Showing 21001 words to 24000 words out of 268471 words
rai sai kayi xaton ko dariya bata ta6a ba, shi ma ya shiga
motar, suna fita compound Aminu ya daga masu hannu, AC din motar Nihad ta kunna,
shi dai bai nuna yasan abinda tayi ba, suna hawa saman titi tayi connecting phone
dinta ta kure waka a motar, shi dai driving dinsa kawai yake, bayan kusan minti
talatin suna tafiya, ganin tafiyar tasa babu direction, ta wani juya ta kallesa
tace "Wai malam baka san inda xaka kai ni bane, ko Aminun bai gaya maka ba?"
Tafiyarsa kawai yake pretending he didn't know she is talking duk da yana jinta,
rage volume din wakan tayi can kasa, a fusace tace "Malam da kai nake" Ya kalleta
yace "Ohk magana kike, wakar ki ce ta hana inji" Ta yi masa wani kallo tace "Da
yake kai kurma ne ba dole waka ya hanaka ji, Aminu wai bai gaya maka inda xaka kai
ni ba?" Yayi slow down sannan yayi parking yace "Ina ta sauraren kice ga inda xaki
ne ai" Buda baki tayi tana kallonsa, Cikin daga murya tace "Aminu bai gaya maka
bane?" Yace "Toh ai ban ga Aminu cikin motar ba" She couldn't stop looking at him,
ita ba abin ta sauka ba, dakewa tayi tace "Saboda ba kai ke xuba fetur a motar ba
shi yasa kake ta yawo da ni a cikin garin kano ba tare da kasan inda xan je ba ko?"
Bai bata amsa ba, bata kuma ga alamar xai ce komai ba, wani dogon tsaki ta ja, ta
gyara xama tace "Dama harka da ɗan kauye ya gaji haka, idan kaga dama Maryam
Abatcha American University of Nigeria xaka kai ni" Without looking at her yace
"Ohk sai kin dinga min kwatance" Tace "Ban gane sai an maka kwatance ba, kai dama
babu inda ka sani a kanon ka xo ka nemi driving a gidanmu?" Yace "Ehh idan aka ci
gaba da nuna min wajajen xan sani ai" Tace "Amma wllh baka da amfani" Tsaki ta ja
tace "Ai sai ka juya kan motar idan dai ba garinku xa mu je ba" yace "In kince aje
can din ma ai sai aje" Bude baki tayi, sai kuma tace "Wallahi yaron nan ka raina
ni" Sai a sannan ya juya ya kalleta jin abinda tace, ta galla masa wani harara tace
"Malam kana bata min lkci xan je makaranta" Yace "Na xata garin namu xa mu" Daga
haka ya juya, rai a bace ta dinga gwada masa inda xai bi har suka iso makarantar,
ganin yayi parking a waje tace "Malam tada motar nan ka shigar dani ciki, ko duk
nan akwai wanda kaga anyi dropping a titi?" ya ci gaba da driving din slowly, dai
dai gate din makarantar ya tsaya ya sauke glass din motar, gaishesa security din
suka yi, ya amsa ya amshi pass ya shiga cikin makarantar yace "Ina?" Rudely tace
"Duk inda ka ga wancan jan motar ta bi kai ma ka bi, bani da lkcn yi maka wani
kwatancen" Bai ce mata komai ba, ya ci gaba da driving dinsa, Dai dai wajen da
motar ta tsaya ya samu waje yayi parking shi ma, ta ciro wayarta ta kira Husnah,
Husnah na dagawa tace "Kin shigo school?" Husnah tace "Ehh, ke kina ina?" Nihad
tace "Ku fito parking space ke da su Naf ku sameni yanzu yanzu, ki tabbatar har da
Zully xa ku taho" Husnah tace "Ke kika yi driving din yau ma?" Nihad tace "Ke dai
nace ku zo sharp sharp" daga haka ta katse wayar, ta zuge zip din jakarta ta fiddo
chewing gum ta jefa cikin bakinta tana tauna a hankali, Shi dae gabansa kawai yake
kallo, Bayan few seconds ya kashe motar ya zare makullin ya ajiye nan kusa da ita
without looking at her, ya bude motar xae sauka, da mamaki tana kallonsa tace
"Heyy, meye hakan kake yi? Waye xaka bar ma motar?" Still bai kalleta ba yace "Masu
shi" Daga haka ya kulle motar ya juya ya bar wajen, kasa cewa komai tayi sbda
mamaki, can ta sauka motar tana bin sa da ido baki bude, sae ga Husnah da Naf with
Zully da wata kawar Zully, Husnah ta karasa kusa da ita da sauri tace "Nihad what
happened, ya da bude baki haka" Nihad ta kalleta tace "I don't think this guy is
okay, ji tafiya yayi ya bar min motar fa Husnah" Husnah tace "Wa??" Nihad tace "New
driver din, kiranku fa nayi wai ku gansa, mu yi masa tijara..." Husnah tace "Wai
wancan me bakar rigar dake tafiya?" Kasa bata amsa Nihad tayi don da gaske mamaki
ne kawai ya cikata, Naf tace "Kawai haka nan ya kama ya tafi babu magana?" Nihad
tace "Not at all, ajiye min makulli yayi kusa da ni, nace wa xai bar ma motar, wai
masu shi.... kawai ya saka kai yayi tafiyarsa" Lkci daya Husnah da su Naf suka
kwashe da dariya har da kyakyatawa, Nihad ta hade rai, Husnah tayi dariya me isarta
sannan tace "Gaskiya wannan drivern dan duniya ne, ni ko na so in gansa wllh, ya
iya bada amsa dai dai da tambaya" Nihad ta hade rai tayi locking motar ta bar su
wajen a tsaye ta wuce aji, bin ta suka yi har sannan suna dariya, a lecture room
suka sameta, Husnah ta xauna kusa da ita tace "Anya ba ajiye aikin yayi gaba daya
ba" Nihad tace "Toh ni ya kamata ya ba makulli? Ko dama ni na basa makullin?"
