Showing 90001 words to 93000 words out of 268471 words

Chapter 31 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

kiran
Umma, Umma na dagawa tace "Auta har kin je gidan ne?" Nihad tace "Umma ni ce" Umma
tace "Aa Nihad, wato dai wannan matsiyacin duk wayar da aka baki sai ya karbe ga
shi tatattce ko?" Nihad ta tabe baki tace "Wallahi Umma" Umma tace "Toh xa mu xuba
da shi kuwa, xan kawo maki waya sannan in mika masa a gabana ya damka maki wayar da
hannunsa" Nihad tace "Kin ma san abinda yayi min Umma?" Umma ta zaro ido tace "Me
yayi maki?" Nan Nihad ta labarta ma Umma garinsu da ya kai ta ta kusa mutuwa, Umma
tace "Ikon Allah, amma shine matsiyacin nan ya samu waje yake nuna ma mutane isa
daga an aura maki shi? Asha ɗan kauyen kayau ne" Nihad tace "Wllh Umma ban gama
rainasa ba sai da naje garinsu, yanxu 100% na rainasa wallah, Umma ko wuta fa babu
a garin, sannan rafi suke xuwa debo ruwa, kai ni baxan ma iya baki labarin garin
nan da baki ba, sai da nayi rashin lafiya kamar xan mutu sannan ya dawo da ni cikin
gari" Umma da ke ta sauraronta tace "Ikon Allah, dama ance talaka da matsiyaci basu
iya samun waje ba, ki ga yanda ya dawo birni ya kile yake daddaga ma mutane kai
alhalin ko mage me gata baxata iya rayuwa a kauyen ba" Nihad ta sauke ajiyar xuciya
tace "Na sha mamaki Umma, ɗan kauyen kayau ne wllh, kuma yanda kika gansa fari haka
family dinsa suke da haske a kauyen" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, in sha Allah
gobe ko jibi ina nan shigowa daughter" Nihad tace "Toh Umma kar ki manta wayar,
idan ya so kamar yanda kika ce sai ki basa ya bani a gabanki sannan ki ja masa
kunne sosai kar yace xai amshe" Umma tace "Kar ki damu sai dai na zo" Daga haka
suka yi sallama, Nihal na kallon Nihad tace "kinsan Mumy bata da lafiya kuwa
Nihad?" Nihad ta kalleta tace "Haba? To ai ni ba a gaya min ba" Nihal tace "Ai kam
bata da lafiya, in kirata ku gaisa?" Nihad ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Ki bari
anjima da daddare xan kirata" Nihal tace "Toh shkkn" Nihad tace "Idan xa ki ci
abinci ga indomie can kitchen ki dafa fa" Nihal ta mike ta fita daga dakin, tana
shiga kitchen taga kayan miya kawai tayi deciding ta dafa jollof rice, tana cikin
grating kayan miyan taji muryar khalil yace "Sannu da aiki" Ta kalli kofar da sauri
sai kuma tayi murmushi tace "Nagode" Yace "Yaushe xa ku kare hutun?" Tace "Nan da
sati biyu" Yace "Ohk nan xaki gama hutun ko?" Tace "Aa ni da gobe xan tafi, i don't
want to over stay my welcome" Murmushi yayi yace "Aa kiyi hutunki kawai a nan" Ita
dai bata ce komai ba tana ci gaba da aikinta, juyawa yayi daga karshe ya bar
kitchen din. Bayan Magriba yana xaune a parlor Nihal ta fito daga daki xata je
kitchen ta xuba ma ita da Nihad abinci, ganin khalil zaune parlon ta koma daki
wajen Nihad tace "Ki fito ki zuba masa abinci, ban fa xuba masa ba tun daxu" Da
mamaki Nihad ke kallonta, sai kuma tace "A saboda me xan xo in xuba masa abinci?
Dama da shi kika dafa abincin ne?" Nihal dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita,
Nihad ta rike ha6a tace "Ji wani iyayi wai in xuba masa abinci kamar wani mijina,
ashe xai tsufa bai ci abincin ba" Tsaki ta ja ta jawo wayar Nihal for the 10th time
ta sake kiran layin Aliyu amma a kashe, kwantar da kanta tayi saman pillow kamar
xata yi kuka don har ta gaji da trying layin nasa, tun xuwan Nihal take abu daya,
Nihal na komawa kitchen ta fara xuba masa abincin a plate sannan ta dauka ta fito
parlor ta nufesa ta durkusa tace "Ga abinci" Yana kallonta yace "Thank you Nihal"
Ta mike ta koma kitchen din ta xuba ma ita da Nihad a tare, kadan Nihad ta ci
abinci duk hankalinta a tashe yake bata samu Aliyu ba, Nihal ta ci abinda xata ci
ta bar mata ta koma saman gado ta dau wayarta tana dannawa, Daga karshe wajen karfe
goma da taga Nihad ba ci xata yi ba ta dau plate din ta fita, Bayan ta kai kitchen
