Showing 201001 words to 204000 words out of 268471 words

Chapter 68 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

bari ta rufe baki ba ya hade
bakinta da nasa giving her a deep kiss, lokaci daya ta ji tana neman faduwa tsabar
yanda ta kasa tsayuwa da kafarta ya jinginar da ita da bango, kissing her
romantically, knocking din kofar dakin aka yi ya saketa da sauri zai koma baya amma
tuni Farooq ya shigo, yana shigowa kuma yayi kasa da kansa ya juya ya fita daga
dakin, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil wanda shi ma kunyar Farooq ya cikasa,
wani harara ta galla masa ta nufi kofa da sauri, ya bi ta da kallo yana shafa kansa
har ta fita daga dakin, sai sunkuyar da kanta take wai ko zata ga farooq a hanya,
amma har ta koma bangaren Mumy bata gansa ba, ta sauke ajiyar zuciya ta shiga
parlon, ƙin karasawa bedroom din Mumy tayi don gani take suna ganinta za su gane
abinda Khalil yayi mata, ta kwanta saman 3 seater tayi lamo zuciyarta na bugawa,
har sannan tana jin kamar bakinsa na cikin nata, the imagination is making her
whole body weak, a hankali ta kai hannu soft lips dinta tana taɓawa. Farooq na bar
masu dakin na Usman kawai ya wuce yayi kwanciyarsa a nan, dama daga bangaren Umma
yake wanda taki fadin dalilin kukan da take kamar warce ta amshi sakon mutuwa, ba
yanda bai yi da ita ba amma taki gaya masa daga karshe tace masa ai hannunta ne ke
damunta, babu yanda ya iya ya fito dakin nata kawai. Daren ranan yanda Umma ta ga
rana cike da bakin ciki haka ta ga dare cike da fargaba, Kamila bar mata dakin tayi
ta koma na Nihad daga karshe tsabar irin kukan da take yi, Umma bata taɓa shiga
tashin hankali irin wannan ba, can kuma wata zuciyar ta dinga assuring dinta ai
Abba bai ji wayar da take ba fa, ta yaya zai ma ji bayan ta tura kofar bandakin,
kawai dai abinda ya ɓata masa rai yanda take magana cikin bandaki, wannan tunanin
yayi contributing wajen calming dinta down, amma fa bata runtsa ba har asuba, ga
dislocation dinta yayi tsami sai azaba yake mata, goshinta ma sai yanzu yake mata
fitinannen ciwo... Da safe Mumy ta shigo duba jikinta, Umma ta ki bari su hada ido
tace "Jiki Alhamdulillah" Mumy tace "Toh Allah ya sauwake, ya sa kaffara ne" Tace
"Ameen Ameen" Mumy ta ɗan zauna a parlon na wani mintuna kafin ta tashi tace mata
zata shiga kitchen, Umma na ganin ta fita ta lallaba ta saka Hijab dinta ta fito
main parlor don Mumy ce da girki kuma tun dazu take jiran ta ji ta a kitchen kafin
ta tafi parlon Abba, bata tadda kowa parlon ba don it is still early, ta nufi
bangaren Abba da sauri ta bude kofar parlon ta shiga, bata gansa a parlonsa ba
which is very rare, yana dawowa masallaci parlonsa yake zama har zuwa lokacin da
zai fita office sannan ya shiga bedroom dinsa ya shirya, hankalin Umma a tashe yake
sosai, gabanta sai faduwa yake, tayi karfin halin nufa kofar dakinsa a hankali ta
murda, zaune ta gansa saman gadonsa ya jingina da pillow yayi nisa tunanin da yake,
ya daga kai ya kalleta, gabanta ya fadi sosai, cike da karfin hali ta karasa cikin
ta zauna saman kujeran dake dakin ta dake tace "Ina kwana yallabai" Abba ya kalleta
kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Lafiya lau" Umma ta ɗan ji hankalinta ya
kwanta jin ya amsa, nan ta fara kame kame ta marairaice tace "Yallabai jiya, kawai
ina bandaki... Dama kuma kasan...." Dakatar da ita Abba yayi yace "Ni ban tambayeki
komai ba Sumayya" Bude kofar dakin aka yi, Mumy tayi turus bakin kofa ganin Umma a
dakin, sai kuma tace "Ohh ban san ma kina nan ba ai..." Umma dai tayi wuri wuri ta
kasa cewa komai, Mumy zata kullo masu kofar Abba yace "Ya aka yi Maryam?" Mumy tace