Husnah ta fashe da dariya har da kife kai.
*Know the frnds of ur kids*
To gain Access to the book Nihad Contact me directly via👇🏻
07087865788
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices,
siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
💖💖 *NIHAAD* 💖💖
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
8......
Throughout the day's lecture mood din Nihad was so dull, gaba daya she wasn't her
self, Husnah tace "Nihad mu je mu ci abinci ni dai na fara jin yunwa" A takaice
tace "I am not hungry" Husnah tace "C'mon babe, wai me ke faruwa ne? Gaba daya you
look dull today, don Allah ki gaya min me ke faruwa" Nihad ta sauke ajiyar xuciya
tace "Wai har ni mutumin nan xai ma walakanci ya ajiye ma makulli ya wuce Husnah?"
Husnah ta ja wani dogon tsaki tace "Ohh this? Wai wannan ne ya canxa maki mood
throughout? Lallai ma, To wai meye abun damuwa, kika sani ko barin aikin ma yayi?
Ni na fi tunani ya ajiye aikin ne, ba gashi da kika tambayesa wa ya bar ma motar
yace maki masu shi ba, probably yayi quitting ne" Nihad dake ta kallonta tace "Sai
ya rasa wanda xai ajiye ma aiki sai ni, me yasa bai kai ma Abba makullin ba, salon
ayi xaton ni ce na koresa? dama babu wanda ke considering dina a gidan banda Umma,
kawai so yake ya kara ja min bakin jini wajen Mumy" Husnah ta ja tsaki tace "Soo
what? Idan ma ajiye aikin yayi ai hakan ke kika fi so, abinda kike ta so ne ya faru
fa, karkari su gama surutunsu na kwana biyu su yi shiru, sannan a samo wani driver
din wanda xa ki juya yanda kike so, ba shikenan ba?" Nihad ta taɓe baki ta mike
tana harhada material din karatunta tace "Xan tafi gida" Husnah tace "Gida kuma? Da
wuri haka? Ke da nace maki xa mu je guest inn din su Bill yanxu, Kai Nihad yau da
kike da full control din mota an bar maki kiyi yanda kika ga dama shine xa ki wuce
gida da wuri, haba yan mata, ki bari wajajen six ki koma gidan mana" Nihad tace "Ni
kawai gida xan tafi duk raina a bace yake" Husnah ta juya ido tace "Toh ai shkkn,
bari in raka ki gun motar" Tare suka isa inda motar yake, Nihad ta ajiye jakanta da
kayan karatunta a bayan motar, sannan ta zaga ta shiga driver seat, Husnah na tsaye
har ta tada motar ta fara tafiya..... Nihad na isa gate din gidansu tayi horn, mai
gadi ya fito da sauri ya bude gate din, ta shiga gidan tayi parking, sannan ta
kashe motar ta sauka, kallon inda mai gadin yake tayi, ta ga shi kadai ne a wajen,
ta nufi cikin gida ba tare da ta dau material din makarantar ta dake bayan mota ba,
Mumy na xaune parlor da Nihal, sai Umma dake parlon ita ma duk suna kallo, ta gaida
su xata wuce, Mumy tace "Bani makullin da kika amsa wajen driver daxu" Tsayawa tayi
cike da mamaki tana kallon Mumy tace "Mumy wa yace ni na amsa makullin?" Umma tace
"Atoh, nima dai nace baxa kiyi haka ba, amma shi algungumin yace kin amshi makulli,
kuma sun yarda" Nihad tayi narai narai da ido tace "A yaushe na amshi makulli
wajensa? Wllh Umma sharri yayi min" Mumy tace "Ban tambayeki ba'asi ba, makulli
nace kawai ki bani, xa kuma mu hade a daki" Nihad ta fashe da kuka tace "Ni wllh
Allah ya isa wannan sharrin da yayi min, Allah ya isa tsakanina da shi munafuki
kawai, ajiye min makullin fa kawai...." Throw pillow Mumy ta dauke ta jefa mata
tace "Tafi ki bani waje, ga ki nan munafuka, wllh tunda haka kika xaba xa mu sa
kafar wando daya dake a gidan nan, kuma daga yau kika sake driving da kanki sai dai
