Showing 114001 words to 117000 words out of 268471 words

Chapter 39 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ta kife kanta saman kujeran gefenta tana
maida numfashi, har khalil ya biya masu kudin daki bata sani ba, sai da ya kai
kayansa ciki sannan ya dawo yana kallonta, she looks sick and tired, yace "Nan din
ya fi maki ne?" Ta dago da sauri tana kallonsa, ya juya ya bar wajen, sai kuma ta
mike ta bi bayansa tana tafiya a hankali, bayan yayi leading dinta har zuwa dakin
ya sake fitowa yayi masu ordering abinci a hotel din, daga nan ya fita pharmacy ya
amso mata paracetamol sannan ya koma dakin, kwance ya sameta saman gadon tana
baccin wahala, ya tafi kan kujera dake dakin ya zauna, bayan few minutes aka
kwankwasa kofar dakin ya mike ya tafi ya bude ya amso abincin da yayi ordering
sannan ya kulle kofar ya dawo ciki ya ajiye abincin, dama abinda yake jira kenan,
ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya shirya sannan ya fita dakin don Bolt din da
yayi ordering na location dinsa, da har zai kulle kofar dakin da makulli sai kuma
ya fasa, yana fita hotel din ya shiga motar suka tafi. Tafiyar kusan minti talatin
da biyar suka yi bayan sun shigo wani anguwa wanda kai kana gani kasan ba kowa ke
shigowa area din ba, Drivern bolt din ya kalli khalil da turanci yake tambayarsa
ana shiga ciki dai ko? Khalil yace masa ya shiga kawai, drivern ya ja motar yana
driving din a hankali zuwa gate din dake gabansa, tasowa ma'aikatan dake wajen suka
yi, drivern ya kalli Khalil da ya sauke glass din motar ya gaisa da su sannan
drivern ya ci gaba da tafiya slowly, tafiyar minti sha biyar drivern yayi ya tsaya
dai dai wani gida wanda nan ne location da Khalil ya saka, ma'aikatan dake wajen
suka taso xuwa gun motar, Khalil ya bude motar ya sauka ya daga ma drivern bolt din
hannu sannan ya nufi gate din gidan, bai amsa gaisuwan da securities din ke masa ba
ya shiga ciki kawai, har ya isa main entrance din babban duplex din babu wanda ya
kalla a compound din balle ya amsa gaisuwan da suke masa, direct part din Maminsa
ya nufa ba tare da ya hadu da kowa a hanya ba, ya bude kofar parlonta na farko a
hankali, babu kowa ciki sai sanyin Ac da kamshi me dadi dake tashi a parlon, ya
karasa daya parlon ya shiga, nan ma ba kowa ciki..... Dai dai nan ta fito daga
bedroom dinta da Mai aikinta, tsaye tayi with shock tana kallonsa baki bude, ko
kwakkwaran motsi bata yi sbda shock, ya karasa a hankali ya rungumeta ya lumshe
idonsa, cike da karfin hali tace "Khalil??" Mai aikinta ma haka ta koma gefe ta
rufe baki da hannu tana kallonsa, kasa ce ma Maminsa komai yayi, ta dago kansa tana
kallonsa hawaye cike idonta tana girgiza kanta, yayi mata murmushi cike da karfin
hali yace "I have missed u soo much Mami" Ta kara rungumesa ta fashe da kuka sosai
tace "How did you get here? Who allowed you in? Ta ina ka shigo?" Ya kasa ce mata
komai lkci daya idanuwansa suka kada, Mai aikin ta nufi kofa ta fita ta kullo masa
kofar a hankali, Mami ta ja sa zuwa bedroom dinta tana kallonsa hawaye na sauka
idonta tace "How did you get here son?" Sauke idonsa kasa yayi ya tafi gefen
makeken gadonta ya zauna, tafiya tayi da sauri ta zauna gefensa ta kamo hannunsa
tana kare masa kallo,
ba ainahin haskensa ba kenan, sannan ba haka ya bar gidan nan ba, ta fashe da kuka
sosai ta dafe kanta ta kasa ce masa komai, yayi karfin halin cewa "Kiyi hakuri
Mami, surely everything that has beginning will definitely have an end" Ta dago kai
cikin kuka sosai tace "Amma ta yaya ka shigo gidan nan Khalil?" Kallonta kawai
yake, Bayan few seconds a hankali yace "Abba ne ya kirani" Mami ta zaro ido tana
kallonsa da kyau tace "You mean da kansa ya kiraka??" Khalil ya gyada mata kai yace
"Yea Mami, i don't know what he is seeing me for" Hankalin Maminsa ya kara tashi,
ta hadiye abu da kyar tace "When did he call you?" Khalil ya sauke idonsa yace
"Jiya...." Mami tayi tagumi with different thought running her mind, can ta tashi
tace "Ohk, but u are not moving an inch from here today, ka bari sai nan da jibi,
babu wanda xai san kana gidan nan, you just remain here for now, ok?" Kallonta
Khalil ya dinga yi ya kasa cewa komai, ta mike ta dau wayarta da sauri tayi dialing
number mai aikinta, tana dagawa tace "Bilkisu kada ki ce ma kowa khalil ya dawo
yana gidan nan, make sure babu wanda xa ki gaya ma har su Mimi" Bilkisu tace "Dama
babu wanda na gaya ma Mami" Mami tace "Good" Daga haka ta katse wayar, Khalil dake