ta fito khalil na kallonta yace "Wani level kike a makaranta?" Ta tsaya tace "Level
daya muke da Nihad" Yace "But in tambayeki" Ta ɗan tsaya sai kuma ta dawo parlon ta
xauna tana kallonsa yace "Ke kika ce ma Abba Ahmadu Bello University kike so?"
Nihal tayi murmushi tace "Aa, kawai cewa yayi can xan je ni" Yace "Ita kuma er
uwarki fa?" Ta sunkuyar da kanta tace "He gave her option" Khalil dake ta kallonta
yace "Ohk ke daga baya baki ce masa makaranta daya kike son xuwa da er uwar taki
ba?" Nihal tace "Ya Usman da Mumy sun masa magana a lkcn, Mumy tace masa tunda har
Nihad ta zaba Maryam Abatcha nima ya biya mun Maryam Abatcha din mu tafi tare ko
kuma duk mu tafi ABU, amma sai yace Nihad kawai xata je ni in tafi ABU, he can't
afford the fee of Maryam Abatcha for the two of us" Shiru Khalil yayi yana
kallonta, can yace "Kuma Ummanku bata ce komai ba?" Nihal ta girgiza kai tace
"Kawai ce min tayi inyi hakuri in tafi ABU din" Khalil ya gyada kai yace "Amma
secondary daya ku ka yi ko?" Nihal ta girgiza kai tace "Shi ma ba daya muka yi ba,
ita Nigerian Turkish tayi, ni kuma Yan dutse nayi" Khalil ya gyada kai yace "Ohk,
yan dutsen kamar su Amina da Sudais nan suke xuwa ko?" Nihal tace "Har Aunty
Kamila da Ya Usman da ya farooq ma can suka yi, Nihad kadai ce tayi Nigerian
turkish" Khalil yace "Amma kamar er uwartaki tafi sabawa da Ummanki akan mamanta
ko" Nihal tace "To ai a bangaren Umma take, ni kuma ina side din Mum dinta, though
I don't know for her" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Maa sha Allah,
hakan yayi.... amma wani saurayinta da ya zo can gida ranan, sun dade tare ne?"
Nihal tace "Wai Aliyu? Yea definitely shi, don ita bata kula wani saurayi idan ba
shi ba, shekaran da ta shiga Maryam Abatcha suka hadu, shekara uku kenan" Yace
"Ohk, kinsan saurayin sosai kenan?" Nihal ta bude ido tace "Nasan shi mana, he is
the son of General Jikamshi..." Muryan Nihad dake labe jikin pillar din corridor
tum daxu ya katse Nihal, cike da bacin rai Nihad tace "A gidan uwar wa kika san
shi? Shi Aliyun kike tunani kinsani? Har da wani gaya masa sunan babansa salon yayi
masa mugun abu irin nasu na kauye? To wallahi baki san shi ba kuma baxa ki ta6a
saninsa ba, dama don ki zo ki hadu da wannan mutumin ku kafa munafurcina ya sa kika
zo gidan nan ashe ban sani ba? To wallahi ni dai ki tashi ki tafi baxa ki kwanan
min a gida ba, ai dai mun ga juna, har da wani ce masa ni kadai nayi Nigerian
turkish, to wani yace kar kema kice ma Abba can kike so? Naga dai choice dina ne
kuma Abba yayi accepting, sannan Maryam Abatcha ma wani yace kar ki sakar ma Abba
kuka kice ke baxa ki je ABU ba sai dai Maryam Abatcha? Wallahi kin ban mamaki har
xaki zauna da bare kuna cakalkalar namana ko tausayina baki ji ba, to Allah ya isa
wannan gulman nawa da kika yi" Nihal dai bata ce mata komai ba, Banda kallon Nihad
babu abinda khalil ke yi, tana huci tace "Shi kuma saboda gulma har da wani cewa
nafi son Umma, dama ashe maza na gulma ban sani ba? Kuma ai Umma da Mumy duk daya
suke a wajena babu wani bambanci, to tunda dai mun ga juna zo ki dau handbag dinki
kiyi tafiyarki" Mikewa Nihal tayi ta nufi daki, Nihad ta bi ta da harara, sai ga ta
ta fito sanye da hijab tana rike da handbag dinta ganin xata nufi kofa Nihad ta
rikota tace "Ina xa ki tafi da daddaren nan" Nihal ta fizge Hijab dinta hawaye cike
idonta ta nufi kofa, Nihad
ta bi bayanta da sauri tace "Ke ni fa wasa nake maki ina zaki da daddaren nan"
Tuni Nihal ta fice daga parlon, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil tace "Don
Allah kayi mata magana, ni wallahi ba haka nake nufi ba" Ko kallonta Khalil bai yi
ba, hakan yasa ta fita da sauri, can ta tarar da Nihal zaune bakin gate dake kulle
tana rera kuka, kukan ta ita ma ta fara ta durkusa gabanta tace "Don Allah kiyi
hakuri wallahi i didn't mean it, ni ba da ke nake ba, da shi nake"