"Aa tambaya zan yi ko yanzu kake son black tea din" Yace "Aa sai anjima" Tace "Toh"
Daga haka ta juya ta kulle masu kofar dakin, Umma ta rasa abun cewa suna ta zaune
haka for almost 3 minutes duk jikinta yayi sanyi, yanxu da gaske ya ji wayar nan da
take? Abba yayi breaking silent din yace "Sumayya" Gabanta yace rassss, ta daga kai
da kyar tana kallonsa amma ta kasa amsawa, Yace "Za ku ba Bloggers 300k don su sake
dawo da Video din Nihad ke da kawarki a social media, kin nuna kina baƙin ciki da
gidan da Nihad ta samu, kin nuna you can't even withstand seeing her married to her
current husband kawai saboda selfish interest dinki, kika ce duk kun siyar da
zobenki na gwal kin kun kai ma malamai, baxan tsaya bin diddigin abubuwan da
malaman suka maku ba Sumayya, baxan yi hakan ba, kawai dai nayi farin ciki da na
gano duk wani abu da kike ma Nihad ba da zuciya daya kike ba, ke kina da wata
manufar taki ta daban ne a zuciya, this is so unfortunate Sumayya, idan kuma aka ce
min da hadin baƙinki video din 'ya ta yayi yawo a gari, kuma da sa hannunki wajen
yin video din ma baxan musa ba, kin gurbata mata rayuwa kin bar mata taɓon da baxai
taɓa gogewa a rayuwarta ba, kin cuceta" Umma ta fashe da wani matsanancin kuka tace
"Wallahi wallahi wallahi Yallabai ban san ta inda wannan video din ya fita ba kaji
har na rantse, believe me wallhi i know nothing about the video, idan kuwa karya
nake Allah ya dauki raina a nan" Kuka take sosai tana kallonsa, Abba yace "Ba komai
Sumayya, koma dai menene bana jin bayan abubuwan da naji kuna fada a waya dake da
kawarki kuma a hakan ma ba daga farko na tsinci wayar naku ba, bana jin zan iya ci
gaba da zama da ke, all what u are saying on phone ya nuna baki son Nihad, baki
taɓa sonta ba, fuska biyu kika dinga mata Sumayya, idan har tun ba yanzu kika fara
cutarta ba kuma kece sillar duk abubuwan da suka sameta Allah Ubangiji ya saka mata
cikin gaggawa, kuma kije na sake ki amma zaki iya ci gaba da zama gidan nan, don da
girmanki bazan ce ki bar min gidana ba, zaki ci albarkacin zuri'an dake tsakaninmu,
zaki ci gaba da zaman yaranki, ki ci gaba da duk harkarki a gidan nan amma babu
aure tsakaninmu, and this should be just between i and you, sai Maryam wanda ita ma
dole ta sani ne for some reasons, amma ko yaranki ni ban baki goyon bayan ki sanar
masu komai ba balle wani a waje, ki ci gaba da duk yanda kike a gidan nan, aure ne
dai babu tsakanin ni da ke" Bitterly Abba ke maganar, Tsabar shock Umma ta kasa
cewa komai ta dinga kallon Abba babu ko kiftawa, Abba yace "Ki je na sake ki
Sumayya" Wani kukan tashin hankali Umma ta fashe da tace "Ka sakeni fa kace
Yallabai, wallahi yallabai sharrin shaidan ne amma kasan ba halina bane, ban taɓa
nufin Nihad da sharri ba dai dai da rana daya, wallahi rudin shaidan ne, don girman
Allah ka rufa min asiri ka janye batun sakin nan, tsofe tsofe da ni kace ka sakeni,
ko albarkacin yara baxan ci ba Yallabai" Abba yace "Albarkacin nasu yasa nace kiyi
zamanki gidan nan kiyi harkarki yanda kika saba, sannan ko Mahaifiyata ni baxan je
ince mata na sakeki ba,
i am leaving it to my self, sai in kece kika je kika fadi a gari...." Kuka Umma
take kamar ranta zai fita tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, saki da
tsufana Yallabai, saki fa kace" Abba yace "Kin ga ki tashi ki je kar ki ja mana
attention a nan, you can leave pls Sumayya" Tashi tayi tana kuka sosai ta nufi kofa
ta fita daga dakin nasa..... Umma na komawa dakinta ta dinga kuka ba ji ba gani,
Kamila dake ta kallonta tace "Toh wai baki kira Hajiya Turan bane" Umma tayi banza
da ita tana rusa kuka uwa yar yarinya.