ki canza wata uwar bani ba" Umma tace "Wai ya kike haka ne Maryam? Shikenan kai da
ɗan ka baxa ka ja sa jiki ba komai ya fada maka sai ka karyatasa baxa ka goyi
bayansa ba, me yasa kike fiffita bare akan naki? Wannan wace irin rayuwa ce? Ki bar
ta tayi bayani ma kin ki sbda rashin adalci" A fusace Mumy tace "Bana son
bayaninta, wani bayani xata min sai kace bani na haifeta ba, ko kuma ban san
halinta ba, wllh daga ni har ubanki babu me irin wannan mugun hali naki don ma
kiji, in har kince ke sai dai ki tuka kanki to wllh ki nemi wata uwar, kuma ai kin
saba cewa a baki makullin ba wnn ne karo na farko ba, don haka babu abinda xa ki
gaya min in yarda" Kuka kawai Nihad take xuciyarta na suya, ta ajiye makullin motar
nan saman kujera tace "Allah ya isa karyan da ya laka min, Allah ya isa tsakanina
da shi..." Tashi Mumy tayi, Nihad na ganin haka ta wuce sama da gudu, Mumy tace
"Tsaya dai ki min rashin kunya" Mikewa Umma tayi ta fita daga parlon, tana fita
compound ta kwalo ma Aminu kira ya taho da sauri, tace "Ina dreban nan yake?" Mai
gadi yace "Ya fita ya ɗan amso abu" Tace "Toh xai dawo ya sameni" Daga haka ta juya
fuu ta koma ciki. Nihad na shiga dakinta ta sa makulli ta dinga rusa kuka ta dau
wayarta tayi dialing number Abba, yana fara ringing ya daga yace "Hello Dear, ina
meeting i will get back to you" Ta fashe da kuka tace "Abba ni dai kawai a canza
driver din nan, bana son ganinsa kuma, i can't withstand the sight of him any
longer, kawai ni dai Abba ka sallamesa" Abba ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Why did
u ask him to hand over the key to you da ya kai ki makaranta?" Nihad ta xaro ido
tace "Abba wllh sharri ya min, ta yaya xan ce ya bani makulli, wllh karya yake min
ni ban ce masa haka ba" Abba yace "Idan na dawo gida xa mu yi magana yanxu muna
meeting ne" Daga haka ya katse wayar, kuka ta dinga yi, nobody is getting her banda
Umma, wato dawowa gida yayi ya laka mata wannan uban sharrin gashi kowa ya yarda,
number Farooq tayi dialing, yana dagawa shi ma ta rushe masa da kuka yace
"Lafiya??" Cikin kuka tace "Yaya dama Abba ne ya dau wani sabon driver, yaya tun da
ya fara aiki yake laka min sharri iri iri, yana sa Mumy na kara tsanata, wai daxu
ya kai ni schl shine ya ajiye min makulli yayi wucewarsa, da ya dawo gida shine ya
je yace ma su Abba da Mumy ni nace ya ajiye min makullin" Farooq yace "To ai
halinki ne wannan, amsan makulli a wajen drivers kiyi driving da kanki, ke ko wani
driver sai kin samu matsala da shi, haka Habibu farkon da ya fara aiki a gidan nan,
why are u always having issues with everybody? Me yasa ita Nihal bata ce an mata
ba" Lkci daya ta hade rai, yace "Shi wannan din yaushe ya fara aiki har kika fara
samun matsala da shi Nihad?" Kin cewa komai tayi, yace "Ki min magana ko in kashe
wayata" Murya can ciki ciki tace "Sallah xan yi" Katse wayar yayi, ta jefar da nata
wayar, wato nobody is even supporting her, then xata dau action da kanta. Tana
kwance bayan tayi wanka tayi sallah wayarta ya fara ring, ta jawo wayar ganin
number da ke kiranta ta mike zaune ta daga tana wara ido tace "Shine baka ce min
xaka dawo ba bayan ko jiya mun yi magana" Yace "How are you?" Ta lumshe ido tace "I
am fine, ya hanya?" Yace "Alhamdulillah, yaushe za mu hadu? I will be leaving for
Abuja next tomorrow" Tace "Wai yau kake nufi xa mu hadu?" Yace "Toh shikenan tunda
