Showing 51001 words to 54000 words out of 268471 words
pizza Nihad tace "Lah
gashi har xan dawo hostel ba ku je gidan mu kun ga wawan yaron can ba" Husnah tace
"Ai ko yau ya kamata kawai mu je" Nihad tace "Toh ae ke wannan gashin dake kanki ne
matsalar kuma ya Farooq na gari wallahi" Husnah tace "A jakarki ba kina yawo da
Hijab din sallah ba" Nihad tace "Eh" Husnah tace "To ara min kawai in sa don baxan
iya wani komawa hostel ba" Nihad tace "Ohk" Zully tace "Kawai ku tashi mu tafi
yanxu tunda biyu ya wuce" Naf tace "Amma yana gidan idan mun je yanxu?" Nihad tace
"Nace maku 24/7 babu inda yake xuwa, da ma talla ya kasa a bakin gate din da ya
dinga ciniki" duk suka kwashe da dariya, tashi suka yi gaba daya suka nufi motar
Naf Husnah ta shige gaba, Nihad da Zully suka zauna baya, gaba dayansu tsadadden
abaya suka saka, Nihad ce kadai ta sa atamfa da gyale. Karfe uku da yan mintuna Naf
tayi parking dai dai gate din gidansu Nihad tace "Ashe dai xan iya gane gidan"
Husnah tace "Ka ji ta bayan na gama baki direction kenan" Nihad ta sauka daga motar
praying and hoping that khalil na bakin gate, sauran yan matan ma duk suka sauka
daga motar, ta shiga gaba suna biye da ita har suka shiga gate din gidan, Aminu ya
mike yana masu barka da xuwa, Nihad na kallonsa daga sama har kasa tace "Ina
Drivern?" Aminu yace "Ai ko minti biyar bai yi da barin nan ba, yaje can ciki ya
watsa ruwa yace min" Nihad tace shit a xuciyarta, why today of all days xai bar
bakin gate din, kallon su Husnah tayi sai kuma da turanci tace masu su shiga ciki
kawai kafin su fito xai dawo bakin gate din, a haka duk suka bi ta har xuwa main
parlor din gidan, Aminu ya bi su da kallo, direct parlon Umma ta tafi da su, Umma
ta fito daga dakinta jin sallama tana kallonsu tace "Sannunku da xuwa" Duk suka
gaisheta suka xauna saman kujera, Nihad tace "Umma frnds dina ne da nake yawan baki
labarinsu, Zully da Naf, Husnah kuma tana xuwa gidan nan ai kin ganeta ko?" Umma
tace "Kwarai kuwa na gane Husnah, sauran ne dai sai yau na san su, Allah sarki,
sannunku da zuwa yan mata, ya karatu?" Duk suka amsa da Alhamdulillah, Umma tace
"Madallah, kun kwaso rana kuwa" Daga haka tace "Ina zuwa" fita tayi daga parlon,
Naf tayi kasa da murya tana kallon Nihad tace "Is she ur step mom that u are
talking about" Nihad tace "Yeah she is" Naf tace "Waow she is really nyc wllh, very
nyc woman" Nihad tayi Murmushi tace "Sure she is" Ba a dau lkci ba sai ga Hafsah da
tray din lemo da ruwa ta ajiye masu bayan ta gaishe su ta fita, sai gata ta dawo da
warmer din abinci da plates da spoon, ta ajiye ta fita, duk suka sauko suka yi
serving kansu, Nihad ma ta dau plate ta debi abincin. Aminu na ganin shigarsu Nihad
gida dama ya tafi da sauri ya kai ma Khalil tsegumin Nihad ta xo da kawayenta su
biyar suna ta tambayarsa da harshen turanci, ko minti daya bai kara a chalet din ba
ya koma bakin gate da sauri ya zauna, sai bayan la'asar su Naf suka shirya xa su
bar gidan bayan sun ci sun yi nak, har da coslow Umma ta hada masu, Umma tace "Toh
kin kai su sun gaida Maryam kuwa Nihad?" Nihad tace "Tana nan ko?" Umma tace "Aa
tana ciki, su je su gaisheta" Ta fita da kawayen nata xuwa ɓangaren Mumy, duk basu
xauna ba suka gaida Mumy da bata wani sake masu fuska ba, kai kana ganinsu kaga
