Showing 186001 words to 189000 words out of 268471 words
shiga bandaki, tana ganin zanin gadon
dake bandakin ta tabbatar da zarginta, ruwan zafi kawai ta hada a bathtub, ta fita
xuwa wajen Mami tana kallonta tace "Za a samu gishiri Hajiya?" Mami tayi karfin
halin girgiza mata kai kawai, Likitan ta koma ciki, dole ta ɗan ɗiga disinfectant
dake bandakin sannan ta fito, sosai taji tausayin Nihad kafin su karasa bandakin,
she is in so much pain, sai ta fara imagining where is the husband that is this
heartless, wannan ma yana da imani kuwa, duk yanda tayi da Nihad ta shiga ruwan kin
shiga tayi tana kuka kamar yanda tayi ma khalil jiya, bata mance wahalan jiya ba,
Sun bata minti kusan biyar a haka likitan na fama ta shiga ta ki, likitan ta kara
ruwan zafi a bathtub din ta fita daga bandakin taje ta samu Mami, tana kallon Mami
tace "Tana bukatar ta shiga ruwan zafi, ban san ko zaki mata magana taji ba, she
isnt co-operating" Mami was lost of words, kawai ta gyada ma Likitan kai, likitan
tace "Zan fita yanzu in siyo mata drugs da allura" A hankali Mami tace "Toh" Daga
haka Likitan ta sauka downstairs, Mami ta shiga dakin sannan ta karasa bandakin, ta
fi minti daya tsaye kafin ta tura kofan, Nihad tayi da ta sanin da bata hakura duk
azaban da zata ji ta shiga a haka ba, bata yi zaton Mami likitan ta tafi ta kira
ba, ga kunyan yanda Mami ta shigo ta ganta, ta kasa yi ma Mami musu banda hawaye
babu abinda take, haka nan ta shiga ruwan, bata san daga inda dauriya ya zo mata ba
a wannan lokacin, Mami ta canza mata ruwan ya kai sau uku, daga karshe ta tara mata
ruwan wanka, duk wannan abun karfin hali kawai Mami take amma her heart is so
heavy, bata yarda su hada ido da Nihad all through ba, kamar yanda ita ma Nihad din
bata iya ta hada ido da ita ba saboda kunya, Nihad na wanka Mami ta wanke bedsheet
din ta fita daga bandakin, zaunawa Mami tayi gefen gado ta rike kanta, ita Khalil
yayi deceiving haka? Tunanin abinda zata masa taji sanyi a ranta kawai take, ta ina
za a fara wannan babban lamarin? Hawaye ya hau sauka fuskarta tana girgiza kai, she
wish all this is nothing but a dream, daga karshe ta mike ta fice daga dakin ta
shiga wani dakin daban, Nihad na fitowa bathtub din taji dama daman abinda take ji,
amma har sannan zazzabin na jikinta, tana dingishi cike da karfin hali ta fito daga
bandakin daure da towel ta kwanta saman gado ta takure waje daya tana jin sanyi.
Bayan wani ɗan lokaci Mami ta goge idonta ta sauka downstairs tana kallon Noor tace
"Ki duba ko akwai yanda zaki dafa mata shayi a kitchen, idan babu kuma ki fita ko
restaurant ne ki siyo mata abinci kafin likitan ta dawo" Noor tace "Toh" Mami ta
juya ta koma sama tana jin jikinta babu dadi kwata kwata, kofar dakin da Nihad ke
ciki ta bude ta ganta kwance har ta fara bacci, Mami ta karasa cikin dakin tana
kallonta tunani iri iri na yawo a zuciyarta, press din dakin ta nufa ta bude taga
babu kaya a ciki, ta kalli akwatinta dake dakin tana tafiya a hankali ta nufi gun
akwatin ta bude tana duba kaya a ciki, wata doguwar riga ta fiddo mata da underwear
sannan ta mike ta karasa kan gadon, bude akwatin da Mami tayi ya tada Nihad, Mami
ta ajiye mata kayan a gefen gado ba tare da ta kalli idonta ba tace "Tashi ki sa"
Nihad ta mike zaune, Mami ta fita daga dakin, hawaye kawai Nihad take, all her
thought was that Khalil left her upon the condition she is in, bai duba halin da
take ciki ba yayi tafiyarsa ya kyaleta haka, rabon da taji haushinsa yanda take ji
yanzu tun farkon zuwansa gidansu.....
