Showing 72001 words to 75000 words out of 268471 words
bata
kara jin damuwan video dinta da ya bazu duniya ba sai a yanzu, dama haka abun ya
tafi viral, a ajin ma sai satan kallonta ake ana kuskus, kai har ma da masu shigowa
duk da ba department dinsu ba don kawai a zo a ganta, sai a sannan tayi da ta sanin
fitowa, kuma fitowar ma da ɗan karamin mayafi, daga karshe dole su Naf suka dauketa
suka fita makarantar xuwa hostel dinsu, Nihad ta zauna gefen gado lkci daya hawaye
ya kawo idonta, Husnah tace "Kin ji ki, meye abun damuwa, abinda ba kanki farau ba
kuma ba kanki za a kare ba, duk dan iskan da ya isa ya tinkare mu yace ai kece a
video yaga yanda xa mu ci ubansa, ni ai baki ce min xaki taho makaranta yau ba da
na hanaki don su yanxu ma suke tashen labarin, kuma ana ta jira aga kin shigo
makaranta sai ga ki yau, ni ban ta6a ganin munafukai yan sa ido marasa aikin yi
kamar yan makarantar nan namu ba, abu kusan sati daya amma kullum maimaita zancen
ake kamar yau ya faru" Nihad ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tace "Da na sani
ban fito ba" Naf tace "Surutun mutane zai sa ki fasa rayuwarki yanda kike so? Ai ba
a biye ma mutane, gwara su yi ta ganinki din har su gaji su yi shiru zancen ya
mutu, yanzu dai ina kika baro ɗan rainin wayon Drivern can?" Nihad na goge idonta
cikin sanyin murya tace "Toh meye hadina da wannan kuma kike tambayata" Naf tace
"Aa babu hadinki da shi kam, ni ai na ga kokarinki ma da kike iya kwana gida daya
da shi, da ni ce kwasan kayana xan yi in bar gidan iyaka Abba yayi bambami a wuce
wajen" Nihad ta kalleta tace "Abbanmu yace xai yi disowning dina if i try anything
of such" sai kuma ta fashe da kuka sosai, Naf tace "Aa ba kuka xa kiyi ba, nema ma
kanki mafita xa ki yi" Nihad tace "Don Allah ku dawo gidan mu zauna gaba daya a
can" Naf tace "Dama gobe muka yi ai za mu je can din" Nihad tace "Tunda na fito yau
don Allah ku dau kayanku kawai mu koma can gaba-daya, the house is nothing but a
living hell for me" Naf ta kalli Husnah dake ta danna wayarta bata ce komai ba tace
"Husnah ya kika ga" Husnah tace "Duk yanda ku ka yi" Naf tace "Toh kawai duk mu dau
kaya ko kala biyar biyar ne mu tafi can din gaba daya" Nihad tayi murmushin jin
dadi tace "Amma naji dadi Nagode wllh" Zully tace "What are friends for, ai
amfaninmu kenan" Nihad
tayi kasa da murya tana kallon Naf tace "How about Aliyu?" Naf tace "Hmm, kinsan
he is off social media tun da abun nan ya faru, to in gaya maki 3 days ago mun yi
chatting da wani frnd dinsa yake ce min ai ba shi da lafiya ma" Nihad tayi narai
narai da ido tace "Da gaske?" Naf tace "Wllh kuwa bari ma in nuna maki chatting
din" Jawo wayarta tayi ta bude ta shiga chatting dinta da wani abokin Aliyu ta mika
ma Nihad wayar, Nihad ta amshi wayar jiki a sanyaye ta dinga bin chat din, abokin
gaya ma Naf halin da Aliyun ya shiga bayan faruwan lamarin yake, ya kuma ce mata
har su abokanansa yayi isolating din kansa daga cikinsu ba ma social media ba
kadai, abokin ya dinga nuna yanda Nihad ta kwafsa ga shi Aliyu yayi trusting dinta
sosai kuma ya sa ran zai aureta duk da tulin manya manyan babes dinsa, Nihad ta
hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka tace "I don't know who did this to me, i