yara marasu tarbiya marasu kamun kai, Nails Naf tayi fixing a farcenta, Zully kuwa
kana iya hango tatoo dake bayan wuyanta duk da mayafin abaya dake jikinta, Husnah
kuma boobs dinta da bayanta ba a cewa komai kuma farko da Mumy ta santa lkcn
farawansu makaranta ba haka take ba, yar siririya ce ita ma, amma lkci daya ta dawo
uwar mata, Duk gaba daya sun tsargu da kallon da Mumy ke masu, Nihad tace "Za su
wuce ne Mumy shine suka shigo su gaisheki" Mumy tace "Toh maa sha Allah, Allah yayi
albarka" suka amsa da Ameen suka fita daga parlon, Mumy ta kira Nihad ta dawo, Mumy
na kallonta tace "Kar ki kuskura ki wuce bakin gate din gidan nan" A hankali Nihad
tace "Toh" Daga haka ta juya ta fita tana turo baki. Downstairs ta tarda su, Zully
tace "Ur mother is too serious oo" Nihad ta kyabe baki ta fita suka bi bayanta, Naf
tace "The real African Mothers they are talking about" Duk suka kwashe da dariya,
tsaye Nihad tayi balcony ganin har sannan Khalil bai fito ba banda Aminu kawai da
take hangowa a bakin gate, Naf tace "Toh ina ɗan iskan drivern ne?" Nihad tayi
shiru, sai kuma tace "Ina xuwa, ku jira ni" Gun Aminu ta tafi tana kallonsa tace
"Kai Aminu har yanxu bai fito bane, zai ɗan rage ma kawayena biyu hanya ne" Aminu
yace "Ni ma kin ga shi nake ta jira a nan Hajiya" Juyawa tayi ta koma balcony tace
"Idan na tafi chalet da few minutes ku biyo ni can din" Tana fadin haka ta dau
hanyar chalet din, bata ga takalmin kowa a bakin kofa ba, dama isiya da Saminu
gantalallu ne wani lkcn idan suka gama duk abinda suke da safe sai su fita, su da
dawowa kuma sai biyar xuwa shidda, a hankali ta bude kofar parlon duk da haka sai
da yayi kara, ta shiga da takalminta tana yamutse fuska tana bin ko ina da kallo,
ba laifi yau parlon bai yi kaca kaca ba, kuma babu wari, cikin sanda ta nufi
corridor din dakuna, ta kai hannu handle din kofar dakin da Khalil yake ta murda a
hankali ta tura kofar dakin, mikewa zaune yayi da sauri daga kwancen da yake saman
gado, lkci daya ya hade rai kamar yanda ita ma ta hade rai, Tana masa wani kallo
tace "Samun waje, kana bakin aikin ne xaka shanya baki da yamman nan kana bacci?"
Khalil ya dau pillow ya daura kan wayarsa dake gefensa sannan ya saukar da kafarsa
daga saman gadon, kallon fararen ƙafafuwan nasa take wa enda kamar bai ta6a taka
kasa ba har ya mike tsaye calmly yace "Don ina aiki gidanku ba shi ne ya baki daman
ki fado min daki kanki tsaye kamar ba musulma ba Hajiya" Wani dariyar rainin
hankali tayi tace "Toh ai naga ba da dakin ka zo gidan ba, ko da shi ka zo?? kuma
ashe kasan aiki kake gidanmu amma kake min rashin kunya iri iri saboda kai
fitsararre ne, banda rainin hankali ma yanxu lokacin shigowa daki a kwanta ne? Shi
kansa mai gidan naga yana wajen aiki yanxu haka, to idan ka ga dama ka fito Mumy
tana kiranka, sako ne dama aka bani in isar maka kuma na isar, idan kuma baka ga
dama ba sai ka shanya bakin ka ci gaba da baccin..." Jin motsi a parlor ta juya ta
ga su Husnah bakin kofar duk sun shigo, alama tayi masu da su karaso, Khalil dake
ta lura da ita ya karasa bakin kofar dakin bata ankara ba kawai gani tayi yayi
banging kofar dakin almost on her face sannan ya sa makulli ya kulle, buda baki
tayi da shock tana kallon kofar su Husnah suka karaso da sauri, tana zaro ido tace
