son gidan har cikin ranta, ya sauka ya bude gate din ya shiga da
motar ciki sannan yayi parking, da kansa ya sauka ya bude mata side din da take, ta
sauke idonta sannan ta sauka daga motar, yana rike da hannunta suka shiga cikin
gidan, sama ya tafi da ita, yana kallonta yace "Which room will u prefer amongst
the room?" Nihad dai sai kallon dakunan take bata ce komai ba, yayi hugging dinta a
hankali ta baya yace "Ko in zabar maki?" Still dai tayi shiru feeling him at her
back, a hankali ta fara kokarin janye jikinta ya ki saketa dragging her closer to
him, murya can kasa yace "Na zabar maki this one" Ta kalli dakin da yake nuna mata
wanda yake kusa kusa da bangarensa na master Bedroom, rubbing her flat tummy yace
"Kina so?" Kai kawai ta gyada masa, wasu abubuwa ya dinga yi mata ita dai bata
hanasa ba sai kafafuwan ta ne kawai suka kasa ci gaba da daukanta, he could feel
how fast her heart is beating, he noticed jikinta ba shi da wuyar reacting to
stimulation, bata ankara ba sai ganinsu a bedroom dinsa tayi....
A hankali Khalil yayi kissing din goshinta yace "Wake up, it's almost Magrib...."
Nihad ta bude Idonta, ya dagota zaune yana kallonta, yana son sanar mata maganar da
Aunty Maryam tace ya gaya mata amma ya kasa don bai ma san ta inda zai fara ba,
Yayi kasa da murya yace "Za mu tafi can gida yanzu" Sosai gabanta ya fadi jin
abinda yace mata, ta kasa ce masa komai. Har suka sauka downstairs Nihad ji take
kamar ta fashe da kuka, ya dau wayarsa da ya ajiye a parlon, nan ya ga missed calls
din Janar har uku, sai na Mami kusan goma, shi gaba daya ya ma mance da wani abu da
ya aikata sai yanzu da yaga kiransu, ya mayar da wayar aljihunsa yana rike da
hannun Nihad suka fita daga gidan. Sai da suka isa gida Khalil yayi parking a layin
yana kallon Nihad, kamo hannunta yayi a hankali, gathering all courage yace "Kin
san kafin Abbanki ya hadani aure da ke ina da budurwata warce har da akwai maganar
aure tsakanina da ita right?" Nihad ta daga kai tana kallonsa kamar bata fahimce
abinda yake nufi ba, Ya lumshe ido ya bude amma ganin irin kallon da take masa
kawai ya fasa ci gaba ya ja motar yana driving din a hankali, ana bude masa gate
yayi parking a parking space, Nihad bata sake second daya a motar ba bayan ya bude
lock din ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan, ya sauke ajiyar
zuciya ya jinginar da kansa jikin kujeran motar. Sai da Khalil yayi sallah sannan
ya shiga gidan yana ciro wayarsa dake ring a aljihu ganin Abbansa ne ya daga, Janar
na gama maganar da zai masa ya katse wayar, Khalil ya nufi bangaren Aunty Hassana
kamar yanda Janar din ya umarcesa yana bude kofar parlon ya ga Janar a tsaye, ga
Aliyu zaune a kasa an nannade masa kafa da uban bandage wanda har yayi stain da
jini, sai zufan azaba yake, Aunty Hassana na zaune parlon sai kallon kafar Aliyu
take ta kankance ido zuciyarta na tafarfasa, Ga Mami a tsaye duk jikinta yayi
sanyi, ko magana bata yi, Hajiya Amina ma na dakin sai girgiza kai take cike da
alhini, Janar ya juya yana kallon Khalil cikin daga murya yace "I need an
explanation to this Ibrahim" Khalil yayi shiru bai ce komai ba, Janar yayi masa
tsawa yace "Magana nake maka" Khalil ya gyara tsayuwarsa jikin kofar yace
"Tsautsayi ne, amma ba da gangan bane" Janar na masa wani kallo yace "Tsautsayi??
Shaye shaye ka fara da zaka kira hakan da tsautsayi? Where u out of ur mind" Khalil
dai yayi shiru, can a hankali yace "Kayi hakuri" Janar ya hau zaga parlon fuskarsa
a murtuke, Can ya juya ya kalli Khalil yace "Sai ka shirya gobe ka tafi Germany ka
hadu da business partners dina na can" Aunty Hassana ta daga kai da sauri tana
kallon Janar baki bude, shi kansa Aliyu kallonsa yayi da sauri, Khalil yace "Ohk"
Daga haka ya juya ya fita daga parlon, Mami ta kasa dago kai don bata yi expecting
jin abinda Janar ya fada ba, Aunty Hassana ta kasa daurewa cikin ɓacin rai tace
"Yaya kasan kuwa illar da yayi ma kafarsa? Har fa ƙashinsa sai da ya tsage ya
dagargaje" Janar ya kalleta yace "Sai a fita da shi waje a sake duba kafar...."
Aunty Hassana na huci tace "Iya abinda zaka gaya ma ɗan ka kenan bayan illata min
ɗa na da yayi?? Amma yaya ka bani mamaki, wallahi ka ban mamaki, iya matakin da
zaka dauka kenan a kan wannan mugun raunin da Khalil ya ji masa??" Janar ya tsaya
kallonta bai dai ce komai ba, tana girgiza kai tace "Toh wallahi baxan yarda ba,
idan na yarda shegiya uwata da ubana suka haifeni, kafin in dau mataki dama sai na
fara kiran duk family sun san abinda ake ciki, duk sai na bi na tura masu video din
kafar Aliyu, Khalil ya nakasa min ɗa amma kai ta business dinka ma kake a Germany
ko?? To wllh bazan yarda ba samm, sai inda karfina ya kare a wannan abinda Khalil
yayi ma ɗa na" Janar yace "Ni kike gaya ma maganganun nan Hassana?" A fusace tace
"Na fada, ai ɗa bai fi ɗa ba, shekaru kusan ashirin baya haka nan yayi masa rauni a
baya har yau taɓon na nan a bayansa, a wancan lokacin ma babu wani mataki da ka
dauka banda asibiti da ka kai Aliyu, kawai ka dauki son duniya son jaraba ka daura
ma yaro yana ta abinda ya ga dama ya zama terror har da su sace sace a lamarinsa,
ohk don ba ubanmu daya ba shine zaka dinga fifita ɗan ka a kan ɗa na?" Janar ya
gyada kai yace "Ki sameni parlona Hassana" Daga haka ya fice daga parlon nata,
Aunty Hassana ta dinga bambami tana zage zage, babu abinda ta mance bata gaya ma
Mami da tayi shiru tana kallonta, daga karshe ta fice daga parlon nata ta bi bayan
Janar tana huci, dama ta saba fesa masu rashin kirkinta kuma ta zauna lafiya a
gidan, babu yanda har shi Janar din ya iya da ita, ita abinda ya kona mata rai
Germany da Aliyun bazai je ba sai Khalil, shine babban baƙin cikinta a yanzu, tana
isa parlon Janar ta ki zama tace "Ina jin ka" Bai ce mata komai ba banda zaga
parlon nasa da yake, bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace "Ki tattara
komai naki ki bar min gidana yau ba sai gobe ba Hassana" Buda baki tayi tana
kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, can tace "In bar maka gidanka kace?" Yace "Ehh
ba sai gobe ba, dama da na duba wasu mugayen halayyenki a baya da yanda kika hadani
da mahaifiyata har ta