Showing 138001 words to 141000 words out of 268471 words

Chapter 47 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

a gidan naku" a hankali
Khalil yace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ba komai, ka tafi gida kawai, gobe da safe
za mu hadu a airport" Yace "Allah ya kai mu" har ya tashi tace "And one last thing
xan bata waya, kar kuma kace zaka amshe, kawai dai ka sa mata ido wajen ganin da su
wa da su wa take communicating" Yayi shiru yana kallonta, tace "Sannan na ba Ayman
layin da na sa mata a wayar da xan bar mata" Shi dai Khalil kallonta kawai yake,
tace "Ka ji abinda nace?" Yace "Na ji" tace "Sai anjima" juyawa yayi ya fita daga
parlon nata. Khalil na sauka downstairs ganin Zeenah a parlor yace "Ina Moon?" Tace
"She is sleeping upstairs" Yace "Ohk, ya preparation din tafiya?" Tace "Mun gama
tun jiya" yace "Good" Ya fi minti biyar tsaye a parlon, daga karshe kawai ya fita
compound, nan gidan ya bar motarsa don akwai wani abokinsa a layin da xa su je wani
wajen tare yanzu. Washegari da safe Khalil ya nufi airport tare da Mami da Mimi
with Noor, Aunty Maryam ta tafi da motarta da yaranta uku da mai aikinta da Nihad,
don tun da taga motar khalil a gidanta ta sanar masa xata taho da motarta airport
sai ya maido mata gida ya dau nasa, Noor kuma tayi driving dinsu Mami su koma gida,
har suka isa Airport Nihad bata daina kukan da take ba, she felt everything is over
for her, it's just like they are sending her away from home for the second time,
she felt insecure without Aunty Maryam, she won't have anyone to confide in
anymore, bayan Aunty Maryam ta isa airport din tayi parking, har ma ta daina ba
Nihad baki ganin ba sauraronta take ba, ta dau waya ta kira khalil, ya sanar mata
sun kusa isowa, tana ta jira har ya shigo airport din with escort, murmushi tayi
don tasan babu abinda ya tsana kamar wannan escort din, kawai dai babu yanda xai yi
don escort din na Mami ne sae in ita tace masu bata bukata, wannan kuma sai in ba
waje me nisa xa ta ba, tuni aka masu providing wajen parking babu 6ata lokaci,
bayan few minutes Mami da su Mimi suka sauko daga motar, Aunty Maryam ma ta sauka
ta tafi ta gaida Mami, yaranta ma duk suka sauka xuwa wajen, Noor ta rungume Aunty
Maryam tace "Ohh i feel like crying Aunty, xa mu yi missing dinki sosai" Mimi ma ta
marairaice tace "Me too Aunty" Mami na murmushi tace "Toh ba sai ku tafi gaba daya
ba" Noor tayi dariya tace "We wish" Nan mai aikin Aunty Maryam ta durkusa ta gaida
Mami, Mami ta amsa tace "Murja sai Uk ko?" Murmushi tayi tace "Za mu yi kewanku
Mami" Mami tace "Toh Allah ya tsare, Allah ya kai ku lafiya" Nihad bata yarda ta
sauka daga motar ba ta hade kai da gwiwa tana shesshekan kuka, Aunty Maryam bata yi
forcing dinta ta sauko ba cause she feel sad seeing her cry that way, Mami tace
"Toh ina yarinyar?" Aunty Maryam ta ɗan yi murmushi tace "Kuka take a motar shi sa
ma ban bari ta sauko ba" Mami tace "Kuka kuma? Kukan me?" Aunty Maryam tace "Sabo
mana Mami" Mami tace "Allah sarki" Tuni aka sauke kayansu zuwa cikin airport din,
Khalil dai na tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu, lkci lkci yake kallon
motar Aunty Maryam, Sai da xa su shiga cikin airport din bayan sun yi sallamar
karshe da su Mami Aunty Maryam ta koma gun motarta ta bude back seat ta dafa
shoulder din Nihad a hankali tace "Be a good girl dear, Allah ya tsare ki, Allah