Har kusan azahar Nihad bacci take tun bayan da Dr Rukayya tayi mata allurai ta bata
magani, ita ma Mamin maganin bacci ta sha don truly bata jin dadin jikinta, tasan
da kyar idan jininta bai hau ba, nan spare room dake gidan tayi bacci har kusan
azahar din ita ma, har a lokacin kuma Noor na gidan, ana idar da azahar Mami ta
sauko downstairs tana kallon Noor tace "Zan kiraki zuwa anjima, xan je gida yanzu"
Noor tace "Toh Mami, Allah ya kiyaye" Daga haka Mami ta fita tare da sojoji biyu
suka maida ta gida, tana sauka compound direct Guard room ta nufa wani soja yayi
saurin bin bayanta yace "Hajiya Oga ya dawo ai an fito da shi" Mami da gabanta ya
fadi don sai da yayi magana taga motar Janar a gidan, ta juya tana kallonsa cikin
karfin hali tace "Yana ina?" Sojan yace "Yana ciki" Mami ta karasa cikin gidan da
sauri, tana shiga main parlor Aunty Hassana na kyabe baki tace "Plan din naku yayi
aiki...." Mami ta kalleta sai kuma kawai ta tafi part din Khalil, bata gansa a
dakinsa ba, ta fito kenan sai ga Mimi ta biyota, Mimi tace "Mami yana part din
Abba, he is very sick" Mami tace "Me yake yi a can?" Bata jira abinda Mimi xata ce
ba ta nufi bangaren Janar, bude kofar parlon tayi, taga Aliyu a tsaye Janar dake
zaga Parlon yana ma Aliyun magana, don shi bai iya tsayuwa waje daya, Ta dinga bin
parlon da kallo bata ga Khalil ba, Aliyu yayi kasa da kai yace "Ina yini" Mami tace
"Where is Khalil" Wani kallo Janar yayi mata ya ci gaba da gaya ma Aliyu abinda
yake gaya masa na zuwa Germany da zai yi akan wani business, Aliyu ya nuna mata
inda Khalil yake, ta karasa ta bude kofar da sauri, kwance ta gansa saman gado yana
bacci, ga allurai da drugs a kan bedside drawer, sai kuma drip da aka sa masa, har
sannan kuma hannunsa daya akwai handcuff, ya bude ido a hankali jin an bude kofar
dakin don baccin nasa sama sama ne, ganin Mami sai da gabansa ya fadi, ya mike
zaune da sauri kusan a firgice, Mami ta dinga kallonsa kafin ta karasa cikin dakin
ta tura kofar tana girgiza kai cike da takaici tace "Wato ni zaka raina ma hankali
Khalil? Ni ka maida yar iska tsohuwar banza, ni zaka raina ma wayo kamar kai ka
haifeni, ka ban mamaki wallahi, ka ban mamaki, dama kuma tun farko ni ce ban tsaya
nayi nazari ba, amma da na tsaya nayi nazari da na gano cewar babu iyayen arziki da
za su hada 'yar su da namiji wai ya kai ta karatu, a da ina alfahari da tarbiyan da
na maka amma banda yanzu, i can't count on you now, ban taɓa tunanin akwai ranan da
zaka saɓa ma Allah ta hanyar zina ba" Khalil ya katseta da sauri yana girgiza kai,
zuciyarsa na bugawa yace "Keep on counting on me Mami, i am not a fornicator, ban
taɓa ba, kuma baxan fara ba, i am sorry ban san ta yanda zan billo ma lamarin bane,
amma Nihad matata ce ta sunna... Da aurenmu na kawota gidan nan, kamar yanda kika
fada da ba don aure ba babu abinda zai sa iyayenta su bari in taho masu da yar su
daga ni sai ita...." Mami kallonsa take babu ko kiftawa with new shock, lokaci daya
ta fashe da matsanancin kukan takaici tana girgiza kai ranta na mata zafi tace "Sai
dai in bayan raina zaka zauna da ita a matsayin matarka... amma matukar da raina a
doron kasa to wllh babu aure tsakaninka da yarinyar nan, wallahi baza ka zauna da
ita ba...." Tura kofar dakin aka yi Mami ta juya da sauri tana share Idonta, Janar
