Showing 12001 words to 15000 words out of 268471 words

Chapter 5 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

Nihad makarantarta ance yayi Miliyan biyu xuwa uku, haka naji
su Saminu ke cewa, Maryam Abatcha naji suka ce sunan makarantar" Khalil yace "Toh
ita me xuwa Maryam Abatcha din su nawa ne gun Mamarta" Mai gadi yace "Ai ita ce ta
fari, sai kanninta biyu duk maza, Sudess da Fadil" Khalil bai ce komai ba ya bude
abincin hannunsa ya dau spoon ya fara ci. Nihad na gama cin abinci ta tafi bangaren
Mum dinta, shiryawa ta sameta tana yi hankalinta a d'an tashe, Nihad tace "Mumy me
ya faru?" Mumy tace "Yanxu Jamila ta kirani wai kanwar mijinta ta rasu" Nihad ta
dafe kirji tace "Kaddai Aunty Salma?" Mumy tace "Ita" Salati Nihad ta saki tace
"Allah sarki, Allah ya ji kanta, Mumy in sa Hijab mu je" Mumy tace "Ki sameni a
waje, drivern bai fita ba dai ko?" Nihad tace "Mumy kiyi driving din mana ko kuma
ni inyi" ko tanka ta Mumy bata yi ba ta dau handbag dinta ta fita, bangaren Umma ta
fara shiga ta sanar mata rasuwan, Umma tace "Allah Ubangiji ya ji kanta, in sha
Allah idan xaki koma gobe sai mu je muyi gaisuwa mu ma, Allah ya ji kan musulmi"
Mumy tace "Ameen, Allah ya kai mu goben" Part din Abba ta nufa, shi ma ta sanar
masa rasuwan daga haka ta fita compound, Mai gadi yayi kasa da murya yana ma Khalil
magana yace "Yauwa kaga Hajiya Mumyn ita ce uwar Nihad, ina ga fita xata yi" Muryar
Mumy suka ji tana cewa "Aminu Drivern ya fita ne?" Mai gadi ya mike da sauri yace
"Aa gashi nan Hajiya a kusa da ni" Khalil ya mike ya gaisheta da ladabi, Mumy ta
amsa cikin mutuntawa tana kallonsa daga sama har kasa, sai kuma tace "Shi ne
Drivern?" Khalil yace "Ni ne Hajiya" Mumy tace "Don Allah xaka ajiye ni nan Hotoro
ne idan ba damuwa" yace "Toh Hajiya" Makullin motarta ta mika masa, ya amsa da
ladabi Aminu ya nuna masa motar Mumy, gun motar ya nufa, Mumy ta daga wayarta dake
ringing ta kai kunne, Nihad ce ta fito ita ma sanye da Hijab har kasa, tana ganinsa
cikin motar Mumy ta wani daure fuska, bayan yayi warming motar ya karaso da motar
har inda Mumy take ya tsaya, Mumy ta bude bayan motar ta shiga, Nihad ma ta bude
baya xata shiga mumy tace "Baxa ki xauna a gaba ba" Without looking at her mum tace
"No, i will be more comfortable at the back" Kulle motar tayi ta bude handbag dinta
ta ciro tsadadden shade dinta ta saka, Khalil ya ja motar Mai gadi na daga masu
hannu har suka fita compound din ya kulle gate, cike da nutsuwa Khalil ke driving
din xuwa hotoro da Mumy tace daga Nasarawa GRA. Suna isa dai dai family house din
mijin kanwarta Jamila ta sa yayi parking, Mumy ta fara sauka daga motar tana
kallonsa tace "Ko xaka je ka dawo xuwa bayan magrib ka daukemu, kar a bar ka kayi
ta jira a nan" Yace "Aa babu komai xan jira daga can tsallaken in sha Allah" Jin
haka Mumy tace "Toh shkkn" Daga haka ta juya ta shiga gidan rasuwar Nihad na biye
da ita a baya. Nihad bata yarda ta xauna cikin jama'a da suka fara taruwa gidan ba
ana koke koke, ta nemi waje at the far end of the compound ta inda generator din
gidan yake ta xauna ita daya a wajen, Iphone dinta ta ciro a jakarta, taga missed
calls din Husnah da Naf, da sauri tayi dialing Number Husnah, yana fara ring Husnah
ta daga tace "Ina kika shiga ne babe" Nihad tace "Wllh mun fita tare da Abba ne,