kuma yayi maki albarka, in sha Allah xa mu dinga waya sosai duk abinda ya dameki
kar ki boye min ki dinga gaya min kin ji, kuma kar ki fasa addu'a da tashin daren
da kike kamar yanda kika saba in sha Allah xaki ga sakayya cikin gaggawa, sannan ki
dinga daukan kiran mutumin da na ba numberki banda walakanci my dear, he is a good
guy, and u will enjoy communicating with him" Nihad ta kasa ce mata komai sai kuka
take, Aunty
Maryam ta juya cike da karfin hali ta bar wajen duk Khalil na kallonsu, Ta mika
masa makullin motarta yace "Allah ya tsare Aunty" Ta gyada masa kai ta nufi cikin
airport din su Mami na daga masu hannu, Khalil ya mika ma Noor makullin motar Mami
dake wajensa, Ta amsa tace "Till we meet home yayanmu" Juyawa yayi ya nufi motar
Aunty Maryam ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, ya riga su Noor fita daga
airport din, har sannan Nihad bata daina kukan da take ba kamar ranta zai fita, shi
ma kuma bai ce mata komai ba, har ya isa gidan Aunty Maryam, bayan an bude masa
gate ya shiga yayi parking motar a parking space, Nihad ta kasa dago kanta, ya
sauka daga motar ya jingina jiki, bayan few minutes ganin ba bude motar xata yi ta
sauko ba ya bude mata, da kyar ta sauko daga motar xata bar wajen tana harde kafa
tana kokarin danne kukan da ya taho mata taji ya jawota kusa da shi, lkci daya ta
fashe da kukan ta rufe fuskarta a jikinsa, drawing her more closer to himself yayi
kasa da murya yace "Da kin bi ta ai" Ya bar ta ta ci kukanta bai hanata ba, har ta
gaji tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta rufe ido tana shaƙar daddadan
kamshin jikinsa, tana kuma jin yanda zuciyarsa ke bugawa. They stood in that way
for almost 5 minutes, lokaci daya yaji ta sakar masa duk jikinta, yayi saurin
rungumeta sosai kar ta zame kasa, he could feel her breathing calmly, kamar kuma
warce aka tsikara ta bude ido da sauri ta janye jikinta shi ma yayi saurin saketa,
ta koma gefe tana murza ido, shi kuma yayi keeping straight face.... she is so
sleepy don jiya ba wani baccin kirki da tayi, ya ciro makullin motarsa ya bude tasa
motar, ya shiga yana warming dinsa tana kallonsa tace "Kayana" Ya daga kai ya
kalleta, ta koma gun motar Aunty Maryam ya bude booth din da makullin, ta ciro
jakunkuna biyu, daya na wasu kaya da Aunty Maryam tayi mata, daya kuma wanda ya
siya mata, ta zuba kayan a booth dinsa ta kulle sannan ta shiga back seat, bayan ya
gama warming motar suka bar gidan, Nihad ta ɗan shinshina Hijab din jikinta jin
kamshin dake tashi a jiki, a hankali ta kwanta jikin motar ta lumshe idonta, har
suka isa gidansu bata sani ba tana bacci, bayan yayi parking ya kashe motar ya
sauka still Nihad bata farka ba, ya bude back seat din yana kallonta, patting din
kujeran motar yayi still bata bude ido ba, sai kuma ya kai hannu jikinta yana
tashinta, sae a sannan ta bude ido da sauri tana bin inda suke da kallo, ganin
compound din jikinta yayi sanyi, ya zaga ya bude booth ya fiddo jakunkunanta, ta
sauko daga motar tana kallon securities din bakin gate din, ya kulle motar yana
rike da jakunkunan nata biyu ya fara tafiya, ta bi bayansa tana jan kafa tayi kalan
tausayi da fuskartar, ta inda ya shigo da ita gidan ranan farko da suka zo ya bi da
ita yanzu ma, har suka isa bangaren Mami, ya kai mata kayanta guess room dake
bangaren, tana tsaye bakin kofar har ya karaso ya shiga parlon Mami sannan ta bi
