Showing 54001 words to 57000 words out of 268471 words
dai sai ta dawo hostel, duk sanda suka yi waya da Umma
sai ta ja mata kunne kan cewar kar fa ta dinga bin duk wani wuri da xata iya haduwa
da Abbanta ko Farooq, ita kanta Nihad is so careful about that, a haka har suka
fara exams, duk cikinsu Nihad ce ke maida hankalin karatu, sauran ko bude takarda,
duk sanda Mumy ta bukaci Nihad ta zo gida sai tayi karyan karatun exams yayi mata
yawa, bayan an gama exams din ma don kar Mumy tace Nihad ta zo gida Umma ta sa
kamila ta kirata tace xa su garin mijinta, haka nan aka kare hutu Nihad na hostel
abun ta suna baza life, su ne har Kaduna da hutun,
sau biyu ta je gidan Kamila shi ma ษon Aliyu ya shigo kasar ne xa su hadu sai taje
gidan kamila shi ma ta ce masa mijinta ne yayi tafiya take taya ta zama......
One more free page.
โ๐ป
07087865788
๐๐ *NIHAAD* ๐๐
โ๐ป
By _Khaleesat Haiydar_
17
End of free pages...
Har aka kare hutun wata biyu Nihad bata nufi hanyar gidan Kamila ba balle nasu
gidan, kamar yanda Mumy ke kiranta kullum haka ma Abbanta, a ko da yaushe cikin
demanding kudi take daga wajensa kuma ko sau daya bai ta6a hanata ba, da tayi
magana xai tura mata fiye da yanda ta tambaya, Umma ma kusan kullum sai ta kirata,
duk kuma wannan abun Abba da Mumy na xaton Nihad na Kebbi tare da Kamila, Umma ce
kadai ta san Nihad na kano sai kamilar, gaba daya Kamila ta daina xuwa gida a zuwan
tana can kebbi, idan da wani abu sai dai Umma ta shirya ita taje gidanta, A kullum
Mumy bin Nihad take da addu'a, ta rasa dalilin da hankalinta ya ki kwanciya tun
barin Nihad gidan, bata da rest of mind kwata kwata, gashi babu abinda xata iya yi
game da hakan, ko me xata ce ma Abba baxai ta6a fahimtar ta ba sai dai ma ya juya
xancen, a ko da yaushe ta kira Nihad sai ta mata nasiha a kan ta dai kula kuma
banda rawan kai da yin kawaye, sai Nihad tace "Mumy ni da ba kowa na sani ba a
garin sannan babu inda muke zuwa, kawai karatu nake ta yi against next semester" A
haka dai kullum take gaya ma Mumy. Ranan wata juma'ah Nihad da kawayenta duk suka
shirya xa su je duba wata kawar Zully da tayi rashin lafiya, Naf ke driving din,
Husnah tace "Amma fa ku kirata ko an sallameta asibiti kar mu je mu yi wahalar
banza" Zully tace "Ai ko dai" wayarta ta dauka ta kira kawartata Yusra ta sa
handsfree, tana dagawa Zully tace "Ya kuna asibitin har yanzu?" Yusrah tace "Wani
asibiti da aka sallame mu tun jiya, ni kin gan ni a Bristol ina shan Ac, Saurayina
Alhaji Muktar ne ya biya kudin kwana hudu sai gashi tafiyar gaggawa ya kamasa yau
da safe kuma yace min xai kwana uku a Abuja, sai jibi kudin xai kare shine nace
gwara in yi zamana a nan" Zully ta kyalkyale da dariya tace "Me ya fi ranki, to
bari mu taho can din kawai" Yusrah tace "Ai ko ku zo, ga abinci ga enough drinks,
sannan ga Ac 24/7" Zully tace "To sai mun iso" Tana katse wayar, Naf ta dau hanyar
Bristol, Husnah tace "Mu ma muje mu sha Ac kawai" Dariya duk suka yi, Nihad tace
"Amma yaushe xa mu fito, kunsan ni bana son xuwa irin wajajen nan in broad
daylight" Husnah tace "Mu da xa mu shiga daki mu yi xaman mu meye na wani damuwa"
Nihad bata ce komai ba ta ci gaba da danna wayarta, suna isa makeken hotel din Naf
ta samu wajen parking, Dai dai nan wayar Nihad ya fara ringing, ganin Abba ne ta
ษan wara ido, Husnah ta kalleta tace "Waye?" Nihad ta nuna mata screen din wayar,