don't know who is this that ruined my happiness" Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace
"Na fi ki son mu gano wanda yayi maki haka Nihad, amma abun akwai rikitarwa ni
wallahi kawai zuciyata ta kasa yarda cewar ke ce a video din, ke baki zama da
undies haka kamar yanda mu muke yi, sannan duk party tare muke zuwa balle ace wani
partyn kika je aka maki haka, abun dai akwai confusion sosai wallahi, wanda ya
sanki sosai sosai ne yayi maki wannan abun, i wish Abba xai ajiye duk wani fushi ya
tsananta binciken ta ina wannan video din ya fito" Zully ta sauke ajiyar xuciya
tace "Ai na dau darasi ni kam, ko daga ni sai singlet da skin tide baxan sake xama
a waje ba balle undies, na saka kaina a shoes din Nihad ya fi a kirga but luckily
the shoe did not even size me, waiii ai ni kashe ni kawai xa ayi a gida wallahi"
Naf ta tabe baki tace "Koma waye da kansa zai tona ma kansa asiri nan ba da dadewa
ba" Nihad ta share hawayen da ya ki tsaya mata tace "Pls Naf try calling Aliyu ki
ga ko zai daga" Naf tace "Toh Allah ya sa ya daga, ko kuma ma dai Allah ya sa ya
shiga" Contacts dinta ta shiga tayi dialing number Aliyu, ai ko ya fara ringing,
gaban Nihad ya dinga faduwa tana kallon wayar, su kansu gaba daya kallon wayar
suke, sai gashi kuwa ya daga, sai da Nihad taji xuciyarta ya kusa shigewa cikinta,
Naf tace "Hello Aliyu what's up?" Daga daya bangaren cikin cool voice yace "Fine
Nafisah, how are you doing" Tace "Cool, ya garin" Yayi shiru, tace "Are u there?"
Yayi kasa da murya yace "U saw how ur frnd played with my heart right?" Nihad ta
kauda kanta hawaye sai zarya yake a fuskarta, Naf tace "Calm down Aliyu, duk wannan
abun set up ne ba wani abu ba, ka fi kowa sanin halin Nihad, sannan mu da muke tare
da ita always xa mu shaideta, wllh wllh Nihad bata tsayawa a cikinmu daga ita
singlet balle undies, wannan lamarin da rikitarwa yake, wa ya sani ko anyi hakan ne
don a raba ku tunda anji xaka turo gidansu" Aliyu yace "But i have warned her
severally Nafisah, na sha ja mata kunne duk yawace yawacen zuwa party ta daina, but
unfortunately bata daina ba, and ga abinda ya faru daga karshe" Naf tace "Kai wai
wa yace maka a wajen party aka yi mata haka? Ko a gida baxa ayi iya yi ma mutum
haka ba sai wajen party kawai? Kai dai kawai ka kyale makiyi Ali" Aliyu yace "I am
so heartbroken Nafisah" Naf tace "So is she also" Yace "Tana ina yanxu?" Naf ta
kalli Nihad sai kuma ta ɗan yi murmushi tace "Mun zo gidansu ne daxu ganin halin da
take ciki shine nace bari dai kawai in kiraka" Yayi shiru, tace "In kai mata wayar
pls?" Nan ma dai shirun yayi, tace "Don Allah kar kace A'a, ko sai kaji ta mutu
xaka fara da ka sani an kai mata wayar? Wallahi she is seriously sick" Yace "Kai
mata" tace "Yauwa my guy" kallon Nihad tayi tana Murmushi, ita dai Nihad ta
sunkuyar da kanta kawai, Naf ta kamo hannunta ta saka mata wayar a ciki, a hankali
ta kai kunne tayi sallama. Aliyu yace "Now u get the reason why nake rabaki xuwa
party?" Bata iya ta ce masa komai ba ta a goge idonta, yayi kasa da murya yace "Why
Nihad, why?" Cikin rawan murya tace "I don't know how everything happened, kayi
hakuri don girman Allah" yace "In yi hakuri Nihad? Ta yaya iyayena xa su amince da
