Showing 222001 words to 225000 words out of 268471 words

Chapter 75 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ta sauka daga motar tana kallon Nihad dake kokarin
saukowa tace "Ki fa yi a hankali" A hankali ta sauko daga motar Mami na biye da ita
a baya making sure ba sauri take ba suka shiga gidan, shi dai Khalil ya bi su da
kallo, Mami ta ajiye mayafinta ta shiga bandakinta ta hada mata ruwan wanka a
bathtub sannan ta fito dakin tace "Shiga kije kiyi wanka, and be careful as u do
so" Nihad ta tashi ta shiga bandakin, Mami ta koma parlonta ta tadda Khalil a zaune
tace "Ka hada mata kayan sakawanta da duk abinda zata bukata a jaka za mu tafi
asibiti..." Da mamaki yace "Asibiti kuma?" Wani asibitin?" Mami bata tsaya basa
amsa ba ta koma ciki ta dau wayarta, kanwarta Hamidah ta kira, yana fara ring
Hamidah ta daga, bayan sun gaisa Mami tace "Flight din naku yau din ne still
Hamida?" Hamida tace "Ummi fa bata gama siyayya ma jikokinta ba in gaya maki Yaya,
shi yasa ma bamu yanki ticket ba har yanzu" Mami tace "Toh ku bari ko nan da 2 days
ne don nima zan fita zuwa US yau" Hamida tace "Ohk me zaki yi a Us?" Mami tace
"Matar Khalil ce bata da lafiya za mu kai ta asibiti" Aunty Hamida tace "Ayya to
Allah ya bata lafiya, yarinyar da Aunty Maryam ta bani labari?" Mami tace "Ehh"
Aunty Hamida tace "Toh shikenan Mami zuwa jibin in sha Allah, Allah ya tsare hanya
ya shirye shirye?" Mami tace "Lafiya Alhamdulillah, ki gaida Ummi" Daga haka ta
katse wayarta. Ba laifi Nihad ta sha shayi har da dankali da safen kuma bata ji
amai ba, Mami dake dakin sai take ga kamar ko wani abu ya samu cikin ne tunda she
isn't looking sick anymore, ga kuma abinci ta ci sosai, this thought make her
palpitate, jiran kiran Janar kawai take duk da it's still 9am, Har ta gama hada
jakan kayanta ga na Nihad da ta ajiye a gefe bayan Khalil ya kawo mata, Nihad na
gama cin breakfast din sai bacci, Mami na ta zaune dakin bata fita ba har karfe
goma, sai ga kiran Janar Mami ta daga yace "Za a kawo mata B-2 Visa nan da karfe
sha biyu, zuwa da yamma za ku bar kasar in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya kai
mu" Yace "Ya jikin nata?" Mami tace "Toh da sauki, but i am hoping Allah ya sa ba
abinda ya samu cikin, yanzu dai bacci take" Janar yace "In sha Allah everything
will be okay" A hankali Mami tace "I hope so"Janar yace "Za mu yi magana zuwa
Anjima" Daga haka ya katse wayar, Mami ta juya tana kallon Nihad dake ta baccinta.
Mimi ce ta shigo dakin wajen karfe sha daya tana kallon Nihad da ke bacci har
sannan ta zauna gefenta tana kallonta, can ta kalli Mami tace "Mami tun baccin dazu
ne bata tashi ba?" Mami tace "Toh dole sai kusa da ita za ki zauna kiyi magana
Mimi, what if u wake her?" Mimi ta mike ta bar wajen ta koma kusa da Mami, Mami
tace "Kice ma Bilkisu da Sarah su gyara kajin nan Hajiya Safeenah zata zo anjima"
Mimi tace "Toh" Daga haka ta fita daga dakin... Bayan Azahar Hajiya Safeenah ta iso
gidan, Mami ta fito parlonta tace "Ni fa nayi tunanin tun dazu da kika kirani zaki
fito" Hajiya Safeenah tace "Sai da na fara biyawa wani waje kafin in zo nan" Mami
tace "Ya gajiya?" Hajiya Safeenah tace "Alhamdulillah, ya yaran?" Mami tace
"Lafiyansu Lau" ina Nadeeyah?" Hajiya Safeenah tace "Tana gida" Mami tace "Toh maa
sha Allah, wani magana kika ce za mu yi jiya kuwa" Hajiya Safeenah ta gyara zama,
bayan ta sauke ajiyar zuciya tace "Jiya da daddare dangin Baban Nadeeyah suka
kirani with different complaints..." Mami tace "Tohh, ikon Allah, me aka masu?"