*Nihad* dari biyar ne, ki fita hakkina ki karanta hankalinki kwance yar uwa

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via👇🏻



07087865788
*Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki
da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai
maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da
boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*


Domin karin bayani ki tuntubi wannan number 👇🏻

✍🏻
+2347057607751


https://chat.whatsapp.com/G91KmKaihzAL76lSmkXqG9


29

Ganin Nihal taki tanka ta sai kuka take, Nihad ta mike da sauri ta koma cikin gidan
zata kira Khalil, a bakin kofa ta kusa buge sa ya turata tayi baya xata fadi ganin
hakan yayi saurin jawota ta fado chest dinsa, ta zaro ido ta daga kai tana
kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya turata gefe ya sauka xuwa wajen Nihal, bin sa
tayi da kallo, yana isa wajen ya durkusa gabanta a hankali yace "Ki yi hakuri
Nihal, don't take all what she said personal" tana goge hawayen da ya ki tsaya mata
tace "Ka bude min gate in tafi gida" Yace "Ba amfani hakurin da nake baki kenan?"
ta girgiza masa kai kawai, yace "Now, Behave like the good girl u always are, tashi
mu koma ciki" Daga haka ya mike, ita ma ta tashi tana ci gaba da goge idonta, yana
gaba tana bin sa har xuwa parlon, Nihad ta riga su shiga parlon kafin su karaso,
bayan sun shigo tana kallon Nihal a hankali tace "Kiyi hakuri plss, i didn't mean
it" Nihal dai bata ce mata komai ba ta yi wucewarta daki, Nihad ta jefa ma Khalil
wani kallo tace "Ai dai kaga abinda ka jawo, kawai ka sa yarinya a gaba kana koya
mata gulma da munafurci alhalin ba halinta bane" Daga kai yayi ya kalleta, speaking
calmly yace "Idan kina ci gaba da min rashin tarbiya, Billah xan tattara ki in
mayar da ke kauyen can" Shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace "Toh
ni nace wani abu ne?" Bai sake kallonta ba, ta turo baki ta juya ta koma dakinta.
Har Nihad ta gama shirin bacci Nihal bata ce mata komai ba, Nihad ta gama saka
kayan baccinta wanda shi kadai ta tsira da shi a gidan ta dawo gefen Nihal da
damuwa tace "Shine ina ta maki magana kin ki cewa komai ko?" Nihal ta daga ido ta
kalleta tace "Me kike son in ce maki?" Nihad tace "Wallahi kema kinsan i didn't
mean it, you know i love u to the extent that i will never hurt you" Nihal ta ɗan
yi murmushi tace "Amma duk kwanan nan jaraba kike min a waya ai" Nihad ta
marairaice tace "Toh me yasa xaki dinga magana da worst enemy dina a waya? Yanxu da
Amina ce ke waya da shi ko wasu can daban ai ni baxan damu ba, amma ke fa kinsan i
Cherish u so much, why will u be communicating with my worst enemy?" Nihal tace
"Toh shikenan, na maki alƙawarin baxan sake waya da shi ba, dama yawanci ina ce
masa ya kai maki waya ne...." Nihad tace "No, just block him kawai" Nihal tace "If
that will please u" Tana fadin haka ta dauko wayarta tayi blocking number Khalil
sanan tayi deleting number daga wayar tana kallon Nihad tace "Done!!" Nihad tayi
Murmushi tace "Kin hakura yanxu?" Nihal tace "On one condition" Nihad na kallonta
