Showing 228001 words to 231000 words out of 268471 words

Chapter 77 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

zafi qau, gashi sae rawan sanyi take, Mumy tace "Ke dae baki
jin magana Nihal, tun yaushe ake bin ki aje asibiti kin ki?" Nihal dae bata ce
komai ba, Mumy ta dauko mata Hijab dinta tace "Sa mu tafi asibitin yanzu" Lokaci
daya hawaye ya kawo Idonta tace "Ban son zuwa asibitin Mumy" Umma ce ta shigo dakin
ita ma jin shiru shiru Nihal bata fito ba, Ganin Mumy tsaye kanta ta karasa da
sauri tace "Menene, zazzabin ne ya dawo?" Mumy tace "Ehh shi ne nace ta tashi mu je
asibiti" Umma ta kwace hijab din Nihal a hannunta ta saka mata ta kamo hannunta
tace "Sauko in kai ki asibiti" Mumy dae ta koma gefe tana kallonsu, hawaye kawai
Nihal take Umma ta dagata daga kan gadon, da kyar tace "Umma amai nake ji" Umma
tace "Kin san yanda Malaria ke maki kika bar sauro suka cije ki a makaranta Nihal"
Nihal ta nufi banɗaki da sauri tana ganin jiri, nan ta dinga yunkurin aman amma
yaki tahowa don babu abinda ta ci, juyawa Mumy tayi ta fita ta koma bangarenta.
Umma ta saka ta gaba suka fita compound, ta kwalo ma Iliya dreba kira ya taho ya
bude masu motar bayan sun shiga, yayi hanyar asibiti da su, a hanya Umma ta ciro
wayarta a jaka tayi dialing number Abba, yana fara ring taji gabanta ya fadi don
tun bayan da ya saketa sai yau tayi dialing number sa, Ba a dau lokaci ba ya daga
yace "Ina jin ki" Zuciyarta na bugawa, murya can kasa tace "Dama Nihal ce bata da
lafiya mun tafi asibiti yanzu, saboda yanayin jikin nata ban san ko za su ce za a
kwantar da ita ba shiyasa nace in kira in gaya maka" Yace "Tun yaushe take rashin
lafiyar?" Umma ta gyara zama cikin sanyin murya tace "Tana tayi a tsattsaye wllh,
sai yau ne yayi tsanani, tun dai da ta dawo makaranta bata jin dadi gaskiya" Abba
yace "Allah ya sauwake, idan kun je asibitin duk abinda ake ciki a gaya min" Umma
tace "Toh in sha Allah, nagode" Katse wayar yayi, taji hankalinta ya ɗan kwanta tun
bayan da ya saketa, idan ko haka ne ai zata dinga son irin cases din nan su dinga
faruwa yanda za su dinga ko da magana ce ta waya da shi, kilan ta hakan sai Allah
ya daidaita su ya hakura har ya maida ta.... Har suka isa asibitin Nihal kuka take,
tun Umma na tunanin zafin ciwo ne har dai da taga irin kukan da take tace "Ke kukan
lafiya kike yi haka kuwa? Meye haka??" Nihal dai bata iya tace komai ba bata kuma
fasa kukan da take ba, she wish kafin su shiga asibitin Allah zai dauki ranta
kawai, a haka har Umma ta sa ta sauko daga motar tana rike da hannunta suka shiga
cikin asibitin, da yake asibitin da suka saba zuwa ne kati kawai Umma ta bada suka
biya kudin ganin likita, suna zaune reception wata nurse ta sanar masu turn dinsu
ne na ganin Dr, Umma ta mike tana rike da hannun Nihal tace "Kiyi ta yin abu kamar
ba mace ba Nihal, ni dai ki kama jiki mu shiga office din" ko rufe baki bata yi ba
taga yarinya ta sulale kafin ta kai kasa tayi saurin kamota tace "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un" Nurses din suka taso da sauri, nan aka yi emergency ward da
ita aka tafi kiran likita, Hankalin Umma yayi mugun tashi ta dinga salati tana zaga
reception din, Patient din wajen sai cewa suke ta kwantar da hankalinta Allah zai
bata lafiya, jakarta da ta bari kan kujera wata mata ta dauka ta kai mata tace "Ana
ta kiranki a waya Hajiya" Umma ta amsa da sauri, ta bude jakar ta ciro wayar taga
Abba ne ke kiranta, daga kiran tayi ta fashe da kuka tace "Yallabai muna shigowa
reception din asibitin ta suma yanzu haka an shiga da ita emergency ward" Abba yace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, bari in taho yanzu dama ina hanya" Daga haka
ya katse wayar, Umma ta mayar cikin jakan ta zauna tana share hawayen idonta....
