Showing 249001 words to 252000 words out of 268471 words

Chapter 84 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ya shiga mota don tuni Nihad ta shiga ta zauna, Habibu da Aminu na daga masu
hannu har suka bar layin, Nihad ta kallesa a hankali tace "Motar taka fa?" Yace "A
airport nake barinsa ai dama, but our flight is in the evening in sha Allah" Tayi
shiru tana kallonsa da mamaki don ta zata airport din za su yanzu, bata ce komai ba
shi ma bai kuma ce mata komai ba, tafiyar kusan minti talatin suka yi yayi horn
baƙin gate din hotel din aka bude masa ya shiga, Nihad na kallonsa tace "All this
while a nan kake dama?" Ya kashe mata ido yace "Yeah" Bata kuma cewa komai ba har
yayi parking ya kashe motar, yana kallonta kasa kasa yace "Kinyi breakfast?" Ta
gyada masa kai tace "Nayi" Yace "Ohk" Tace "Kai fa?" Yace "Done" Bude motar yayi ya
sauka, ita ma ta sauka sannan ya kulle motar, suka jera a tare suka shiga cikin
hotel din, ya amshi makulli a reception yana gaba tana biye da shi har zuwa dakin
da yake ciki, ajiye hand bag dinta tayi saman bedside drawer tana kallonsa a
hankali tace "Now tell me, where did u know Habibu?" Dariya yayi without looking at
her, ya ajiye wayarsa gaban mirror, ya cire shirt din jikinsa sannan ya hau saman
gadon ya kwanta yana nuna mata gefensa with smile all over his face yace "Dawo nan
ki ji inda na san Habibu" Ta dinga kallonsa, ganin taki tahowa yayi kasa da murya
yana kallonta yace "Then.... let forget about that question forever" Sauke idonta
tayi ta cire mayafin jikinta ta linke ta ajiye sannan ta cire dankwalin ma ta linke
ta ajiye, ta nufi saman gadon ta hau a hankali ta kwanta gefensa tana kallonsa....




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah



Ur evidence via 07087865788



Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun
turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin
kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki
ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin
sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta
dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp
09084473900

76

A hankali yace "Come.... closer" Ta kafesa da manyan idanuwanta tana kallonsa babu
ko kiftawa, ya daga kafada yace "Ohk then" Yana fadin haka ya juya mata baya ya
kwanta, murmurshi tayi ta karasa kusa da shi a hankali ta daura kanta a bayansa
cikin sanyin murya tace "Ina jin ka" Juyowa yayi ya jawota jikinsa yayi pecking
lips dinta yana kallonta da kyau yace "What did u want to know?" Tace "Ina son
sanin menene alaqarka da Habibu, da kuma abinda ya kawoka gidanmu" Yana shafa dogon
gashinta a hankali yace "Only that?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk.... Bayan na bar
gidanmu Mami ta so in tafi Uk inyi zamana a can, but i refused saboda bana son
rayuwan turai, i then decided to come to kano, i love kano so much but occasionally
muke zuwa can, so ban taɓa rayuwa a garin ba.... i have a friend da muka fara
karatu tare da shi a India, ɗan nan kano ne, but mind u, we were among the few that
were privileged to get scholarship zuwa india to study medicine babu kosisin mu,
unfortunately he lost his Mum halfway muna cikin karatun, wanda hakan yayi
affecting performance dinsa badly, and sadly he was expelled from the school ya
dawo kano, all through our stay together in india ban taɓa nuna masa waye Abbana ba
don gaba daya Clique din namu opportunity ne ya kawo mu kasar, so kawai ina
rayuwata irin na kowa da kowa da muka taho karatun tare like i am also a
nobody...." Nihad dai sai kallonsa take, ya ja dogon hancinta yace "Zaki tsammanin
hancinki??" Murmushi tayi tace "Are you teasing me?" Yayi er dariya ya manna nasa
dogon hancin da nata yace "Toh naga naki ya fi tsayi" Tace "Ba wani nan naka ya fi"
Ya lumshe ido har sannan dogon hancinsa na manne da nata inhaling each other's
breathe, a hankali tace "Ka ci gaba" Ya buda idanuwansa da suka sauya kala murya
can kasa yace "Ohk" Ya kwantar da ita saman kirjinsa yana ci gaba da shafa gashinta
yace "Still after Mu'azzam left India muka ci gaba da mutunci sosai da shi, though