aurenmu bayan duk sisters dina babu warce bata ga wannan video din naki ba, hatta
mum dita ta gani, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nihad dai bata ce komai ba,
Yace "How will we mend this damage?" Nihad tace "Abbana yace min wai ya min aure"
Aliyu yace "Ban gane yayi maki aure ba, kina nufin aure Abba xai maki?" Cikin kuka
tace "Ehh har ya min" Aliyu yace "Stop it Nihad, yaushe yace maki haka" A raunane
Nihad ta sanar masa yanzu ita da khalil suke zama gida daya, kuma Abba ya sanar
mata wai yayi mata aure da shi, lkci daya ya birkice mata yace "Baby yanxu kina
nufin aure aka maki, aure da drivern nan na gidanku?" Nihad ta girgiza kai da sauri
tace "Ni ba a min aure da shi ba, kawai Abba ne ke fadan hakan, ni ban yarda an min
aure da shi ba" Aliyu yace "Nooo, it can never be, not when i am alive, hakan baxai
ta6a yiwuwa ba, na yi isolating kaina from everything na kwana biyu ne but nasan
baxan ta6a iya rabuwa dake ko da nayi attempting din yin hakan ba, i know i will
come back to you, kuma ko iyayena bana jin xa su hanani in aureki don sun san ina
son ki, ko da nude video dinki ne yayi yawo i stil love u Nihad, and i will still
marry u" Nihad dai ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai yace "Ki kulan min da
kanki Nihad, do not break my heart for the second time pls, sannan ta ina xan dinga
samunki ko 2 days ago i tried ur number naji switch off" a hankali tace "Xan kiraka
da sabon line dina idan na koma gida" Yace "I will be expecting pls" Sallama suka
yi, Naf ta amshi Wayarta tace "Alhamdulillah" Nihad ta ɗan yi murmushi, Husnah tace
"Gaskiya Aliyu ya san kaddara, yanxu ke kuma sai ki san duk yanda xa kiyi ku raba
jaha da wancan driver din, koma yaya xa ayi kawai ya sake ki tunda Aliyu is still
willing to marry u" Nihad ta kalleta tace "Ya sakeni?? To da aurena yayi da xai
sakeni? Ai kawai xama muke gida daya bisa umarnin Abba, but i am for Aliyu alone"
Zully tace "Atoh, kunsan akwai wani aure da xaka ji sa kamar wasan yara, to irin
auren nan naku da drivern kenan, ko ni bana kallonsa a matsayin mijin Nihad
wallahi, kilan kawai Abba is playing u, amma ta yaya ma xai ce ya maki aure da
dreba" Nihad tace "Toh kun ga lkci na wucewa mu tafi pls" Naf tace "Bari in kara
watsa ruwa" Zully ta mike tace "Ina zuwa in kwaso kayana" daga haka ta fita daga
parlon, Husnah ta kalli Nihad tayi kasa da murya tace "In baki shawara? Toh wallahi
kar ki yarda su wani bi ki, gwara kiyi tafiyarki ke kadai daga baya ni kadai sai in
biyoki gidan, idan ba haka ba akwai matsala" Nihad tace "Matsalar me fa?" Husnah
tace "Toh shkkn ki tsaya tambayar ta me, naga dai ni kika fara sani kafin su, kuma
ta dalilina kika san su, don haka kawai yanxu kice masu gidanku xa ki daga can ne
xaki wuce gida kina komawa gida kuma xaki kira kice mu taho gaba daya" Nihad tace
"Toh shkkn" Mikewa Husnah tayi ta fita daga dakin. Khalil ya fito compound jin ana
Knocking gate, yana bude gate din ya ga Farooq a tsaye, welcoming dinsa Khalil yayi
with smile all over his face, Khalil ya rufe gidan suka koma can parlor tare,
Farooq na cewa "Gobe xan koma aiki shine nace bari in shigo yau dai" khalil yace
"Allah sarki" Suna shiga parlon Farooq na bin ko ina da kallo yace "Ina take?"