Husnah tace "Ohk, bari kawai mu sauka mu tafi ciki, sai ki tsaya motar ku yi waya,
idan kun gama ki fito ki kulle sannan ki kirani mu gaya maki room number" Nihad
tace "Ohk" Duk suka sauka daga motar, Naf ta mika mata makulli suka wuce ciki, tuni
wayar Nihad ya katse sai ga Abba ya kara kiranta, dagawa tayi hade da sallama tace
"Abba ina yini?" Yace "Lafiya lau dear, how are you?" Tace "Alhamdulillah Abba ya
aiki?" Abba yace "Mun gode Allah, yaushe xa ku yi resuming ne?" Nihad tace "In two
weeks time Abba" Abba yace "Ohk, yaushe kamilar tace maki xa ku dawo?" Nihad tace
"Ana saura 2 days mu koma school, tare da mijin xa mu dawo gaba daya" Abba yace
"Ohk that's good, take care dear" Nihad tace "Alright Abba, bye" Katse wayar Abba
yayi, ta bude motar ta sauka sannan ta kulle, tana rike da jakarta bayan ta kulle
motar ta nufi entrance din hotel din tana kokarin dialing number Husnah, sunanta ta
ji an kira, ta juya da sauri, wani tsohon saurayin Husnah ne, ya nufota da sauri
yace "Hi Nihad" Ta ษan yi murmushi tace "How are you Kabir" Yace "Alhamdulillah, ya
kwana biyu?" Tace "Cool" Yayi er dariya yace "Kina da appointment yau a nan kenan?"
Ta ษan kallesa sai kuma tace "Tare da kawayena nake, suna ciki" Yace "Ohk maa sha
Allah, ya school" tace "Fine" A tare suka jera xuwa cikin reception din hotel din
yana jan ta da hira, zaune yake a haraban hotel din karkashin inuwa tare da wani da
baxai wuce sa'ansa ba yana sauraron duk abinda yake ce masa, da ido ya bi ta da
Kabir, at first he quickly imagined ba ita bace kamace kawai, but yanayin tafiyarta
da kuma jakar hannunta wanda duk ya sani ya sa shi ajiye goran ruwan dake hannunsa
ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Buga table din abokinsa yayi da mamaki yace
"Heyy!!" Da sauri ya dauke idonsa daga kallonta ya kalli abokin nasa, abokin yace
"Why are u staring at her that way, burge ka tayi ko me? Kaga yarinya da saurayinta
sun zo holewarsu kayi ta kallonta?" Still bai ce komai ba sai kallon abokin nasa
yake babu ko kiftawa, Abokin yace "Khalil" Sauke idonsa yayi daga kallonsa sai kuma
ya sauke ajiyar xuciya yace "Yea mamaki abun ya bani shi yasa na bi su da kallo"
Dariya Sultan yayi yace "Haba kai ma ai kasan wannan ba sabon abu bane, yan matan
yanxu kam ai sun xama abinda suka zama sai addu'a, basa ma jin kunyan iskanci
yanxu, ko wani hotels ka bi su ne, baka lura bane ko 10 mins ba ayi ba set of 3
girls suka wuce mu a nan, su ma kuma duk gun samarin suka zo na sani" Shi dai
khalil bai ce komai ba, he was really shock, yarinyar da aka ce tana Kebbi ce ya
gani a Bristol, Sultan yace "Kai dai tunda kana da Nadeeyah and upon her parents
wealth she is decent sai ka gode ma Allah" Murmushi kawai khalil yayi, Sultan yace
"Kuma kuna magana da ita all this while?" Khalil yace "Muna yi" Sultan yace "Tasan
kana kano?" Girgiza masa kai kawai khalil yayi, Sultan yace "Ya batun turawa
gidansu?" Khalil yace "Yana nan" Sultan yace "Toh Allah ya nuna mana, but ya kamata
kayi nazarin duk abinda nace maka Khalil, pls do so Frnd" Khalil ya sauke ajiyar
xuciya yace "In sha Allah, and i appreciate u Sultan" Sultan yace "Nima nagode da
ka bani lokacinka har ka saurareni" Murmushi kawai khalil yayi, Sultan ya mike yace
"Toh ka koma can inda ka samar ma kanka aiki kar a fara nemanka ko" Khalil yace
"Ina jiran wani ne still" Sultan yace "Wa kenan?" Khalil yayi kasa da murya yace
"Another caring frnd like you" Sultan ya sauke ajiyar xuciya yace "All this shall
