Showing 261001 words to 264000 words out of 268471 words
Nihal sallama ta ajiye wayar
tana kallon agogo dake nuna karfe biyar da yan mintuna, ko awa daya bai yi da fita
ba ya dawo, downstairs ta sauko ta tafi kitchen don saka masa abinci kafin ya shigo
cikin parlon, tana cikin hada masa abincin sai ga shi ya shigo kitchen din ya kulle
kofar yana kallonta daga sama har kasa saboda kananun kaya ne a jikinta yace "Kin
yi baƙi fa a parlor" Ta ɗan buda ido tace "Baƙi? Su waye?" Yace "Idan kin fito zaki
gansu...." Tace "Plss hijab dina a sama" Yace "Ohk, let me get you" duba tuwon da
ya rage tayi taga babu yawa, sai ga shi ya dawo ya mika mata Hijab din, Tace "Su
nawa ne?" Ya ɗan juya ido yace "Just 4" a hankali tace "Abincin ba shi da yawa
balle in basu, sai dai drinks" Yace "Ki hada masu har nawa ki basu" Ta zaro ido
tace "Sai kai kaci me?" Yace "Zan hakura in sha tea" Tace "Aa wallahi, kawai mu bar
su haka" Dariya yayi yace "Toh shikenan mu je" Ita ta fara fitowa daga kitchen din
ya bi bayanta, Still tayi a parlon tana kallon wa enda ke zaune da mugun mamaki, ta
wani doka uban kara da gudu ta tafi ta rungume Aunty Jamila cike da farin cikin
ganinta tace "Aunty yaushe ku ka zo?? Nobody told me u people are coming wllh" Ta
gefen ido Inna da ta hakikance a kan kujera take kallonta, Aunty Jamila na murmushi
tace "Ni dai daga ni... Ba gashi kin ganmu ba ko da ba a gaya maki mun zo ba" Nihad
ta rasa inda zata sa kanwar mum dinta don farin ciki, can tace "Don Allah Aunty me
yasa baku ce min za ku zo ba in maku special girki, kuma mun yi waya da Mumy ma
bata gaya min ba" Inna sai girgiza kafa take a parlon, Kamila kuwa sai kallon Nihad
take ganin yanda ta wani cicciko sannan tayi wani mugun haske tayi kyau kamar ba
ita ba, gaba daya Kamila ta kasa daina kallonta, kai kana ganinta kasan ta samu
kwanciyar hankali over, Aunty Jamila tayi kasa da murya tana tura Nihad da ta daura
hannunta saman cinyarta tace "Wai baki da hankali ne, baki ga su Inna ba?? Baza ki
je ki gaishesu ba" Da sauri Nihad ta juya sai kuma ta mike da gudu cike da farin
ciki ta nufi Inna da nufin rungumeta, Inna ta daga mata hannu da sauri ta dakatar
da ita ta tsuke fuska tace "Aaa, gaskiya har yanzu ban gama dawowa dai dai daga
wujijjigar mota ba, dama in za mu koma ma ai sai dai Jirgi, koma gun Jamila ai ita
kadai kika sani" Nihad ta turo mata baki ta tafi wajen Hajiya Hauwa ta durkusa
gabanta ta gaisheta da murmushi fuskarta, Hajiya Hauwa ta amsa tace "Fatan mun same
ku lafiya Nihad?" Nihad tace "Alhmdlh Ummi, ya su Billy?" Hajiya Hauwa tace "Duk
suna gaisheki" Nihad ta kalli Kamila da ta mayar da ita TV sai bin ta take da kallo
ganin har da wani hips da Butt tayi, Nihad tace "Aunty ina wuni" Kamila ta sauke
boyayyen ajiyar zuciya tace "Lafiya lau Nihad, ya gida?" Nihad ta sunkuyar da kanta
tace "Alhamdulillah, ya su Umma" Kamila tace "Lafiya lau, duk suna gaisheku" Mikewa
Nihad tayi ta koma kitchen da sauri duk suka bi ta da kallo, Inna tace "Tunda mun
zo mun ga gida har mun gaisa to a zo gaskiya a maida mu inda aka dauko mu, na fi
gane ma can" Aunty Jamila ta kalli Inna tace "Don girman Allah ki rufa mana asiri
Inna, duk wannan abinda kike yi wllhi bashi da amfani" Inna tace "Kar ki gaya min
maganar banza Jamila, banda marigayi da ya haifi Nihad din har ya aura mata Halilu