ta kallonta yace "But i have to go out before Magrib Mami" Mami ta zaro ido tana
kallonsa tace "Out to where? u are going nowhere for now Khalil, ko nan da second
parlor dina baxa ka fita ba i am telling you, u will remain here for now" Kasa ce
mata komai yayi ya dinga kallonta, ta juya da sauri ta fita daga dakin, ba a dau
lokaci ba sai ga Mami da tray me dauke da different fruits ta ajiye masa, Mai
aikinta dake biye da ita ta ajiye nata tray din, before 5 minutes duk aka cika masa
gabansa da abinci iri iri da natural drinks, bayan mai aikin ta fita Mami ta kasa
daina kallon ɗan nata, tana yi tana share hawayen da ya ki tsaya mata, har sannan
gani take kamar a mafarki ne, gani take xata farka taga babu shi, dawowa tayi kusa
da shi cike da karfin hali tace "Tell me what u want to eat in zuba maka son, fried
rice? Jollof rice, tuwo da miyar taushe, sinasir? Cous cous? Is it the pepper
chicken u are taking first or the cow leg pepper soup?" Kallonta kawai yake ya kasa
cewa komai, lkci daya jikinsa yayi sanyi, he knows he missed all this, ta fashe da
kuka ta rungumesa tace "My prayers was always with you son, i know i have missed u
a lot, i just had nothing to do about it" Kuka take sosai, ya runtse ido yace "Pls
ki daina kukan nan Mami, i was fine and comfortable all through, kawai dai na kan
yi kewanki da kannena sosai hakan ne kadai ke samin damuwa" Mami ta sake sa ta
sauka ta fara zuba masa abincin iri iri a plate, shi dai kallonta kawai yake, bayan
ta gama zuba masa tace "Ka ci duk abinda kake son ci sai kayi wanka son, let me get
u what to change" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, fadawa yayi
saman gadon, gaba daya hankalinsa ya tafi kan Nihad da ya bari ita daya a dakin
hotel, from where will he start convincing his mami har ta hakura ta bar sa ya
fita?? Not even that, don kuwa wannan me sauki ne, now!! from where is he going to
start explaining to Mami cewar ai an masa aure? Ta yaya zai fara mata wannan
gagarumin bayanin and how will she even take it balle uwa uba Abbansa, tunanin
hakan scent cold all over his body, ya mike zaune a hankali yana jin wani sanyi na
shigarsa sosai, tun barinsu kano hankalinsa bai tashi haka ba sai yanzu, ta ina zai
fara wannan bayanin yace ai an masa aure wanda shi ma ba da son ransa ya amshi
auren ba, Yaya iyayensa da relatives dinsa da ma yan uwansa gaba daya za su dauki
wannan babban lamarin, aure without his parents consent, this now is his biggest
challenge so far, rike kansa yayi bayan yaji kansa ya wani tsara masa, After some
minutes Mami ta dawo dakin da kayansa da ta saka a leda don ma kada wani ya gani,
kannen Khalil kuwa duk ta hanasu zuwa ɓangarenta a sunan she is not okay and she
needs privacy, da sauri khalil ya dago bayan Maminsa ta shigo dakin, ganin bai ta6a
abincin ba da damuwa tace "C'mon pls ka sauko ka ci abinci Khalil kar ya huce, ko
dai akwai wani abun dake damunka har yanzu..." Khalil ya dinga kallonta yana
tunanin ta inda zai fara, can dai yayi karfin halin cewa "Mami na ji kince baxan
fita ba, kuma fitan da xanyi yanxu is very urgent" Mami ta zauna kusa da shi cikin
rawar murya tace "I am afraid baxan sake ganinka ba kuma Khalil, kilan idan ka fita
baxa a sake barin ka shigo gidan nan ba, i can't..." kawai sae ta fashe da kuka
tana girgiza kai cikin tashin hankali tace "Haka jikina ke bani, i can't endure
loosing u for the second time son, ban san me zai faru da ni ba idan hakan ta
kasance, me xaka fita kayi Plss?" Ya sauke idonsa da ya kada, bayan few seconds
cikin sanyin murya yace "Mami gidan da nake zama a garin kano da nace masu zan taho
Abuja yau sun hadani da er su muka taho tare da ita, zata karbi admission letter
dinta a wani makaranta da tayi applying a nan, she knows nobody in here Mami, kuma
har yanzu tana makarantar tana jirana" Mami tace "Oh my God, is that so?? Allah
sarki, bari in kira driver sai ka bani numberta in tura masa yaje ya daukota yanzu"
Khalil was shocked at what she just said, Mami ta mike da sauri xata dauko wayarta
ya bi ta da kallo, can sai gata ta dawo kafin ta kira Drivern yayi saurin cewa
"Mami she is just a young girl, bata da waya a hannu, dama sai xata fara karatun ne
za su bata waya, kawai ce mata nayi zan zo in dauketa a makarantar later" Mami dake
kallonsa tace "Toh ka fadi inda kace ta jira ka a makarantar mana in kira Drivern
in sanar masa yaje ya daukota, why are you making this a big deal son??" Khalil ya
