Showing 111001 words to 114000 words out of 268471 words

Chapter 38 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

firgitar da tayi, Nihad ta kasa
karasawa cikin dakin ta makale jikin kofa ganin yanda kamannin Husnah ya canza, ita
tsoronta ma take ji yanzu, shi kam ya karasa can cikin dakin har gun gadon ya kalli
su Naf calmly yace "Sannunku" Siyama kawar Naf tana Murmushi ta tashi daga saman
kujeran da take zaune ta ajiye masa tana kallonsa keenly, cikin taushin murya tace
"Yauwa sannu da zuwa, have a seat pls" Ya dan kalleta yace "Nagode kiyi zamanki"
Kallon siyamar kawai Nihad take babu yabo babu fallasa, ai tun da Husnah ta kalli
khalil sau daya bata sake yarda ta kallesa ba sai mutsu mutsu take yi a inda take
zaune kamar warce cinnaka ke cizo, Naf, Zully, da su siyama sai kallon khalil kawai
suke, ya dafa gadon da Husnah ke kai yana kallonta da kyau yayi kasa da murya as if
talking to him self yace "How are you feeling?" Naf ta kalli Zully da sauri, Husnah
dai kai kawai ta gyada ba bakin magana, ko kadan Nihad bata ji abinda yace ba, Yana
gyada kai yace "Quickest recovery dear!! And u are always welcome to our home you
Slattern!!" Yana gama fadin haka ya juya ya bar wajen duk suka bi sa da kallo,
Zully da Naf sai kallon juna suke da wani expression, Husnah dai bata dago kai ba,
Yana isa bakin kofa ya amshi fruits din hannun Nihad ya ajiye masu nan bakin kofar
a saman wani table, ya juya ya kullo masu ward din, har suka shiga mota Nihad
bata iya ta ce komai ba kamar yanda shi ma babu abinda yace, she still can't
believe Husnah ce ta koma haka.... Tana ganin ya dau hanyar gidansu ta daga kai ta
kallesa, a kofar gida yayi parking ta sauka ta shiga gidan ba tare da ta jira sa
ba, tana shiga parlor ta kalli Nihal dake zaune parlor tana welcoming dinta da
fara'a, Nihad bata wani saurareta ba tace "Umma fa?" Nihal tace "Bata nan" Nihal ta
taso tana kallonta tace "Kin ga yanda kika yi wani fresh kika kara haske sis, amma
kin rame, mu je ki gaida Mumy" Daga haka ta ja ta zuwa bangaren Mumy, Nihad dai
gabanta sai faduwa yake don yau kuma bata san me Mumy xata ce mata ba, ga mamakinta
da ta gaida Mumy sai taga ta amsa mata normal normal, cikin sanyin murya tace "Mumy
ina su Sudais" Mumy tace "Sun tafi islamiyya ya gida?" Tace "Lafiya lau" Mumy tace
"Ina Ibrahim din?" A hankali Nihad tace "Yana kofar gida" Mumy tace "Ohk" Nihad ta
daga kai ta kalli Mumy dake kallonta, tace "Mumy su sudais basu ta6a zuwa wurina
ba" Mumy tace "Za su je in sha Allah" Nihal dake zaune parlon ta mike ta fita, Mumy
na kallon Nihad tace "Kin shiga kin gaida Abbanki ne, yana parlonsa" Nihad ta
girgiza kai tace "Aa" Mumy tace "Toh in za ku fita ki shiga ki gaishesa" Nihad dai
ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, bayan few seconds a hankali Mumy tace "Ina
sake tunatar maki ki rike mijin ki, ki bi sa, ki masa biyayya, ki zauna lafiya da
shi, farin cikinsa ya zama naki, bakin cikinsa ma ya zama naki, a yanzu baki da
wani gata a duniya sama da shi, shi ne gatanki Nihad, kar ki yarda ki bari baraka
ya shiga tsakaninku har a ji kanku, Abbanki ba kallonki zai yi ba, tunda a haka
kaddarar ki ta zo sai kiyi hakuri ki rungumi kaddararki sai Allah ya dubeki, in sha
Allah ina da yakinin Ibrahim baxai cuceki ba, baxai bari kiyi kuka ba in har kika
amshesa a matsayin mijin da Allah ya zaba maki a nan duniya" Nihad ta daga kanta
hawaye na sauka idonta tana kallon mahaifiyarta, Mumy tace "Duk wani wanda zai