bayansa, Mimi ce kadai zaune parlon, Mami kuma na bedroom dinta, ya zauna saman
kujera Nihad dai ta koma gefe ta tsaya, kana ganinta kasan she isn't happy being
here, ya ɗan hade rai ya nuna mata kujera, ta sauke kanta kasa ta zauna saman
kujeran, Mimi na kallonta tace "Hi" Nihad ta daga kai ta kalleta, Mimi na murmushi
tace "I am Mardiyya, and you?" Nihad dai sai kallonta take jin yanda tayi
pronouncing R din sunan alamar dae bata cikakken R 😜, Khalil ya juya ya kalli Nihad
jin tayi shiru, Nihad ta kalli Mimi tana ɗan murmushi tace "I am Nihad" Mimi ta
wara ido tace "Waow, You have a nice name, ina da wata fwend with ur name" Khalil
na kallon Mimi yace "Hey take her to the guess room ta kwanta, she is sleepy" tashi
Mimi tayi tace "Ohk mu je" Nihad ta tashi tana kallonsa, sai kuma ta bi bayan Mimi
har zuwa dakin, babba ne dakin sosai sai kace ba guess room ba, furnitures din
dakin ma kadai abun kallo ne, sannan ga bandaki shi ma babba a ciki, har da kayan
kallo akwai a dakin, Yanda aka gyara dakin kuwa ga zanin gado sai sheki yake kai
kace akwai mutum a ciki ne, Mimi tace "An wriga an gyara dakin yau, so za ki iya
kwanciyarki" Nihad tayi murmushi cause her intonation and most especially how she
pronounces her letter R is very funny to her, can dai tace "Thank you" daga haka ta
kwanta saman gadon, Mimi ta juya ta fita, nan da nan bacci ya dauke Nihad... After
sleeping for many hours ta bude ido a hankali, tsaye ta ga Khalil a dakin yana jera
mata kayanta a press din dake dakin, Kallonsa take kawai don bai san ta tashi ba,
duk Abayas din ya jera su waje daya, haka Hijab da atamfofi da Aunty Maryam tayi
mata kusan kala takwas, tana ganin xai ta6a inner wears dinta ta sauko daga kan
gadon da sauri ta turo baki tace "Ka bar min xan yi kayana da kaina" ya juya ya ɗan
kalleta, sai kuma ya kwashi duk inners din ya mayar da su cikin jakar ya koma gefe
ya tsaya yana kallonta, taki Kallonsa, a takaice tace "I need space" Daga sama har
kasa ya kalleta sai kuma ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga
dakin, duk sai da tayi seperating inners din nata, sannan ta koma ta kwanta tayi
lamo saman gadon tana tunanin Mumy.


I really appreciate ur patronage lovely fans, Allah ya biya maku bukatun alkhairi,
ya saka ma iyayenku da gidan aljanna.

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

And you show ur evidence via
07087865788

43

Mikewa Nihad tayi bayan ta tuna wayar da Aunty Maryam ta bata, ta sauko daga kan
gadon ta tafi inda empty bags din suke ta duba wanda wayar ke ciki bata gani ba,
mamaki ne ya cikata ta dinga kallon jakar, ta duba second bag din nan ma taga babu
wayar babu alamarsa, Knocking aka yi a kofar dakin ta mike tsaye da sauri tana
kallon kofar, can ta karasa ta bude taga Mimi a tsaye, Mimi tace "Ki fito mu ci
abinci" Nihad tace "Toh" Mimi tace "At Mami's parlor" Nihad ta gyada mata kai, Mimi
ta bar bakin kofar, komawa dakin Nihad tayi ta dau mayafinta tana kallon agogo,
karfe sha biyu saura ake cin abincin rana kenan a gidan, ta dai nufi kofa ta fita
zuwa parlon Mami tana tafiya a hankali, Mimi na zaune with 3 different foods a
gabanta, Nihad ta karasa tana kallon abincin, Mimi ta nuna mata wajen da zata
zauna, Nihad ta zauna, Sai ga mai aikin Mami ta shigo da ruwa me sanyi da drinks a
hannunta ta ajiye masu tana kallon Mimi tace "Za a kawo fruit Salad din ne?" Mimi