and i left my phone at home, what's up kun fitan ne?" Husnah tace "Tun yaushe, ke
in gaya maki akwai labari wllh" Nihad tace "Yanxu dai kuna ina?" Husnah tace "Tahir
guest palace, kiyi kokari ki taho yanxu kar ayi ba ke" Nihad tace "Husnah Hijab fa
ne a jikina, mun xo wani gaisuwa da Mumy a hotoro" Naf ta amshe wayar don a
handsfree Husnah ta sa, tace "Haba dai minti nawa kin shiga boutique Nihad" Nihad
tace "Toh shkkn bari in amshi makullin motar Mumy a hannun driver in taho kawai,
nasan before magrib xata koma gida kafin nan na dawo" Naf tace "Shkkn xa mu jira ki
a Tahir din be fast pls" Katse wayar Nihad tayi tana bin compound din da ido trying
to figure out where her mum is, har ta kare xaga tsakar gidan da idanuwanta bata ga
mumy ba alamar dai ta shiga cikin gidan, tashi tayi da sauri ta nufi gate ta bude
ta fita, nan ma ta dinga waige waigen inda xata hango drivern, tun da ta fito ya
ganta, don yana xaune daga tsallaken bakin titi wajen mai siyar da Fruits, hada ido
suka yi ta tsallaka da sauri ta nufesa babu yabo babu fallasa tace "Hey ka bani
makullin mota xan mika sako in dawo yanxu" Kallon me siyar da fruits din yayi kamar
dai da shi take, nan da nan Nihad ta harxuka cikin tsawa tace "Malam da kai nake fa
kake kallon wani" Ya kalleta sai kuma ya kara kunnensa gaba yace "Na'am?" Nihad was
soo mad at him, xuciyarta ya dinga tafarfasa ta rasa abun ce masa, shi ma kuma bai
kuma cewa komai ba sae ma dauke kansa da yayi, ruwan da ta gani cikin roba gun me
siyar da fruits din ta fixgo a fusace ta juye masa gaba daya tun daga saman kansa,
duk mutanen dake wajen suka kame a inda suke baki bude suna kallonta da mamaki,
Tana huci cikin bacin rai tace "Kai din banzaaa kana driver din gidanmu har xan
dinga maka magana kana mayar ni mahaukaciya, who do u think u are?? Waye kai??"




To gain access to the book, contact me directly via👇🏻



✍🏻
07087865788

5️⃣ *NIHAAD* 💖💖




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




~~~~~



Tun da Nihad ta kwara masa ruwan bai dago kansa da ya sunkuyar ba, lkci daya
kamanninsa suka sauya, sae kuma dai ya daga kai ya kalleta, Tana hararansa tace "To
wllh kaji ka sani, ka rasa aikinka a karkashin mu daga wannan moment din, yau ba
sai gobe ba xan sa Abbana ya dau wani sabon driver din ya sallameka, baka yi
deserving aiki a gidanmu ba..." Mai fruit din na girgiza kai rai bace yace "Amma
baki da mutunci, baki da kirki, baki san darajan da Allah yayi ma d'an Adam ba,
kuma uwa uba baki da tarbiya wllh..." Tayi masa wani matsiyacin kallo tace "Kai
kuma wa ya sako da kai Malam? Kai a wa xaka sako min bakinka cikin lamarina? Ina
ruwanka? Ko xaka tilasta ni in san darajan d'an Adam din ne??" Wani tsaki ta ja
tana harararsa, Wani mutumi a wajen ya karbe a fusace yace "Xa ki samu dai dai dake
a duniya wllh, ke yanxu irin tarbiyar da aka maki a gidanku kenan? Tir kuwa da
tarbiyan gidan nan naku, tir da tarbiyan da iyayenki suka maki, idan haka arxikin
ke sa mutane a hanyar halaka Allah ya hanamu..." Nan kowa na wajen yayi mata caaa,
ko wanne na gasa mata magana son ransa har da masu xaginta, abun da tayi ya basu
mamaki sosai ya kuma ta6a su, barin yanda suka ga khalil yayi shiru yaki ce mata
komai, har da masu ce mata arxikin ma sai sun nemesa sun rasa, da surutunsu ya
isheta ta ja dogon tsaki tace "Duk ku ji da abinda ya dame ku malamai, bani da ikon
