Showing 60001 words to 63000 words out of 268471 words
da na kirata tace min haka" Nihad tayi karfin halin
cewa "Husnah kin san wa Abbana ya aura min?" Husnah ta gyara xama tana gwale ido
tace "Aa waye?" Nihad ta kwanta gefen gado hawaye me xafi na sauka idonta tace
"Husnah of all people wai drivern gidanmu Abba ya aura min" Husnah dake xaune sai
da ta mike tsaye tace "Whattt???" Bude kofar dakin aka yi Nihad ta mike xaune da
sauri lkci daya ta hade rai, yana mata wani kallo ya karasa cikin dakin fuska daure
yace "Kar ki sake ta6a min waya a gidan nan" Wani matsiyacin kallo tayi masa ta
wurgar da wayar tana ta6e baki tace "Wannan gwangwanin kake kira waya?" Kallonta
kawai khalil yake babu ko kiftawa trying his possible best to calm himself, Nihad
ta ja tsaki ta tashi ta koma can karshen gado ta xauna fuska daure tace "Wai waya,
kai baka ma ji kunyan kiran wannan waya ba" Gyada kai yayi ya juya ya durkusa ya
dau wayar da batur dinsa da yayi gefe daya ya mayar sannan ya mike ya nufi kofa ya
fice daga dakin, wani sabon kukan ta saki tace "Wayyo Allah na." Wajen karfe sha
biyu da rabi Nihad da har ta gaji da kukan da take ta ji ana kwankwasa gate din
gidan, kamar tana expecting hakan ta mike da sauri tana share idonta ta fice daga
dakin, dai dai fitowarsa shi ma daga dakin da yake, ta wani hade rai, ko kallonta
bai yi ba ya nufi kofa ya fita, wani mugun tsanarsa da tafi ta ko yaushe take ji a
ranta, even with joke baxata ta6a kiran wannan mutumin wai mijinta ba, mijinta ta
ina? Shi har ya isa ya xama mijinta? This is even weird to imagine, bakin kofar
parlon ta tafi ta tsaya fuska daure, yana bude gate din Umma ta shigo, har kasa ya
durkusa yace "Barka da xuwa Hajiya, ina yini" Wani kallo Umma tayi masa sae kuma ta
kyabe baki ta wuce ta bar sa durkushe a wajen, Nihad na ganin Umma ta taho da gudu
ta Rungumeta ta sakar mata kuka da karfi tace "Umma na shiga uku, me yasa Abba xae
min haka, me yasa Abba xae lalata min rayuwa, Umma ashe duk ba sona ake a gidanmu
ba ban sani ba" Umma ta rungumeta cike da damuwa tace "Yi shiru mu shiga ciki
Nihad, yi shiru" A haka Umma ta ja xuwa parlor, khalil da ya bi su da ido ya tafi
kan dakalin da ya xauna daxu ya xauna, Umma na rungume da Nihad bayan ta zauna kan
kujera tace "Wai ba nace kiyi shiru ba ko in tashe in tafi ne?" Nihad ta girgiza
kai tana shessheka a hankali tana goge idonta, Umma tace "Ke yanxu kin yarda an
aurar da ke kenan?" Nihad ta daga kai tana kallon Umma da kumburarran idonta, ba
idonta ba har fuskarta ya koma ja, Umma tace "Ohh kin yarda kenan an daura maki
aure da Driver?" Nihad ta girgiza kai disgustingly tace "Allah ya kiyaye wllh" Umma
tace "Toh Alhamdulillah, yanda ko wace budurwa take rayuwarta haka xaki ci gaba
babu batun auren kowa a kanki, kar ki kuskura ki amince wai kina da wani wai shi
miji, a nan din ma bai wuce ɗan aiken ki ba kuma drivern ki, ki sa a ranki kema
budurwa ce da xata iya shiga duk inda take so ta fito, ki ci gaba da rayuwarki
yanda kika saba, sannan kar ki kuskura ki raga masa balle ya ga fuskar kawo maki