a gidan ubanwa za ku hadu da wannan daular har ku bar duniya? Ta dalilin jikata ce
fa har ku ka samu matsayin barin Najeriya, to ahir kar ki kawo min raini" Ita dai
Hajiya Hauwa ta ja bakinta tayi shiru, Kamila tace "Ai gaskiya Aunty Jamila ta
fada, mu dai ba duk inda aka bamu masauki nan za mu zauna ba, ina mu ina zabar inda
za mu zauna" Inna tace "Toh wallahi sai na zaba na darje, kuma ban ga masaukin da
zan zauna da ya wuce gidan Janar ba, banda lalacewa ina matsayin kaka ina ni ina
zama gidan yara? Kuma ai inda muka fara sauka nan ne masaukinmu a shari'ance ma,
kawai kawai ku yi ta abu ba wayewa kamar kauyawa, maimakon ku yi komai kanku tsaye
irin na wayayyu" Kamila tace "Ga ki ga gidan Janar din ai sai ki bi hanya ki koma"
Inna ta kunduma mata zagi tace "Dama na ji takaicin taho da ke da aka yi kawai na
ja bakina ne nayi shiru bance komai ba, amma banyi farin cikin biyomu da kika yi ba
wllh" Hajiya Hauwa tayi kasa da murya tace "Don girman Allah a bar maganar nan
Inna, gidan surki ne fa" Inna na huci tace "Toh nayi shiru" Nihad na shiga kitchen
taga Khalil ya cika masu tray da ruwa da lemo, tace "Yauwa my dear" Yace "Yanzu za
a basu abincin ko baza a basu ba?" Dariya tayi taki ce masa komai ta dau tray din
ta fita, ta kai masu parlor, ita dai Inna duk hankalinta yayi gidan Janar, kafin
Nihad ta koma kitchen din har ya sa masu abincin a plate, yace "Zan ɗan fita in
siyo abu yanzu, sai ki zaga da su gidan idan suka gama cin abincin" Nihad tace
"Toh" Daga haka ta dau abincin ta kai masu parlon, Khalil ya fito shi ma yace masu
yana zuwa sannan ya bar gidan, Duk yanda Nihad tayi da su Aunty Jamila su ci
abincin kin ci suka yi, wai sun ci abinci kafin su fito, Inna dai ta nemi plate ta
saka rabin tuwon da miyar vegetable ta debi isasshen nama ta zuba lemo a cup, Aunty
Jamila ta kyabe baki ta dauke kai, Nihad ta mika tace "Aunty mu je sai ku ga ko
ina" Sama duk suka wuce gaba daya har da Kamila da Hajiya Hauwa, dakin Khalil ne
kadai Nihad bata shigar da su ba, amma har parlonsa ta kai su, Kamila na nuna kofar
dakin tace "Shi kuma wancan fa?" Murmushi Nihad tayi ta sunkuyar da kanta bata ce
mata komai ba, Hajiya Hauwa tayi dariya tace "Dakin mijinta ne, kuma dama bai
kamata ma mu shiga ba, maa sha Allah gida yayi kyau Nihad, Allah ya sa gidanki ne
na har abada, Ya sa ki zama tsohuwar gida" Kamila tace "Ameen" Downstairs suka
sauko ta nuna masu dakin dake kasa da bandaki, sannan kitchen, dama dining area din
is open kuma sun gani, Sosai Aunty Jamila taji dadin yanda suka samu gidan so neat,
kuma ko ina kamshi yake, da Nihad ta san da zuwansu babu abinda zai hana ta cewa
sai da taji za su zo ta gyara ko ina, amma tasan Khalil bai gaya mata ba, Duk suka
dawo parlon Inna har ta handame tuwon ta koma gefe ta zauna, Hira suke ta yi a
parlon amma Inna bata cewa komai, can dai tace "Amma fa kada magariba tayi mana a
nan Jamila ki kirasa ki ji inda yake, tafiyar magariba babu dadi wallahi" Kamila
tace "Toh wai idan nan din za mu kwana fa? Kika san yanda suka yi da mamarsa?" Inna
ta kalleta tace "Kamila kike ko Kamilu? To wllhi ki fita harkata a kasar mutane
kada in maki tijara, ina ruwanki da lamarina ne komai nace sai kin tsomo min
bakinki me wari? A garin gaɓa gaɓa aka haifemu da za mu yarda mu kwana a gidan yara