Hajiya Safeenah ta girgiza kai tace "Wai mijin da Nadeeyah zata aura da babansa
basu je sun gaishesu ba anyi al'adun can, kawai ina ta iko da yarinya" Mami tayi
shiru tana kallon Hajiya Safeenah, can tace "Amma lokaci bai kure ba kuwa
Safeenah?" Hajiya Safeenah tace "Na gaya masu bikin saura sati daya suka ce ae
kawai a daga" Mami tace "Ikon Allah, to tun da basu fadi haka ba sai yanzu?" Hajiya
Safeenah dai bata ce komai ba, Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina ce mahaifin
Nadeeyah a Nigeria ya rasu?" Hajiya Safeenah tace "Toh yaushe rabonsa ma da Yemen
din kafin ya rasu, shekaransa kusan talatin a kasar nan, to idan ba tashin hankali
suke so ba meye na cewa sai anje an gaishesu bayan yana da ran ma ba damuwa suka yi
da shi ba" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh zan sanar ma Janar in sha Allah,
sai kawai a bi su a yanda suke so don a samu zaman lafiya" Hajiya Safeenah tace
"Wallahi ko bacci ban yi ba jiya, sun daga min hankali sosai, karamar magana ce
suka mayar babba" Mami tace "Kai, Allah dai ya kyauta" Hajiya Safeenah tace "Toh
Ameen" Mami tace "Dama dazu ce maki zanyi za mu je US ganin likita sae kuma kika ce
min ai zaki shigo yau ma" Hajiya Safeenah tace "Wa ye ba lafiya?" Mami tace "Matar
Khalil din ce ba lafiya" Hajiya Safeenah tace "Subhanallah, Allah sarki, Allah
Ubangiji ya bata lafiya, karfe nawa za ku tafi?" Mami tace "Zuwa la'asar in sha
Allah" Hajiya Safeenah tace "Toh Allah Ubangiji ya bata lafiya, tana ina yanzu?"
Mami tace "Tana ciki tana bacci" Hajiya Safeenah tace "Allah ya sa kaffara ne" Mami
tace "Ameen" Sun ɗan taɓa hira, Hajiya Safeenah ta ci abincin da su Bilkisu suka
kawo mata sannan tace ma Mami zata koma gida tana da baki, Mami ta rakata har Main
parlor, Hajiya Safeenah tace "In dai kun fita zuwa airport ki sanar min, sai in
hadu daku a can mu yi sallama Hajiya" Mami tace "Toh in sha Allah" Daga haka Hajiya
Safeenah ta bar gidan, Mami na komawa parlonta sai ga Khalil ya shigo, Ya zauna
yana kallonta yace "Ya me jikin Mami?" Mami tace "Alhamdulillah, ai kun yi waya da
Abbanka ko?" Khalil ya girgiza kai yace "Aa" Mami tace "Toh anjima za mu je USA da
ita a dubata da kyau" Ya sauke idonsa yayi shiru, can yace "Mami Visa fa?" Mami
tace "Yayi sorting komai out an kawo mata dazu" Yace "Amma na ganin likita ko?"
