Showing 87001 words to 90000 words out of 268471 words

Chapter 30 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ta tafi gun mota tana kuka kamar an aikota ba tare da ta
damu da mutanen dake kallonta a wajen ba, bude mata back seat yayi yace "Shiga inda
kika fi jin dadin zama ki xage mutane kiyi masu rashin kunya...." Ta shiga bayan
motar tana kuka kamar ranta xai fita, ya ajiye mata ledan maganinta ya koma driver
seat ya ja motar suka bar wajen..... Wani eatry Khalil yayi parking ya kashe motar
bayan ya ɗan sauke glass ya sauka sannan yayi locking motar, ita dai kuka kawai
take don har ta saka a ranta cewar in har taga sun nufi hanyar kauyen nan to suma
kawai xata yi a cikin motar kuma duk abinda xa ayi mata baxata farfado ba, ba a dau
lkci sosai ba ya dawo rike da ledan take away, ya ajiye a back seat sannan ya shiga
mazaunin driver yana kallonta ta madubi yace "Bari a kai ki inda xa ki yi wanka
kafin mu koma, don naga babu wajen wanka a garin" daga haka yayi reverse suka bar
haraban eatry din, Rokonsa Nihad ta dinga yi hankali tashe tana cewa ya rufa mata
asiri su koma gida amma bai tanka ta ba, a wani hotel taga ya shiga yayi parking,
tsaf ta gane hotel din don sun ta6a xuwa da su Husnah, yanxu da gaske wankan xata
yi su koma wannan kauyen?? yana parking ya sauka ya kulle motar ya bude side dinta
fuska daure yace "Sauko malama" A hankali ta sauko daga motar, ya dau ledan
maganinta da abinci, yana gaba tana biye da shi suka shiga reception din hotel din,
ya gaisa da masu aiki a nan, makulli kawai ya amsa alamar dai ya kama dakin
tuntuni, ganin yayi hanyar stairs ta bi bayansa tana ji kamar iska xai kadata ta
fadi, ya bude dakin ya shiga ita ma ta shiga sannan ya kulle kofar, bin dakin take
yi da kallo, taga tray me dauke da kayan shayi da cup din shayi alamar an sha
shayi, ya kunna wutan dakin ya sauke curtains sannan ya shiga bandaki, tana jin
alamar wanka yake yi ta zamo kasa a hankali ta zauna ta jawo ledan abincin da ya
ajiye ta bude, fried rice da yaji liver hade da spicy jollof rice a gefe ta gani,
sai peppered chicken, tayi unwrapping cokalin daga tissue dake jiki, har wani rawa
jikinta yake ta fara cin abincin, Nihad da bata wani cin abinci sai gata ta cinye
abincin nan tasss naman kawai ta ci kadan ta bari don ita cin nama aiki ne a
wajenta, kai ta yage yage kana bata baki da maiko, ta bude chilled chivita dake
leda shi ma kadan ta sha sannan ta ajiye, Sai a sannan ta fara gani dai dai ta
daina jin jirin da take ji, fitowa khalil yayi daga bandaki ya dinga kallonta da
mamaki, can yace "Amma wa yace maki naki ne da kika dauka kika ci?" Ko kallonsa
bata yi ba balle ya sa ran amsa, sai kuma ta mike ta wuce ta gabansa ta tafi jikin
window tana kallon waje da motocin dake ta tafiya saman titi, waii lallai ta
jinjina ma yan kauye, Allah Ubangiji ya kawo masu mafita. Tana jin ya fita daga
dakin ta juyo a hankali ta dawo gefen gado ta zauna tana tunanin irin rayuwar da
tayi na kwana biyu kacal, ita kanta tasan ta rame kuma ta yi baki, tashi tayi daga
karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana sallan Magrib,
banda Aliyu babu wanda ke ranta, ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ta murda
taji a kulle, dawowa tayi ta fada saman gado ta lumshe ido, nan da nan bacci ya
dauketa......




