Showing 69001 words to 72000 words out of 268471 words
kenan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ya bar ta a ciki,
bayan ta ci dariyarta ya isheta sai kuma ta mike ta hade rai, a hankali ta dauke
tukunyar shinkafar da Aunty Jamila ta girka, ta dau na miyan ma duk ta kai dakinta
da plate da spoon sannan ta koma ta jawo kofar kitchen din ta saka makulli ta zare,
sai ta ga ta yanda xai sha shayin yau, infact forever and ever, don ta kulle
kitchen din kenan har abada, Dakinta ta wuce ta bude akwatunta ta binciko duk kayan
ta ajiye makullin karkashin akwatin sannan ta mayar da kayan ta kulle akwatin ta
koma gefen gado ta zauna. Tun kafin tayi sallan magrib tayi wanka, don haka ta zuba
abinci ta ci, ta tashi ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta dauro alwala, tana yin
sallan isha'i ta sa ma dakinta makulli ta ta dawo ta kwanta. Washegari bayan Nihad
tayi wanka ta wanke bandakinta,
she can be lazy in all aspects but not when it comes to her bathroom and Bedroom,
bayan ta fito sai da ta fara gyara dakinta sannan ta saka kaya, sbda mugunta haka
ta zuba sauran shinkafar da sanyi ta ci, ta koma bandaki ta kuskure bakinta da
mouth wash ta fito, Hijab har kasa ta daura saman kayanta, sannan ta dau jakar da
take xuwa makaranta da shi ta bude kofa a hankali ta fito parlor, yana kwance saman
doguwar kujera, ta galla masa wani harara ta karasa cikin parlon, ta tsaya bayan 2
seater, ta dake tace "Makaranta xaka ajiyeni malam" Khalil ya daga kai ya kalleta,
sai kuma ya mike zaune yace "Ohk, wace makarantar?" Babu yabo babu fallasa tana
juya ido tace "Wanda ka saba kai ni" ya gyada kai yace "Ohk" Sai kuma ya koma ya
kwanta, a mugun fusace tace "Kana bata min lokaci lectures din safe gareni, ko kuma
ka bani makullin motarmu inyi tafiyata" Khalil yace "Ki jira duk sanda Allah ya
nufa kin koma can gidan naku da xama sai ki ci gaba da xuwa makarantar, amma a nan
gidan kam ke da fita ko nan da gate sai wani ikon Allah, na soke xuwa wannan
makarantar har abada" Da mamaki take kallonsa baki bude, sai kuma ta hadiye abu da
kyar tace "Kai kuma a uban wa xaka gaya min haka? Kai a wa xaka soke min xuwa
makarantata?" Ya kalleta yace "Kira Abbanki ki tambayesa" Bata san sanda ta fashe
da kukan takaici ba tana kallonsa, yace "Allah ya amfana ɗan wanda kika samu" Yana
kai wa nan ya mike ya shige daki ya bar ta wajen, sulalewa kasa tayi tana kuka
sosai, wai yau common driver ne yake ce mata baxata je makaranta ba wai ya soke,
whatttt??? Nihad ta ci kuka ta gode Allah a wajen kafin ta shiga daki, komai na
duniyar ta ji ya isheta.... Throughout ranan haka ta yini a kwance tana hawaye,
tana mugun son tayi magana da Umma amma babu dama, don babu wayar da xata yi kiran,
she needs to tell Umma this, bayan Umma bata da wani wanda xata gaya ma, tana jin
an kira la'asar ta mike zaune, sosai kanta yayi mata nauyi, ga magungunanta rabon
da ta sha tun jiya, kuma bata jin xata sha, shiru shiru bata ji alamar ya fita gate
ba gashi har an tada sallah, mikewa tayi a hankali ta fita parlor, ta dinga bin
parlon da kallo ta kalli bakin kofa taga ba takalminsa, to har ya fita kenan bata
ji ba, komawa corridor din dakunan tayi ta kai hannunta handle din kofar dakinsa ta
murda a hankali kofar ya bude, ta leka cikin dakin ta ga ba kowa, kallon karamar