kamo hannunta a hankali yace "Mami tsoronki kada in fita a hanani shigowa a bakin
gate ko? but trust me ya sanar masu zan zo ya kuma masu izinin barina in shigo shi
yasa har suka barni na shigo, idan da ba haka bane da baxan ta6a shigowa gidan nan
ba" Mami ta fashe da kuka tace "Bana son kowa yasan ka dawo Khalil" Khalil ya
girgiza kai a hankali yace "Mami, surely in dai yan gari xai tambayesu ko na zo
kuma za su sanar masa na zo ina gidan, kiyi hakuri in je in daukota yanzu in dawo
Mami, i promise you ko awa daya baxa ayi ba zan dawo" Mami dai tayi shiru tana goge
hawayen dake ta sauka idonta, sosai zuciyarsa ya karaya ganin yanda Maminsa ke
kuka, ya rungumeta ya runtse ido yace "Kiyi hakuri Mami, kowa a rayuwar nan da irin
tasa kaddarar, and Alhamdulillah so far" Mami ta gyada kai tace "Haka ne son" Yayi
kasa da murya yace "Ni kaina bana son ganin kowa na gidan nan a yanzu, don haka ki
kwantar da hankalin ki, i will follow the back door idan xan fita..." Cikin sanyin
murya tace "Toh mota fa?" Yace "I will order Bolt" Mami bata kuma cewa komai ba,
yace "In sha Allah idan na dawo zan ci abincin Mami" Yana fadin haka ya lumshe ido
yayi pecking dinta a forehead sannan ya mike, ta bi sa da kallo hawaye na zuba
idonta har ya fita daga dakin.




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

And ur evidence via 07087865788




Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki
kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi
gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai
na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin
keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏


36

Khalil na isa hotel din ya nufi dakin direct ya bude kofar, sosai ya ji gabansa ya
fadi ganin babu kowa cikin dakin, da sauri ya karasa ciki yana kallon abincin da ya
ajiye mata yaga ko ta6awa bata yi ba, lkci daya yaji zufa na keto masa, kallon
kofar bandaki yayi nufi can da sauri ya bude kofar nan ma babu ita a ciki, nan yaji
hankalinsa ya kara tashi ya fice daga dakin ya sauka kasa yana kallon receptionist
din wajen yace "Don Allah yarinyar da muka shigo dazu..." Kafin ya karasa
receptionist din tace "Ta fita ai" kasa daina kallonta yayi, yayi karfin halin cewa
"Ta fita? When pls?" Matar tace "Some minutes ago" juyawa yayi da sauri ya nufi
kofar fita daga cikin hotel din, receptionist din ta bi sa da kallo, Khalil na fita
bakin titi yana waiga gefensa ya ganta can zaune daga jikin hotel din kamar
marainiya, lokaci daya ya hade rai ya nufeta, ita bata ma lura da shi ba tayi nisa
cikin tunanin da take, yana isa dai dai inda take yace "Baki da hankali ne zaki
fito nan bayan kinsan jakata na dakin?" Ta daga kai ta kallesa, sae kuma a hankali
tace "To ba kai nake nema ba" yace "Me yasa zaki nemeni? Saboda me?" Ita dai bata
ce komai ba, sai a sannan ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya juya ya bar ta
wajen, ordering wani bolt din ya mayar da wayarsa a aljihu ya juyo yana kallonta
yace "Ki jira ni a nan" Daga haka ya koma dakin don dauko jakarsa, yana fitowa sai
ga motar, bayan sun gaisa da drivern ya sa jakarsa a booth, ya juya ya kalli Nihad
dake kallonsa, ai bata ma jira yace ta taso ba ta taso ta nufosa, ya zaga ta daya
side din ya shiga motar, tana dai ta tsaye, jin bai ce mata komai ba ta bude
bangaren da take tsaye ta shiga ta jawo kofar motar a hankali. Kamar me Bolt din
dazu wannan ma sae da ya tambayi khalil ko zai iya shiga ciki ganin unguwan da suka
zo, Khalil ya sauke glass din side dinsa ya daga ma securities din wajen hannu
sannan suka wuce, Nihad dai tun da suka shigo anguwan nan take kalle kalle uwa
idanuwanta za su fito, she is wondering where he is taking her to, duk inda suka
wuce sai taga securities, very tight security, bata ta6a jin tsoron kasancewa da
Khalil ba sai wannan moment din, she looked at him looking very afraid, to ko dai
inda ake yankan kai ma zai kaita, sosai gabanta ya dinga faduwa hankalinta yayi
mugun tashi, ta dinga kallon Mad houses din da suke ta wucewa na masu kudi da suka
amsa sunan su kudi a kasar, hakurin Nihad ya soma karewa ta juya a hankali ta sake
kallon Khalil for the 5th time, gabansa kawai yake kallo fuskarsa babu yabo babu
fallasa, Ai bata san sanda ta marairaice masa ba cikin rawan tace "Don girman Allah
ina zaka kai ni? Don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri, ina ne nan ka kawo ni?"
