Showing 132001 words to 135000 words out of 268471 words

Chapter 45 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

saboda offense din da ba yin kanta ba, her stepmom is behind all
that happened to her amma bata sani ba ta kuma ki kwantar da hankalinta ta gano
hakan,
makira ce matar kuma azzaluma, ta lalata mata rayuwa ta dora ta a kan abubuwa da
yawa da basu dace ba, wanda ita nata yaran bata basu wannan tarbiyar ba, duk
nutsattsu ne babu na banza a yaranta, farkon faruwan incident din ai mahaifin nata
bai koreta daga gidan ba amma matar nan ta san yanda tayi har ya koreta after
almost one month da faruwar incident din, and i am telling you ba directly take
abubuwanta ba, ni nasan mahaifinta baya cikin hayyacinsa ya koreta daga gidansa,
coincidentally kuma nima na masu sallama xan bar gidan kenan in taho Abuja bayan
Abba ya kirani, kawai naga baxan iya barin ta tafi wani wajen ba, And you know what
Aunty.... bamu ta6a shiri da yarinyar ba duk tsawon xamana a gidan, amma sbda
kirkin mahaifiyarta na tausaya mata muka taho nan Abuja tare" Aunty Maryam ta sauke
wani ajiyar xuciya tace "Dangin mahaifiyarta fa?" Ya girgiza kai yace "Babu su a
nan" Aunty Maryam tayi shiru cike da tausayin Nihad, can tace "Kai yanzu menene
next plan dinka Khalil?" Ya girgiza kai yace "I don't know Aunt, i am confuse, ban
san ta yanda xan yi convincing Mami har ta zauna nan zuwa sanda mahaifinta xai huce
ba, gashi jiya da daddare ma sai da tace min ta amshi abinda xata amsa yau ta tafi
sbda gobe weekend" Aunty Maryam tace "Kar ma kace mata komai don ba lallai ta
fahimta ba, kawai dai ko da zata sake maganar admission letter din kace still fa ba
a samu ba.... Nihad have to stay here kafin a samu wani solution din gaskiya, she
is too young for this trauma at her age, kishiyar uwarta bata mata adalci ba, gashi
ni kilan nan da sati biyu xamu yi tafiya" Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace
"Aunty to me yasa baxan samar mata admission din ba kawai, sai ta zauna Abujan a
zuwan dai karatu take" Aunty Maryam tace "Eh wannan ma shawara ce mai kyau kuwa,
amma wani makarantar xaka samar mata?" A hankali yace "Nile or Baze University...."
Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonsa da mamaki tace "Did you know the tuition
fees of those Universities kuwa?" Ya ɗan yi dariya yace "Ohhh nawa ne ma?? shi su
Mimi ke zuwa i think?" Tace "In ba dai ko Abbanku ya hada har ita ya dinga biya ba,
tunda kowa ma biya ma kudin makaranta yake ai naga" Khalil yayi murmushi yace "I
will process the admission for her as soon as possible in sha Allah" Aunty Maryam
tace "Toh Allah ya rufa asiri, kaga dai dai kenan ma tunda sabon session xa su
shiga" Bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru tana ta nazarin abubuwa iri iri,
can ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanzu duk wani hanya da xa a bi a gano ta
inda wannan video din nata ya fita babu shi kenan? Ai bai kamata ayi shiru babu
bincike ba, kamata yayi anyi ta bincike har Allah ya sa a gano wanda yayi wannan
ta'asar, duk da babu tantama ni nasan da sa hannun matar ubanta, sannan ina zargin
kawayenta ma, don ta gaya min ko su waye" Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam
tace "Amma tunda har ta iya tashi cikin dare ta kai ma Allah kukanta ni nasan komin
daren dadewa wataran gaskiya zai bayyana, ta yanda komai ya faru duk Allah xai nuna