zugaki kar ki zauna lafiya da shi ba sonki yake ba, makiyinki ne shi Nihad" Nihad
ta gyada kai da kyar hawaye na bin kuncinta tace "Toh Mumy nagode" ita kanta Mumy
daurewa kawai take, cike da karfin hali tace "Idan ma da wani abu zaki iya dinga
amsar wayarsa ki kirani har zuwa lokacin da zai yarje maki rike waya, Allah ya maki
albarka, Allah ya baku xaman lafiya me dorewa" Nan ma Nihad kai kawai ta gyada ma
Mumy hawaye na sauka idonta, Sallama khalil yayi bakin kofar parlon, Mumy ta amsa
ya shigo ciki, kallo daya yayi ma Nihad dake goge hawayen idonta ya zauna kasa ya
gaida Mumy a hankali, ta amsa da fara'a tana tambayarsa gida, Mikewa Nihad tayi
wasu hawayen na sauka idonta ta fita daga parlon ta koma main parlor, Nihal na
ganinta ta mike tana kallonta har ta zauna kan kujera, Nihal ta karasa ta zauna
kusa da ita a sanyaye ta jawota jikinta tace "Kiyi hakuri sis, nasan duk abinda
Mumy ta gaya maki abu ne da zai taimakeki har karshen rayuwaki, i want to see u
happy and lively once again as before plss sis" Nihad ta fashe da kuka sosai, Nihal
ta rungumeta ita ma tana hawaye, Nihad tayi kukanta me isarta Nihal na rarrashinta,
daga jajayen idonta tayi tana kallon Nihal da ita ma idonta yayi ja, cikin rawar
murya tace "But kema ai kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba ko Nihal? U know
baxan taba yin wannan video din in bar shi a wayana, ba halina bane yin video haka"
Tana fadin haka ta kara fashewa da sabon kuka, Nihal ta rungumeta a sanyaye tace "I
know sis, ba halinki bane hakan, but we are hoping one day one time gaskiya zata
bayyana, in sha Allah xaki yi dariya wataran, in sha Allah" Kai kawai Nihad ta
gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata, A hankali Nihal tace "Mu je
parlon Abba ku gaisa, he is inside" Nihad dai tayi shiru, Nihal ta mike ta kamo
hannunta suka nufi parlon Abba, Nihal ce tayi sallama bakin kofar parlon, ya amsa
ta shiga ciki tana rike da hannun Nihad, tun da yaga Nihad ya hade rai sosai, Nihad
dai ta kasa dago kanta, Nihal ta sa suka zauna kasa daga gefen Abba tana kallon
Abban a sanyaye tace "Sister dita ce ta zo za ku gaisa Abba" Sai a sannan Nihad ta
daga idanuwanta ta kalli Abba cikin rawan murya tace "Abba ina yini?" Abba ya mike
yace "Wa ya kawo ki gidan nan" Cikin kuka tace "Tare muka zo da shi" Abba yace "Ba
nace bana son in sake ganin kafarki a gidan nan ba, wato u want to dare me shi yasa
kika zo right?" Nihad na kuka tace "Don Allah Abba kayi hakuri" A fusace Abba yace
"Toh bari kiji, yau ya zama first and last day da zan sake ganin kafarki a gidana,
bana bukatarki, bana bukatar ki kwata kwata, kije can kiyi rayuwarki amma wllh kar
in sake ganin kafarki a gidan nan, idan kuwa ba haka ba duk abinda na maki You
caused it for ur self, sannan ita ma uwarki xan dau mummunan mataki a kanta in har
kika sake shigo min gida" Nihal ta fashe da kuka sosai tace "To nima Abba ka samar
min wani wajen daban don in na koma makaranta babu abinda xai sake dawowa da ni
gidan nan, why will u be so harsh on her kamar ita ta rubuta ma kanta ƙaddara, why
are you doing all this to her Abba, so kake wani abun ya sameta, kar ka manta she
neva bargained for all what is happening to her, me yasa baxa mu taya ta rungumar
kaddararta ba ko zata samu sassauci a ranta? Me yasa zaka dinga korarta Abba??" da
mamaki Abba yace "Ohk rashin kunya za ki min? Ni kike gaya ma wannan maganan??"