wayarsa dake saman gado ta dinga yi, dai dai nan ya bude kofar bandaki ya fito,
tayi masa wani tsinannen harara ta juya ta koma dakinta. Bayan ya dawo masallaci
yana zaune compound bai shigo parlon ba yaji an kwankwasa gate, ya dinga kallon
gate din kafin ya mike ya tafi bakin gate din, har sannan ba a fasa kwankwasawa ba,
yace "Waye?" a fusace Umma tace "Malam xaka bude min kofa ko kuwa? Ji wani tambayar
walakanci wai waye, shi dama talaka ai bai iya samun waje ba, ka tashi ka garkame
gida kamar na ubanka, da an kwankwasa kuma kace waye, to masu shi ne sai ka bude
ko?" Khalil na tsaye yana sauraronta, sai da ya dau kusan 40 seconds kafin ya bude
gate din, Umma ce tsaye da su Husnah a bakin gate din, Yayi kasa da kansa yace "Ina
yini" Umma tayi mitsi mitsi da ido tace "Ban yini ba, nace ban yini ba, ɗan marasu
mutunci" Ya so juyawa ya bar wajen amma ya kasa sbda girma da mutuncin da Abba ke
da shi a idonsa, Husnah, Naf da Zully suka dinga kallonsa babu kwakkwaran kiftawa,
duk tambaya daya ce ke yawo a xuciyarsu, wannan shi ne dreban, is he the driver?
Husnah tace "Umma wai shine driver din??" Umma tace "Gashi kuwa kin gansa" Duk suka
kalli junansu, Husnah ta tafe hannu tana kallon khalil tace "Wato kai ne ɗan rainin
wayon da ya barmu bakin gate jiya? Kai ga ka shafaffe da mai ko?" Naf na nuna sa da
yatsa tace "Kai kana buzu har xaka zo kasar mutane kana bubbusa hanci kamar
algaita? Waye kai? Kuma uban me kake takama da shi? Kasan mu su waye da kake
tunanin zaka mana walakanci ka kwana lafiya?" Zully tace "Ai ni na ma rasa ta cewa,
wato wannan dai shine driver me ba kawar mu though time, toh hasken naka kake
takama da shi kake tijara ko me?" Nihad ce ta taho da gudu ganin Umma ta rungumeta
cike da farin cikin ganinta, Sai kuma ta sake Umma ta rungume su Husnah gaba daya
har da hawayenta sbda tsabar farin ciki, juyawa khalil yayi ya bar wajen kamar zai
tashi sama, Husnah tace "Sai ga mu ga ɗan rainin wayon nan yau" Nihad ta sauke wani
ajiyar xuciyar takaici, Umma tace "Wato bai baki wayar ba dai" Nihad tace "Wallahi
kuwa, ya ki bani" Umma tace "Mu je ciki, sai na ci kaxa kazansa, wato yanxu baya
ganin kowa da gashi sbda Alhaji ya gama bada mu gabansa yayi mugun raina mu, yo ya
bada mu mana tunda har xai dau yar sa ya basa, idan ma hadin yake son yi ina 'ya
yan abokanansa?" Duk suka dukufa xuwa cikin parlon Umma na ƙare ma Khalil zagi su
Husnah na tayata, shi kam tuni ya shige daki ya sa makulli, sabuwar waya dal Husnah
ta siya ma Nihad har da sim card a ciki, murna wajen Nihad ba a cewa komai, gaba
daya ta mance damuwar da take ciki, Umma tace "Kinga shikenan sai ki kwantar da
hankalinki yanxu, tunda sun ga gida kullum kya gansu, kafin dai su dawo nan din
gaba daya" Nihad ta marairaice tace "Umma fa kulle gate din yake yi kuma makullin
na jikinsa" Naf tace "Amma fa kamar a jikin gate din ya bar makullin yanxu da ya
bude mana fa" Husnah tace "Idan ko haka ne kawai cirewa xa mu yi mu je a yanko mana
spare" Zully tace "Bari in duba" Mikewa tayi ta fita, sai ga ta ta dawo rike da
makullin tace "Ai ko dai gashi" Umma tace "Toh Alhamdulillah, tunda dare bai yi ba
yanzu me xai hana ku je inda ake yankan spare din a yanka maku?" Naf ta mike tace
"Yanzu kuwa, kawai kudi za mu cika masu yau yau din nan xa a yanka a bamu" Naf da