ya tona asirin koma wanene, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya sa mu fi karfin
zuciyarmu" Sai wajen karfe goma Khalil ya sauko downstairs daga parlon Aunty
Maryam, Babu kowa parlon kasa ya nufi guess room da Nihad take, ya bude kofar dakin
a hankali ya shiga ya ganta kwance tana bacci, for almost 4 days sai yau take bacci
peacefully kuma me nauyi, ya karasa cikin dakin yana kallonta, juyawa yayi daga
karshe ya fita ya kulle dakin. Ba laifi throughout ranan Nihad ta saki jikinta a
gidan Aunty Maryam she really felt at home, Aunty Maryam bata barta ta zauna ita
kadai ba, har fita suka yi tare da yamma ta rakata xata yi siyayya a shopping mall
sae dai ta bata nikaf ta saka saboda yan kwakkwafi masu gane mutum farat daya,
Aunty Maryam ta bata baki sosai a kan kar ta wani damu kanta in Allah ya yarda
asirin wa enda suka mata haka zai tonu, kuma xata ga yanda Allah xai yi da stepmom
dinta, hakan yasa damuwan Nihad ya ragu sosai ta samu relieve, bayan sun dawo daga
shopping Mall din Aunty Maryam ta ware mata nata abubuwan da ta siyo mata ta bata,
Nihad ta amsa a hankali tace "Nagode Aunty, Allah ya saka da alkhairi" Daki ta kai
ta dawo ta zauna parlon, Aunty Maryam na ba Mus'ab dinta abinci Nihad tayi kasa da
murya tace "Aunty don Allah xaki iya ara min wayarki in kira Mumyna?" Aunty Maryam
ta dau wayar ta mika mata, Nihad tayi dialing number Mumy sannan ta kirata, lkci
daya jikinta yayi sanyi jin wayar a kashe, ta mayar ma Aunty Maryam tace "Wayar a
kashe yake" Aunty Maryam tace "Anjima sai ki sake trying" Nihad tace "Toh" Wayar
Aunty Maryam ya fara ring ta dauko ganin Mami ce ke kiranta ta daga, bayan sun
gaisa Mami tace "Ya ake ciki ta amsa kuwa Maryam?" Aunty Maryam tace "Kinsan sabon
session ne Mami, so ina jin sai zuwa next week xa su fara badawa gaskiya, har yanxu
bata samu ba kam" Mami tace "Wai wani makaranta ne?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai
sani ba gaskiya" Mami tace "Toh Allah ya kyauta, amma na so ace ko yau ko gobe ta
koma gida" Aunty Maryam tace "Toh tunda Allah bai nufa ba sai mu saurari yanda ya
tsara" Mami tace "Yana nan gidan naki ne Khalil din?" Aunty Maryam tace "Aa" Mami
tace "Ohk tun safe ya fita naga kuma bai dawo gida ba" Aunty Maryam tace "Kilan
yana can gidansu budurwarsa" Mami tace "To a gaida Mus'ab" Aunty Maryam tace "Xai
ji" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Aunty Maryam ta dinga tunanin ta
yanda xa su bullo ma yayartata. Aunty Hassana ce xaune bangaren Hajiya Amina tana
kallonta rai a dagule tace "Yanzu dai kin kara tabbatar da cewar bayan malaman da
fatima ke bi na kasar nan har kasansu ma malamai yi mata aiki suke ko?" Da sauri
Hajiya Amina tace "Aa na yarda wallahi...." Aunty Hassana tace "Wai ni yau yaya zai
buda baki yace in bar masa parlonsa sbda na kawo masa shawarar kar ya tura Khalil
Zanzibar, yaushe har ya dawo gidan balle a san ko ya sauya hali ko bai sauya ba,
har zai kara yarda da shi ya daura sa kan miliyoyin kudinsa, kar ki dada kar ki
raga shine yaya ya hayyako min har yana cewa in bar masa parlonsa cikin tsawa"
Hajiya Amina tace "Toh wai yanzu me malamin yace maki da ku ka yi waya" Aunty
Hassana tace "Ta lalata mana aiki, kuma da tsafi aka lalata aikin" Hajiya Amina ta
rike ha6a tace "Aikin kusan miliyan daya fa?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciyar
takaici tace "Wato an bata sa'ar dai dai sanda xata gaya masa ya shigo gidan babu