Nihal ta mike tana kuka sosai ta dago Nihad suka fice daga parlon, Tsaye khalil da
ya fito daga part din Mumy yayi yana kallonsu, nan saman kujera suka zauna suna
kuka a tare, sai ga Abba ya fito parlon, Yana ganin khalil yace "A kan wani dalili
ka kawota gidana? Ba nace maka ko da wasa bana son ganinta a gidana ba, don me zaka
karya min umarnina?" Shi dai khalil bai iya yace komai ba sai kallon Abban yake,
Strictly Abba yace "Toh yau ya xama rana ta karshe da zaka kawota gidan nan, kai ma
ba sai ka zo ba kuyi zamanku a can kawai, wai ma ba cewa kayi zaku koma zaria ba?
Me ya zaunar da ku har warhaka? To Gobe ka tattarata ku bar garin nan, bana kuma
bukatar duk abinda zai sake dawowa da ita kano, gidan da kace ka samar maku da
farko nasan akwai sauran kudin da na tura maka last week a account dinka kayi
amfani da shi ka biya hayan gidan, sannan ka ajiye min makullin motata...." Shiru
khalil yayi yana kallon Abba babu ko kiftawa, duk wannan abun Umma da dawowarta
daga anguwa kenan tayi still bakin kofa ta kasa karasowa, Mumy ma da ta jiyo muryar
Abba ta fito tana tsaye kofar parlornta, Abba ya kalli Nihad yana nuna mata kofa
cikin tsawa yace "Tashi ki fita" Tashi Nihad tayi da sauri Nihal ta rikota cikin
kuka sosai tace "But she have all right to stay Abba, u can't just send her away
because of a mistake she never bargained for her self, ba ita ta rubuto ma kanta
kaddarar nan ba ai naga" muryar Umma suka ji tana cewa "Kul Nihal, kul.... Karen
hauka ya cije ki ne kike ja'in ja da mahaifinki? Ashe ke mahaukaciya ce dabba ban
sani ba? Are you stupid? Kaji min mahaukaciya shashashar yarinya, ko duniyar ce
baki son gamawa da lafiya?" Nihal ta sake Nihad tana kuka sosai ta mike da gudu ta
wuce dakinta ta dau waya ta kira Yaya farooq, Umma ta nufi Abba tace "Alhaji ka
yayyafa ma zuciyarka ruwan sanyi kada wani abu yaje ya sameka don Allah" Cikin
tsawa Abba yace "Su fitar min a parlor kawai" Umma ta kalli Nihad da damuwa tace
"Tashi ki fita Nihad...." Sai kuma ta kalli khalil tace "Ka ajiye masa makullin
motar ibrahim, ku je kawai kun ji" Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta nufi kofa
Khalil ya ajiye makullin motar dake hannunsa saman kujera ya bi bayanta har suka
fita daga parlon, Juyawa Mumy tayi tana share hawayen dake ta zuba idonta ta koma
bangarenta, Abba ya shige parlonsa a fusace Umma ta bi bayansa da damuwa. Har suka
kai gate Nihad ta kasa daina kukan da take, tun da suka fito dama Aminu ke
kallonsu, don duk wanda ke compound din nan ranan sai ya jiyo muryan Abba, Aminu
dai ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, a karo na farko ya ji tausayin rayuwar
Nihad, xuciyarsa ya karaya sosai, Khalil ya dafa sa a hankali yace "Xa mu yi waya"
Daga haka ya fita gate din Aminu dai ya bi su da kallo ya kasa cewa komai, har suka
isa titi Nihad bata daina kukan da take ba.




☝🏻
*Day before yesterday's update that some people are still waiting for!*

Settled!! so i will keep on updating yanda na saba from tomorrow.



Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah.