*Nihad* is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via👇🏻



✍🏻
07087865788




Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki
da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai
maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da
boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*


Domin karin bayani ki tuntubi wannan number 👇🏻

✍🏻
+2347057607751

28

A hankali Nihad ta bude idonta ta dalilin sanyin da take ji, at first sai da tayi
imagining cewar ai fa kauyen nan take, a firgice ta tashi xaune tana tattaba daya
side din gadon don wutan dakin a kashe yake, amma taji ba kowa wajen, jin laushin
duvet yasa ta tuna ashe a hotel suke, wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, ta
sauka daga kan gadon tunda hotel din ba bakonta bane ta san inda switch yake, tana
tafiya a hankali ta xagoya xata kunna wutan taci tuntube da mutum ta fada kansa duk
da a zaune yake, da farko tayi mugun tsorata amma tana jin kamshin turarensa ta
gane shi ne, tashi tayi ta dafa bango ta kunna wutan, zaune ta gansa saman darduma
alamar sallah yake, ta zaga daya side din ta kalli agogon dakin ta ga karfe biyu da
minti goma, komawa tayi gefen gado ta zauna tayi tagumi, sai kuma ta tuna bata yi
isha'i ba ta tashi da sauri ta shiga bandaki. Har ta idar da isha'i sallah yake
shima, ta ɗan yi jim kamar xata tashi ta koma ta kwanta can dai kuma kawai ta mike
ta hau sallan nafila, har ta mance rabon da tayi qiyamul lail, sai dai in
mistakenly ta kwana dakin Nihal shine Mumy ke tashinsu su yi sallan dare, don dare
daddaye ne Mumy bata sallan dare, a wannan daren kuma tayi addu'a sosai a kan Allah
ya toni asirin duk wanda yayi ruining happiness dinta cikin gaggawa, abinda bata
ta6a yi ba tun da abun ya faru, daga karshe tayi addu'ar Allah ya sa khalil ya rabu
da ita na har abada don ita ba class dinsa bace, sannan baxata ta6a zama da shi a
matsayin mijinta ba, ta kuma yi addu'an bayan Khalil ya rabu da ita Allah ya
mallaka mata Aliyu, wajajen karfe Uku da rabi ta fara jin bacci, ta ɗan saci kallon
side dinsa, yana zaune saman darduma shi ma da alamar ya idar, amma kana kallonsa
xaka san yayi nisa tunanin da yake, and he look so distressing, dauke idonta tayi
daga kansa tayi kwanciyarta saman inda tayi sallan, har dai bacci ya dauke wajen
karfe hudu bata ga alamar Khalil xai kwanta ba. Da asuba loudspeaker din masallacin
dake hotel ne ya tasheta, bata gansa a dakin ba alamar ya tafi masallaci, bayan ta
idar tana zaune saman darduma tana azkar ya shigo dakin, ba tare da ya kalleta ba
ya shiga bandaki, tana ta zaune kan darduma taji ring din wayarsa kallon gaban
madubin tayi da sauri don bata san wayar na nan ba, kuma bata ta6a jin wayarsa na
ring ba sai da vibrate, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi gaban madubin, Mami
ta gani gaban screen din karamar wayar, ta dauka kenan kawai ya bude bandakin ya
fito da sauri ya nufota yace "Keee" Ba karamin rikicewa tayi ba ta juyo wayar na
hannunta, zaro ido tayi ta saki wata er kara ganinsa daure da towel ta durkushe
kasa ta rufe fuskarta da gwiwanta a tsorace, yana isa inda ta durkusa ya warce
wayarsa a hannunta ya koma bandakin, duk da taji rufewar kofar bandakin taki dago
kanta, bayan kusan minti daya ta dago a hankali tana kallon kumfan da ya sa mata a
hannu wajen warce wayarsa, turo baki tayi ta mike jiki a sanyaye ta koma can daya
side din gadon ta kwanta tare da juya ma kofar bandakin baya. Tana ji ya fito daga
bandaki bayan kusan minti sha biyar sai kuma ta ji ya fita daga dakin gaba daya.