ta kalli Nihad tace "Will you take fruit Salad?" Nihad ta girgiza kai alamar a'a,
Mimi ta kalli Bilkisu tace "No need" Bilkisu ta juya ta fita, Mimi ta zuba abinda
xata ci a abincin gabansu, tayi ma Nihad alamar ta diba, Nihad ta dau plate ta debi
shinkafa da miya, daga Nihad har Mimi cakalkala abincin kawai suke yi, ita Mimi sae
danna wayarta take, daga karshe ta mike tana kallon Nihad dake mamakin wai har ta
gama cin abincin kenan, Mimi tace "Let me go and brush My teeth" Nihad ta gyada
mata kai kawai, Mimi ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba Noor ta shigo parlon
kallo daya tayi ma Nihad ta dauke kai ta nufi dakin Mami ganin Mami bata nan ta
juya ta nufi kofa zata fita, Nihad ta bi ta da ido har ta fita, Mimi na dawowa
parlon ta kira Bilkisu ta waya ta zo ta fitar da sauran abincin daga parlon.... Har
yamma Nihad na parlon Mami, wayar da bata gani ba yayi mugun tsaya mata a rai, kuma
ta ma san wa zai dau wayar, Lokaci lokaci Mimi ke shigowa wajenta a parlon, seems
basa wani zama nan bangaren sae Mami ta kirasu ko kuma sun shigo gaisheta, shigowar
Mimi na karshe tace "Pls mu je ki rakani saloon xan yi gyaran gashi" Nihad tace
"Toh" Mimi ta jirata har ta dauko Hijab dinta sannan suka fito Main parlor din
gidan, Nihad sai estimating uban tafiyar da suka yi kafin su shigo ainahin parlon
gidan wanda girmansa ya wuce misali take, the house is really huge, Tun da suka
shigo parlon Aunty Hassana dake waya ta bi su da ido, can ta katse wayar da take
tace "Ke Mardiyya zo nan" Mimi ta dawo tana kallonta, ko kadan Nihad wasn't
comfortable at the way the woman was looking at her, Aunty Hassana tace "Wacece
wannan?" Mimi ta kalli Nihad da tayi tsuru tsuru tace "Aunty bakuwa ce" Aunty
Hassana tace "Bakuwar wa?" Mimi ta buda hannu tace "Bakuwar Mami" Nihad tayi karfin
halin cewa "Ina yini" Aunty Hassana na kallonta daga sama har kasa tace "Lafiya"
Mimi ta jawo hannun Nihad suka bar parlon, Sajida da shigowarta parlon kenan ta
kalli Aunty Hassana tace "Wallahi Mama she is the one" Aunty Hassana tace "Anya
kuwa? Naga wannan fara ce sosai fa" Sajida tace "I am telling you the fact, ita ce,
bari in dauko wayata ki gani" Daga haka ta tashi da sauri ta tafi ta dauko wayarta
ta shiga video tayi playing ta mika ma Mamarta wayar, Aunty Hassana tace "Toh ba
cewa ku ka yi tare da wannan ɗan iskan suke ba? Kun ce shi ya kawota gidan" Sajida
tace "We are not sure, kawai muna shiga parlon Mami muka ganta a zaune, kilan er
uwarsu ce saboda yau da Aunty Maryam xata tafi ne ta sake dawowa gidan nan, all
those while tana gidanta" Aunty Hassana tace "Kaiii, da yar uwarsu ce xan santa, da
kyar dai in ba shi ya kawota gidan nan ba, idan kuwa ba shi bane ya aka yi sai da
ya dawo ita ma muka ganta a gidan, amma ba komai xan samu yaya anjima idan ya dawo,
ae dai baxa a kawo masa yarinya gidansa bai sani ba, xai min bayanin ko wacece"
Nihad ta dinga kallon motar da wani mutumi sanye da camouflage yayi parking dai dai
inda Mimi ke tsaye, ya sauka ya bude masu back seat, kana ganin shigar da Mimi tayi
na English wear ga baƙin shade dinta a ido sannan ga wani jaka da ta rataye xaka
san ba karya, she looks so cute and beautiful, Nihad bata ta6a jin da akwai wanda
xata ji ya fita komai a rayuwa ba sai yanzu, ita da ganin kanta take babu ya ita,
har University da take zuwa ma kallon kasa kasa take masu ba kowa take ma magana ba