hukunta driver din gidanmu aka ce maku, ina ruwanku da abinda na masa banda sa ido
irin na mutane" Tana fadin haka ta juya, sai ta kara jin ranta ya wani baci, yanxu
ya xata yi da xuwa wajensu Husnah, kwata kwata bata son hawa adaidaita, duk k'uran
duniya ya kare ma mutum, kuma ma ai ba girmanta bane taje Tahir guest palace a
adaidaita Sahu, bata sake bi ta kan mutanen wajen ba ta tsallaka titi abun ta, bin
ta da kallo kawai Khalil ke yi, mutanen wajen sai hakuri suke basa, wani dattijo
dake tsaye shi ma wajen a kan idonsa aka yi komai ya dafa khalil cike da jimami
yace "Kayi hakuri yaro, rayuwa ce, amma bari in baka shawara wannan aiki ba shine
xai kai ka aljanna ba balle ka ji shakkun barinsa, ka ajiye masu makullinsu, da dai
wannan axababben walakancin gwara ko dako ne kayi ka ci abinci, balle siffarka bai
yi kama da ta rago ba, ga ka namiji har namiji, ka nemi wata sana'ar sai Allah ya
dubeka, ni ko duk arxikin duniyar nan xa a tattara min amma a hada min da walakanci
to wllh na hakura da arxikin gwara inyi ta xama da talauci na, balle irin wannan
walakanci da cin fuskar da yarinyar da aƙalla xaka bata shekaru sha uku ko sha hudu
tayi maka a kan titi a bainar nasi babu kunya babu tsoron Allah, sannan babu ladama
a tattare da ita, aa gaskiya ka sake duba lamarin nan dai, Allah Ubangiji ya saka
maka wannan cin xarafi da cin mutuncin da tayi maka" Wani matashi ne da gidansu ke
nan bakin titin ya fito da wata jallabiyarsa yana kallon khalil yace "Ga wannan mu
shiga wancan shagon sai ka canxa, Allah ya saka maka abinda tayi maka" Mikewa
Khalil yayi ya amshi rigar yana kallon mutumin yace "Nagode sosai" shagon da ya
gwada masa ya nufa, duk mutanen wajen suka bi sa da kallo cike da tausayi barin ma
da suka ga ya ki cewa komai, ya shiga shagon, me shagon ya basa waje ya canxa
kayansa, wayarsa dake aljihunsa ya fara cirowa ya dinga jujjuya wayar kafin ya
ajiye gently a saman bench, canxa kayan yayi, me shagon ya taho masa da babban leda
don ya linke tasa kayan ya sa a ciki, amsa yayi ya masa godiya sannan ya linke ya
saka a ledar yana rike da ledar ya fito shagon, mai shagon ya kalli wayarsa da ya
bari kan bench, ya d'an bude ido yana sake kallon wayar sannan ya kalli khalil da
har ya wuce, da sauri yace "Malam ka bar wayarka" Dawowa Khalil yayi da sauri ya
dau wayar, ya zira a aljihun jallabiyar, yana ɗan murmushi yace "Nagode kwarai"
daga haka ya fita me shagon ya bi sa da kallo kamar me naxari. Mumy ce tsaye bakin
gate ta dalilin kiranta da aka yi ganin Nihad can tsallake ga jama'a a tsattsaye
sun taru an sa ta a tsakiya, Mumy na kallon Nihad tace "Lafiya Nihad, me ke
faruwa?" Nihad ta rungume hannunta tace "Mumy ko ba wancan driver din bane, wllh
bashi da kunya ko kadan" Mumy tace "Me yayi maki?" Nihad tace "Wai fa Sajida ce
tace min tana anguwan nan, dama akwai wani textbook da nake son amsa a wajenta,
shine nace ya d'an ajiye ni, can gaba ne ba nisa, shine fa yake gaya min maganar
banxa, shi wai baxai je ba" Mumy tace "Sai aka yi yaya?" Nihad na yatsina fuska
tace "Shikenan, su kuma wa encan bansan me yasa suka taru haka ba" Mumy tace "Ina
drivern?" Nihad ta kalli tsallaken titin ta ga ya fito wani shigo da jallabiya,
Kafin ta ce komai Mumy tace "Mu je wajen nasa" Da sauri Nihad tace "Aa Mumy kyalesa
kawai, ni ai ban biyesa ba, haka yayi min daxu ma a gidan Baffa, aa kawai dai ki