na kallon Khalil with the expression of soldiers yace "Wacece matar taka???" Mami
ta fashe da kuka sosai tana girgiza kai tace "Ban taɓa dana sanin haifanka ba sai
yau Khalil, kuma ina me tabbatar maka sai dai ka zaɓi ko ni ko yarinyar, baxan taɓa
hada zuri'a da ita ba wallahi tallahi, this time around duk abinda ubanka zai maka
yayi maka sannan nima ka jiraye nawa hukuncin, sai na nuna maka ni na haifeka ba
kai ka haifeni ba" Daga haka ta fice daga dakin, zufa ya dinga keto masa yaji kansa
yayi masa mugun nauyi, lokaci daya zazzabinsa ya dawo masa sabo, Janar dake ta
kallonsa yace "Wace yarinya kenan take magana a kai??" Lokaci daya hawaye ya kawo
idon Khalil idan Mami tayi masa haka waye kuma zai tsaya masa, yana kallon Abbansa
ya kasa cewa komai saboda shock, Abba ya masa tsawa yace "I am talking to somebody"
Khalil ya rike kansa with shaky voice yace "A gidan da na zauna a kano suka bani
aurenta, ni kuma na amsa saboda sun amsheni a lokacin da aka nuna ba a bukatata a
gidanmu, i can't tell them no" Janar na ta kallonsa yace "So now, where is the
girl?" Khalil ya kasa dagowa yace "Tana gidana" Janar ya hau safa da marwa a dakin
kamar me pareti, can yace "Sai suka ce kuma ka boye mana ko?" Khalil ya dago a
hankali yana kallon Abbansa with tears in his eyes, Janar na gyada kai yace "Zaka
kai ni har kanon gidan iyayen yarinyar to make confirmation, and if i should find
out u are lying sai na karya maka kafa i promise, idan kuma din da gaske matarka ce
that's fine...." Daga haka ya juya ya nufi kofa Khalil ya bi sa da kallo zuciyarsa
na bugawa.......
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting
fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don't like any
of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil
perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114
57
Mami na fitowa bangaren Janar Aunty Hassana ta bi ta da kallo ganin yanda take
kuka, can ta kalli Aliyu da shi ma ya bi ta da kallo yana tsaye parlon, Aunty
Hassana ta bude hannu murya kasa kasa tace "Lafiya na ganta haka?" Aliyu ya daga
kafada yace "I don't know...." Aunty Hassana tayi shiru, can ta mike ta nufi
bangaren yayan nata da sauri, A parlonsa ta samesa yana dube duben wasu takardu, ta
nemi waje ta zauna da damuwa tace "Yaya lafiya naga Aunty fatima ta fito tana
kuka?" Janar ya daga kai ya kalleta yace "Toh me ya hanaki bin ta ki tambayeta? Ko
ita ta turo ki ki tambayeni?" Aunty Hassana ta ɗan yi yaƙe tace "Haba ai bata ma
tsaya ta saurareni ba, kawai dai i was just worried ganinta da nayi cikin wannan
yanayin shi yasa na fara shigowa nan, amma bari in je in sameta" Tana fadin haka ta
mike har ta nufi kofa sai kuma ta dawo tace "Ya jikin Khalil din Yaya?" maimakon ya
amsa mata sai ya daga wayarsa dake ring wanda wani babban sojan ne ke kiransa, kofa
ta nufa ta fita daga parlon duk kanta a daure, to lafiya ta fito tana irin wannan
kukan kamar warce uwarta ta mutu, ko dai sakinta yayi? Tunanin hakan ba karamin
dadi yayi ma Aunty Hassana ba, da ace bata yaɓa mata magana bane dazu da ta shigo
parlon da sai ta bi ta bangaren nata, amma yanzu da kunya ai ta bi ta, kyaɓe baki
tayi a ranta tace "In ta yi wari ma ji dai" Daga haka ta tafi bangarenta don Aliyu