tace "Ina jin ki" Nihal tace "Ki tashi ki tafi dakinsa" da mamaki Nihad ke
kallonta, can tace "Amma ina ga baki da hankali, inje dakinsa inyi masa me? So now
u are keeping it in mind cewar mijina ne shi da har xa ki ce in je dakinsa? Why
will u leave such thought a xuciyarki idan har ke masoyiyata ce?" Nihal bata ce
mata komai ba ta ja bargo ta lumshe ido, Nihad ta ja tsaki ta mike ta koma can edge
din gadon, ta fi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike fuskarta daure
tana kallon Nihal tace "If that will please you shikenan" Daga haka ta dau Hijab
dinta ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, bayan ta saka hijab dinta ta kunna
wutan corridor din tana kallon kofar dakinsa, can ta kyabe baki a ranta tace ba
gwara taje parlor ta kwanta abunta kawai, kashe wutan tayi ta karasa cikin parlon
tana tafiya a hankali sbda duhu, laluban dogon kujeran da xata kwanta ta shiga yi
bayan ta shigo tsakiyar parlon, a tsorace ta koma baya rana zaro ido bayan
lalubenta ya kai ta har jikinsa, ya mike zaune yana haskata da karamar wayarsa,
kunya taji ya kamata ta juya tana sosa kai xata bar wajen, yace "Da wani abun da
kike so ne???" Ta juyo duk da bata ganin fuskarsa sbda haskata da yayi ta daure
fuska tace "Wani abu kamar me?" Yace "Kin fi ni sani ai tunda kika biyo ni nan kina
tattaba ni" Tsayawa tayi tana kallonsa kamar me son fahimtar abinda yake nufi, can
tace "Kai kasan abinda kake nufi ni ban sani ba" yace "Aa ki dai fada abinda kike
so" a takaice tace "Abinda ke ranka shi nake so" daga haka ta xabga masa harara
xata bar wajen ya fixgota ta fado gefensa, a tsorace tace "Don Allah kayi hakuri
wallahi kwanciya na zo in yi, ni ba wajen ka na zo ba" Cikin husky voice dinsa yace
"Duk dakinki babu wajen kwanciya sai kin fito parlor?" Ta boye fuskarta a huge
muscles dinsa tace "Nihal ce tace idan ina son ta hakura sai na je dakinka, to ni
kuma ina son ta hakura" kallonta kawai yake yana kara tabbatar da ainahin
childishness dinta, Wani sanyayyen kamshi ke tashi a jikinta har gashin kanta, lkci
daya kuma ya hade rai ya saketa, ta dago kai a hankali tana kallonsa, matsawa yayi
daga kusa da ita ya koma daya side din kujeran, With full audacity tace "Xan shiga
dakinka in kwanta kuma kar ka sake ka shigo har sai na fito" Bai tanka ta ba, ita
ma bata jira yace komai ba ta mike ta nufi dakinsa, murda kofar dakin tayi ta shiga
tana bin ko ina da kallo, wani kamshi ke tashi a dakin, ta kalli jakarsa dake dakin
ta juya ta kalli kofa, tana ta tsaye tana kallon kofar sai kuma ta nufi jakar ta
tsugunna ta bude zip din, Chargern Iphone ta fara cin karo da, ta dinga kallon
chargern tana jujjuyawa, wannan kuma na waye? Ko dai na Nihal ne? Tabe baki tayi ta
ajiye, ta maida idonta kan Diary Milk chocolate masu uban yawa a jakar, kai....a
ina ya samu kudin siyan wannan uban chocolate din, ko da yake kudin babanta ne,
wato saboda samun waje har da su siyan chocolate, wani hoto ta gani ta dauka tana