Aunty Maryam ta girgiza kai tana kallon Mami tace "Mami i am not supporting Khalil
in anyway, ki fahimce ni Mami, yanzu ko Janar ne yace bai yarda da auren nan ba ba
sai inda karfinki ya kare ba Mami? Ki daure ki dinga duba halacci irin na iyayen
yarinyar wllh sai kiga kin samu rest of mind kin rungumi auren nasu hannu bibbiyu,
uban yarinyar fa cewa yayi saboda kyawawan halin Khalil ya aura masa 'yar sa, ki ga
fa kauye yaje yayi hiring mutane a matsayin iyayensa ya kai ma uban yarinyar, amma
hakan bai sa uban ya kyamacesa ba ya basa er sa, mun dai je gidan kinga babu alamar
tsiya tare da su, kuma da ganinsu kasan yan babban gida ne, Mami in dai Nadeeyah ce
damuwarki to ki kwantar da hankalinki babu wanda yace Khalil bazai aureta ba, ai
Janar bazai ma yarda ya mayar da shi karamin mutum ba dole ce masa zai yi ya hadasu
gaba daya, kai idan ma tsoronki idan Khalil ya dawo zai iya cewa ya fasa to ko ni
kadai na ishesa wallahi, balle kar ki manta Mami muna nan duk bamu san da aure
tsakaninsa da Nihad ba amma kuma ai bai fasa shirye shiryen aurensa da Nadeeyah ba,
ya yarda har aka kai kudi aka sa masu lokaci, da bai da niyyar auren nata ai
kakkaucewa kawai zai dinga yi...." Mami ta dakatar da ita tace "Bana son ki dinga
kawo min maganar shirme Maryam, ko min rashin sona da auren nasa ba sai dai in zuba
ido inyi shiru ba tunda aikin gama ya riga ya gama, kina ganin zance ya saki
yarinyar ne? Ni takaicin dake damuna yanda har ni ya iya boye ma auren, Maryam babu
ranan duniyar da bana kiran Khalil fa, a rana nakan kirasa sau uku sau hudu, ko
kece ɗanki ya maki haka baza ki ji dadi ba Maryam, yasan dai ko da za a juya masa
baya akan batun auren nan ni bazan juya masa idan ma zan yi fushi na ɗan lokaci ne,
amma yayi min haka saboda bai daukeni a bakin komai ba wai har ni ya boye ma, kinga
kuwa ai babu ruwana da wani aurensa da yarinyar yaje can ya karata, babu ruwana"
Aunty Maryam ta kwantar da murya tace "Babu dadi amma kiyi hakuri kada fushin nan
da kike da shi ya shafesa Yaya, gaskiya yayi babban kuskuren boye maki ko da zai
boye ma kowa, but plss forgive him Mami, sannan ki sa ma auren nasu albarka don
Allah, ki rungumi Nihad a matsayin surkarki ko don halaccin da iyayenta suka ma ɗan
ki, kin dai ga uwarta mutuniyar kirki mara son hayaniya, ubanta ma kin ga babban
mutum ne da yasan darajan ɗan adam, ki duba wannan kiyi hakuri ki ja ta jiki
matsayin surkarki pls Mami" Mami ta mike ta dau gyalenta tace "Hajiya Safeenah na
jirana, sai na dawo Maryam" Daga haka ta nufi kofa Aunty Maryam ta bi ta da kallo.