ma ya bar parlon. Mimi na zaune gefen Mami duk hankalinta a tashe ganin yanda Mamin
ke kuka, tace "Ko ma menene don Allah ki daina kukan nan Mami for the sake of ur
health" Mami dai ta kasa daina kukan da take, she still can't believe abubuwan da
Khalil ya gaya mata, ita in particular zai yi fooling haka? Ita zai yaudara haka ya
kawo yarinya for almost 2 months tana gidan sai yau ne zai bude baki yace wai
matarsa ce, ta ina hakan zai yiwu? Ai bazai taɓa yiwuwa bane tunda ba film ake
acting ba, zata nuna masa ita ta haifesa ba shi ya haifeta ba, Ta jawo wayarta for
the 4th time ta kira Aunty Maryam amma bai shiga ba, har ta tashi zata dau mayafi
zuwa gidan Hajiya Safeenah sai kuma ta tuna to idan ma taje can din kukan me zata
ce mata tana yi? Me zata ce mata ya faru? Ai bata jin zata iya sanar mata da wannan
mugun abu da Khalil ya aikata, haba wannan ai abun kunya ne, Mimi ta fashe da kuka
tace "Mami na tambayeki me ya faru kin ki gaya min, kuma sai kuka kike, don Allah
kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki koma menene" Mami ta fashe da sabon kuka tana
fatan da ma ace duk wannan abun mafarki ne..... Tun bayan fitar Mami khalil ya kasa
komawa ya kwanta, gaba daya hankalinsa yayi mugun tashi, bai ki ya ga fushin
Abbansa ba, amma baya wasa da fushin Mami, he strongly detest anything that will
make her angry, bai taɓa zaton haka zata dau al'amarin nan da zafi ba, he never
expect that from her, he was thinking Abbansa ne idan yaji zai kusan harbesa, sai
yaga Abba ma bai dau issue din personal ba, sai Mami da ya dau hope ya daura mata
yana ganin ko wani bai goyi bayansa ba ita zata goyi bayansa dari bisa dari, A
hankali ya zare drip din hannunsa ya sauka daga saman gadon duk da yanda yake jin
jikinsa ya nufi kofa ya fita, Janar ya daga kai yana kallonsa, tunda khalil ya
kallesa sau daya ya dauke kai ya nufi kofar fita daga babban parlon, Janar yace
"Hey Mr Man, koma ka kwaso drips din da magunguna da ka bar min a dakin...." Khalil
ya juya ya koma dakin ya kwaso duk kayan treatment din nasa ya fito, Janar ya bi sa
da kallo sai kuma yace "Ita yarinyar da ake magana akai tana ina?" Tsayawa khalil
yayi kamar baxai juya ba sai kuma ya juyo yace "Can gidana" Janar yace "Tana ciki
aka kulle gidan?" Khalil yayi shiru, Janar ya dau wayarsa zai kira daya daga manyan
sojojin dake tare da shi, Khalil yace "Daga gidan Mami take yanzu" Janar yace "Toh
wa ya bata izinin zuwa? Sannan wa ya kai ta har ya bude mata gidan?" Shi dai khalil
bai ce komai ba, can dai ya juya ya fita daga parlon. Hajiya Amina ce tayi sallama
cikin parlon Mami, Mimi tayi saurin tashi don kofar bedroom din a bude yake ta nufi
kofa ta fito tace "Ina yini Mama?" Hajiya Amina na kokarin kutsa kai ta shige dakin
tace "Lafiya lau ina Hajiyar?" Mami tayi kamar bacci take, hakan bai hana Hajiya
Amina karasawa cikin dakin ba, tace "Hajiya rasuwa aka min nace in zo in gaya maki"
Babu yanda Mami ta iya haka ta bude idonta ta mike zaune tace "Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un, wa ya rasu?" Hajiya Amina na kallonta tace "Makociyar kanwata Nana,
kinsan muna mutunci da matar, yau ta rasu wajen haihuwa" Mami tace "Allah sarki,
Allah ya ji kan musulmi" da mamaki Hajiya Amina tace "Lafiya na ganki haka Hajiya?"