35
Bayan sun isa gida Khalil ya ba mai adaidaita sahun da ya kawosu kuɗinsa, Nihad dai
ta jingina da gate ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta tana kuka kamar ranta zai
fita tana jin xuciyarta na mata zafi, har sannan she is finding it hard to believe
Abbanta ne yace baya son sake ganinta har abada, wai yau ita Abba ke ce ma haka,
where is all the love he showed her? she wish her life could end now let all this
be over, Khalil ya bude gate din ta shiga ciki da sauri tana kara sautin kukanta,
da ido ya bi ta bayan ya kulle gate din har ta shiga parlor, yana tafiya a hankali
ya tafi inda yake zama ya zauna ya jinginar da kansa da bango, har aka yi magrib
yana wajen a zaune yayi nisa tunanin da yake, at this point he knows he is confuse
because things have taken another turn, he neva saw all this coming, daga karshe ya
mike gwiwa a sanyaye yayi alwala a tap din dake compound din ya fita zuwa
masallaci, bai kuma fito daga masallacin ba har sai da aka yi sallan isha... Yana
dawowa ya shiga parlor, tana zaune a parlorn ta hade kanta da gwiwa har sannan bata
daina kukan da take ba, ya karasa ciki yana kallonta, zaunawa yayi saman kujera
still looking at her, he don't even know what to say to her, beside he don't even
have anything to say to her, he felt exactly what she is feeling right now some
years ago, and he knows the feeling, tuna hakan yasa zuciyarsa yayi rauni, tashi
kawai yayi daga karshe ya shige dakinsa ya kulle kofar. Khalil bai sake fitowa ba
sai kusan karfe sha biyun dare, kwance ya sameta inda ya bar ta bacci ya dauketa,
ya karasa ya durkusa gabanta yana kallonta, gently yayi tapping dinta, ta bude ido
da sauri, sai kuma ta mike xaune tana murza idanuwanta da suka kumbura, yace "Ki je
ki ci abinci ki yi sallah" Daga haka ya mike ya koma dakinsa ya kulle kofar, ta
jinginar da kanta da kujera wasu hawayen masu zafi na sauka idonta, gaba daya taji
duniyar yayi mata zafi, me yasa Abbanta zai ce mata baya son ganin har abada, me
yasa abbanta zai yi mata irin wannan koran kuma Umma na jinsa amma bata ce komai
ba, she saw everything that happen amma tayi shiru, sosai ta fashe da kuka kamar
ranta zai fita, bayan kusan minti talatim ta mike a hankali jiki ba kwari ta wuce
dakinta tana jin jiri, alwala kawai tayi, tayi magrib da Isha ta kwanta kan
darduman tana duk addu'an da ya zo bakinta hawaye na sintiri a gefen fuskarta,
daren nan Nihad bata yi baccin kirki ba, da baccin ya dauketa zata farka a firgice,
wajajen karfe tara na washegari Khalil ya bude kofar dakinta yana kallonta yace "Ki
dau duk abinda za ki dauka ki fito parlor, ina jiranki yanzu" Yana fadin haka ya
juya ya bar wajen, Nihad ta mike zaune just staring at the door, sosai kanta ke
mata ciwo kamar zai fashe, bayan few minutes ta mike ta canza hijab kawai ta fito
parlorn tana tafiya a hankali, yana zaune ya jinginar da kansa da kujera bayan ya
kashe duk wani abun wuta na gidan, ya kalleta yace "Ina kayan?" Ta girgiza kai
cikin karfin hali tace "Ba abinda xan dauka" Shiru yayi bai ce komai ba, can yace
"Ki je ki karya..." Nan ma ta girgiza masa kai alamar baxata yi breakfast din ba,
bai kuma cewa komai ba, ita dai tana ta tsaye parlon kanta a kasa, har zuwa lkcn
tana ganin scene din abinda ya faru jiya ya kasa bacewa a idonta, daga karshe
Khalil ya mike yace "Mu je" Bin bayansa tayi tana jin kamar zata fadi har suka fita
daga parlorn, ya kulle gidan, suna fita gate taga motar haya irin warce ke zuwa