Wajen karfe takwas ta gaji da kwanciya ta tashi ta zaga ta shiga bandakin, wanka
tayi ta fito bayan ta goge jikinta ta maida kayan da ta cire, tana zaune gefen gado
ta jinginar da kanta da gadon tana kallon Tv duk da hankalinta baya kan kallon ya
bude kofa ya shigo dakin, tunda ta kallesa sau daya bata yarda ta sake kallonsa ba,
ta dai ga ya canxa kaya, shi kam bai kalli inda take ba ya dau towel din da ta
yasar saman gado ya shigar da shi bandaki ya fito, ya dauko magungunan da ya siyo
mata jiya dake yashe kasan dakin ya jefa mata gefenta ya hade rai yace "Wato dama
lafiyarki qlau kika sa naje chemist nayi asaran kudina ko?" Ba tare da ta kallesa
ba tace "Kudin babana dai" kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace "Gaskiya ne,
kudin babanki ne, sai ki taso mu koma can garin kiyi kumallo a can gidanmu, kinga
can ai kudin babana ne ba na baban wani ba" Kallonsa tayi da sauri, ganin hada
abubuwansa dake dakin kawai yake, tayi karfin halin cewa "Wani garin xan je in yi
kumallo?" Ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace "Ina jiranki a waje" Ta fashe
da matsanancin kuka tace "Ni wallahi baxa ka maida ni wannan garin ba, wai kai baka
tsoron Allah ne?" Juyowa yayi ya rungume hannu ya jingina da kofa yace "Sai ke"
Cikin kuka tace "Allah baxan je ba, kaji har na rantse, dama ba kwana biyu kawai xa
mu yi ba? To wllh baka isa ka maida ni ba" Yace "Ohk, xan nuna maki kuwa na isa,
sannan in mun koma sai mun yi wata daya kafin mu bar garin, kinga baxa ki kara min
gorin kudin babanki nake ci ba" Cikin tashin hankali tace "Kaga don girman Allah
kayi hakuri ka daina ce min haka, wallahi in ka sake maida ni kauyen nan xan iya
mutuwa kawai" Khalil yace "Toh mu je a ga adadin kwanakin da xaki iya a can din
kafin ki mutu" Cikin kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri"
Shiru yayi na few seconds, sai kuma yace "Ohk, baxan maida ki garin ba amma da
sharadi" Tana goge idonta tace "Ina ji" Ya fi second talatin yana kallonta kafin
yace "Nasan komin daren dadewa xa mu rabu... Don haka idan Allah ya kai mu lokacin
ina son ko me xai faru baxa ki fasa nuna ma iyayenki cewar ke kika bukaci mu rabu
ba ni ba....." Nihad dake ta kallonsa da mamaki tace "Toh me yasa yanxun baxa mu
rabu ba kawai, kuma wallahi babu wanda xan gaya ma, kaga babu wanda xai sani sae mu
biyu" Yana kallonta yace "Ohk ta yaya kike tunanin xa mu rabun yanxu?" Ta gyara
xama tace "Kawai kace ka sakeni, babu me sani sai ni da kai" Yace "Toh idan aka yi
hakan sai me xai faru?" Ta daga kafada tace "Ba komai, kawai kayi rayuwarka inyi ta
wa, ni xan ma iya bar maka gidan gaba daya kawai sai dai in dinga xuwa diban
kayana, idan kana so ma sai ka saka yan haya ka dinga karban kudin kana xubawa a
aljihu" Khalil ya ɗan yi murmushi ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, sai ki ci gaba da
iskancinki daga inda kika tsaya kenan ko?" Tayi masa wani kallo tace "Me kake nufi?