Zully ne suka tafi da makullin wajen yankar makulli, Nihad ta dauko ma Husnah
makullin kitchen xata dafa masu taliya wai, Nihad na kallon Umma ta marairaice tace
"Umma yau na shirya xan je makaranta ya hanani wai ya soke" Buda baki Umma tayi
tana kallon Nihad, sai kuma tace "Toh ba a haifi ubansa ba balle shi, shi har ya
isa ya soke maki karatu? Bari dai su yanko makullin kawai, ki kwantar da hankalin
ki, ai indai da raina babu me cutarki a duniya Nihad, sannan nace maki ki wani
manta da batun dreba kiyi rayuwarki yanda kike so, ga makulli nan xa a kawo ai,
rayuwarki kawai za ki dinga yi yanda kike so kanki tsaye" Nihad ta sauke ajiyar
xuciya tace "Toh Umma" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanxu shkkn har yau
Aliyu ba neme ki ba ko?" Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad ta girgiza kai hawayen
na sauka fuskarta tace "Ai blocking dina yayi Umma, kuma sim din ma na karya ai...
Umma ban san waye yayi min haka ba kilan don a rabani da Aliyu ne." Kuka take yi
sosai kamar ranta xai fita, cikin rawar murya tace "Wallahi ina sonsa Umma, gashi
yanxu an rabani da shi" Umma tace "Aa ki daina cewa an raba ku, kina fara xuwa
makaranta duk yanda xa ayi ki nemi numbersa ki nema, ba kince min a kawayenki akwai
me numbersa ba?" Nihad ta gyada kai hawaye na gangarowa fuskarta tace "Naf tana da
numbersa, dama can sun san juna a Uk" Umma tace "Toh ko wajenta ki amsa, kar ma ko
da wasa ki wani ce ai Abbanki ya maki aure ko da xa ku fara magana da shi" Nihad
dai tayi shiru bata ce komai ba, har kusan magrib Umma na parlor da Nihad, Husnah
ta kawo taliyar duk suka ci, all this while kuma khalil na kwance daki ko masallaci
bai fita ba, Karfe bakwai su Naf suka dawo da makulli, Umma tace "Yauwa yan
albarka, gasu nan kuwa har uku, toh sannunku, Allah ya maku albarka" ta mika ma
Nihad daya, ta saka daya a jakarta sannan ta basu su ma daya, tace "Toh kun ga dare
yayi ni xan koma gida, ku sai anjima ko? Ko dai a nan xa ku kwana kawai?"
Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence via👇🏻
07087865788
23
Husnah ta kalli su Naf jin abinda Umma tace, Naf tace "Aa Umma bamu zo da kaya ba,
mu ma kawai yanzu xa mu wuce, idan ya so ko gobe ne ma dawo" Umma tace "Toh shkkn,
hakan ma yayi, Allah yayi maku albarka, tunda ba da mota na zo ba mu je kawai ku
ajiye ni" Duk jikin Nihad yayi sanyi ganin xa su tafi su bar ta, babu yanda ta iya
haka ta rakasu har bakin gate suka wuce sannan ta dawo cikin gidan tana ta kumbure
kumbure. Sai da su Naf suka kai Umma har kofar gida tayi masu godiya tana sa masu
albarka, sannan suka juya ita kuma ta shiga gate, Aminu na gaisheta ko bin ta kansa
bata yi ba ganin Abba a tsaye balcony, karasawa balcony din tayi da sauri tace "Har
ka dawo daga gidan Baffan?" Abba na kallonta daga sama har kasa yace "Daga ina
kike?" Ta sauke ajiyar xuciya tace "Kayi hakuri ban ce maka xan fita ba, na fita
babu izinu, wallahi Yallabai Nihad ce kira ba dare ba rana ko da yaushe cikin kuka,
to shine yau da abun ya isheni nace bari dai in je in ga wani hali take ciki a
gidan, kasan tun da muka kai ta ai ban koma ba" Abba dake ta sauraronta har ta kai
aya yace "Toh daga yau kada ki sake xuwa gidan...." Da mamaki Umma tace "Kamar yaya