raini, ba kowa bane shi facce drivern gidanku kuma har a yanxu dreban ne, kuma ɗan
aike" Nihad tace "Toh Umma yanxu a gida daya xa mu xauna da shi kenan? Wallahi i
just can't imagine that, ta yaya xa ace muna gida daya da shi?" Umma tace "Ka ji
ki, Toh ina ruwanki da shi? Meye hadin ki da shi? Rayuwarki kawai xaki dinga yi
kamar kina gidan ubanki, kar ki yarda ko kallon kirki ya hada ku da shi, har yau
shi din ma'aikacin gidanku ne don haka a karkashin ki yake" A hankali Nihad tace
"Toh, amma Umma shikenan baxan ci gaba da karatuna ba kenan" Umma tace "A saboda
me? Ai kwantar da hankalin ki, yanxu daga nan gidan Alhaji Abubakar xan nufa tunda
dai sun aurar da ke sai su bari kuma ki ci gaba da karatun ki" Nihad ta sauke
ajiyar xuciya tace "Nagode Umma" Umma tace "Kar ki yarda ki kara xubar da hawayenki
a banza a hofi, ke da ma kika samu freedom din kanki yanxu, da kin tashi fita kawai
fitar ki xa ki yi kanki tsaye babu neman izinin ko wani shege, sanda kika ga dama
kuma xa ki dawo babu me tuhumarki" Nihad da ta ji hankalinta ya kwanta sosai tace
"Haka ne Ummana" Umma tace "Toh ko ke fa, sannan duk kawayenki xa su iya xuwa nan
su dinga kwana kuna yini tare, kuyi duk wani sabgarku a nan babu me cewa don me"
Nihad tace "Gaskiya ne Umma, amma ni damuwata kawai ganinsa da xan dinga yi a
gidan, baxai yiwu ya koma can gidan ba kawai gaba daya ni kadai in zauna a nan,
wllh i hate the sight of him, na tsani ganinsa, na tsanesa" Umma tace "Aa ke kuma,
ai xai ci gaba da aikinsa na tuki, kinga duk safiya xai dinga xuwa can gidan kilan
kuma sai ya dawo da Abbanku daga office sannan ace xai dawo nan gidan" Nihad ta
yatsina fuska, Umma tace "Ke ma abinda idan kika fita kilan sai daren xa ki dinga
dawowa gida" Nihad tace "Dama mana, yanxu kawai xance su Husnah da Naf su kwaso
kayansu su dawo nan mu zauna" Umma tace "Shikenan kuwa" Nihad ta sauke ajiyar
xuciyar relieve, Umma tace "Kin ci abinci kuwa?" Girgiza kai Nihad tayi, Umma tace
"Me yasa? To tashi ki tafi kitchen ko indomie ne ki dafa" Nihad tace "Toh" Mikewa
tayi cike da energy ta wuce kitchen, sosai ta samu nutsuwa bayan abubuwan da Umma
ta gaya mata, ta dafa indomie sannan ta fito, Umma tace "Bari in xo in tafi don in
samu Alhaji Abubakar a gida" Nihad tace "Umma bani da waya wllh" Umma tace "Akwai
nokia din yayanku bari ko Amina xan ba ta kawo maki anjima" Nihad tayi Murmushi
tace "To Umma Nagode" sai da ta gama cin indomie sannan Umma tace ta taso ta
rakata, Nihad ta mike suka fito compound da Umma, har sannan khalil na xaune inda
yake, Ya mike yana kallon Umma yace "Sai anjima Hajiya" Umma ta wani kallesa, sai
kuma ta kyabe baki ta ci gaba da tafiyarta Nihad ta hade rai tana biye da ita a
gefenta, Komawa yayi ya zauna ya bi su da kallo, suna isa gate Umma tace "Toh sai
kin ji ni, idan Amina ta kawo maki wayar sai ki kirani don xan sa a siyo maki sim
ayi register sai ta taho maki da shi" Nihad tace "Toh Umma" Umma tace "Maza tafi
kiyi sallah ga azahar yayi, sai ki kwanta ki huta" daga haka tayi mata sallama ta