Khalil bai basa amsa ba kawai ya tafi kitchen don ya dauko masa ruwa, Farooq ya dau
throw pillow da ke kan kujeran da yake kokarin zama sai ya ga Iphone, duk tunaninsa
na Nihad ne duk da a gabansa Abba ya kwace Iphone din nata, Farooq ya zauna yana
jujjuya wayar amma sai ya ga ba na Nihad bane, dai dai nan khalil ya fito daga
kitchen with bottle water and glass cup, still yayi yana kallon Farooq.....
Nihaad is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence of payment via 👇🏻
07087865788
24
Farooq ya daga kai ya kallesa har sannan kuma wayar na hannunsa yana jujjuyawa,
karasowa parlon Khalil yayi ya ajiye ruwa da glass din hannunsa, ya ki yarda su
hada ido da Farooq yace "Oh kamar fa na makotanmu ne da suka shigo daxu, babu
tantama wayar daya daga cikinsu ne, ban ma kula ba sai yanxu...." Farooq dake ta
kallonsa ko kiftawa babu kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Now tell me who you
are Khalil!!!" Khalil ya ɗan yi jim, can yace "Ban fahimce ka ba" duk wannan abun
ya ki yarda su hada ido da Farooq, mikewa Farooq yayi ya dafa sa yace "Tell me what
ur mission is, what is ur intention of coming to stay with us? ka gaya min kai
wanene, menene manufar xuwanka gidanmu" Sai a sannan khalil ya daga kai ya kallesa
amma bai ce komai ba, Farooq yace "From day one, i know u are not who u claim u
are, u lied about ur personality to us, you have a mission definitely, be it
revenge, spy, Dss.... And what have u!" Khalil ya girgiza kai a hankali yace "I
have no mission Farooq, and my intentions of staying with u people is pure, aiki
kawai ya kai ni gidanku, baya ga shi kuma babu wani abinda ya kai ni gidanku...."
Farooq na kallonsa keenly yace "I will like to know u more" Khalil ya koma ya
zauna, kamar baxai ce komai ba sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "Duk abinda na
gaya maka a kaina a baya hakan yake, i am a nobody like i said earlier, i was just
opportune to go to school, i was opportune to be a literate, nayi diploma a fce nan
kano wanda har yau ban samu aiki ba, bayan wannan komai game da ni na gaya maka a
baya, u can even call Habib and confirm" Farooq yace "But meyasa kace iyakarka
secondary?" Khalil yace "Ina tsoron kar a ki bani aiki a gidan ne" Farooq dai
kallonsa kawai yake as if forcing himself to believe him, Can yace "Wani course din
kayi?" Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace "Business Admin" Farooq ya koma ya
zauna kamar me naxari, ta gefen ido Khalil ke kallonsa hoping he is fully
convinced, Farooq na daga kai Khalil yayi saurin dauke idonsa daga kansa, Farooq ya
sauke wani ajiyar xuciya yace "Ohk then, in sha Allah xa mu yi magana da Abba,
nasan xai yi iya kokarin ganin ya samar maka aiki dai dai da qualifications dinka"
Khalil yace "Toh nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Farooq yace "Ameen" Bayan
few minutes Farooq yace "Ina Nihad din?" A hankali Khalil yace "Ban san inda ta
tafi ba" Da wani expression Farooq yace "Ban gane baka san inda ta tafi ba, isn't
she under ur control now?" Khalil yace "Nayi kokarin hanata fita amma ta ki" Farooq
yace "What? Sai kai kuma ka saka mata ido har ta fita?" Khalil dai yayi shiru.