after going back to Nigeria shagon Abbansa ya koma zama a kasuwar kurmi inda
Abbansa ke siyar da magunguna irin na gargajiya, bayan na dawo Nigeria na so ya
zana jamb ya nemi admission ko a Buk but he told me the zeal to study has left him
since his mother's death, so nayi assisting dinsa in many ways that i can a sannan,
har ya bude nasa shago a nan kasuwar shi ma yana siyar da irin abinda Babansa ke
siyarwa but in a modernize way, After having issues with my dad wajen Mu'azzam na
tafi a kano, then yana hayan wani self contain a wani local unguwa, na dai manta
sunan anguwan, a wajensa nake kwana, a nan nake komai na, da safe mu siya abinci mu
ci sannan in bi sa zuwa noisy kasuwan mu zauna shagonsa tare, that almost affect me
mentally don ban saba ba, amma kuma bana son inje in zauna a hotel even though i
can afford it, ina bukatar zama tare da mutane for the sake of my mental health
because allegations din da Abbana yayi min is too much for me to bear" Nihad dai
sai kallonsa take babu ko kiftawa, yace "Habibu ya kan shigo kasuwan kurmi sosai,
don yana da wani aboki me siyar da kayan koli, shagon abokin kuma kusa da na
Mu'azzam ne, duk in Habibu ya zo wajen surutunsa ke announcing presence dinsa, a
haka dai har muka ɗan fara sabawa da shi don yakan leko shagon mu, and mind u har
sannan Mu'azzam bai san wanene mahaifina ba, don ni duk inda zanje bana show off da
Dad dina ko dukiyarsa.... i knew Habibu for like 3 months a kasuwar kurmi, har dai
muka saba sosai da shi, rana daddaya ne baya shigowa kasuwar, though shi Mu'azzam
baya wani kulasa fa, to saboda ni sai ya dade shagon Mu'azzam muna hira, so wataran
yake sanar min ai ya kusa komawa kauyensu na Getso gaba daya da zama don uban
gidansa ya bude masa shago a can, sai nake tambayansa waye uban gidan nasa, that's
how he started telling me about ur late dad, ya gaya min yayi serving dinsa for
almost 10 years now, and he was like ba don ci gaba bane da bazai bar gidan ba don
yana jin dadin aiki a gidan, yana jin yan gidan kamar yan uwansa, he told me they
are one of the nicest people he have ever met, ya kuma lissafo min workers din
cikin gidan da yanda ake basu 3 square meals everyday sannan ga wajen kwana, har
cewa yayi idan yana gidan mantawa yake ba gidansu bane...." Ya ɗan kalli Nihad dake
kallonsa with full attention, yace "As at then, i was missing the love at home, i
so missed my Family, i am not use to zaman kasuwa that is so noisy and polluted, i
imagined living with this nice family as a worker also, may be hakan zai rage min
kadaici da kewan nawa family din, ban yi kasa a gwiwa ba nace ma Habibu ko zai
taimaka min nima in fara tuki a gidan" Nihad ta sauke idonta kasa lokaci daya gaba
daya mood dinta ya canxa, Khalil ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Habibu
refused, saying ya riga da yayi ma wani abokinsa alkawari, kuma ma Alhajin bai ce
ya kawo wani ba tukun, bluntly ya nuna bazai kai ni gidan ba, kin san yan kauye da
baƙin ciki at times, guess what i did..." Nihad ta daga kai ta kallesa a hankali,
yayi murmushi yace "I gave Habibu 200k just to get that Job, cause i need a new
family badly.... He was so shocked at first da na basa kudin, amma ko kwana biyu ba
ayi ba sai ga Habibu ya zo ya sameni wai yayi ma Alhajin magana yace ya kawo ni,
that was how everything started, a hanyar mu ta zuwa gidan yake sanar min ai ce ma
Alhajin yayi kauyenmu daya, ga gidansu ga namu, don haka kada inje in canxa baki, I
just smiled and said Ohk, kaf yan gidan Habibu bai min maganan kowa ba sai ke, He
told me idan ina son in dinga samun extra income in maki biyayya sannan duk inda
kika ce in kai ki kawai in kai ki sannan babu ruwana da kalan rayuwarki, komai zan
gani in yi shiru ni dai kawai in amshi kudi idan kin ban...." Nihad ta kasa barin
su hada ido, shi dai murmushi kawai yake yana kallonta, murya can kasa yace "And
you were the second person i met in that house after Aminu...." Nihad taki cewa
komai cause she remembered vividly ranan ganinsa tayi zaune a balcony wai yana
jiran Abba, tayi ta masifa don me zai zo nan ya zauna maimakon ya zauna kan benci a
bakin gate, daga nan kuma ta dinga tunano irin rashin mutuncin da ta dinga yi masa