wuce, Nihad ta kulle gate din, fuska daure ta nufi cikin gidan. Har bayan magrib
Nihad na ta jiran Amina ta kawo mata waya amma shiru, gashi babu yanda xata yi ta
kira Umma duk da tana da numberta a kai, wannan ne yasa ta kara shiga wani damuwa,
karfe takwas da rabi ta mike a hankali ta fito daga dakinta, dai dai nan Khalil ma
ya fito... sosai gabanta ya fadi ta ɗan koma baya, sai kuma ta daure fuska, ko
kallonta bai yi ba ya shiga parlor, ta bi sa da kallo taga kamar fita zai yi, tuni
turarensa ya gauraye duk parlon, ko burgeta kamshin nan nasa baya yi, ta kasa kunne
taji ko fita gate xai yi, ai ko taji ya bude gate, da sauri ta shige dakinsa ta
kulle kofar, banda kamshi babu abinda dakin ma yake, ta tafi gefen gado ta dau
karamar wayarsa da ta gani ta hau dialing din number Umma sharp sharp, yana fara
ringing Umma ta daga hade da sallama, Nihad ta marairaice tace "Umma ni ce" Umma
tace "Aa Nihad, Number waye haka duk zero zalla" Nihad tace "Wayar yaron nan ne
Umma, ya fita yanxu shine na dauka da sauri na kiraki kafin ya dawo" Umma tace "Kin
ji shiru ko, wllh ba a samu anyi rijistan layin yau ba sai gobe wai, don haka gobe
da kaina xanje ayi, ita kuma Amina tana dawowa islamiyya xan bata ta kawo maki kin
ji" Nihad tace "Toh shkkn Umma, Allah ya kai mu goben" Umma tace "Toh Ameen, sai da
safe daughter" Daga haka ta katse wayar, Nihad na duba call logs don ta kira Husnah
tunda daxu ta saka numberta a wayar amma bata gani ba alamar ya goge number,
instead sai number Nihal ta gani wanda ko awa daya ba ayi ba da suka yi wayan da
ita, ta dinga kallon number babu kiftawa, bude kofar dakin aka yi, Nihad ta zaro
ido hade da kurma ihu a tsorace ta saki wayar hannunta jikinta na rawa, tsaye yayi
bakin kofa yana kallonta da wani Strict expression, lkci daya ta wani sha kunu ita
ma, can dai ta tafi can jikin bango har sannan gabanta na faduwa amma bata nuna
hakan a fuskarta ba, ya karaso cikin dakin ta hadiye wani abu da ya tokareta a
makogwaro da kyar xuciyarta sai bugawa yake tana kara shigewa jikin bango, yana
dukawa zai dau wayar ta yi hanyar kofa a mugun guje, da hannu daya yayi hanzarin
fixgota ta fasa ihu tana kokarin kwace kanta tace "Wallahi xan cijeka idan baka
sakeni ba, ni me xanyi da gwangwanin wayarka"
*Da kun kai hannunku xa ku danna wajen fowarding littafin nan xuwa groups ku dubi
girman Allah, ku dubi darajan annabi S.A.W, da kuma son da ku ke ma iyayenku ku
tuna da cewar nace don girman Allah ayi hakuri kar a min sharing to groups with
over thousand members, plss i am begging sincerely ba da fada ba ko gadara, ayi
hakuri a min wannan alfarman, masu siya kawai don su tura groups su yi hakuri domin
Allah kar su yi haka, And if u should come across this book roaming in any group
kayi kokari kayi subscribing before reading saboda ba free book bane, ur conscience
shouldn't allow u to read my dear, ko yaya ne try and give something, ina kuma
alfahari da duk wa enda suka yi patronizing dina, ina kuma maku fatan alkhairi...*
Nihad is just....