fa Alhaji? Shikenan saboda iftilai ya fada ma yarinya sai ka sallama ma duniya ita,
mu ma kuma ka nemi mu sallama ma duniya ita? duka duka nawa Nihad din take
fisabilillahi Yallabai? Yarinyar da ko shekara ashirin bata yi ba a duniya, me ta
sani akan rayuwa at this her early stage? so kake wani cutar yaje ya kamata a banza
mu shiga uku? Kai kanka kasan wannan yaron tun zuwansa gidan nan ba shiri suke ba,
jininsu bai ta6a haduwa ba amma ka rasa wanda zaka hadata aure da sai shi? Me yasa
ma idan hadin ne baxa ka hadata da wanda bata sani ba bai santa ba, sai Dreban
gidansu? Haba wannan ai babu adalaci yallabai, baka kyauta mata, wannan fa
kaddararta ce, sannan ace duk soyayyar da kake mata amma ka rufe ido ka saka
rayuwarta a garari kawai don an samu wasu shegu sun hada mata makirci?" Abba yayi
shiru yana kallonta, can yace "Yanzu shawara kike bani a warware auren kenan?" Umma
ta kalli Abba, ganin how sincerely he spoke, tayi kasa da kai tace "Ni ba haka nake
nufi ba, kuma ai kai ba karamin mutum bane aji an daura aure kuma an warware sa,
mutuncin da kimarka ya wuce haka, kawai dai ina jimamin abun ne, amma don Allah kar
ka hanani zuwa wajenta ko ba komai zan dinga kwantar mata da hankali har ta hakura
da wannan auren" Abba yace "Sumayya" Ta yi shiru tana sauraronsa, on a serious note
yace "In har kina son zaman lafiya da ni toh na haneki da kara taka kafarki zuwa
gidan nan, idan da wani abu xai kawota gida ba sai kin je, ina kara ja maki kunne
babu ke babu gidansu, sannan ko mutuwa take ke kina tunanin zan sa a warware auren?
Ai sai dai ta mutu a dakinta" Umma tace "Tabdi, to yallabai kamar yanda baxan yi
shiru ba idan Nihal ce aka ma haka to Nihad ma baxan yi shiru ba don duk daya suke
a wajena babu banbanci, don haka hanani zuwa gidan 'ya ta bai taso ba...." Abba
yace "Good! Don Allah gobe ma ki shirya ki kara komawa gidan, ina me tabbatar maki
a nan xaki ga the other side of me" Yana kai wa nan ya juya ya shige cikin gida,
Umma ta bi sa da kallo sai kuma ta kyabe baki ta bi bayansa. Su Husnah na komawa
hostel duk suka shantake a saman gado babu zancen sallah balle salati, Naf ta sauke
wani ajiyar xuciya tayi kasa da murya tace "Amma don Allah ku ya ku ka ga wannan
drivern? Isn't this strange?" Zully ta riƙe ha6a tace "Not as i expected, anya kuwa
da gaske shine drivern? Ni fa har muka dawo ina kokwanto a raina gaskiya" Husnah
tace "Kun ji ku, idan fa an bibiya irin shuwan nan ne fa wanda ba shi da galihu,
farin fatarsa ce tasa ku ke kokwanto ko driver ne shi ko ba driver ba?" Zully ta
kalleta tace "Aa maganar gaskiya duk da Umma ta tabbatar mana da shi din ne har
xuciyata na kasa yarda, ta yaya wannan cikakken mutumin xa ace driver ne? His
skin... Ko ku baku lura da shi ba, no plss he is so fresh abeg" Naf tace "Ohhhhoo
ashe dai bani kadai ma lura da skin dinsa ba, ni wallahi da ba don kar inyi karya
ba ma sai nake ganin kamar na ta6a ganinsa, ko me kama da shine oho" Husnah ta
kyabe baki tace "Kanku ake ji" Zully tace "Kai amma gayen nan Allah ya xuba masa
kyau frankly speaking, kawai mu fadi gaskiya, duk inda me kyau xai shiga shi ma xai
shiga, kuma ina tabbatar maku Nihad haukan ta bai taba barin ta nutsu ta kare masa
kallo ba" Husnah tayi wani dariya tace "Kai kuma da da wani zance, Ina amfanin kyau