come to pass in sha Allah Khalil" khalil ya ษan yi murmushi ya mike tsaye ya mika
masa hannu sannan yace "I truly appreciate ur care Sultan, nagode kwarai" Sultan
yace "Mention not abokina" Har mota Khalil ya rakasa sannan ya dawo ya zauna inda
yake zaune har sannan yana cike da mamaki, har karfe shidda na yamma yana xaune
wajen bai ga fitowar Nihad ba balle shi mutumin da ta shiga ciki da, kiran Aminu ne
ya shigo wayarsa ya ciro ya daga ya kai kunne, Aminu yace "Toh na ji ka shiru daga
cewa xaka bakin titi ka dawo" Khalil yace "Ina nan dawowa yanxu" Aminu yace "Toh ga
manyan mangwaro ma Hajiya Inna ta zo ta bada a ajiye maka" Khalil yayi murmushi
yace "Toh nagode, sai na dawo" daga haka ya katse wayar. Har aka yi magrib Khalil
bai ga fitowar Nihad ba, babu warce ta fado masa a rai sai Mahaifiyarta, ya ji
tausayinta sosai, mata me kirki da mutunta ษan Adam, and such a nyc woman didn't
deserve Nihad as a child... Wayarsa ya dauka yayi dialing number Nihal ya kai
kunne, tana dagawa tayi masa sallama, ya amsa yace "Ya kike?" Tace "Alhmdlh, ina
yini?" Yace "Lafiya lau, ya lectures?" Tace "Ya shirin jarabawa dai" Yace "Ohh haka
ne, ya shirin jarabawa?" Tace "Alhmdlh" yace "Tare xa ku dawo da er uwarki kenan?"
Nihal tace "Noo, ai ita tana kebbi" Yace "Ko?" Tace "Eh" Yace "Ita da wa suka tafi
kebbi?" Nihal tace "Wannan yayar tawa da ka kai ni gidanta kwanaki" yace "Ohk,
yaushe xa su dawo?" Tace "Jiya da na tambayi Umma tace min nan da sati biyu" Khalil
ya ma rasa abinda xai ce, jin shiru tace "Hello" Yace "Eh ina jin ki, to shkkn,
dama tambayarki xan yi ya jarabawa" Tace "Toh Nagode" Yace "Sai anjima" Daga haka
ya katse wayar, kallon cikin hotel din yayi, yana ta xaune har kusan Isha'i ganin
Nihad ba fitowa xata yi ba ya mike ya tafi can inda yayi parking motar gidansu
Nihad ya shiga ya bar hotel din, direct gidan Kamila ya nufa, bayan sun gaisa da
mai gadin yace "Matar gidan na nan?" Mai gadin yace "Ehh tana ciki" Khalil yayi
shiru, sai kuma yace "Ohk an aiko ni wajenta ne" Mai gadin yace "Toh bari ayi mata
magana" Yana shiga gate khalil ya juya ya shiga motar ya bar layin. Direct gida
khalil ya nufa erasing everything off his mind kamar ba ayi ba, after all it's none
of his business and will neva be any of his business. Bayan sati biyun da Umma tace
ma Abba su Nihad xa su dawo kano, sai ga Nihad tare da kamila a gidan da yamma,
babu irin rokon da Umma bata yi ma Kamila akan su xo gida tare da kyar dai daga
karshe ta yarda suka taho gidan da Nihad, akwatin kayanta daya kawai ta dawo gida
da, tun da suka shigo gate Khalil ke kallon Nihad, ita kuwa shaff ta mance da wani
batunsa a gidan sai yanxu da ta gansa, tana ganinsa kuwa mood dinta ya canxa, shkkn
kuma ta dawo miserable house din nan da driver din nan a ciki, noo gaskiya ita dai
baxata iya ba, xata roki Umma ta yi come up with another plan da xai sa ta sake
barin gidan, Kamila ce kawai ta amsa gaisuwan mai gadi da khalil da ke gaisheta,
Nihad kuwa tafiya take cike da isa ta nufi entrance din parlor, tayi wani kyau ta
kara haske, kana ganinta kasan bata da damuwar komai, ba komai ya haddasa mata kara
haske ba sai cream me shegen tsada irin nasu Husnah da take shafawa yanxu, ga
sabulu ga shower gel, Khalil ya bi ta da kallo, suna shiga parlor Aminu yayi kasa
da murya yace "Kaga yanda tayi wani haske tayi kyau uwa warce ta tafi duniyanci?"