bar sa" Mumy tace "Tsallaka mu je nace, bana son surutu" Nihad tayi shiru ganin
Mumy ta tsallaka ta bi bayanta, amma gaba daya she isn't comfortable, Mumy ta nufi
driver, yana ganinta yace "Hajiya har kin fito?" Tace "Aa ya sunanka?" Yace
"Ibrahim" Tace "Ohk, ya ku ka yi da Nihad?" Gaba daya mutanen wajen kallonsu suke,
Nihad dai na tsaye ta ki karasowa ta wani sha kunu, Mumy ta kalleta tace "To karaso
mana Nihad" tana tafiya a hankali ta karasa inda suke tsaye da Umma ce baxa ta ji
wani shakku ba xata biyo amma Mumy bata da tabbas, Mumy na kallon khalil tace "Ina
jin ka" Nihad ta amshe tace "Na fa gaya maki abinda ya faru Mumy, nan nan wajen
Sajida xai ajiye ni in amso textbook shine yake min maganar banxa har sa zagina, ni
ko biyesa ban yi ba" Mai fruit dake tsaye shi ma ya saki salati yace "Wllh karya
take Hajiya, ba haka aka yi ba, ai ina nan a xaune, bokiti guda na ruwa ta dauka ta
kwara masa kawai ba laifin tsaye balle na xaune, baki ga ya canxa kaya ba, duk a
kan idonmu aka yi komai" Mumy bata bari me fruit ya rufe baki ba ta tsinka ma Nihad
mari, Nihad bata gama recover ba ta kuma sauke mata wani, wanda hakan ya ba mutane
da yawa dake wajen mamaki, dama ashe ana hukunta 'ya yan masu kudi, hakan ya kuma
mugun burgesu, fuska daure Mumy tace "Wuce ki basa hakuri" Nihad da tunda aka
haifeta tana jin ba a ta6a marinta ba ta dinga ganin dishi dishi, ta dafe kuncinta,
wani tsawa da Mumy tayi mata sai da ya dada hargitsa ta, Mumy tace "Tafi ki basa
hakuri nace kar 6allaki a nan" Bata san sanda ta nufesa ba ta tsaya a gabansa
hawaye cike idonta cikin rawan murya tace "Kayi hakuri" Shi dai kallon Mumy yayi
yace "Hajiya kiyi hakuri duk bai kai haka ba" Mumy ta bude handbag dinta fuska a
murtuke ta fiddo dubu biyu ta jefa mata nan kasa tace "Ki tsayar da Tricycle ki
kama hanyar gida yanxun nan, kuma ina nan biyo ki a baya, dama don kiyi displaying
bad altitude dinki kika biyo ni kenan, xan yi maganinki" Kuka kawai Nihad take tana
jin kamar ta kwanta nan kasa tayi ta birgima ko xata ji sanyi, ko damuwa da mutanen
dake kallonta wajen bata yi ba, Mumy na kallon khalil tace "Kayi hakuri don Allah
Ibrahim, ita kuma xa mu hadu a gida" Daga haka Mumy ta tsallaka ta koma cikin gidan
rasuwa. Nihad ta bude jakarta tana kuka sosai ta ciro wayarta tayi dialing number
Abba, yana fara ringing Abba ya daga ta kara rushewa da kuka me karfi tace "Abbaa"
Sai ta xama abar kallo a wajen, Abba yace "Subhanallah what happen Nihad?" Kin cewa
komai tayi banda kuka babu abinda take rera masa, Abba ya katse wayar ya kira Mumy,
tana dagawa yace "Where is Nihad?" Mumy tace "What about her?" Abba yace "Ta kirani
yanxu tana kuka, and she is not responding to my questions" Mumy tace "Ka rabu da
ita, ai muna tare, sai anjima" Daga haka Mumy ta katse wayar. Sai bayan magrib Mumy
ta dawo gida, Khalil yayi parking ya sauka daga motar, Mumy ma ta sauka, da ladabi
ya mika mata makullinta, ta amsa tace "Nagode, kuma kayi hakuri da abinda yarinyar
nan tayi maka ka ji" Ya d'an yi murmushi yace "Ba komai Hajiya, nagode" Juyawa tayi
ta shiga cikin gidan, shi kuma ya nufa gun mai gadi. Umma na jin shigowar motar
Mumy ta shigo main parlor, Tana tsaye tana jiranta har ta shigo, Umma tace "Kin
bani mamaki Maryam, yanxu a kan wani shegen driver xaki kama yarinya a titi cikin