Bayan kusan minti arba'in wani likita ya fito yana kallon Umma yace "Hajiya mu je
office" Umma ta mike da sauri ta bi bayansa zuwa office dinsa, Zaunawa tayi kujeran
dake gaban table dinsa tana kallonsa, ya gama kauda files din table din sannan ya
kalleta, hankali tashi tace "Ya jikin nata Dr?" Yace "Alhamdulillah, ina mijinta?"
Umma tayi kasake tana kallonsa sai kuma tace "Miji kuma?? Budurwa ce fa Dr, bata yi
aure ba, Ni mahaifiyarta ce kuma ni na kawota" Likitan ya dinga kallon Umma, can
yace "Kuma er cikinki?" Umma tace "Kwarai kuwa, second to the last born dita ce, ta
gama final exams dinta a Ahmadu Bello University ta dawo gida shine take ta zazzabi
sama sama, to dama idan sauro ya cije ta gaskiya tana wahala haka, nafi tunanin
fita karatun daren da take ne yasa ta kwaso malarian" Likitan ya girgiza kai yace
"I am sorry to say Madam, mun gano tana dauke da ciki wata biyu da sati biyu" Still
Umma tayi tana kallon bakin likitan kamar yare yake mata ba Hausa ba, Likitan ya
girgiza kai ya ajiye mata takardan test din yace "She is 2months 2 weeks pregnant"
zumbur Umma ta mike jin pregnant, tana kallonsa bakinta na rawa tana zaro ido kamar
zasu tuttulo waje tace "Meye kuma pregnant likita nace maka budurwa ce, ko dai
result din wata ka kawo min, meye haka kake gaya min don Allah, bata taba aure ba
fa, ta yaya zaka gaya min haka kamar kana shaye shaye?" Ya dau takardan da ya ajiye
mata ya mika mata yana kallonta yace "Ga test result din Hajiya" lokaci daya Umma
taji wani azababben jiri ya ziyarceta, kan kace me taga office din ya fara juya
mata, sai taga ko ina ya koma bakikirin, kafin likitan ya taso ya yo kanta ji kake
timmm a kasa ta kara buga goshi dai dai inda bai gama warkewa ba a tiles din office
din sai ga jini kamar an buda pampo, Likitan ya fita ya kira nurse biyu... Wani
dakin daban aka kwantar da Umma da har bayan minti ashirin bata farfado ba, sai
tsarkewa numfashinta yake kamar zai dauke har sai da aka saka mata oxygen, ga wani
bandage da aka tula mata a goshi inda ya kara fashewa, likitocin suka ji tausayinta
sosai bayan likitan da ya sanar mata Nihal na dauke da ciki ya gaya masu duk yanda
aka yi a office dinsa, duk suka dinga Allah wadaran Nihal. Tun shigowar Abba
asibitin yake kiran wayar Umma bata dagawa, hakan yasa ya kashe motarsa kawai ya
shiga cikin asibitin, bayan sun gaisa da nurses din yace "An kawo wata mara lafiya
yanzu, tare da Baabarta suka zo...." Wata nurse da ta ganesa don in dai Nihad bata
da lafiya shekarun baya yawanci shi ke kai ta asibiti, kuma duk tunaninta ma Nihad
ce aka kawo yanzu, Nurse din sai duk jikinta yayi sanyi tace "Ina zuwa sir" Wajen
likitan da yayi attending ma Umma ta tafi ta sanar masa ga mai gidan Umma ya zo,
yace tayi masa iso zuwa office dinsa, Nurse din ta kai Abba har office din likitan,
Abba ya zauna yana kallon likitan bayan sun gaisa yace "Jikin nata yayi critical ne
haka? I need to see her first pls" Likitan yace "It's okay sir, daughter dinka ce
ko?" Abba yace "Sure, she is my daughter" Likitan ya sauke ajiyar zuciya yace "I am