Khalil bai ce komai ba, but he really felt sorry for Abba and Mumy, ya jima bai
hadu da mutane masu kirki da karamci irin tasu ba, a watanninsa kusan shidda a
gidan Abba ya ja sa jiki kamar nasa, ya kai ya kawo yanxu hatta Atm card Abba na
basa ya ciro masa kudi wanda ko Habibu baya ba Atm card dinsa, shi ko Abba ya ya6a
da hankali nutsuwa da girmamawa irin ta Khalil, ya sha gwadasa ya aikesa ya siyo
masa abu sai ya linka kudin sau uku ya basa yace haka ake siyarwa amma in sha Allah
sai Khalil ya kawo masa canjinsa, ya gwadasa ta fanni daban daban wanda shi khalil
bai ma san yana yi ba, duk gidan babu wanda yake da matsala da warce ta zama second
Nihad sai Umma, gaba daya ta dau
karan tsana ta daura masa tun da Nihad ta fesa mata yana waya da Nihal, to uban me
Nihal dinta xata yi da shi, duk abinda take yi kuma baya damun khalil, Usman ma dai
in ya zo basa wani gaisawa, amma Farooq idan yana gari mayar da bakin gate wajen
zamansa yake yi sbda Khalil, xaka yi tunanin ya ta6a saninsa, kawai he enjoys
gisting with him sbda yana magana kamar wanda yayi ilimi me zurfi, gashi he knows
almost everything that's happening in the world wato he is current, suna dadewa
sosai suna hira.... Sai kuma Hajiya Inna da takanas sai ta aiki dreban gidansu
Hamid ya zo ya kira mata khalil xata aikesa don hankalinta yafi kwanciya ta basa
dukiyarta a kan yaran gidan, kuma aiken baya wuce na dari ko dari biyu. Tun da
Nihad ta shiga bangaren Mumy bayan ta fito daga bangaren Umma Mumy ke kallonta, ita
dai tana xaune tana ta danna waya, Mumy tace "Wani mai kike shafawa Nihad?" Nihad
ta daga kai tace "Mumy cream din Aunty Kamila ne tace in dinga shafawa" Mumy bata
ce komai ba, bayan few seconds tace "Ina sauran kayanki?" Nihad tace "Mumy Aunty
Kamila tace in bar su a can gidanta" Mumy tace "To tashi driver ya kai ki ki kwaso
yanxu" Nihad ta marairaice tace "Mumy ni fa ba abinda nake bukata a cikin kayan"
Tsawa Mumy tayi mata tace "Baxa ki tashi ba" Tashi Nihad tayi kamar xata yi kuka,
sai kuma tace "Toh Ai Aunty Kamilan na nan ki bari idan ta koma gida Mumy" Mumy
tace "Ba dai gobe za ku fara lectures ba?" Nihad ta gyada mata kai a hankali, Mumy
tace "Toh dama ki tabbatar baki dawo gidan nan ba tare da akwatunan ki ba" Mumy na
fadin haka ta wuce dakinta, Nihad ta turo baki ta mike ta fice daga parlon, ita har
ta mance yaushe rabon a harareta balle a mata fada sai yau... Washegari bayan ta
shirya xuwa makaranta sai da Mumy ta kara jaddada mata kwaso akwatunan ta, har da
guntun hawayenta, bayan ta fito compound ta ji ranta ya kara baci da ta tuna cewar
shegen mutumin nan ne har yanxu Driver din gidan, kuma ita wllh baxata wani je ta
hau adaidaita Sahu ba, tana isa gate suka hada ido da shi don kallon sama har kasa
yake mata, wani matsiyacin kallo tayi masa tace "Da bashi ne kake kallona haka?"
Aminu dai sai gwaggwale ido yake, Ta wani ja tsaki ta ma gwammace taje ta hau
adaidaitan sbda ganinsa kadai na kona mata rai, ficewarta tayi daga gate Aminu yace
"Ohh fitina ta dawo ni Aminu, wllh har na manta da ita a duniyar nan" Khalil dai
bai ce komai ba. Bayan kwana biyu da komowar Nihad gida tana kwance bedroom din
Umma tana bata labarin yanda suka yi da Aliyu jiya da daddare, Umma dake xaune
gefen gadon ita ma ta mike da sauri tace "Kice wllh" Nihad na Murmushi tace
"Wallahi Umma" Wani guda Umma ta saki tace "Alhamdulillah, Allah na gode maka...