wanda xai hanasa, shine ya shigo kansa tsaye asiri kuma yayi tasiri aka xuba masa
ido babu wanda ya dakatar da shi, uban ma ya kasa cewa komai har yanzu shine ya
billo da turasa Zanzibar yayi masa business" Hajiya Amina tace "Toh ni ance ba shi
kadai ya dawo ba, kuma har yanzu ban ga yarinyar da aka ce ya dawo tare da ba,
kinga ai ko yau naje bangaren, kuma har dakin Hajiya Fatiman na shiga kai tsaye ko
yarinyar na ciki amma ban ganta ba" Aunty Hassana tace "Farhana tace fa bata gidan,
tun da suka gane ita ce me wannan video din na kwanaki ya fitar da ita wai daga
gidan, kinga tabbacin tsiyarsa kawai yaje ya tsula a duniya ya dawo, babu tantama
kuma karuwarsa ce" Hajiya Amina tace "Wai daxu baki ga uwar yarinyar da ake son
makala masa ta zo ba kuwa??" Aunty Hassana tayi wani dariya tace "Ai ko zata mutu
baxai auri er ta ba sai dai in har ba Hassana sunana ba, Nadiya take ko wa? Toh
wallahi baxai aureta ba, ba dai dukiyar yayana ake hari ba? to sai dai su gani su
hanga daga nisa, ita fatima ta zaci ta fi kowa wayo shine take kokarin xata makala
masa yar aminiyarta tunda kasarsu daya su hadu su wawushi dukiya ta ko ina su ci
karensu ba babbaka, su yi wandaka son ransu su gayyato jajayen danginsu da abokai
ayi biki a ci uban kudi, to kuwa xan ga ta yaya, don da dai in bari ya auri
yarinyar nan gwara ya dauwama babu auren har ya mutu, yanzu in zai yi auren ai
dukiya ne ba ta wasa ba yaya xai kashe, don har lefe shi xai yi masa, toh kiyi
imagine nawa xai basu su yi lefen, ai miliyan 10 ma albarka" Hajiya Amina tace "To
ke yanzu baxa ki yi ma Malam magana ayi duk yanda xa ayi ya auri ko Farhana ko
Sajida ba? Ai gwara yan gida su mora da yan waje" Aunty Hassana tayi wani dariya
kawai ta kyabe baki bata ce komai ba, Hajiya Amina tace "Allah kuwa da dai ya auri
yarinyar nan gwara anyi haka kawai mu san har yanzu mu ne" Aunty Hassana na girgiza
kafa tana wani Murmushi tace "Ke kin zata a banza ne har yanzu ba ayi auren nasa da
Nadeeyah ba, sai yayi ta ce masu ba yanzu ba har ya bar gidan nan?" Hajiya Amina
tace "Toh yanzu gashi ya dawo ga kuma uwar yarinya har ta fara mana sintirin gida"
Aunty Hassana tace "Xata yi ta gama, baxai auri er ta ba, balle wata kuma can"




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

41

Umma ta shigo dakin da taga Nihal ta shiga for almost ten minutes bata fito ba,
wato dakin Nihad, dube dube ta sameta take yi a dakin, tun da Nihal taga shigowar
Umma ta dakatar da abinda take ta zauna gefen gado, da mamaki Umma tace "Me kike
nemar mata a daki tun daxu?" Nihal dai bata ce komai ba, Umma ta kyabe baki tace
"Ke idan fa kika ce xaki tafi makaranta a haka ba tare da kin saki ranki kin dawo
yanda kike harkokinki da ba to ina me tabbatar maki zaki samu matsala a makaranta
wannan time din, abinda baki ta6a ba, eh ansan er uwarki ce kuma ba dadi to amma so
kike ki targada naki future din ne? Ko damuwar nan ne xai dawo maki da Nihad, to ma
ta dawo ta maki me? yarinyar da ke can kauyen mijinta" Ita dai Nihal bata ce komai
ba still kuma bata kalli Umma ba, Umma ta kara kyabe baki ta karaso ta zauna gefen
gado tace "Ba kwanaki can kina da number shi dreban ba, ni da ma kin kirasa in ji
ko kauyen nasu na nan garin suka tafi ko Zarian ya tafi kauyen uwarsa da yace"
Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace "Ba da ke nake ba kika min shiru Nihal?"