Ni nake yin iskanci? Kana nufin ni yar iska ce?" Yayi wani murmushin takaici yace
"Toh baxan yi abinda kike so yanxu ba, kawai dai ki sa a ranki lokacin hakan na
zuwa, nan ba da dadewa ba" Ta kyabe baki tace "Ni fa lokacin da kake nufi da yanxu
duk daya ne ni a wajena" Ya daga kafada yace "Gwara dai a jira lokacin" Ita dai
bata kuma cewa komai ba amma a ranta tunani take ashe ma ba wani babban sharadi
bane, dama ita ai babban burinta su rabu na har abada, Ta kallesa tace "Ka dai yi
alkawarin rabuwa da ni??" Yace "In sha Allah" Wani farin ciki taji ya rufeta tace
"Toh nima in sha Allah ko ma me xai faru xan ce nice nace mu rabu babu ruwanka"
Yace "Toh" Tace "Toh nima ina da deal dina in har kana son inyi abinda kace nima
sae kayi abinda nake so" Yace "Ina sauraronki" tana gyara zama tace "Na farko ina
son ka bar ni in ci gaba da xuwa makaranta na, na biyu baxa ka hana duk wanda xai
zo wajena xuwa ba, like kawayena infact everybody, na uku xaka bani spare key na
gida nima, sannan na karshe ina son ka bar ni da wayata..." Kallonta kawai khalil
yake, ta langwabar da kai ta wara ido tace "Ehh, ni gwara nawa minor request ne,
babu abinda xai ragu a jikinka idan kayi accepting, naka request din kuwa kilan har
tsine min xa a iya yi a gida amma kuma ban damu da hakan ba na amince xanyi yanda
kace" Khalil yace "Abu biyu kadai xan iya maki a abubuwan da kika ce, idan kuma
kinga hakan bai maki ba kawai a bari, mu ci gaba da zaman mu yanda muke, kuma dole
a titi ace maki matar drivern gidanku" Ta marairaice sai kuma tace "Toh ina ji, ka
gaya min abu biyun" Yace "Babu xancen xuwa makaranta sannan baxa ki rike waya
ba!!!" Shiru Nihad tayi tana nazari, wato kawayenta xa su iya xuwa gidan sannan xai
bata makullin gida, daga kai tayi ta kallesa taga kallonta yake yana jiran jin me
xata ce, tace "Toh ai shikenan, na amince" Yace "Sannan abu na karshe wanda
muhimmancinsa kusan daya da sharadin farko...." Tace "Ina jin sa" Yace "Babu ke
babu kallon inda wayata take balle ki ta6a, a takaice babu ruwanki da wayana har
xuwa lokacin da xa mu rabu" Nihad ta kyabe baki tace "Toh dama ni meye ruwana da
torchlight phone dinka bawan Allah??" Ya gyada kai yace "Toh" Juyawa yayi ya fita
daga dakin, ta mike ta dau ledan magungunanta ta saka Hijab sannan ta bi bayansa. A
reception ta tarar da shi ya bada makullin dakin ya fita compound din hotel din ta
bi bayansa, wani ma'aikacin hotel din ne irin masu share share ya ganta yace "Ahh
Hajiya kwana biyu kin buya, ya kawayenki" Nihad ta juya ta kallesa, murmushi tayi
tace "Lafiya lau ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, yau baku zo da kawayen naki ba
kenan? Naga kullum tare ku ke" Sai kuma ya kalli Khalil dake tafiya yace "Au ashe
da oga ku ke...." Katse sa Nihad tayi da sauri tace "Aa, drivern gidanmu ne, ya
kawo ni in amshi sako wajen wani" Murmushi kawai Khalil dake tafiya xuwa inda ya
ajiye mota yayi ba tare da ya juyo ya kallesu ba, Ma'aikacin ya fasa gaida Khalil
da yayi niyyar gaidawa, sai kuma yace "Allah sarki ni na zata oga ne ae nagansa
kalarki, to na gaisheki Hajiya" Bude jakarta tayi taga dari biyar ta zaro ta mika
masa, ya amsa da ladabi yana mata godiya, tuni Khalil har ya kai gun mota ya bude
driver seat ya shiga, Nihad ta karasa ta bude back seat ta shiga ta kulle, har suka
isa gida bai ce mata ba bata ce masa ba, bayan yayi parking ya sauka ya tafi ya
kulle gate, sannan ya nufi entrance din gidan ya bude kofar main parlor, Nihad dake