"Kun ga abinda yayi min yanxun nan" Naf ta kwankwasa kofar da karfi tace "Ashe dai
kai karamin ɗan iska ne mahaukaci tunda har ka kulle kofar, da ka jira mu karaso
kaga ikon Allah mana, wallahi da sai mun ji uban da ya tsaya maka yau kafin mu bar
nan, kuma wallahi kaji kunya tunda har mata suka tsorata ka ka kulle kofa da sauri"
Nan duk suka hau gaggayan bakaken maganganu marasu dadi a bakin kofar dakin, ita
dai Nihad mamakin abinda yayi mata
ya sa ta kasa cewa komai sai kallon kofar take, suka kare masa zagi na cin mutunci
tass sannan Husnah na huci tace "Mu je, ai akwai wani lokacin, ni ban san shegen
matsoraci bane ba ma ai...." Duk Khalil na jin su, and he was calming himself and
controlling his mood at the same time, duk da it's too much and too heavy for him,
lokaci daya launin idonsa ya canza, daga karshe ya daina juyo muryarsu gaba daya,
Mikewa yayi walking slowly ya tafi bakin window ya tsaya yana kallon waje ko
kiftawa baya yi, tunda ya xo gidan sai ranan ya ji da gaske he truly hate the sight
of Nihad, at first he was trying his best not to hate her sbda bai iya tsanar
mutum, shi yasa yake kokarin ganin bai tsane mutum ba no matter what, but he now
realized he hate everything about her, da ya san xai zo gidan nan har ya hadu da
ita da ya hakura da zuwan nasa no matter what and he is going to loose nothing,
juyawa yayi ya tafi jakarsa ya bincika har kasa ya fiddo wani abu me kamar diary da
pen dinsa, ya bude plane page yayi rubutu da bai wuce layi uku ba ya ajiye pen din
yana kallon takardan, rufewa yayi ya mayar karkashin jakar ya kulle sannan ya mike
ya koma gun window din ya tsaya, he is so hurt, it's been long he felt this way,
but they can't just come and insult him then go scot free, wayarsa dake vibrate
saman gado ya karasa kamar bai son tafiyar ya daga pillown ya dau wayar, Nihal ce
ke kiransa, ya ajiye wayar ya zauna gefen gado har ya katse, sake kira tayi hakan
yasa ya dauka ya daga ya kai kunne cikin low voice yace "Barka da yamma Hajiya"
Nihal ta gaishesa tace "Friend dita fatima tace min ka amsar min sakon nagode
sosai, Allah ya saka da alkhairi" Gently yace "Ameen, ya karatu?" Tace
"Alhamdulillah" Yace "Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen nagode" Yace "Ki turo number
Tailor din naki" Tace "Toh xan tura maka, nagode" Yace "Yauwa sai anjima" Daga haka
ya katse wayar ya ajiye gefensa. Da daddare Nihad ta shiga bangaren Umma da
sleeping dress dinta, zama tayi a bedroom dinta har ta fito daga bandaki tace "Ya
aka yi Nihad?" Nihad tace "Umma dama wancan drivern xaki taya ni yi ma magana gobe
da safe xai kai ni can gidan Aunty Kamila da kayana idan ya so daga can sai Naf ta
zo da mota ta kwasar min kayan mu tafi hostel" Umma tace "Toh ke me yasa baxa kiyi
masa maganar ba, tsoronsa kike ko me?" Nihad ta wani zaro ido tace "Cabdi, inji
tsoron wa? Ko Abbana bana tsoronsa sai wani mere Drivern gidanmu, kawai bana son ko
wani magana ya sake hadani da shi har abada a gidan nan, don naga ba shi da manner
sannan ya gama rainani, tunda Mumy ta mareni a gabansa shkkn ya daina respecting
dina yana ganin dai dai muke, duk Mumy ce ta janyo min komai, to wannan yasa na yi
vow har motar ma baxan dinga shiga tare da shi ba, wannan ma kawai dole ne ya sa