sorry to say sir, mun gano er ka na dauke da cikin wata biyu da sati biyu" Abba ya
dinga kallonsa babu ko kiftawa as if trying to apprehend what he just said, Likitan
ya ajiye masa result din yana kallonsa, Abba ya sauke idonsa kasa, the Dr can see
tension and shock written all over him, Likitan ya sauke ajiyar zuciya yace "Kar ka
daga hankalinka Alhaji, it shall be well in sha Allah, daga hankali da mahaifiyarta
tayi ya janyo tayi pass out dazu, yanzu haka ita ma tana kwance ba a kuma jima da
cire mata oxygen ba, kuma jininta ya hau, don haka kayi hakuri ka dauki dangana, ka
kuma kula da matarka har Allah ya bata lafiyarta, yaran yanzu ne ka haifesu baka
haifi halinsu ba, sae dae a bi su da addu'ar shiriya kawai" Duk wannan abinda yake
fada Abba bai ma san me yake cewa ba, Likitan ya mika masa bill din yace "This is
the bill sir, in kuma tare kake da dreba yayi kokari ya maida ka gida Alhaji, you
need to relax and accept this with good faith" Abba ya mike yace "It's okay, it's
okay" Kudi masu yawa ya ciro aljihunsa ya ajiye kan table din likitan ya juya,
Maimakon yayi hanyar kofar fita, sai yayi hanyar bandakin likitan, Likitan yace "Ga
kofar can Alhaji, don Allah ka kwantar da hankalinka saboda shekarun ka" Da sauri
Abba ya nufi kofar fita bai dai ce ma likitan komai ba har ya fita ko rufe office
din bai yi ba, likitan ya ga ya bi right maimakon left, Likitan ya girgiza kai with
pity, suna samun ire iren cases din nan sosai, but ya za ayi? Sai dai kawai Allah
ya kyauta ya shirya yan baya. Wata nurse ce tsaye kan Umma tana duba ko jininta ya
dawo dai dai amma taga har yanzu 180 ne, Umma ta bude Idonta da yayi mata nauyi da
kyar tana kallon nurse din ta cafko hannunta tana harhade magana tace "Nurse a ina
ake cire ciki a garin nan? Ko kuna cirewa a nan??" Nurse din ta girgiza kai tace
"Ba a cire ciki a asibitin nan Hajiya" Umma tayi karfin halin mikewa zaune cikin
rawan murya tace "Don Allah gaya min inda kika san ana cire ciki, don Allah ba don
ni ba, ki rufa min asiri ki gaya min er nan" Nurse din tace "Hajiya ban san
asibitin da ake cire ciki ba gaskiya, nima sabuwa ce a nan" Umma ta fashe da
matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace,
komai ya tabarbare min ni Sumayya, wayyo Allah na" Nurse din dai sai kallonta take,
Umma ta fizge ruwan hannunta ta sauka daga kan gadon tana share hawayenta da sauri
tace "Ina jakata, ina aka kai jakata" Nurse din ta nuna mata, Umma ta dauka da
sauri da nufin ciro waya ta kira Abba tace masa an sallamesu ba sai ya karaso ba,
ko ina na jikinta rawa yake ga wani ciwo da zuciyarta yake, sai hada zufa take ta
ciro wayarta taga miss calls din Abba har biyu, da
sauri tayi dialing kiran, yayi ring har ya katse bai dauka ba, ta kara kira nan ma
har ya katse no response, Nurse din dai ta juya ta fita tana girgiza kai, Umma ta
sauka daga kan gadon tayi zaman dirshan a kasa tana kuka kamar ranta zai fita tace
"Allah na tuba ka yafe ni, Allah na tuba, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na
shiga uku na lalace duniya tayi min zafi, na shiga uku ni Sumayya" Sai kuma ta mike