kanana? Wannan ai sai ace lalacewa ta samemu, mu wallah bama haka a al'adanmu, ku
kira min Halilun ni in masa magana da kaina" Nihad tace "Toh meye a nan din da baza
ku kwana ba Inna?" Inna tace "To ai ni ba er iskar kaka bace da zan kwana cikin
yara" Kamila tace "Toh sai a kama maki hotel kawai, mu mu kuma sai mu kwana a nan,
washegari kuma mu tafi tashar motar" Inna ta dinga kallon Kamila alamar ta ma rasa
abinda zata ce mata, can dai tace "Ni dama ban taɓa mamakin mutuwar aurenki ba,
halinki ya kashe maki aure, shi ne zaki zo ki kashe na er uwarki saboda baƙin ciki,
to da wanda ya bada shawaran a taho dake, da wanda ya daure ma shawaran taho dake
kugu, dake kanki da kika biyo mu duk Allah ya isa tsakanina da ku bam yafe ba"
Nihad ta fashe da dariya har da kyakyatawa, Kamila dai ta kyabe baki ta dauke kai,
shigowar motar Khalil gidan ya sa hankalin Inna ya kwanta, yana shigowa parlon tace
"Halilu tafiya da magariba babu dadi wallahi, naga kuma karfe shidda har ya gota"
Yace "Inna baza ku kwana a nan ba?" Tace "Haba Halilu, sai kace tabaɓɓiya, ai da
kunya in kwana a nan, ni dai a nemo min duk inda zan kwana amma banda gidan nan"
Kamila ta bude baki a ranta tace sannu Mumy, shi dai Khalil murmushi kawai yake,
Kamila tace "Toh ko a sama maki hotel Inna?" Inna ta juya da sauri tana kallon
Kamila amma ta kasa cewa komai, Aunty Jamila sai danne dariyarta take, ita kanta
Hajiya Hauwa sai murmushi take, Khalil yace "Toh kawai bari a maida ke can gidanmu
Inna" Inna ta sunkuyar
da kai tace "Toh" Aunty Jamila tace "Mu kam zaka ajiye mu a gidan Hajiya Safeenah"
Da mamaki yace "Aunty me yasa baza ku kwana a nan din ba" Ita dai inna har ta mike
ta zuge zip din jakarta ta rataya ta nufi kofa, Aunty Jamila tace "Aa mun yi da
Hajiya Safeenah za mu je can gidan nata" Yace "Ku bari sai gobe kawai Aunty" Aunty
Jamila tace "Mun fa ga gida Khalil, Allah Ubangiji ya sanya Alkhairi, ya baku zaman
lafiya, kuma goben in sha Allah da safe za mu koma" Nihad taji ba dadi ganin da
gaske baza su zauna ba tafiya za su yi, nan da nan mood dinta ya canza, tana ji
tana gani suka bar gidan ta dawo parlor tana kuka a hankali. Bayan magrib Khalil ya
dawo gidan, yana dawowa kuma ya sa ta shirya suka tafi asibiti, da yake asibitin da
yake aiki ne kafin ya samu matsala da Abbansa nan da nan suka yi attending masu,
bayan kusan awa daya da zuwansu asibitin Khalil ya shiga ward din da Nihad take
kwance tana ta game da wayarta, tun bayan da aka dubata take wajen a kwance, ta
juya tana kallonsa har ya karaso kusa da gadon ta mike zaune a hankali tace "Are
they done?" Shiru kawai yayi yana kallonta, ta kamo hannunsa tace "Kayi shiru"
Zaunawa yayi gefenta ya sakar mata murmushi drawing her closer to himself murya can
kasa yace "I love you wife" Ta lumshe ido tace "I love you too" Yace "We can go
home now" mikewa tsaye yayi ya taimaka mata ta sauko daga kan gadon sannan suka bar
asibitin. Washegari Janar ya biya ma su Aunty Jamila flight za su koma kano amma
banda Inna, Flight din karfe daya ne na rana don haka karfe sha daya da rabi Khalil
ya tafi da Nihad can gidan don tayi masu sallama, a bangaren Hajiya Amina aka masu
masauki, ganin kowa ya gama shiryawa banda Inna Nihad tace "Inna ke baki shirya