mutane ki doka sbda rashin sanin ciwon kai?" Bata ba Mumy space din magana ba ta ci
gaba rai a bace, "Wallahi kin ban mamaki da gaske, ke a dole sai kin xama me kirki
me mutunci a idon duniya? yanxu menene amfanin abinda kika ma Nihad a bakin titi a
kan wani matsiyacin talaka ɗan iska can? To wllh in dai ba Ibrahim ne ubansa ba sai
ya bar gidan nan yau, aikinsa ya kare a gidan nan, idan yayi ma Nihad ya ci bulus
har kuma da tsaraban mari da duka da ya ja mata to wllh babu er da xai ma hakan a
gidan nan ya kwana kalau, ba a haifi Ubansa yace xai ma Nihal ko Amina haka ba, don
haka yau ba sai gobe ba xai kama gabansa, mu bama hulda da yan iska, sau biyu kenan
duk a yau ta kawo min kararsa, ashe d'an iska Habibu ya turo ma Alhaji ba a sani
ba, to kuwa xai kama gabansa yanxu yanxun nan, kwanansa daya dubi isa da mulki da
yake gwadawa ya yanmu?, nan gaba ai har Alhajin ma cewa xai yi baxai tuka a mota
ba" Mumy bata kuma tsayawa ta saurareta ba ta wuce part dinta. Mai gadi na kallon
Khalil bayan ya gama shanya kayan da Nihad ta xuba masa ruwa yace "Hakuri kawai
xaka yi, amma lallai yarinyar nan shaidaniya ce a siffar mutum..." shi dai khalil
bai ce komai ba, mai gadi yace "Ga can abinci da aka kawo mana, na debar maka naka
na ajiye" Khalil yace "Aa na koshi, yanxu wanka nake so xan yi" Mai gadi yace "To
mu je in raka ka bangarenku" A tare suka nufi boys quarters din bayan mai gadi ya
dauko wata er jakar kayan Khalil da ya bari a dakinsa tun xuwansa da safe, suna
shiga parlon banda warin kartin maza babu abinda yake, ko ina soo dirty and unkept,
ga saminu yayi bake bake kan 3 seater yana kallo ga plate din abinci da ya ajiye
saman kujeran, Isiya na one sitter yana shan rake da yake tarawa nan kasa gefensa,
Shafi'u kuma na 2 seater ga tasa plate din abincin ya gama ci ya bari saman kujera,
Mai gadi ya nufi Saminu yayi kasa da murya yace "Saminu ko xaka ɗan sam masa waje
ya dinga
kwana a dakinka, ka gansa bashi da matsala wllh..." Ko rufe baki Mai gadi bai yi
ba Saminu yayi saurin cewa "Aa nima dakin yayi min kadan" Mai gadi ya kalli Isiya
dake jin abinda ya ke cewa, kafin mai gadin yace masa komai yace "Toh wai ba falo
kace xai dinga kwana ba" Shafi'u yace "Shi dai na gani, Duka dakunan kaga ai babu
waje, wa ke son takura" Khalil ya amshi jakarsa dake hannun mai gadi, mai gadi yace
"Ko xa mu je can dakin nawa ka dinga kwana" Khalil yace "Aa kar ka damu, kayi
komawar ka bakin gate" Yana fadin haka ya nufi space da aka tanadar domin dinning
area a parlon, Kofar da ya gani ya bude ya ga kitchen ne, ya dinga kallon yanda
suka mayar da kitchen din kamar na mahaukata duk da ba girki suke ba, tsintsiyar da
ya gani wanda bai ga alamar ana amfani da shi ba ya dauka, ya hau share dinning
area din, mai gadi ya juya ya fita daga parlon da sauri jin kamar ana horn. Cikin
yan mintuna khalil ya gama gyara area din har da mopping, yana gamawa sai ga mai
gadi ya kawo masa wani yakunannen zanin gado, amsa yayi ya shimfida a saman tiles
din wajen, sannan ya bude window, ya shiga bandakin dake parlon, still yayi yana
bin bathroom din da kallo, ko public toilet is far far better and neater than this,
fita yayi ya koma gun mai gadi don ya amshi omo. Abba yayi shiru yana sauraron
Mumy, Mumy ta ci gaba tace "Kawai ita Hajiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login