Yaushe yace xa su xo?" Nihad tace "Nan da sati biyu" Umma tace "Alhamdulillah,
Alhamdulillah, amma in ji baki gaya ma kowa ba?" Nihad tace "Aa ke kadai da Husnah
na fada ma" Umma tace "Kin ji ki, wacece kuma Husnah, meye na gaya mata xa a kawo
kudin ki? Duniyar nan da ta lalace yanxu ai kowa boye kansa yake, kar ki sake gaya
ma kowa" Nihad tace "Har Mumy?" Nihad tace "Aa ba dai kin gaya min ba ai shkkn, ni
xan mata magana sannan inyi ma Abbanku magana, amma sai xuwa next week" Nihad tace
"Toh Umma" Wani gudar Umma ta kuma saki tace "Allah nagode maka diyata xata xama
surkar Janar jikamshi" Dariya kawai Nihad tayi, Umma tace "Toh sai ki kula ki kama
kanki kar ki sake kula kowa tunda dai kina da tsayayye yanxu" Nihad tace "Toh, amma
Umma yana wani ce min xai rabani da su Husnah" Umma tace "Ahhh!!! shi kuma ya
haka??" Nihad tace "Wallahi, kuma ni banga abinda xai sa ya rabani da su ba" Umma
tace "Toh ke dai kar ki musa masa ku samu matsala, kiyi ta bin sa duk abinda yace
kice to, su kuma ko a hankali ai xa a rabu, ke da kasar waje xa ku xauna? Ko ba
haka ba" Nihad tace "Haka yace min" Umma tace "Toh kinga, su Husnah da ba kasar
wajen xa su bi ki ba" Nihad tace "Ai shine" Umma tace "Kai amma nayi farin ciki da
wannan labarin Nihad, Allah Ubangiji ya nuna na yan baya haka" Nihad tace "Ameen,
Umma bari in dauko wayana" Umma tace "Toh je ki dauko" Daga haka ta fita daga
dakin. Ko da wasa Nihad bata sanar ma Mumy ba, tana ta sabgar gabanta throughout
the week, kuma har tambayarta Aliyun yayi ko ta gaya ma Mumy tace masa eh. Duk da
warning din da Umma tayi ma Nihad na kan cewa kar ta sake gaya ma kowa Aliyu xai
turo sai da ta gaya ma Farooq, kamar yanda take favourite din Abbanta haka take
favourite din Farooq a gidan, a WhatsApp suke chatting ta gaya masa sai ga shi ya
sauka ya kirata, tana dagawa yace "Are you serious?" Tace "Ehh ya farooq" Yace
"Tohh maa sha Allah, Amma Abba bai sanar min ba" Nihad ta zaro ido tace "Yaya Umma
tace xata gaya masa" Farooq yace "Ohk, toh Allah ya kai mu next week din, though
xan shigo kano jibi" Tace "Toh Allah ya kai mu" Sallama yayi mata ya katse wayar,
Tana komawa saman chatting taga message din Nihal tana congratulating dinta, wato
har Umma ta gaya mata, murmushi Nihad tayi tace "Thanks twinny" Washegari da Nihad
ta fito xata school khalil ya bi ta da kallo disgustingly as usual, sarai jiya
Nihal ta gaya masa xa a kawo kudinta next week ta kuma gaya masa daga familyn da xa
a kawo kudin, and he really pity the well reputable family, da shi kansa wanda xai
aureta din, ganin irin kallon da yake mata ta tsaya tana kallonsa tace "Wai kai
Allah ya tsine maka ne da xaka dinga min wani irin kallo idan kaga na fito? Ko da
wani abu da muka hada ne ban sani ba? Toh wllh wllh wllh duk ranan da na sake
fitowa ka min kallon walakanci Allah sai na gaura maka mari, kaji har na rantse"
Khalil na kallonta yace "Ki mari wa?" Cike da rashin kunya tace "In mareka nace, ko
uban waye kai da kake tunanin baxan iya marinka ba? Ni fa wallahi bayan na