Karfe shidda da yan mintuna na yamma Nihad ta gama shiryawa don Khalil ya sanar ma
Aunty Jamila Flight din nasu na karfe takwas din dare ne, Aunty Jamila ta nuna mata
gefen gado ta zauna tana kallon gorunan dake gabanta wanda a jiki duk aka rubuta
KMZ (Kayan Matan zuru 08033308307) Nihad dai ta sunkuyar da kanta taki yarda ta
sake kallon Aunty Jamila, Aunty jamila sai dai ta mika mata cup tace ta kwankwade,
Nihad ba halin mata musu, da ta shanye kuma take maida mata cup din ta kara mata
wani hadin, har zuman KMZ sai da ta bata, a karshe ta bata gumbar kwakwa ta ci,
sannan Aunty Jamila ta fita daga dakin, Sosai gumbar yayi ma Nihad dadi wanda bata
ma san sanda ta cinyesa tass ba, Amina ta leko dakin tace "Wai ana jiranki a waje
Aunty" Nihad ta mike da sauri ta shiga bandaki ta wanke bakinta da mouth wash
sannan ta fito, tun da tayi wanka dazu ta saka er gown bayan ta shafe duk jikinta
da turare, sai yanzu da ta sa Hijab har kasa ta fito, parlon Mumy ta shiga ta
sameta tare da Aunty Jamila, ta durkusa jikin kujera ta kasa kallonsu, a hankali
tace "Za mu tafi" Aunty jamila tace "Toh Allah ya tsare Nihad, babu kayan da zaki
dauka?" Nihad ta girgiza kai tace "Akwai kaya a can" Aunty jamila tace "Toh
shikenan, shi ma yanzu ya fita, yana can waje yana jiranki, saura kiyi watsi da duk
abubuwan da na gaya maki dazu" Nihad dai bata ce komai ba, can ta daga kai ta kalli
Mumy taga kallonta take, Mumy ta sauke idonta tace "Allah ya tsare, sai ayi ta
biyayya, Allah ya maku albarka gaba daya...." A hankali Nihad tace "Ameen" Mumy
tace "Jamila kiyi mata magana taje ta duba Umma kafin su tafi tunda ni na mata taki
ji" Aunty jamila tace "Wace Umma, baki ji fitarta ba dazu?" Mumy tace "Au haba?"
Aunty Jamila tace "Ai ko ta fita bayan la'asar da katon bandage a goshi ni na zata
ma asibiti zata amma kuma naga bata dawo ba har yanzu" Mumy tace "Toh shikenan
tashi ki je, kin bar sa a waje yana jiranki" Nihad ta mike kanta a kasa ta kara
masu sallama sannan ta nufi kofa ta fita duk suka bi ta da ido, A compound ta tar
da Khalil bakin gate yana zaune kusa da Aminu, Ga Iliya driver a cikin mota yana
jiransu, Aminu sai washe baki yake yana kallon Khalil kamar ranan ya fara ganinsa,
Khalil ya ciro dubu dari cash ya ajiye masa gefensa a kan bencin da suke yace "Ka
ci gaba da cin tsirenka da lemon kwali duk dare, idan kuma kaji da inda ake yankan
fili a unguwa me kyau ka kirani ka gaya min" Aminu ya kasa cewa komai sai kallonsa
yake kamar wawa, Isiya da Saminu dake makale jikin kofar dakin Aminu don wani Cele
suka mayar da khalil sai sinne kai suke kamar munafukai, Khalil ya mike ya ciro
dubu hamsin ya mika masu su biyu sannan ya bar wajen zuwa parking space, Nihad dake
tsaye ganin ya taho ta bude back seat ta shiga, shi ma back seat din ya bude ya
shiga, Aminu dake matsar kwallan farin ciki ya bude masu gate, ba bakin magana ya
dinga daga masu hannu yana jijjiga kai har suka bar gidan, Isiya da Saminu suka hau
raba kudi, Aminu na kulle gate din ya juya ya kallesu bayan ya share guntun hawayen
idonsa yace "To ai dai kun ga amfanin mutunta ɗan Adam a rayuwa, kiri kiri ku ka
hanasa daki farkon zuwansa gidan nan, ku ka dinga masa rashin mutunci sai da ya
nuna maku shima fa ɗan banza ne sannan ku ka shiga taitayinku amma ko ga maciji
bakwa yi da shi, to da nine shi wallahi da alawa ko biscuit zan hada ku yau" Sai
kuma ya tuntsire da dariya har da kyakyatawa, banda hararansa babu abinda suke yi,
horn yaji na katon mota, ya koma gate din da sauri yana leka waje, Katuwar mota ce
shake da kayan dakin Kamila da komai nata na gidan mijin ya turo a kawo alamar babu
komawa, Aminu ya saki baki sai kuma ya wangale gate din da sauri motar ta shigo
gidan.