Nihal ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Bani da number sa" Umma tace "Toh amma
ai farooq bazai rasa ba tunda shi ma Allah ya zuba masa shisshigi kira min shi ki
tambayesa yanzu ina jira" Nihal ta dau wayarta tayi dialing number Ya Farooq ta sa
handsfree, yana fara ringing ya daga bayan ta gaishesa tace "Yaya wai kana da
number Khalil?" Farooq yace "Wa ke tambayar numbersa?" Duk da alamar da Umma ta
dinga yi mata kan cewar kar tace ita ce ke tambaya amma Nihal bata kalleta ba tace
"Umma ce" Farooq yace "Noo bani da shi, sai anjima" Tace "Toh sai anjima" Katse
wayarsa yayi, Umma ta hade rai tace "Akan meyasa xaki ce masa ni ce ke nema?" Nihal
tace "Nima na tambayesa Shekaranjiya yace bashi da, don ki tabbatar da hakan yasa
na sake kiransa amma ni nasan bashi da number" Umma tace "Toh ai shikenan, dama wai
da sai mu ji kauyen da suke, in ya kama mu je sai mu je kafin ki koma makaranta"
Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, Nihal ta mike ta ci gaba da duba
takardun da take. Ranan asabar da rana khalil na zaune parlon Mami sai ga kiran ya
Farooq gaba daya ya mance sun yi waya few days ago yace masa xai shigo zaria, Ya
ɗan kalli Mami dake parlon, bai daga wayar ba har ya katse, Ya farooq ya sake kira,
mikewa yayi ya nufi kofa yace "Mami sai later" Daga haka ya fita daga part din gaba
daya sannan ya kira Ya farooq, ya farooq na dagawa bayan sun gaisa ya sanar masa
zai taho zaria from kaduna, Khalil yace "Ohk amma kaga muna gidan wata kanwar
Baabata mun je gaisheta" Farooq yace "A ina kenan?" Khalil yace "A Abuja take"
Farooq yace "Ohk, babu damuwa Usman na Abuja, so xai je inda ku ke in sha Allah"
Khalil bai iya yace masa komai ba da farko, can kuma yayi saurin cewa "Toh Allah ya
kai mu" Farooq yace "Zan tura maka numbersa yanzu ko da xai kiraka" Khalil yace "Ba
damuwa" Daga haka suka yi sallama, kamar ance ya daga kansa ya ga Farhana a tsaye
tana sauraron wayar da yake, ya hade rai yace "Ke ya kika tsaya min a kai?" Bata ce
masa komai ba tana rungume da laptop dinta ta wuce tana ta6e baki, ya bi ta da wani
mugun harara. Khalil na shirin xai fita da yamma sai ga kiran number da Farooq ya
turo masa daxu, wato number Usman, yayi jim yana kallon wayar, can ya daga ya kai
kunne, gaisawa suka yi, Usman yace "Yauwa wani anguwan ne a Abuja?" Khalil ya ɗan
buda ido sai kuma yayi saurin cewa "Bari in tambaye Kanwar Baabar tawa" Usman yace
"Ohk ina jira" Katse wayar yayi yana tunanin abinda xai yi next, bayan ya gama
shiryawa ya fito zuwa bangaren Mami sannan ya kira Usman, yana dagawa yace "Tace
Suleja ne" Usman yace "Ohk, akwai tazara sosai tsakaninmu, amma idan na shirya zuwa
zan kiraka" Khalil ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Toh Allah ya kai mu" Usman
yace "Ba Nihad din wayar mu gaisa" Khalil yace "Idan na shiga gida xan kiraka yanzu
ina waje" Usman yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, Mami da ta fito parlon
tana kallonsa tace "Waye a Suleja?" Yace "Wasu ne" Tace "Ohk" Sannan ta zauna saman
kujera a hankali tace "Ina son za mu yi wata magana da ke damuna Khalil" Ya kalleta
yace "Toh ina ji Mami" Tayi kasa da murya tace "It's High time kayi settling down
son, tun baka bar gidan nan ba almost 2 years ago Abbanka ke maka magana har Allah
ya kaddara tafiyarka, babban burina a rayuwa a yanzu shine in ga kayi aure...."
Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace "Mami kinsan fa she aure lokaci ne, idan time
din yayi sai kika nayi Mami...." Tace "I am not talking about you settling down wai
saboda ina son ka auri Nadeeyah, No son, idan da wata warce kake so daban fine,
present her to us xa mu yi accepting as far as tana da tarbiyya, i can never force
u on marriage son, kar kaga ko Nadeeyah yar aminiyata ce shi sa nake so ka aureta,
a'a idan dai kasan da wata warce kake so da aure go ahead ka nemi aurenta just make
sure yar gidan mutunci ce me tarbiyya ce like i said, sannan she should be from a
reputable family, ka dai san halin Abbanka ai" Khalil yayi murmushi yace "Toh Mami
ai ba ke kika hada mu da Nadeeyah ba, i met her abroad without knowing she is ur
friends daughter, ba ta dalilin ke da Mumy muka san juna da ita ba, kawai Allah ne
ya hadamu..." Mami tace "Haka ne, amma kaga ai yan sa ido gani suke mu muke cusa
maka ita ka aura, don ta Hajiya Safeenah ma ta fi son Nadeeyah tayi aure a can
Yemen tunda danginta suna can, kuma dama ita a can din ta tashi" Khalil yace "In
sha Allah, as soon as i come back from this business trip xan kai ma Abba batun
Mami.... Nima ina son settling down" Mami tace "Toh Allah ya nuna mana, amma kwana
nawa xaka yi a can?" Yace "It depends, but nasan baxan wuce wata daya ba, but duk
sati xan dinga shigowa Nigeria" Da mamaki Mami tace "Duk sati kuma? Me xaka dawo yi
kai da ya kamata ka zauna can har ka gama abinda ya kai ka" Khalil yace "Bana son
xama can har na wata daya, duk weekend xan dinga dawowa" Mami tace "Toh shkkn, amma
ka sanar ma Abban naka?" Ya girgiza kai yace "He said i should do what suite me"
Mami tace "Toh Allah ya tsare ya baka nasara" Yace "And one more thing Mami, ki
amsar min Cv's dina and my assets that he clutch" Mami tayi kasa da murya tace "No,
kai ya kamata kayi masa maganan wannan idan ka dawo, kuma ina ga ko ka dawo din ma
kar ka masa magana kawai ka zuba masa ido ka gani" Khalil yace "Aa i am asking him
Mami" Shiru tayi bata ce komai ba, ganin ya mike tace "Toh shikenan son, Allah ya
daura ka a kansa, Allah kuma ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya" Yace
"Ameen" Daga haka yayi mata sallama ya fita daga parlon. Khalil na fita gidan Aunty
Maryam ya nufa, can sama ya tafi ganin babu kowa a parlon kasa, ta fito daga
bedroom dinta ta shigo parlor ta zauna ya gaisheta ta amsa tace "Ya su Mami?" Yace
"Lafiya lau" Tace "Toh maa sha Allah, ya ake ciki?" Yace "Gobe ne zanyi tafiyar
Aunty" Aunty Maryam tace "Toh Allah ya kai mu, sai ka dawo yaushe?" Yace "Nan da
wata daya xan gama komai" Tace "Waii, ai ba lallai xaka dawo ka tarar da ni kilan a
kasar nan ba, yanzu ya ake ciki maganar admission din?" Yace "In sha Allah an fara
processing tun jiya" Sai kuma a hankali yace "But Aunty ya za mu yi da Mami yanzu?
Kinsan halinta fa, and i don't want her to be angry with me as a result of this
issue" Aunty Maryam tace "I will think about that khalil, in sha Allah xan san
yanda xa ayi, har yanzu nima tunanin ta inda xa a billo nake wallahi, da ina nan
babu abinda xai hanani riketa a gidan nan" Bai kuma cewa komai ba, amma tunani
yake, how will Mami be convinced, shi kuma he will neva let her stay in the
hostel.... Bai wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login