kwando kwando babu ko tsoron height dinsa a gidan har zuwa sanda Abbanta ya daura
mata aure da shi, cikin sanyin murya yace "And i found the family i was looking for
in that great house, Aminu was more than kind to me tun farkon shigowata gidan,
wannan yasa i will make him great in life in sha Allah" Cikin sanyin murya khalil
yace "Abba!! Allah ya ji kansa ya gafarta masa, he took me in without second
taught, yayi accepting dina lokaci daya, har yayi min tayin zama a gidan if i wish,
apart from salaryn da yake bani a ko da yaushe cikin min ihisani yake, he trusted
me even with his Atm card a lkcn kuma ko wata hudu ban cika ba a gidan, and
Nihal... Duk sanda na ganta ina mata kallon Mimi, she made me feel free staying in
that house, she treated me with kindness.... Mumy kuma ina mata kallon mahaifiyata
cause she was so nice to me from the start, i still remembered her giving me one of
her expensive duvet and many other things, bata taɓa hana kananun yaranta zuwa inda
nake ba a gidan, Farooq!!! He ignored i was just a driver and we became friends,
idan yana gari tare muke zama da shi baƙin gate mu yi hira wani lokacin har zuwa
karfe sha biyun dare, na sha cin abinci a plate daya tare da shi da Aminu, Usman
kuma bai taba ganina ya wuce bamu gaisa ba duk da he is an Introvert, Fadil and
Sudais made me their new uncle and love me, even Amina bata taɓa wuceni bata
gaisheni ba....." Hawaye ya fara sauka idon Nihad ta kasa ce masa komai, shiru yayi
bayan yaji saukan hawayenta, can ya rungumeta a hankali yace "And you made my stay
a memorable one wife, i enjoyed almost every bit of ur altitude toward me, it made
my stay in the house worth remembering, duk sanda naga kinyi watsi da ni sai inji
kawai i need to find a way da zan jawo hankalinki gareni har kiyi min halin, i know
i am the cause of most of our fight, wani lokacin kuma ina yin hakan ne just for u
to react, sai kuma a hankali na lura u are being used and controlled, Lastly....
ban taɓa kawo kaddaran aure tsakaninmu ba, and i blessed the reason that made me
meet u Ummina...." Kuka take a hankali bata ce komai ba, ya rungumeta sosai wani
sabon sonta na kara shigarsa, cikin rawan murya tace "I.. i am sorry for
everything, i am sorry i treated u badly, i am sorry for all what i have done to
you, don Allah kayi hakuri" Whispering into her ears yace "I love you for all what
u did to me" Kuka kawai take tana ganin kamar ba haka bane a zuciyarsa, may be he
is only trying to calm her down, amma tasan bazai taɓa manta abubuwan da tayi masa
a gidansu ba. Sai bayan isha'i suka sauka garin Abuja, tun kan su iso dama Drivern
Mami ke jiransu a airport, Nihad bata san if she is happy coming back to Abuja ba
or she isn't, ita dai gata nan gata nan ne kawai, a haka dai har suka iso gidan
Janar, Mami ta ji dadi sosai ganin yanda tayi move on bayan rasuwan mahaifin nata
don har ta marmaro, nan ko bata san handwork din ɗan ta bane, har parlon Janar suka
tafi gaishesa don yana gidan, Janar ya tambayeta su Mumy da Inna, Nihad tace "Suna
nan lafiya" Basu wani jima parlonsa ba suka koma bangaren Mami, abinci iri iri Mami
ta sa aka ajiye masu a parlon nata kafin su dawo, sai da suka yi sallah sannan
Nihad ta fara zuba masa abincin don su biyu ne kadai a parlon, Mimi da Noor sun
koma dakinsu, ya sauko ya zauna kasa yana kallonta ta ajiye masa abincin a gabansa,
ya girgiza kai yace "Ae tare za mu ci, ba sai kin zuba wani ba" Ta zaro ido tace
"Aa ni bazan iya ba...." Yace "Toh return the food inside the warmer nima bazan ci
ba" Murmushi tayi murya can kasa tace "Mami fa zata iya shigowa yanzu" Yace "Ita ma
zuwa tayi ta ci abinci tare da mijinta" er dariya Nihad tayi bata dai ce masa komai
ba ta dau wani spoon din ta fara cin abincin a hankali, yayi murmushi ya dau nasa
cokalin ya fara ci, may be don suna ci
from the same plate ne yasa suka ci da yawa barin ita, bayan sun gama cin abincin
Nihad ta tafi kai sauran abincin kitchen Mami ta shigo parlon, ta zauna tana kallon
Khalil tace "Hope the family are doing better now" Khalil yace "Alhamdulillah" Mami
tace "To maa sha Allah, Allah ya kara masu hakuri da dangana" Yace "Ameen" He was