500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence via 07087865788
19
Hadeta Khalil yayi da bango fuskarsa a daure yana kallonta cikin kakkausar murya
yace "Zan maki gargadi na karshe, kar ki sake ta6a min wayata a gidan nan, kar kuma
ki sake shigo min nan, ina me baki wannan shawarar" Nihad dai gabanta sai faduwa
yake ganin how huge he is a gabanta, ita bata ta6a sanin ma haka yake da tsayi ba,
gashi ya murtuke fuska uwa ba drivern gidansu ba, amma duk hakan bai sa ta fasa
daure masa nata fuskar ba ita ma, sai dai bata ce komai ba, komawa baya yayi yana
kallonta, irin kallon kyama sannan ya nuna mata kofa calmly yace "Fita" Ba musu ta
nufi kofa, tana isa dai dai kofar ta juyo ta kallesa tana wani yatsine fuska har da
harararsa tace "Sai ka gaya min nawa ka siya shegen wayar taka in baka kudin wanda
ya fi shi yanxun nan, ban ta6a ganin wanda ke takama da rakani kashi ba sai kai"
Still yayi yana kallonta babu ko kiftawa, tana gama fadin abinda xata fada ta bar
wajen da sauri tayi hanyar dakinta ta shige ciki ta kulle kofar tana sauke ajiyar
xuciya, jingina tayi da kofar wani bakin ciki da takaici ya turnuketa wai yau ita
da drivern gidansu ne kadai a gida daya har yana gaya mata maganar banza, ta ji
xuciyarta na tafarfasa, she is still yet to believe this, ta kasa yarda wai da
gaske wannan mutumin Abba ya sa su gida daya su dinga xama, how will that even be,
fadawa tayi saman gado ta fashe da kuka tace "Wayyo Abba me yasa xaka min haka" Ita
da dai drivern nan ai gwara ko almajiri ne Abba ya nemo mata su xauna gida daya, ta
ci kukanta me isarta bacci ya dauketa a haka. Washegari har kusan karfe goma bata
fito ba ga wani mugun yunwa da take ji, tashi tayi da kyar daga karshe ta shiga
bandaki tayi wanka ta fito, daya daga akwatunanta dake dakin ta bude ta fiddo wata
doguwar rigarta ta saka, xaunawa gefen gado tayi feeling so sad and dejected, daga
karshe ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta fito parlor,
babu kowa parlon sai take away din abinci da ta gani a tsakar parlon, ta saci
kallon ko ina na parlon sannan ta karasa inda abincin yake tana ta6e baki ta bude
take away din tana kallon abincin ciki, jollof rice ne sai sheki yake da katon
kaza, ko rabi kuma bai ci ba, kazar ma bai wani ci ba ya bari, ta bude ledan dake
wajen taga drinks ne sai chocolates me yawa, vibration din waya taji saman kujera
ta kalla da sauri amma bata ga wayar ba, wanda hakan yasa ta gane wayar na
karkashen throw pillow dake saman kujeran, har xata kai hannu ta daga pillow din ta
ji an kulle kofar kitchen, sosai gabanta ya fadi ta juyo da sauri suka yi ido hudu
da shi ya fito daga kitchen din rike da cup din shayi, sai a sannan ya ji vibration
din wayarsa ya karaso da sauri, wanda tun kan ma ya karaso Nihad tayi hanyar
dakinta tana harararsa, ya ajiye cup din hannunsa ya bi ta da kallo har ta shige
dakin, xaunawa yayi saman kujera yana kallon throw pillow din kamar me son gano ko
ta ta6a ko bata ta6a ba, da sauri ya dau wayar kafin ya katse ya daga ganin Abba
ne, gaishesa yayi da ladabi Abba ya amsa yace "Anjima da yamma ka daukota ku zo
gida ina son magana da ku" Khalil yace "Toh in sha Allah" Abba yace "Ai motar na
can gidan ko?" Khalil yace "Ehh yana nan" Abba yace "Ina sauraronku xuwa nan da
bayan la'asar" Khalil yace "In sha Allah" Daga haka Abba ya katse wayar, ajiye
wayarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, this spoilt his mood the more, Allah
ya sani he can't endure staying under the same roof with this Brat, he wish this
never happened, he detest the sight of her, da yasan this is how things will end
babu abinda xai kawosa gidansu, da baxai fara ba, yanxu ta yanda ma xai ce ta
shirya su je gida shine babban aiki a wajensa, ko magana baya son yana hadasa da