Mami tace "Ehh" Yace "Ohk" Mami tace "Yanzu Hajiya Safeenah ta fita gidan nan, wai
dangin mahaifin Nadeeyah sunce sai kai da Janar kun je sun sanku" khalil ya buda
ido sosai yana kallonta, Mami tace "Toh abinda suka ce kenan wallahi, ina ma son in
kira Janar din yanzu in fara gaya masa kafin mu fita kasar" Khalil dai bai ce komai
ba, can ya mike ya nufi dakinta ta bi sa da kallo, har sannan bacci Nihad take, ya
karasa kusa da gadon ya zauna gefen ya kamo hannunta, a Hankali ta bude ido tana
ganinsa murya can kasa tace "Yunwa nake ji?" Shima yayi kasa da murya yace "Me za
ki ci Dear?" Tace "Pounded yam" Yace "Ohk let me get u immediately" Da sauri ya
fita daga dakin Mami dai ta bi sa da kallo, kiran Janar ne ya shigo wayarta, tana
dagawa bayan sun gaisa yace "Ya jikin nata?" Mami tace "Alhamdulillah, bacci dai
kawai take yi" Yace "Toh Allah ya sauke, you should be cautious of time pls, kar
kuma kuyi missing jirgin" Mami tace "Ina duba agogo wllhi" Yace "Good" Tace "Kana
ji Janar?" Yace "Ina ji" Nan ta sanar masa abinda Hajiya Safeenah ta zo gaya mata
dazu, Janar yace "Waye zai kama ya tafi Yemen yanxu? Don't i have what to do??"




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788




Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son
sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da
xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan
turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba.
Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu
xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da
hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls
guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda
hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls
guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din
da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman
in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800,
6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar
maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰

67

Mami tayi shiru tana sauraron Janar jin ya fusata sosai, ya ci gaba cikin fada yana
cewa "Me yasa tun farko basu kawo wannan batun ba sai yanzu da lokaci ya kure? Why
will they say this just a week to the wedding? Dama ita uwar yarinyar kadai ta
shirya abunta ta hada mu da masu amsan kudin auren yarinya ba tare da sanin dangin
ubanta ba, me yasa ku mata ku ke da karancin tunani ne wai?" Mami tace "Haba dai
ranka shi dade, aminin babanta ne fa, babanta ba shi da kamarsa har ya bar duniya,
tun a yemen suka san juna suka kuma ci gaba da zumunci har a nan, yau ko da uban
Nadeeyah na da rai ina tabbatar maka shi wannan Alhaji Mashkur din ne zai daura ma
Nadeeyah aure ba shi, dama tun asali dangin uban basu son Hajiya Safeenah saboda
Ubanta bafillatanin Nigerian ne uwarta ce er kasar yemen kaga ai ita bafullatana
ce, bayan ubanta ya rasu kuma mahaifiyarta ta koma yemen da ita, kawai dai suna son
daga ma Hajiya Safeenar hankali ne shi yasa suka billo da batun zuwa yemen gun
dangin Baban Nadeeyah, me yasa tun da aka sanar da su zancen auren basu ce haka ba
sai da lokaci ya zo, they knew nothing about the girls wellbeing, neman magana ne
kawai, don haka kayi hakuri tunda har sun ce a kara dagawa ai sai a daga din a bi
komai a sannu babu gaggawa, ayi making preparations na zuwa can Yemen din....."