kamar mahaukaciya ta figi jakarta ta fice daga ward din, Nurses din ta sama a
reception jikinta na rawa tace "Tana ina?" Duk suka tsaya kallonta, wata nurse ce
ta kai ta ward din da Nihal take, zaune take ta hada kanta da gwiwanta tana kuka
kamar ranta zai fita, tun dazu take kukan amma daga nurses har Doctors din babu
wanda yace tayi shiru ko tayi hakuri, gaba dayansu ma haushinta suke ji, Umma ta
fashe da matsanancin kuka ta jingina da bango tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" Nihal dai ta
kasa dago kanta, har shidewa take saboda kuka, Umma tayi kukan har sai da taji ba
dadi sannan ta nufeta tace "Allah ya isa tsakanina dake Nihal, sakayyar da zaki min
kenan duk so da kaunar da na nuna maki cikin 'ya yana? Da cikin shege zaki biyani?
Me na maki zaki min haka Nihal?" Nihal dai bata dago kanta ba sai kuka kawai, Umma
ta goge idonta da sauri tunawa da tayi Abba zai iya karasowa yanzu, Da kyar tace
"Sauka mu tafi, munafuka matsiyaciya, Allah ya isa tsakanina dake wllh, sauko daga
kan gadon nan" Nihal ta sauko daga saman gadon tana kuka sosai, Haka Umma ta tasa
ta a gaba suka fice daga asibitin ita gaba daya tama manta ana biyan wani abu wai
kudin asibiti, bata ga iliya a haraban asibitin ba duk da tace ya jira su, bata
damu da hakan ba don hankalinta baya jikinta, a haka har suka isa titi Umma na can
gaba tana rusa kuka, Nihal na biye da ita a baya, suka samu adaidaita a haka har
suka isa gida, Kafin su karasa gate din gidan Umma ta goge hawayenta ta sa
adaidaitan ya saukesu ta basa kudinsa, Nihal dai na tsaye tana jin dama kawai a dau
ranta a wajen, Umma na kallonta da kyau tace "Don kaza kazanki ko wani tambaya aka
maki kice Malaria ne an maki allura gobe kuma za mu koma asibitin da safe" Ita dai
Nihal bata ce komai ba hawaye ne me zafi ke sauka idonta, a haka suka shiga
gidan....
Khalil na zaune bayan isha wayarsa na kare kunnensa yana magana da Mami, yana son
tambayarta Nihad amma ya kasa, gashi ita ma bata ce masa ga ta ba duk da ko minti
biyu basu yi suna wayar ba, Can dai yayi karfin halin cewa "Mami ya me jikin?" Mami
tace "Da sauki, gobe za mu taho in sha Allah...." A hankali yace "Toh Allah ya kai
mu" Tace "Ameen, sai anjima" Daga haka ta katse wayar, ya dinga kallon screen din,
he is missing his wife badly amma ko ɗan gaisawa Mami taki bata wayar su yi tun da
suka isa can, Number Nihal yayi dialing for the 3rd time yanzu, don tun bayan
magrib yake kiranta bata dagawa, yanzun ma har ya katse bata daga ba, ya ajiye
wayar ya fita zuwa parlon Abbansa don yana gidan, don yana son jin yaushe yayi
fixing na tafiyarsu Yemen din.... Kallonsa kawai Janar yake yi har ya gama tambayar
tasa, can Janar ya sauke glass din idonsa yace "Ka samu wani abokinka ku je, don
bani da lokacin zuwa kasar..." Khalil yayi shiru yana kallonsa, Janar yace "Sun ma
raina ma mutane hankali, kuma duk inda tsabga ta rainin hankali yake to babu ni a
ciki, tun asali me yasa basu kawo wannan zancen ba sai yanzu? So i don't think da
wani abu da zai kai ni kasar nan yanzu" Khalil ya sunkuyar da kansa kawai.