Sai ta sakar masa kuka a hankali jin ya ki ce mata komai, shi dai ko kallonta baya
yi, ko ma wanene yanda Khalil yayi keeping serious and straight face sai ya tsorata
balle Nihad da dama can matsoraciya ce, Shi kam drivern bolt din slowly yake tafiya
sbda Securities that are everywhere don zuwa lkcn gari yayi duhu, amma sai kayi
tunanin rana ce don ko ta ina haske ne tarr, har dai suka isa dai dai gidansu
Khalil, sai dai ba ta inda ya shigo dazu bane, wannan second gate din gidan ne dake
ta baya, drivern ya tsaya yana duban ma'aikatan da suka nufo motar gadan gadan,
Khalil ya bude motar ya sauka, suna ganinsa suka gaishesa suna komawa baya, Ganin
Nihad taki saukowa daga motar ya zaga ta inda take ya bude motar yana kallonta babu
yabo babu fallasa yace "Malama kina bata masa lokaci" Ta marairaice tana kallonsa
cikin rawan murya tace "Don girman Allah ina ne nan din ka kawoni, kayi hakuri ka
gaya min" Gaba daya tayi zuru zuru da ita kamar ba Nihad ba, shi dai kallonta kawai
yake, can yace "Neman taimako na zo yi nan din, tunda kin ga bamu da inda za mu je"
Ta gwalo ido sosai tana kallonsa da mamaki, can tayi karfin halin cewa "Taimako
kuma? Unguwar masu kudi ne sosai fa, ba kowa ne ke shigowa nan ba wallahi, kuma ko
kallonmu baxa su yi ba sai ma su kore mu ko su sakar mana karnuka, wllh ka shigo
idan ba haka ba securities din nan za su iya sa mu tsallan kwado yanzun nan" ya
dafa motar yana kallonta da kyau yace "Sa'armu za mu gwada, kuma ni nasan ina da
sa'a sai in ke ce baki da, Malama ki sakko kina bata ma me mota lokaci" Da sauri
Nihad ta kalli me tukin motar dake jiranta ta sauka patiently, can ta kalli khalil
pleadingly tace "Ni dai don Allah ka zo ka shiga mu koma, babu abinda za su mana a
nan" Yace "Idan muka koma kina da kudin da za mu ci abinci gobe? Ko kina da kudin
da zaki sake biya mana daki a hotel din?" Kallonsa ta dinga yi, lkci daya jikinta
yayi sanyi, hawaye ya kawo idonta, sai kuma ta sa hannu ta share idon nata a
hankali tace "Sai ka bani waya in kira ya Farooq nasan zai turo mana kudi" Yana
kallonta yace "Aa, wannan gidan dai nake son shiga in gwada sa'a ta" Ta kallesa
zata yi magana ya hade rai yace "Kina bata masa lokaci malama" a hankali ta sauko
daga motar tana kallon Khalil hawaye na bin kuncinta, ya daga ma mai bolt din hannu
ya ja motarsa ya bar wajen, cikin kuka tace "Toh ni dai da kace ya maida ni in
jiraka a can hotel din, in ya so kai kadai sai ka shiga gidan" Wani kallo yayi mata
ya nufi gate din gidan da tuni aka bude masa, Ta gefen ido take kallon securities
din gabanta na faduwa don wasu dirka dirkan bayin Allah ne, can dai tana ganin
Khalil ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri, ga mamakinta basu kulle ba suka
jira har ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login