Nihad ce ta sauka bakin gate ita da Husnah da tayi ma kawayensu karyan xata je park
ta amso sako, nan kuma ta gaya ma Nihad inda xata jira ta su hadu sannan su taho
gidan gaba daya, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin motar ya Farooq a waje, Husnah ta
zaro ido tace "Toh yanxu ya xa mu yi kenan?" Nihad ta hade rai tace "Toh ba daga
makaranta nake ba, shiga kawai za mu yi, ai ba yawo na tafi ba" Husnah tace "Aa,
kinsan yayan nan naki ba saiti garesa ba haka kawai inje ya ritsa da ni" Nihad tace
"To me xai min? Kawai mu shiga idan ya so sai ki zaga bayan gidan ki nemi waje ki
zauna, idan ya tafi xan fito in gaya maki sai ki shigo" Husnah tace "Toh gwara haka
dai" A tare suka shiga gidan Nihad ta kulle gate, duk da yanda gabanta ke faduwa
hakan bai hanata dakewa ba ta nufi cikin gidan kamar wata boss, Husnah ma dai duk a
tsorace take, tayi sauri ta zaga bayan gidan ta nemi waje ta zauna, a hankali Nihad
ta murda kofar parlon ta shiga ciki da sallama, ta kara kicin kicin da fuska ta
karasa cikin parlon tana kallon yaya Farooq da ya bi ta da ido, ta ɗan durkusa tace
"Yaya ina yini" Mikewa yayi, yayi ball da ita cikin xafin nama, yace "Daga gidan
uban wa kike?" Ta fashe da kuka ta mike xata gudu ya fincikota, jikinta na rawa
tace "Yaya wallahi makaranta na tafi ba ko ina ba, ka kira makarantar ma ka
tambaya" Duk a gigice take don a wajen duka xa a iya ba Farooq A1, Ya kai mata wani
wawan mari yace "Uban wa ya baki izinin tafiya makaranta?" Ta rushe da kuka jiki na
rawa tace "Wallahi na gaya ma Umma kafin in fita, ita tace in tafi, ka kirata ka
tambayeta" Hauri ya kai mata yace "Ke da Umma ce a gidan nan? Ko Umma ke da iko
dake yanxu?" hankali tashe tace "Don Allah kayi hakuri yaya baxan kara ba wallahi,
kaji har na rantse maka" Shi dai khalil na xaune bai ce komai ba sai kallonsu yake,
Har baya Husnah ke jiyo muryar Nihad tana ihun neman agaji, ba shiri ta mike ta
nufi gate da gudu tun kan Nihad tace tare su ke, da hannu farooq ya dinga makan
Nihad, mari kuwa yayi mata har sau uku, kuka take iya karfinta tana basa hakuri
tana cewa baxata kara fita ba, daga karshe yayi ball da ita ta mike tsaye da gudu
ta shige dakinta ta sa makulli tana rusa kuka, Farooq yace "Gobe ko nan da gate ki
fita in samu labari ki ga yanda xan faffasa maki jiki da belt, munafuka kawai" Ko
minti uku bai kara a gidan ba yayi ma Khalil sallama, khalil ya rakasa har mota,
farooq na kallonsa da kyau yace "Kar ka kuskura ka raga mata ko na second daya idan
tace xata dinga kawo maka raini" Khalil ya ɗan yi murmushi kawai, Farooq yayi masa
sallama ya ja motarsa ya bar layin, juyawa khalil yayi ya koma cikin gidan, ya
zauna saman kujera ya dau Iphone dinsa hade da sauke ajiyar zuciya, tashi yayi ya
tafi daki ya ajiye wayar, Nihad na jin ya bude kofar dakinsa ta fito da sauri,
parlor ta tafi ta tabbatar da gaske yaya farooq ya tafi, sai da ta kara duba
takalmansa nan ma taga babu alamar dai ya tafi, share hawayenta tayi ta nufi dakin
nasa ta bude hade da turawa da karfi, tana kallonsa cike da rashin mutunci da tsiwa
tace "Toh da ka kirasa ka gaya masa sai aka yi yaya? Nace sai me da ka kirasa?
Mutuwa ka ga nayi bayan muguntan da yayi min? Kuma ka zata xan fasa fita in tafi
makarantana ne ko in tafi duk inda nake so? To wallahi karya kake yaro don ko gobe
ma ba a haifi wanda xai hanani xuwa makaranta ba kaji in gaya maka, Kuma da kai da
ka kirasa da shi da dokeni Allah ya isa ban yafe maku ba...." Wani tsaki ta ja tana
hararansa cike da tsana, ya girgiza kai yace "Akwai lkcn da matsayin