don babu yanda xa ayi kayana ya dau adaidaita sahu" Umma tace "Balle ma shiga
adaidaita Sahu ba girmanki bane, ita kuma Maryam in taga disgaki gaban ma'aikatan
gidan shine dai dai sai ta ci gaba, shi yasa a rayuwa kar ki kuskura ki raga ma
talaka ina maki wannan hudubar, don da ya ga fuska shikenan raini sai wanda ya
manta, barin yan kauyen nan shi yasa ko kallon arziki kar ki yarda ya hadaku ma"
Nihad tace "Ai ni dama bana masu kallon arxiki Umma" Umma tace "Ya dai fi miki,
ajin ki daban da nasu, shkkn ki je ki kwanta goben xan masa magana idan Allah ya
kai mu" Nihad tace "Nagode Umma" Zata fita dakin Umma tace "Kuna dai waya da Aliyun
ko?" Nihad ta juyo tace "Ehh muna yi, yanxu ma da shi muka gama magana na fito"
Umma tace "To madallah, yaushe xai kara zuwa?" Nihad tace "Umma kinsan akwai wani
business din Abbansu a can kasar waje shi ne manager so he is not always in
Nigeria, though sauran business din Abban nasu na nan kasar ma duk shi ke running
dinsu, haka ne ma yasa bayan watanni kadan yake shigowa Nigeria, amma yace min in a
month time xai shigo in sha Allah" Umma tayi shiru, Nihad tace "His father owns a
big company shi da wani White Man, so Aliyu is managing it for him in there" Umma
ta ɗan yi murmushi tace "Ba shakka, Allah ya sanya Alkhairi, kice koman baban nasa
a hannunsa yake" Nihad tace "Ehh, he is his dad favorite also" Umma tayi murmushi
tace "Kamar ke kenan ko" dariya kawai Nihad tayi ta nufi kofa Umma ta bi ta da
kallo har ta fita daga dakin sai kuma ta sauke ajiyar xuciya. Washegari Umma ta
samu Khalil bayan ya dawo daga kai su Amina makaranta, da ladabi ya gaisheta
fuskarta kamar bata ta6a dariya ba tace "Kai nan da karfe tara xaka kai Nihad gidan
yayarta" Khalil da kansa ke kasa yace "Toh Hajiya" Juyawa tayi ta bar sa wajen a
tsaye, ya daga kai ya bi ta da kallo. Kamar yanda Umma tace karfe tara saura Nihad
ta fara fitowa daga akwatunan ta nan balcony ta ajiyesu ta tafi bakin gate tana
kallon Khalil dake zaune, Ta ɗan tabe baki tace "Ga akwatunan da xa a sa a booth a
can balcony" Ko kallon direction din da take tsaye bai yi ba, sai ma kara hade rai
da yayi, tace "Malam magana fa nake maka fa" Still khalil yaki kallon inda take
balle ta sa ran yace wani abu, Aminu ya mike da sauri ya tafi balcony din Nihad ta
bi sa da kallo, sai kuma ta kalli khalil cike da takaici amma ta kasa ce masa
komai, har Aminu ya gama kwaso kayan ya ajiye a garage, ya taho gun khalil yace
"Ɗan bude booth din a xuba su" Mikewa Khalil yayi ya tafi gun motar bayan ya bude
booth ta makullin ya shiga driver seat, Nihad ta bi sa da wani shegen kallo, tana
mamakin irin wannan feeling din da yake, sai kuma ta ji haushin kanta da bata sa
Aminu ya kwaso akwatunan ba tayi ma wannan banzan magana ya kyaleta, bayan ya tada
motar ta tuna bata ma Mumy sallama ba, komawa cikin gidan tayi ta tafi bangaren
Mumy, khalil ya fi minti sha biyar a kofar gida yana jiranta cikin mota, tana sane
tayi xamanta cikin gida don yayi ta jiranta a mota, sai da taga ta 6ata minti
ashirin sannan ta mike ta fita tana rike da handbag dinta, back seat ta zauna ta
kulle motar tana kallonsa, ya ɗan kwantar da driver seat ya rufe idonsa kamar mai
bacci, da har xata masa magana ta tuna sabon vow din da ta dauka na cewar ba
maganar da xai sake hadata da shi, yau ne last. Har bayan minti biyar bata ga ya