Har suka kusa airport Khalil kallon Nihad yake, ita kuwa taki barin su hada ido,
can dai yayi kasa da murya yace "Ko mu bar tafiyar gobe kawai?" Sai a sannan ta
kallesa amma bata ce komai ba don gaba daya she is feeling her body so weak and
she's been sopping tun barinsu gida, ya kara yin kasa da murya yace "Ai baki gaji
da kanon ba ko?" Ta gyada kai a hankali tace "Ehh" Yace "Mu koma kawai a bari gobe
in sake wani booking din kenan?" Nan ma a hankali tace "Ehh" Yace "Ohk" Sai kuma ya
kalli Iliya yace "Baba juya kan motar kawai" da ladabi Iliya yace "Zuwa ina ranka
shi dade??" Khalil yace "Kawai nemi waje kayi parking kada a baka wahala, bari inyi
driving din da kaina" Yace "Ahh haba ranka shi dade ai mun saba, shekaru talatin da
suka wuce trailer nake ja daga nan arewa zuwa legas" Khalil yace "Kai dai yi
parking kawai Baba" Ba musu yayi parking gefen hanya, Khalil ya sauka ya tafi
driver seat din, Iliya ya koma daya gefen, Khalil ya ci gaba da driving din.... Da
mamaki Nihad ta dinga kallon dai dai inda Khalil yayi parking bayan tafiyar kusan
minti talatin da biyar da suka yi, Yana kallon Iliya yace "Nan za mu sauka baba,
sai ka koma gida" Dubu goma ya ciro ya basa, Iliya ya amsa ya dinga godiya ya sauka
daga motar ya dawo driver seat bayan khalil ya sauko, Khalil ya bude back seat yana
kallon Nihad, ta wani hade rai tace "What is the meaning of this?" Yace "Kina bata
ma Baba lokaci" Zata yi magana ya kamo hannunta zai sauko da ita daga motar, ganin
haka ta sauko da sauri, ya kulle motar ya daga ma Iliya Hannu, Iliya ya ja motar ya
bar wajen, Nihad ta daga kai tana kara kallon Bristol Hotel wanda ta zo sau ba
adadi da su Husnah, ji tayi ya kama hannunta ta bi sa zuwa cikin hotel din tana
tafiya a hankali......




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788




*Ina kuke ma'abota kamshi?😁😁 To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da
hadaddun turarukan wuta na gida, na jiki da kuma ns kaya. Akwai perfumed body oils
masu dadin kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba
ya isheki ga yana dadewa a wuri bai fita ba, Maza ku garzayo Albait Al sahal domin
Ku Sami naku Cikin sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa.... Duk wacca ta
siya beyi mata ba ta dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me
via WhatsApp 09084473900*


61

Nihad na shiga dakin hotel din ta zauna gefen gadon dakin a hankali, ya ajiye
wayoyinsa ya kalleta yace "Will be right back" Ita dai bata ce masa komai ba ya
nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, bin dakin da ba bakonta bane ta
dinga yi da kallo, memories da bata son tunawa suka dinga dawo mata, lokaci daya
tayi saurin kauda tunanin cause it's making her sad, ta jinginar da kanta a hankali
jikin gadon ta lumshe ido... Can dai ta gyara zamanta da sauri, ita dai tasan ba
lokacin period dinta bane but she is feeling as if her period just came, beside sai
tayi wata hudu ma bata yi period ba ita, tashi tayi ta tafi bandakin amma sai ta ga
opposite dinsa, bayan few minutes ta fito ta dawo ta zauna gefen gado, wayarsa da
ya ajiye side drawer ya fara ring, ta juya tana kallon wayar taga Nadeey a jikin
screen din, ta dinga kallon wayar ko kiftawa babu, lokaci daya ta wani hade rai,
sai kuma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login