Janar yace "Fatima" Mami tace "Ina jin ka" Yace "A dai nan kwana kusa daga sati
daya har zuwa sati biyar masu zuwa bani da time din zuwa Yemen to be frank with u,
i am occupied, nayi scheduling duk kwanakin nan, i don't have time, wait ma dai
tukun, idan ba rainin hankali ba ni me zanje yi masu a yemen, shi da yake neman
mata a can ai sai ya shirya yaje ya gaishesu, ni me zan je in masu?" Mami ta
girgiza kai tace "Aa mu ba haka ake a wajen mu ba gaskiya, da shi me neman auren,
da ubansa, da kawun uban nasa ne za ku je gaishe da dangin uban yarinyar, kai har
ma da dangin uwarta ko da a wani gari suke" Janar yace "I see" Mami tace "Ka daina
duba cewa ai shekaru 36 da suka wuce baka je can neman nawa auren ba, kar ka manta
a hannun wan mahaifina nake a kasar nan a wancan lokacin, you just have luck sai
bayan da aka yi aurenmu sannan suka koma can din gaba daya, banda haka da dole ne
sai kaje wallahi" Yace "To a sannan ina naga kudin zuwa Yemen?" Murmushi kawai Mami
tayi, sai kuma tace "Da da kudin ma ai danginka baza su bari kaje ba tunda ba sona
suke ba" Janar yace "Let me pick a call" Daga haka ya katse wayar, Mami ta sauke
wayar daga kunnenta tana tunanin ta inda zata fara convincing dinsa yaje gaida
dangin uban Nadeeyah, kallon agogo tayi ganin karfe uku ta mike da sauri ta shiga
daki don tada Nihad ta shirya su tafi airport, suna gama shiryawa ta kira Hajiya
Safeenah ta sanar mata ga su za su tafi airport, Khalil ya bi Mami da kallo babu ko
kiftawa, ta tafi ta dau Handbag dinta ganin kallon da yake mata tace "Kana kallona
haka, idan kuma in bar ka da ita ne to sai in bar ka ba sai naje ba, amma kada ka
kuskura in ganka a US ko a mafarki wallahi" Ita dai Nihad ta sa Hijab dinta Mami ta
saka ta a gaba suka fita daga dakin suka barsa nan tsaye kamar statue. Khalil na
zaune gaban motar Mami, ita kuma tana back seat tare da Nihad suka iso airport,
suka tarar da Hajiya Safeenah har ta isa airport din da wata er uwarta, Hajiya
Safeenah kadai Nihad ta gani ta dauke kai cikin dubara ta kuma ki sauka daga cikin
motar, Bayan Mami sun gaisa da er uwar Hajiya Safeenah tace "Ina Nadeeyah, tana
gida ne" Hajiya Safeenah tace "Aa tare muke, ta hadu da wata Coursemate dinta ce,
mun baro su can suna gaisawa" Mami tace "Allah sarki" Khalil ya zagoya ya gaida
Hajiya Safeenah da sister dinta suka amsa da fara'a, Hajiya Safeenah tace "Ya me
jiki? Tana ma ina ban ganta ba" Mami ta bude motar tana kallon Nihad da ta makale
ciki, sai ta fara kokarin saukowa daga motar Mami tace "Aa zauna ba sai kin fito
ba" Hajiya Safeenah na kallon cikin motar tace "Sannu kin ji, Allah ya sauwake, ya
baki lafiya" Nihad ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini" Hajiya Safeenah tace
"Lafiya lau daughter, Allah ya baki lafiya kin ji" Ita dai Nihad bata ce komai ba,
sister dinta ma tayi mata fatan samun lafiya, daga nesa Nihad ta hango Nadeeyah na
tahowa haka kawai taji gabanta ya fadi, ta dai dauke kai daga kallonta har ta iso
inda suke, Nadeeyah ta gaida Mami da ladabi, Mami tace "How are you dear" Nadeeyah
tace "Alhamdulillah, ya me jiki?" Mami tace "Jiki Alhamdulillah" Hajiya Safeenah ta
koma gefe tare da Mami tace "Kinga ko da dangin Mahaifin Nadeeyah basu tado da
zancen aje can a gaishesu ba ai dole za a daga bikin nan har Allah ya ba takwararki
lafiya Hajiya" Mami tace "Toh yanzu na dai fara ma Janar magana amma bamu gama ba
gaskiya" Hajiya Safeenah tace "Aa da baki masa maganan yanzu ba ma, har sai Fatima
ta samu lafiya, lafiya ai yana gaba da komai Hajiya" Mami tace "Haka ne" Nadeeyah