ita, mikewa yayi ya dau wayarsa ya zura a aljihu ya fice daga parlon xuwa compound
don ya fi zama comfortable xama a nan, abinda Nihad bata sani ba shine shi ya ma
fita shiga damuwa kawai dakewa yake yi, kuma bata ki jininsa ba yanda shi ya ki
jininta. Ganin yunwa na neman mata illa ta kara fitowa parlor, this time around
hanyar kitchen ta nufa tana bin ko ina da kallo, ga kayan abinci amma babu kayan
miya, gashi ita ba gwanar cin indomie ba ce, babu yanda ta iya haka ta dafa
indomien ta fito ta wuce dakinta, tana ajiye indomien ta fashe da kuka sosai cike
da tausayin rayuwarta, why did this happen to her, waye yayi mata haka yayi ruining
happiness dinta all of a sudden, tasan duk rashin jin ta ko da singlet bata xama
comfortable zama a inda ba gidansu bane, ko su Husnah da take bi she is very
cautious of her self and her body, kuka take yi sosai wishing duk wannan abun bai
faru da ita ba, indomien da bata ci ba kenan daga karshe, kawai ta tashi tayi
alwala tayi sallahn azahar ta kwanta gefen gado hawaye na sauka idonta. Ana la'asar
Khalil ya shigo parlor ya zauna yayi dialing number Abba, Abba na dagawa ya
gaishesa sannan yayi kasa da murya yace "Abba tace ita baxata ba" Abba yace "Ohk,
ba ta waya" Khalil yace "Toh" Mikewa yayi ya nufi hanyar dakin da take ciki, yanda
kasan yana kallonta jikin kofar haka ya hade rai yana kallon kofar, sai kuma yayi
Knocking kofar, Nihad da ke kwance har sannan ta mike zaune tana kallon kofar, sai
da ya sake Kwankwasawa ta mike xaune ta wani hade rai, sai kuma ta tashi ta tafi
gun kofar ta bude cike da tsiwa tana harararsa tace "Lafiya kake kwankwasa min kofa
Malam? Ko da bashi ne?" Mika mata wayar hannunsa yayi ba tare da ya kalli fuskarta
ba, ta kalli wayar da kamar baxata amsa ba sai kuma tayi tunanin kila Umma ce,
fixge wayar tayi daga hannunsa tana kallon Number sai taga number Abbanta ne, sosai
gabanta ya fadi, tayi karfin halin kai wayar kunne, cikin sanyin murya tayi
sallama, Zaro ido tayi tana sauraron abinda Abba ke ce mata with strictness, can ta
kalli Khalil da ya koma can gefe ya jingina da bango ya rungume hannunsa, Abba bai
bar ma Nihad space din cewa komai ba ya katse wayarsa daga karshe, ta fashe da wani
matsanancin kuka tana kallo Khalil tace "Allah ya isa, ban yafe maka ba wllh,
yaushe kace min mu je can gida nace Aa?? Wallahi ni baxan ta6a yafe maka ba" Sai
kuma ta durkushe wajen tana kuka sosai ta kalli wayarsa dake hannunta tayi wurgi da
shi ta mike ta shige cikin daki ta fada kan gado tana rera kuka, ya dau wayar tasa
ya bar wajen. Bayan Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta dau hijab din da tayi
sallah ta saka sannan ta fito daga dakin, compound ta fito ta gansa xaune driver
seat ya bar motar a bude alamar dai ita yake jira, fuskarta a murtuke ta bude back
seat ta shiga ta xauna, ya sauka daga motar ya tafi ya bude gate..... Har suka kusa
gida Nihad bata daina hawayen da take ba a motar, Horn khalil yayi mai gadi ya leko
ganinsa ya daga masa hannu yana washe hakora ya bude gate din, Khalil na parking ya
kashe motar ya sauka ya tafi gun Aminu, tuni Nihad ta shige cikin gida, Aminu yayi
kasa da murya yana zazzare ido yace "Wani labari muke ji haka mutumina??" Khalil
yace "Na me fa?" Kafin Aminu yace komai, Khalil yace "Bari in shiga in fito yanxu"
Aminu yace "Toh ina nan ina jiranka" Juyawa khalil yayi ya nufi entrance din gidan,
Khalil na tsaye balcony yayi dialing number Abba ya sanar masa sun iso, Abba ya
masa izinin shigowa har parlonsa, babu kowa main parlor, Khalil yayi sallama
bangaren Abba, Abba ya amsa sannan ya shiga ciki, kansa a kasa ya zauna nan saman
Carpet ya kara gaida Abba, Abba ya amsa ganin Nihad bata shigo ba yace "Tana ina?"
Khalil