ba?" Inna ta kalleta tace "Ai ba gidan Halilu nake ba da zaki min wannan tambayar
Nihad, kuma Janar din da kansa yace in zauna in ɗan kwana biyu in kara hutawa kafin
in koma, ni da ce masa nayi aa amma ya dage, da kyar dai na amince don dai kar
mutum yace baka ji maganarsa ba" Kamila tayi dariya tace "Lallai kam" karfe sha
biyu da wani abu aka kai su Aunty Jamila Airport, Nihad taji kamar ta bi su taje
taga Mumy, haka ta dinga daga masu hannu har suka shiga airport din, sannan Khalil
ya koma can gida da ita. Dakin Mimi Nihad ta tafi, shi kuma Khalil ya tafi bangaren
Maminsa, ita kadai ya samu a parlor tana kallo ya zauna yace "Innan fa" Mami tace
"Yanzun nan ta tafi taje tayi wanka" Yace "Ohk" Tace "Yanzu yau za ku tafi da kayan
nata gida?" khalil yayi shiru sai kuma yace "A dai bari ko zuwa gobe Mami" Mami
tace "Allah ya kai mu" Yace "Kwana biyu ma bata jin dadi tana lower abdominal pain"
Mami tace "Subhanallahi to dubata kayi ko asibiti ka kai ta?" Yace "Jiya da daddare
muka je asibiti, an yi mata Ultrasound sound scan and they found out she is 3
months pregnant" Mami ta dinga kallonsa with confusion, tace "Pregnant kuma?" Yace
"Yeah, i think she miscarried just one baby, dayan na nan" Mami da ta kasa rufe
baki tace "Ikon Allah, kai kuma kana matsayin likita duk baka ga hakan ba sai da ku
ka je asibiti?" Ya ɗan yi murmushi yana shafa kansa yace "Ni sai jiya naga symptom
shi yasa ma na kai ta asibiti amma ban taɓa lura ba" Mami tace "Toh Allah Ubangiji
ya raya mata wannan, Allah ya kara mata lafiya, maa sha Allah" Yace "Ameen" Mami
tace "Amma kuma tana cin abinci?" Yace "Tana cin komai, kuma babu aikin da bata yi,
there is nothing like sign of the pregnancy fa" Mami tace "Toh gaskiya ta rage
aikin ko ma ta bar yi gaba daya kar a samu matsala tunda kace tana ciwon mara, idan
baza ka samar mata me aiki ba sai Mimi ko Hanan suje su taya ta zama for sometimes
don a dinga taimaka mata da aikin gidan, don Noor ba wani abun kirkin da zata
taɓuka" Shi dai yayi shiru bai ce komai ba. Basu bar gidan ba sai wajen karfe
takwas na dare bayan Mami ta basu abinci su tafi da shi a warmer, Nihad har mamakin
yanda Inna ta saki jiki a gidan kamar ta taɓa zuwa take, ko aike zata yi a dauko
mata abu a bangaren Hajiya Amina sai dai tace aje bangarenta a dauka mata abu kaza,
kayanta kala biyu dama har ta jera cikin Siff, ga atamfofi kala biyar da Mami ta
bada a dinka mata don ma Mami ta bata dogayen riguna sababbi irin na Saudi.... A
kwana a tashi babu wuya wajen Allah sai ga cikin Nihad ya kai har wata biyar, Duk
watanni biyun nan Hanan na gidanta babu abinda bata mata, sai Nihad taga yanda Mimi
take haka Hanan din ma take bata da matsala kwata kwata, she is kind and nyc to be
with, a zaman Hanan tare da su kuma Hajiya Amina ta zo har sau biyu, kuma Khalil
bai taɓa nuna mata komai ba zai zauna su yi hira sosai in ta tashi tafiya kuma shi
zai kai ta tasha don a kaduna take rayuwarta, ya kuma hadata da kudi not less than
50k, Satin Inna biyu a gidan Janar aka yi mata passport suka tafi Makka tare da
Mami su yi Umra, Mami ta so tafiya da Nihad amma saboda condition dinta sai bata ma
kawo ma Janar batun ba, suna dawowa Umra kuma da yake ta kano suka sauka Mami ta
kai Inna har gida, bayan tafiyar Mami Inna har da matsar kwalla don gani take kamar