ta tsaye tana jiran ya xo ya bude ta kyabe baki ta bi bayansa suka shiga parlon,
wani ajiyar xuciya ta sauke direct ta nufi dakinta. Bacci sosai Nihad tayi bayan ta
shiga dakinta, wajen karfe sha daya da rabi ta farka ta dalilin yunwan da take ji,
a hankali ta mike ta shiga banɗaki tayi wanka ta wanke baki sannan ta fito, bata
gansa a parlor ba har ta nufi dakinsa sai kuma ta fasa bude kofar ta dawo parlor ta
zauna tana jiran ganin fitowarsa bude kofar parlor aka yi ta juya da sauri, taga ya
shigo parlon rike
da leda kallo daya yayi mata ya dauke kai ya karaso cikin parlon, a takaice tace
"Makulli xaka bani xan fita in siyo kayan miya, sannan anjima xan je kasuwa siyo
atamfofi don na kyautar da duk kayana a can garinku" Ya girgiza kai yace "Baya daga
cikin sharadinmu, duk me kike bukata xa a siyo a ajiye maki" Ta kyabe baki tace
"Toh a fita a siyo min kayan miya" Cike da isa tayi maganan, yace "Sai sanda nayi
niyya" Yana gama fadin haka ya ajiye ledan hannunsa ya nufi kitchen don dauko
plate, bin sa tayi da kallo yana shiga tayi saurin dauke ledan abincin nasa ta
shige daki da sauri ta sa makulli, shinkafa ne da miyya da yaji uban nama sannan ga
coslow a wani karamin takeaway din, ga ruwan roba me sanyi da drink, tayi er dariya
ta gyara zamanta ta dau cokali ta fara cin abincin. Wajajen karfe uku Nihal ta kira
Khalil, bayan sun gaisa yace "Kin dawo lafiya?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha
daya, yaushe xa ki zo ganin er uwar taki?" Nihal tace "Shine dama nake son in ce
mata xan zo yau, ka kai mata wayar pls" Yace "Xan gaya mata, Allah ya kawo ki
lafiya" Tace "Ameen" daga haka ya katse wayar, tun da Nihad ta shige masa da abinci
daki bata sake fitowa ba, don bayan ta ci ta koshi ma ramuwan baccin da bata yi a
kauye ba ta ci gaba da yi. Wajen karfe biyar Nihal ta iso gidan, Khalil ne ya bude
mata gate bayan ta kirasa a waya ta sanar masa tana bakin gate, ta sunkuyar da kai
ta gaishesa ya amsa da murmushi yace "How are you Nihal?" Ta daga kai ta kallesa
tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha Allah" Tana biye da shi suka shiga parlon gidan,
ganin ta zauna a parlon ya daga kafada yace "Tana can daki, ki shiga" Nihal tace
"Ko zaka dan mata magana ta fito" Yace "Aa, just go in" Mikewa tayi ta nufi kofar
dakin da ya nuna mata, a hankali ta kwankwasa kofar, Nihad ta juya tana kallon
kofar, to me xai ce mata yake mata Knocking, can dai ta mike ta nufi kofar ta bude
a hankali, ido hudu suka yi da Nihal, wara ido tayi ta rungumeta tace "Yaushe kika
dawo Nihal?" Nihal na Murmushi tace "3 days ago" Sai kuma Nihad ta hade rai ta koma
cikin dakin, Nihal ta bi ta da kallo sai kuma ta bi ta cikin dakin ta kulle kofar,
Nihad tace "Wato ke har xa a iya hada baki dake a cuceni ko Nihal? Ni nasan babu
yanda xa ayi kice baki san komai a kan abin nan da Abba yayi min ba" Innocently
Nihal tace "Wallahi ban san komai ba Nihad, kiji har na rantse" Nihad tace "Toh sai
aka ce maki yarda xan yi da ke? Bayan nasan har tadi ku ke yi da drivern nan a waya
amma kice baki sani ba?" A hankali Nihal tace "Allah ne shaida na, amma meye ribata
idan nayi maki karya?" Nihad ta tabe baki tace "We have already sort out things da
shi daxu da safe, and we are okay with our plan" Nihal tace "What plan?" Nihad tace
"Ba sai kin ji ba, ina umma?" Nihal ta mika mata wayarta tace "Tace in na xo ki
kirata" Murmushi Nihad tayi ta amshi wayar ta tafi can karshen gado ta hau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login