kaduna, Abuja anyi parking a bakin gate din, tana dai tsaye har ya gama kulle gate
din gidan ba tare da ya kalleta ba yace "Shiga motar za ki yi" A hankali ta kai
hannu ta bude bayan motar ta shiga ta zauna ta kulle, ya zauna a gaba, tun da aka
haifeta bata ta6a shiga ire iren wannan motar ba sai yanzu, ta goge hawayen dake
makale idonta tana wasa da fingers dinta, sai da Khalil yasa suka fara zuwa can
gida ya mika ma Aminu makullin gida yace ya ba Abba, Aminu har da kwallarsa yace
"Toh yanxu sai yaushe kenan??" Khalil na kallonsa yayi murmushi cikin sanyi yace
"Khairan in sha Allah Aminu" Daga haka yayi patting shoulder dinsa ya shiga motar,
Aminu ya bi sa da kallo, dama tun da suka shigo layin Nihad ta hade kai da gwiwa
hawaye na sauka idonta don bata ma son taga gidan nasu, balle ace kallon karshe ta
ma gidan, har kuma suka bar layin bata dago ba sai shesshekar kuka take tana ganin
duk abinda ke faruwa kamar a mafarki, sai da taji sun yi nisa sannan ta dago kanta
tana goge hawayen da yaki tsaya mata.... Ba su yi awa daya ba suna tafiya taji
zuciyarta na tashi saboda warin fetur da take ji motar na yi, daga karshe ta toshe
hancinta da hijab din jikinta, tun dai tana daurewa har dai suna dab da isa garin
zaria ta tabo khalil dage gaba, ya juya da sauri, ganin yanda ta rufe bakinta da
hannu biyu yasa shi ce ma Drivern ya nemi waje ya tsaya, dreban na bakin a gefen
titi ta sauka da sauri ta dukurkusa gefen hanyan tana yunkurin amai, Khalil ya
sauko daga motar ya jingina da motar yana kallonta, kasancewar ba abinda ta ci yasa
bata yi aman ba, sai kokarin kakaro shi take amma babu abinda ya fito, shi dai yana
tsaye yana kallonta, bayan few minutes ta mike da kyar ta koma motar tana maida
numfashi, shi ma ya koma cikin motar, driver na mata sannu ta gyada masa kai kawai,
a haka suka ci gaba da tafiya, kafin su isa kaduna tayi hakan yayi sau hudu amma
duk bata iya tayi aman ba, Khalil ya sa drivern ya tsaya a wani restaurant cikin
garin kaduna ya sauka ya siyo mata abinci, yana fitowa daga restaurant din ya ganta
durkushe jikin motar ta sauko, duk tayi zuru zuru kamar ba ita na, tana ganinsa ta
mike da kyar, hawaye cike idonta cikin sanyin murya tace "Ni baxan iya ci gaba da
tafiya a motar nan ba, yana min warin fuel" Yace "Ohk, yanzu ya za ayi kenan?" Tayi
shiru bata ce komai ba tana share hawayen idonta, yace "Ko kina da kudi ki biya
mana jirgi" Ta daga kai da sauri ta kallesa, can kuma tace "Ina za mu je ne?" Yayi
shiru yana kallonta, sai kuma ya dauke kai yace "in kina da kudin jirgi sai ki siya
mana ticket kawai, babu ke babu jin warin fetur, in kuma baki da halin wannan za ki
iya siya mana ticket din jirgin kasa mu tafi mu hau yanzu" A hankali tace "To ai ni
bani da ko sisi a account dina" Yace "Shine kike korafin mota na maki warin fetur?"
Ita dai bata ce komai ba, yace "Kina bata mana lokaci" Juyawa tayi ta bude motar ta
shiga ya mika mata ledan hannunsa ta amsa ya kulle motar sannan ya shiga front seat
yana kallon dreban yace "Muje" Driver ya tada motar suka ci gaba da tafiya, iya
wahala Nihad ta wahala kafin su isa Abuja, abincin ma ta kasa ci, banda ruwa kawai
da ta sha, shi ma duk sai da ta amayar da shi, sai bayan la'asar suka shigo Abuja,
wani hotel kawai ya sa drivern ya sauke su, drivern ya sauko masa da kayansa daga
motar, Khalil yayi masa godiya sosai, sannan drivern ya ja motarsa ya bar wajen, A
reception din hotel din Nihad ta zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login