Umma na shiga parlor taga Mumy ta fito daga bangaren Abba, Mumy na kallonsu tace
"Ya jikin Nihal" ba tare da Umma ta kalleta ba balle taga idonta tace "Da sauki"
Daga haka ta tura Nihal suka yi gaba zuwa ɓangarenta, Mumy dai ta tafi ta zauna
parlor har family Dr din wan Abba wato Alhaji Abubakar da ta kira dazu ya iso
gidan, ta kai sa har ɓangaren Abba, tana kai sa dakin ta fito ta zauna parlor, ita
dai tasan lafiya ya fita yau babu ko alamar ciwon kai amma ya dawo a haka, a
zuciyarta kuma tace ikon Allah kenan, bayan kusan minti talatin likitan ya fito, ta
mike ta nufesa tana kallonsa tace "Dr ya jikin nasa?" Yace "Dole sai mun je
asibiti, jininsa ya hau over" Hankali tashe Mumy tace "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un" Mumy bata san sanda ta tafi ta dauko Hijab dinta ba a ɓangarenta da sauri.




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788




Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son
sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da
xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan
turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba.
Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu
xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da
hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls
guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda
hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls
guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din
da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman
in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800,
6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar
maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰

69

Khalil na tsaye balcony a sama yana kallon motocin suka gama shigowa babban
compound din, wani soja ya bude ma Mami motarta ta sauko, Nihad ma ta sauko suka
nufi entrance din shiga gidan, Mimi da Noor dake zaune main parlor suka yi
welcoming dinsu suka wuce Upstairs gaba daya zuwa bangaren Mami, Suna shiga parlor
Nihad ta zauna saman kujera, Mami ta sa Bilkisu ta tafi ta hada mata ruwan wanka a
bandakinta, Bilkisu na fitowa daga bedroom din Mami ta kalli Nihad tace "Shiga kiyi
wanka, sai ki kwanta ki huta, hope u are not hungry?" Nihad ta girgiza mata kai
tace "Aa na koshi" sannan ta mike ta shiga bedroom din Mami, Mami ta bi ta da
kallo, ko da ta fito wanka taga akwatin kayanta an kawo mata cikin dakin, ta dau
doguwar riga mara nauyi ta saka sannan ta kwanta gefen gadon.... Mimi na fito da
tsaraban da Mami tayi a Uk a cikin wani babban akwati Khalil ya shigo parlon, duk
yawanci kaya ne da ta siya ma Nihad irin English wears, su Mimi ma ta siyo masu
abubuwan da tasan sun fi so, Zaunawa Khalil yayi saman kujera yana kallon Mami yace
"Barka da isowa Mami" Ita ma ta kallesa tace "Yauwa" Yace "Ya hanya" tace
"Alhamdulillah" Bai sake cewa komai ba, Tace "Abbanka yace min ya samar maka aiki
ko?" Khalil yace "Ehh haka ne" Mami tace "Toh Allah ya sanya Alkhairi" Yace "Ameen"
yana ta zaune parlon yana kallon Mimi dake ta fiddo kaya tana waow, can kawai ya
mike ya nufi Bedroom din Mami, yana shiga ciki kuma ya kulle kofar, Nihad ta daga
kai ta kallesa don har sannan bata yi bacci ba, ya karasa kusa da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login