expecting Mami zata ce su tafi gidansu duk da yasan dare yayi amma bata ce haka ba,
sai ma wani hiran na daban da ta kawo masa, Nihad dakin Mimi kawai ta tafi don ta
hadu da Mami a hanya sanda zata kitchen. Washegari da safe Khalil na zaune parlon
Abbansa ya je gaishesa, Janar yace "So sun shirya maka sanda zaka tafi can Yemen
din kenan?" Khalil ya daga kai ya kalli Abbansa don nobody is even saying anything
to him about the wedding anymore, kuma ba wai basa waya da Nadeeyah bane don har
kusan karfe sha daya jiya yana waya da ita, a jiya da suka dawo ma ya zata Mami
zata yi masa magana don sun ɗan yi hira, amma har yayi mata sai da safe ya tafi
dakinsa bata ce masa komai game da bikin ba, Janar yace "Tunanin me kake?" Khalil
ya sauke idonsa yace "Abba na zata tare za mu je can din ai" Janar yace "No, of
course no, sai dai representative dina but my schedules are tight" A hankali Khalil
yace "Ohk sir" Janar yace "But let me ask you, Ibrahim kana ganin zaka iya adalci
tsakaninsu kuwa?" Khalil yayi shiru yana kallonsa, Janar yace "I am asking this
because, ita dama wannan da zaka aura yanzu choice dinka ce, and i know kuna tare
da ita for long, ita kuma wannan matar taka.... aure ne da Mahaifinta ya hada ba
kai kace kana so ba" Murya can kasa Khalil yace "Zan iya in sha Allah" Janar yace
"Toh Madallah, Allah ya baka ikon hakan, i will talk to ur Uncle sai ku tafi can
kasar tare da shi, may be this weekend in sha Allah, sai iyayen nata su sanar masu
da zuwan naku" Khalil yace "Toh nagode Abba, Allah ya kai mu" Janar yace "Ameen"
Bai jima a parlon ba ya mike ya fita ya tafi bangaren Mami ita dama duk asuba yake
shiga gaisheta, Abbansa ne dai sai kusan takwas ko tara yake shiga gaishesa, xaune
ya sameta a second parlor dinta tare da Mimi da Nihad, Nihad tayi shiru ganinsa, ya
kalli Mami da Mimi dake kallonta, Ya zauna saman kujera, Mimi tayi masa murmushi
tace "Ina kwana yayanmu" Yace "Lafiya lau" Nihad ta ɗan kallesa tace "Ina kwana"
yace "Lafiya lau" Mami na kallon Nihad tace "Ina jin ki" Sunkuyar da kanta tayi
kawai tayi murmurshi, sai kuma ta ɗan saci kallon Khalil amma ta kasa ci gaba da
maganan, Mami ta yi murmushin ita ma tace "Toh ku je ku shirya...." Nihad ta mike
ta nufi kofa, Mimi tayi dariya ta tashi ta bi bayanta har suka fita parlon, Khalil
ya kalli Mami yace "Me take gaya maki?" Mami tace "Ina ruwanka da abinda take gaya
min" Ya shafa kansa yace "Ohk then" Mami bata sake ce masa komai ba, shi ma yayi
shiru, bayan wani lokaci ya kalleta yace "Mami Abba yace da weekend sai mu tafi can
Yemen din, So sai su sanar masu a can din about our coming..." Mami dake ta
kallonsa tace "Toh ai can gida zaka je ka samesu ka gaya masu ko?" Ya ɗan buda ido
yace "Na zata zaki kira Mom din Nadeeyan ki gaya mata kawai Mami" Mami tace "Aa ka
dai je ka gaya masu da kanka ya fi" Yace "Toh" tace "Kayi breakfast ne?" Ya bi
flask da warmers dake parlon da kallo, sai kuma ya girgiza kai, Mami tace "Su Mimi
ne suka yi yanzu, and it's still hot" Ya sauko ya zauna saman Carpet yana bude
warmers din gaba daya, sai kuma ya debi abinda zai ci, ya hada Lipton, jefi jefi
suke magana da Mami har ya gama breakfast din ya mike zai bar parlon sai kuma ya
juyo yace "Mami naji kince su shirya ina za su?" Kallonsa kawai Mami take yi, hakan
yasa ya juya ya fita daga parlon, Direct dakin Mimi ya tafi ya ganta ita kadai a
dakin tana fiddo masu kayan da za su sa da Nihad, ita kuma Nihad na bandaki tana
wanka, yana kallon Mimi yace "Ina za ku naji Mami tace ku je ku shirya?" Tace "Nima
ban sani ba, amma tare za mu fita da ita" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Ohk, let
me disturb you a little, can u pls make me a cup of coffee ki kai min daki" Tace
"Ohk" Daga haka ta nufi kofa ta fita, bandakin ya karasa ya bude, Nihad dake
kokarin fitowa daure da towel ta koma bandakin da sauri ta zaro ido tana kallonsa a
tsorace imagining ta inda ya bi ya shigo, ita dai tasan ta bar Mimi a dakin to ko
fita tayi, shigowa taga yayi ya kulle kofar, ta marairaice masa tace "What is this
u are doing, Mimi idan ta shigo fa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login