bude ido ba balle ya tada motar su bar wajen, ta wani hade rai tana kallonsa, wasa
wasa har sai da aka yi minti goma suna nan a haka, tana ta control din kanta kar
tayi masa magana, Aminu dai sai lekosu yake yana dariya kasa kasa, wato sai ya rama
shanyasa da tayi cikin mota, tana ta xaune motar ta cika tayi fam amma taki cewa
komai kuma bata sauka ba har sai da aka yi minti ashirin da biyar sannan ya bude
ido ya gyara zamansa ya kunna motar suka bar wajen, da yake ya ta6a kai Nihal gidan
yayarsu kamar yanda ta ce masa, saboda shi ma baya son wata magana ta hadasa da
Nihad direct gidan ya nufa ba tare da ya damu can din ne ko ba can ba, the ride was
so silent, ko wannensu fuska a tamke, lkci lkci take satan kallonsa sai kuma ta
kyabe baki ko ta ja tsaki can kasa kasa, har yayi parking dai dai gate din gidan
kamila ya kashe motar, Nihad ta bude ta sauka ta tafi ta kira mai gadin gidan tace
"Don Allah ka zo ka sauke min kayana a mota" Ya fito daga gate din ya bude booth
don khalil ya riga ya bude, nan ya ciro mata akwatunan ya kai su bakin gate, kafin
ya ciro na karshen tana kallonsa tace "Don Allah ka je kace ma wancan drivern nace
ba sai ya wani zo yana kai ni makaranta ba don bana bukatarsa kwata kwata" Mai
gadin ya tafi yana kallon Khalil bayan sun gaisa yace "Wai Hajiya tace ba sai ka zo
kai ta makaranta ba" Khalil yace "Ok" Juyawa yayi ya tafi ya cire akwatin karshe ya
kulle booth din, khalil ya ja motar yayi zoom off, Nihad ta bi sa da harara tace
"Uwa motar ubansa, wllh ni ce sanadin aikinka a gidan nan mu dai je zuwa, sai kayi
da ka sanin sanina a rayuwarka" Shi da mai gadin kallonta yake yana kokarin kai
akwatunan cikin gidan, ko karamin bata dauka ba haka ta bar masa su dukka ta wuce
ciki, Kamila dake parlor tace "Mutanen Maryam Abatcha American University" Murmushi
Nihad tayi tace "Aunty ina kwana?" kamila tace "Lafiya lau, amma fa ki kira warce
xata xo ta dau kayan naki xuwa hostel don karfe sha biyu xan fita nima" Nihad tace
"Ehh tace min karfe sha daya xata zo" Kamila tace "Toh ya dai fi, daxu ma Mumy ta
kirani wai in sa maki ido nace toh" Nihad tayi dariya tace "Aunty kamila mumy sai
tayi ta treating dina kamar wata er yarinya" Kamila tace "Gaskiya kam, ga ki ke ba
yarinya ba, makarantar ki ma ba ta yara ba" Dariya kawai Nihad take, Kamila tace
"Atoh dai" Karfe sha daya Naf da Husnah suka iso kofar gidan Kamila na tsaye
compound duk suka saka akwatunan a motar Naf, Bayan sun gama tace "Toh Allah ya
tsare" Nihad tace "Ameen Aunty" su Naf suka mata sallama, tana kallonsu har suka
bar compound din ta juya tayi komawarta ciki, murna a cikin Nihad ba a cewa komai,
a haka ta koma rayuwarta a hostel babu me sa ta babu me hanata, duk sanda Mumy ta
kirata sai ta shige bandaki ta kulle su yi waya don kar ma taji hayaniyar su Naf da
Husnah, night party kuwa sai wanda suka mance ne baxa su ba, duk yanda suka so
rinjayar Nihad ta dinga shan kwayoyin da suke sha bata ta6a sha ko da wasa ba, sau
daya Husnah ta shammace ta ta xuba mata a lemo shi ma sai da ta kwana ta yini tana
baccin wahala, hakan ya sa suka rabu da ita da batun drugs, sai kuma suka fara jan
ra'ayinta zuwa kwanan hotels da suke da boyfriend dinsu, nan ma dai ta ki, ko min
daren da suka yi a waje ita