na kallon cikin motar da Nihad take, har sannan da murmushi fuskarta ta ɗan saka
kai cikin motar cin sanyayyen murya tace "Hi, ya jikin, hope u are feeling much
better" Nihad ta ɗan kalleta, sai kuma ta mata wani kallo ta dauke kai ta tsuke
fuska tana kallon daya side din, duk Khalil na kallonsu but sai yayi saurin kauda
kansa, Nadeeyah ta bar jikin motar ta tsaya a gefe, gaba daya jikinta a sanyaye,
Khalil dai bai yarda ya kalli inda take ba, duk da yana son mata magana amma ya
kasa saboda Nihad, wanda ita ma sai kallo take taga ko zai mata maganan, Mami da
Hajiya Safeenah suna gama maganar da za su yi aka yi Conveying din Mami da Nihad
zuwa Lounge din da zasu jira har karfe hudu da rabi kafin tashin jirginsu, har
zagawa Khalil yayi zuwa daya side din mota kafin Nihad ta sauka zuwa Lounge yana
mata magana amma ta maka masa wani harara ta ki kulasa ta sauka Mami ta saka ta
gaba suka wuce, ya kalli Nadeeyah da har ta koma gun motarsu tana jiran Mum dinta
da Aunt dinta su karaso, yana kallon Drivern Mami yace "Bani makullin mota, ni zan
dawo da shi gida" Sojan zai yi magana Khalil ya ciro wayarsa yayi dialing number
Mami ya sa handsfree tana dagawa yace "Mami zan fita da motar ki" Mami tace "Ohk"
Bai sake kallon Sojan ba ya cire Makullin jikin motar ya kulle, ya nufi motar su
Nadeeyah, haka nan convoy da suka kawo Mami suka juya suka bar airport din leaving
Mami's Ride behind. Khalil na kallon Nadeeyah yace "Mu je in ajiye ki gida" ba tare
da ta kallesa ba tace "Nah don't worry za mu koma tare da su Mum" Aunt dinta ta
kalleta tace "Ki je mana" Ita dai Hajiya Safeenah bata ce masu komai ba, Nadeeyah
ta langwabar da kai tace "Na riga na shiga nan ne Aunty" Khalil yace "Ohk then,
later" Ta gyada masa kai, Yayi ma su Hajiya Safeenah sallama ya juya ya koma gun
motar Mami, Drivernsu ya ja motar suka bar airport din.
Umma ce zaune dakinta da ta kulle da makulli tana waya kasa kasa tace "Na gaya maki
tun ranan har yau... kin ga dai kusan sati uku kenan ko to ban sa shi a ido ba,
iyaka duk wani expenses na kudin magani da kika sani shi ke badawa bai taɓa cewa Aa
ba, dama Farooq ne ke kai ni asibiti tun da ya koma bakin aikinsa sai Kamila ta
rakani idan ta ga dama, wani lokacin da Amina nake zuwa...." Tana magana hawaye na
zuba idonta, ta ci gaba tace "Usman kuma ai na gaya maki sati biyu kenan da ya fita
Nijar yana buga bugansa a can, Turai duniyar ta min zafi, ji nake kamar zuciyata
zata iya fashewa a ko wani lokaci, ga Kamila babu zancen komawa dakinta mijin har
yayi wani auren, Ɗan nata guda daya ma ya amshe ya kai ma uwarsa, Nihal da nake sa
ran wannan ɗan ministan zai aureta tace min basa tare ai yanzu, da na tambayeta
waye kuma a kasa yanzu sai tace min babu kowa, to ina lafiya Turai? Gashi yau kusa
da wata uku kenan gata nan gata nan ne dai kawai kamar ba Nihal dita ba, har da
wannan sauyin nata ke damuna yanzu haka, sannan da na tuna Nihad ga gidan da fa
take aure sai naji zuciyata kamar ta tsinke, Turai kinsan bani da komai kuma yanzu
balle a ci gaba da neman taimako, zoben nan guda daya ne kawai ya rage min, ta ina
zan fara Turai?" Turai tace "Sumayya ki kwantar da hankalinki kada kije damuwa ta
sa maki ciwon zuciya, iya laluran hawan jinin da kika samu a kwanan nan ma ya isa
haka, in sha Allahu komai zai dawo dai dai Sumayya, yanzu abinda zai faru zan aiko
Fa'iza ta amsa zoben in siyar in je can Zaria gun malamin da ya fara mana aiki
shekaru takwas da suka wuce, kince saki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login