Mami tayi yake tace "Wallahi bana jin dadi ne" Cike da damuwa Hajiya Amina tace
"Naga idanuwanki sun kumbura kamar warce tayi kuka? Kukan me kike haka" Mami tace
"Har da baccin da bana samu yanzu" Hajiya Amina tace "Ayya, Allah ya sauwake, ya
Khalil ya kara ji duk da na shiga bangaren Janar din ban gansa ba" Mami ta daga kai
da sauri tace "Baya can?" Hajiya Amina tace "Aa ya fita gaskiya kuma ai ruwan bai
ci ace ya kare ba" Mami bata kuma cewa komai ba, Hajiya Amina ta nemi waje ta
zauna, duk wani salon bugan ciki babu wanda bata yi ma Mami ba ko zata samu hint
din abinda ke faruwa a gidan amma Mami sai kaucewa take, gashi ita dai bata ga ana
hada kaya ba alamar anyi saki, ta dai gaji da zama ta mike tace "Toh Allah ya kara
lafiya Hajiya, bari in je in ci gaba da abinda nake yi" Mami tace "Toh Nagode" Daga
haka ta fita daga dakin, Mami ta dau wayarta da sauri ta shiga kiran Noor, har ya
katse Noor bata daga ba sai ga shi ta biyota, Mami ta daga tace "Khalil yaje gidan
ne???" Noor tace "Aa, amma muna hanya Mami, Sojojin ne suka ce Abba yace su maida
mu gida" Mami tayi shiru ta ma rasa abinda zata ce, can ta katse wayar kawai, ta
kara dialing number Aunty Maryam ko zata sameta amma still baya shiga, to ina ta
shiga haka??? Tun da Nihad ta ga anguwan da suka shigo jikinta ya kara yin sanyi
taji kamar ta fashe da kuka, a duniya babu inda take jin bata son ganin kanta irin
wannan gidan da za su, har cikin ranta bata son gidan, ta dinga kokarin ganin
hawayen dake taruwa idonta bai zubo ba amma ina, sai da ya zubo, ita dai Noor na
zaune ta daya end din tana ta danna wayarta, har suka iso gidan bayan an idar da
sallan magrib, Noor ta bude motar ta sauka tana kallon Nihad dake dannar kanta kar
ta fashe da kuka, A hankali Nihad ta bude motar ta sauka, Noor ta nufi entrance din
gidan Nihad na biye da ita tana tafiya a hankali tana goge idonta, har sannan zafi
take ji sosai idan tana tafiya, Noor ta jira ta har ta shigo parlon don Abba ya
sanar mata suna isowa direct su nufo bangarensa, babu kowa main parlor din, Nihad
na biye da Noor walking slowly har suka shiga bangaren Abba, Noor tayi sallama
kafin ta shiga Nihad ta ki shiga ta tsaya bakin kofar gabanta na faduwa, Noor ta
juya ta kalleta, Nihad ta sunkuya da kanta, sai kuma ta shiga cikin parlon, Sojoji
ne su hudu a tsaye parlon Janar na basu instruction, Noor ta tafi saman kujera ta
zauna don in dai ka shigo parlon Janar baya barin ka zauna a kasa, Nihad dake bin
parlon da kallo ta rakube jikin tsadadden kujeran dake parlon tana kallon katon
hoton Janar dake manne jikin bangon parlon yana sanye da kayan soja da hularsa,
daga kasa an rubuta Lieutenant General Abubakar I Jikamshi, lokaci daya sojojin
suka juya suka nufi wani kofar daban wanda ba sai sun bi ta babban parlon gidan ba
zasu fita compound, Noor ta kalli Abbanta tace "Good evening Sir" maimakon ya amsa
sai ya kalli Nihad yace "Ke ya sunanki?" Nihad sai da taji gabanta ya fadi don
muryarsa kadai ma ya isa firgita mutum, Ta hadiye abu da kyar tace "Sunana Fatima"
Yace "Yar wace gari ce?" Tace "Kano" Janar ya kalli Noor yace "Go and call me
Ibrahim immediately" Noor ta mike ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai ga ta
ta dawo bayan taje ta sanar ma Khalil Abba na kiransa, ta zauna tace "Abba yana
zuwa" Janar na nuna ma Nihad kujera yace "Have a sit" Da kyar ta girgiza kai tace
"Zan zauna a nan" A bit