kallon matar da ke jikin hoton warce baxata wuce shekaru 54 ba, kana ganinta kaga
halfcast, keenly Nihad ke kallon hoton tana ji a jikinta kamar ta ta6a ganin wannan
matar, amma a ina?? Duk yanda ta so tunawa ta kasa, as in, she k6s sure ta ta6a
ganin hotonta but where?? Bude kofar dakin aka yi ta mike a rikice, da sauri ya
nufota ya warce hoton daga hannunta ya hadeta da bango yana mata wani mugun kallo
lkci daya kamanninsa suka sauya, Sosai ta tsorata jikinta na rawa tace "A bude fa
naga jakar xan...." Turata yayi har sai da ta fadi kasa rigijib, ya dau jakar gaba
daya ya fice daga dakin. Da safe karfe tara saura khalil na zaune parlor Nihal ta
fito, ta tsaya jikin kujera ta gaishesa ya amsa yace "How was ur night?" Tace
"Alhamdulillah, Nihad bata tashi ba har yanxu?" Duk da tun jiya da daddare rabonsa
da dakin bayan ya fita amma haka yace "Probably" Tace "Ohk, ni xan tafi" Yace "Ina
za ki tafi?" Ta sunkuyar da kanta tace "Umma ta aikeni gidan wata frnd dinta in
amsar mata sako, so karfe tara matar ke fita aiki, shine tace in je kafin tara"
Khalil yace "But baki yi breakfast ba ai" Tace "Na tashi da azumi yau" Shiru yayi
yana kallonta tace "Idan ta tashi kace mata naje amsar ma Umma sako" Yace "Toh mu
je in ajiye ki" Da sauri tace "Aa ba fa nisa, kuma in sha Allah xan dawo anjima"
Yace "Are you sure?" Tace "Sure" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen" Daga haka
ta nufi kofa ta fita. Goma saura Khalil ya tashi ya shiga dakinsa don wanka yake
son yi kuma yaga bata da niyyar fitowa, kwance ya sameta a kasa, ya tsaya bakin
kofa yana kallonta, ta mike xaune cikin rawar tace "Ba shkkn ba hankalinka ya
kwanta kafana na min ciwo yanzu" Kallon kafar yayi, kafin ya karasa kusa da ita ya
durkusa ya daga kafar, ta sakar masa kuka ta janye, hade rai yayi yana kallonta sai
kuma ya sake jawo kafar, ihu ta kwala tace "Wallahi ciwo yake min" Targade ya ga
tayi a kafar, ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, da kyar ta iya daurewa
ta shiga bandaki da asuba ta wanke bakinta da mouth wash ta dauro alwala ta fito
tayi sallah, kamar kar ta ɗan motsa xuwa bandakin shine kafar yayi mata tsami kafin
gari ya waye, dawowa dakin yayi ta daga kai tana kallonsa, ya karaso gabanta ya
durkusa ya bude man zafin hannunsa, ita dai kallonsa kawai take, bayan ya debi man
zafin ya kamo kafarta, zaro ido tayi tana kokarin janye hannunsa a kafarta ya daure
fuska yace "Kar ki sake ta6a ni Malama" yana gama fadin haka ya fara ja mata kafar
yana kokarin gyara mata targaden, ai bata san sanda ta yunkuro ta rirrikesa ba tana
kukan azaba tace "Nashiga uku Abba" Bai sarara mata ba har sai da ya tabbatar kafar
ta dawo dai dai, kuka kawai take ta kankamesa duk ta hada zufar wahala, bayan ya
sakar mata kafa shi ma ta sakesa tana komawa baya, kallonta kawai yake, ta turo
baki tana share idonta, yace "Sallan asuban ma yafe maki aka yi sbda kinyi targade
ko" Ta hade rai tana kallonsa tace "Ai ni ba kafura bace" Bai ce mata komai ba ya
mike ya nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login