ba nera? kina jin mutum na tukin mota for a living, kun ishe ni da wani yana da
kyau? kawai Nihad din ma kadai ya raina dan ya ganta er karamar yarinya ne, mu kuwa
da muka kusa talatin a duniya baki ga da muka masa wankin soso da sabulu bai iya
yace mana komai ba sai sissine kai da yake, ni fa baxan yi mamaki ba idan aka ce
shege ne mutumin nan, kilan uwarsa a titi ta haifesa ta yarda shi shine yake ta
garari har ya samu driving gidansu Nihad" Zully ta kwashe da dariya ita dai Naf
bata ce komai ba, Husnah ta kalleta tace "Ya dai... Kin yi shiru" Naf ta ɗan tabe
baki tace "No kawai ni dai i am not comfortable cewar shi din mere driver ne, he
might definitely have a mission, haba u girls should think deep mana, sai kace ba
big babes ba, ko kayan jikinsa idan kuka lura ai ba na banza bane, ni fa har
takalminsa sai da na kalla, wallahi da kyar idan mutumin nan ba wani mission garesa
ba" Husnah da Zully suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Husnah tace "Wllh shi
ba kowa bane don ma ki ji in gaya maki, a wannan zamanin babu wanda xai bata lkcnsa
ya zo gidan mutane for almost a year now wai da sunan mission, sai kace wani film
ko novel, mission for almost one year ace ba ayi accomplishing dinsa ba har yanxu?
Ke dai ki yarda ɗan talakawa ne mukus me shegen girman kai, don yaga fatarsa ja ce
sannan gashinsa irin na halfcast shine yake wani feeling, ba ga ire irensa ba a can
Ibadan da Lagos suna bara bakin titi, kilan shi ma daga can ya gudo arewa bayan ya
girma" Zully tace "Kuma haka ne wallahi, gasu can a karkashin gadan lagos har
Ibadan" Zully ta kyabe baki ta mike tace "Ni dai bari in je in yi wanka in zo in
kira babyna, ba ruwana da wani batun shegen dreba can" Naf tace "Yanxu yaushe za mu
je mata can din, kun san fa mun sa mata rai" Husnah tace "Mu bari kawai jibi don
gobe kinga xa mu je minjibir park" Naf tace "Ehh haka ne kuma, Allah ya kai mu"
Washegari tuesday da safe Nihad ta shirya tsaf xata makaranta abunta tunda ga
makulli a hannunta, mayafinta ta yafa ta dau jakarta bayan ta feshe turare kusan
kala biyar a jikinta ta fito daga dakin, yana jin fitowarta yayi saurain mayar da
wayarsa dake hannunsa xuwa bayan kujeran da yake zaune, bata ko kallesa ba ta nufi
kofa ta fita abun ta, da ido ya bi ta imagining if tsallake gate din xata yi,
rabonsa da ita tun jiya bayan ya bude ma Umma gate da suka zo, can dai ya mike ya
fita parlon ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah, tana isa gate ta bude
jakarta ta ciro makullin tana kokarin bude gate din taji yace "Keee" bata fasa bude
gate din ba ta juya ta kallesa bayan ta bude tace "Saboda baka yi karatu ba baka
san muhimmancin karatu ba kana tunanin ka isa ka hana ni zuwa makaranta ko, to baka
isa ba, ba a kuma haifeka ba" Tana gama fadin haka ta fice daga gate din, mamaki ne
ya cika sa yayi saurin ciro makullin aljihunsa yana kallo yaga it's intact, then
where did she get a space key?? bai yi attempting bin ta ba balle har tayi
showcasing altitude dinta a bakin titi, ya juya ya koma parlor filled with
surprise. Ba karamin mamaki su Husnah suka yi ba ganin Nihad a school, Nihad ta
zauna aji jikinta duk a sanyaye don tun da ta shigo schl ake nunata, wai ga warce
ke cikin video din nan, har ta iso ajin da suke lectures idon jama'a na kanta,