ko da kuwa an mata, don tana ganin ba class dinta bane su, sai gashi yanzu kawai
taji ta raina kanta, Mimi na kallon Nihad ganin yanda ta ja gefe ta tsaya tace
"Shigo" Nihad ta shiga motar ta kulle a hankali, mutumin ya ja motar aka bude gate
suka fita daga gidan, Mimi ta ajiye wayarta da take dannawa tana kallon Nihad tace
"Here is a question for you Nihad" Nihad ta dinga kallonta ba ko kiftawa, Mimi tace
"How did u come to know my broda?" A hankali Nihad tace "Wanne?" Mimi ta ɗan yi jim
tace "Yayana fa nake nufi, wanda ku ka dawo tare da shi dazu da safe" Nihad tace
"Ohk, Yayanki ne?" Mimi ta buda ido tace "Yea he is my senior brother, we are
having same father and same mother, Mami is our Mum, Noor is my senior sister, she
is his immediate but ya girmeta sosai, ya bata 12 years, xan nuna maki ita idan mun
koma gida kilan baku hadu ba har yanzu" Nihad sai kallonta take don truly Mimi na
nugun kama da shi, both the nose and eyes, a hankali Nihad tace "Pls ki gaya min
gaskiya gidansu ne wannan gidan da muka fito?" Mimi ta wara manyan Idonta tace
"That's funny, he is the first and only male child of our father, did he tell you
ba gidansu bane?" kallonta kawai Nihad take tana jin ita fa yanzu da ta ga ainahin
cikin gidan da irin girmansa da kyau ta kasa yarda gidansu Khalil ne, ita kawai
yanxu gani take kamar rikonsa ake a gidan ko kuma gidan ɗan uwan babansa ne, abinda
ta saka a ranta kenan don she is beginning to get confuse ta yaya ma xa ace wannan
gidan nasu ne, mutumin da yaje gidansu yake driving ana biyansa for almost a year,
sannan har kauyensu ya kai ta, to me yasa xai kawota irin wannan gidan yanzu ta
yarda nasu ne, Mimi da ke ta kallonta ta katse mata tunaninta tace "What are u
thinking about?" A takaice Nihad tace "I am finding it hard to believe, and I don't
think i will believe" Mimi tayi murmushi tace "Now i understand, he acted like he
is a nobody right?" Nihad tayi shiru tana kallonta, Mimi ta shiga gallery dinta
taje inda take ajiye hotunan yayan nata, wanda sun fi dari ta shiga ta mika ma
Nihad tana kallonta, farkon hotonsa da Nihad ta gani ta dinga kallo babu ko
kiftawa, sanye yake da farin labcoat with stethoscope round his neck, ta tafi next
hoton, ta gansa cikin private jet an masa unaware picture, yayi crossing kafa yana
danna waya with a serious face, ga tsadadden non-alcoholic wines a gabansa,
designers ne kayan jikinsa, irin kyan da yayi kuwa a hoton ba ace wa komai, Nihad
ta dinga kallon hoton don karya ne mutum ya kalli hoton bai sake kallo ba, bata san
sanda tayi zooming ba still wanting to confirm and be sure shi din ne dai, taga
wallahi shi ne, da zaka shiga zuciyarta kaga mamaki da shock da ya cika sa, a
hankali ta tafi next picture din ta gansa a Newyork, then another in Los Angeles,
Paris and another in United kingdom, infact duk yawanci hotunan a kasashen waje ne,
wasu hotunan da turawa, wasu larabawa, she is really shock at all what she is
seeing, sai kuma ta fara ganin hotunansa da Nadeeyah, a hotonsu na uku tare ta ki
ci gaba da kallon, ta ɗan kalli Mimi dake danna second phone dinta giving it all
her attention, tayi tapping dinta ta mika mata wayarta, Mimi tace "Are you done?"
Nihad ta gyada mata kai, amsar wayar Mimi tayi ta mayar cikin jaka ta ci gaba da
abinda take da dayar wayarta, har suka isa saloon din Nihad bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login