an dawo da ita wani kauye ne.... Cike da farin ciki Nihad ta gama hada kayanta kala
hudu zata Kano tare da Khalil da Hanan don yau Mumy ke fita takaba kuma a yau din
mutanen Ayman za su zo nema masa auren Nihal, tun a daren jiya suka tafi gidan
Janar suka sallami Mami, don haka karfe tara na safe suka kama hanyar airport don
jirgin karfe sha daya ne. Nihad bata damu da condition dinta ba tana shiga dakin
Mumy ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mumy ta janyeta tace "Ke baki da
hankali ne?" Aunty Jamila da Aunty Suwaiba suka rike haɓa suna kallonta, Aunty
Suwaiba tace "Aa babu alamar hankali kam a nan Yaya" Nihad ta zame kasa tana dariya
tace "Wallahi nayi missing dinki Mumy" Sai kuma ta kalli Aunties dinta tace "Au
dukkan ku nayi miss" Murmushi kawai suka yi, nan ta gaishesu gaba daya, Hanan ta
shigo dakin da sallama duk suka amsa mata, ta durkusa saman Carpet ta gaishesu suka
amsa mata da fara'a suna tambayarta ya hanya.... Mumy na ce ma Nihad taje ta gaida
Umma bata mata musu ba ta mike ta fita zuwa bangarenta, tana shiga parlon taga ana
ta hada kaya, Ta gaida Kamila dake parlon, Kamila ta amsa tace "Kun zo lafiya?"
Nihad tace "Alhamdulillah" Sai ga Umma ta fito, Nihad ta dinga kallonta don kamar
ba ita ba ta rame sosai ba kadan ba kamar bata taɓa jiki a rayuwarta ba, Nihad ta
gaisheta, Umma ta amsa da fara'a tana tambayarta Khalil, Nihad tace "Sai anjima zai
shigo" Umma tace "Toh sannunku da zuwa" Nihad dai tayi shiru, can dai ta kasa
daurewa tace "Ina za aje da kayan?" Umma tace "Kaduna zan koma wajen yayata" Nihad
tayi shiru tana kallonta, Bayan wani lokaci cikin sanyin murya Umma tace "Toh duk
dai abinda ya faru a rayuwa rubutattce ne daga Allah, duk wayon ka da dubaranka
idan Allah ya rubuta ga kaddararka babu yanda zaka yi ka tsallake ta, sai in Allah
yayi ka me yawan ibada da addu'a sannan kuma me tsoronsa, sai ka ga Allah ya sauya
maka kaddararka mara kyau zuwa me kyau, to mu kam Allah Ubangiji ya yafe mana kura
kurenmu, ya sa mu yi tabbataccen tuba kafin mutuwa, sannan ina neman afuwanki
Nihad, ki yafe min...." Da sauri Nihad ta girgiza kai tace "Ni na yafe maki tuntuni
Umma, Allah ya sa mu dace duniya da lahira" Umma ta share hawayen da ya taru idonta
bata dai ce komai ba, babu yanda Mumy bata yi da ita kan ta zauna gidan ba amma
taki don in har ta ci gaba da zaman gidan nan tasan conscience will neva allow her
have peace of mind, a kullum sai abubuwan da suka faru a baya sun dawo mata,
memories iri iri sun ki barin ta na gidan, har inna dake koranta a baya sai da ta
sa baki ta zauna amma taki tace gwara ta koma gun yayarta kawai sai ta dinga kawo
masu ziyara, Kamila da Nihal kuwa su zauna gun Mumy, zata tafi da autarta Amina. A
ranan bayan an kawo kudin auren Nihal Umma ta shigo parlon Mumy, ta zauna saman
kujera a hankali tace "Toh Maryam, a yayyafe don Allah...." Inna dake zaune parlon
ta fashe da kuka tace "Kiyi zamanki cikin yaranki kin ki Sumayya" Umma ta girgiza
kai tace "Duk abinda zan masu nasan shi Maryam zata masu har ma fiye da yanda ni
zan masu Inna"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
80
4 months later
Nihad ta fito bandaki Aunty Maryam na biye da ita a baya, Aunty Jamila ce tsaye
jikin press din kayanta tana duba mata kayan