ba yau ba" Da sauri tace "Noo ba haka nake nufi ba, i only asked, okay yanxu xan
shirya in fito in sha Allah" Yace "Where are we meeting?" Tace "U suggest" Yace
"How about Royal park..." A hankali tace "Kasan fa an canza mana driver" Yace "Ohh
really, when?" Tace "Kwanan nan" Yace "So u are not use to the new one ko?" Ta taɓe
baki tace "Aa wannan dan rainin hankali ne, i don't think we can eva get use to
each other" Yace "To yanxu ya za mu yi? Sbda ke na sauka kano fa" Tace "For now pls
mu hadu ko a wellcare ne, dama xan ɗan yi shopping..." Yace "Nahh, baxan iya fita
don kawai in je wellcare ba, kina nufin a tsaye xan ganki sannan mu rabu?" Tace "No
pls, after today i will plan where we will be meeting, ba kace next tomorrow xaka
koma ba" Yace "Karfe nawa xa ki wellcare din?" Tace "Kawai shiryawa xan yi yanxu"
Yace "Drivern ne zai kawo ki?" Tace "To ya xan yi shi din xai kawo ni, dama kuma
Abba ya bani kudin shopping kawai dai ban je nayi ba ne har ynxu" Yace "Okay idan
xa ki fito ki kirani" Tace "Tohm, i will call you" Daga haka ya katse wayar. Sosai
taji xuciyarta yayi sanyi duk wani bacin rai dake tare da ita ta nema ta rasa kawai
muryarsa da ta ji. Bayan ta shirya ta fito ta tafi bangaren Mumy, Tana tsaye a
parlon tace "Abba ya turo min kudin shopping, cream dina da sabulu sun kare, ina
son xan je in siya yanxu, sai driver yayi dropping dina a can" Mumy tace "Gobe
Nihal xata je shopping xata koma makaranta, sai ki bari ku tafi tare" Nihad da
gabanta ya fadi tace "Mumy bani da cream din da xan shafa ne fa, let me get even if
it's just the cream today idan ya so goben sai mu je tare, ina gama siyan cream din
xa mu dawo gida" Mumy tace "Allah ya tsare, sannan kuma ki yi masa abinda kika
saba, ki tabbatar tare xa ku dawo gidan nan da shi" Nihad dai bata ce komai ba ta
juya ta bude kofar dakin sannan ta fita. Tana fita compound taga bata ga drivern
ba, ta tambayi mai gadi yace "Yanxun nan ya bar nan, ya shiga can bangarensu.... "
Chalet din ta nufa, ta hangosa zaune saman matakalan dake wajen waya kare a
kunnensa, yana hangota ya katse wayar kuma ya ki kallonta, ta karaso babu yabo bbu
fallasa tace "Hey idan ka ga dama zaka ajiyeni a well care yanxu yanxu" tana fadin
haka ta juya ta bar wajen. Da ido ya bi ta, sai kuma ya mike ya ciro makullin a
aljihunsa ya bi bayanta, tana tsaye compound din ta kira Aliyu, ta sanar masa gata
nan xata fito, bayan ta gama wayar ta karasa ta shiga bayan motar, sai da suka hau
saman titi sannan yace "Kwatance xa ki yi" Ta hade rai tace "Kai ko ina sai kace
baka sani ba sai an maka kwatance, baka da Google map ne??" Yace "Ban da" Tsaki ta
ja, haka ta dinga gwada masa inda xa su bi har suka iso well care, parking yayi a
space da ake parking din, tayi dialing number Aliyu, yana dagawa tace "Are u
inside?" Waige waige ta fara yi jin abinda yace, tace "I am also outside, where did
u park?" Sauke glass tayi, lkci daya ta hangosa, murmushinsa me kyau ya sakar mata
yana kallonta, xata katse wayar yayi saurin cewa "Waitt" sai ta fasa kashewa tana
sauraronsa, yace "What if idan an ɗan basa wani abu mu ce ya jira mu a nan, mu je
eatry... i am jet hungry" Rasa abinda xata ce masa tayi, don ta ce ma Mumy baxata
dade ba, can ta saci kallon Khalil ta ga idonsa a kan Aliyu yake ko kiftawa bai yi,
duk da glass din a dage yake, kuma tinted ne ba me duhu can ba, a ranta tace wannan
ma yayi kama da wanda xai amshi abu idan an basa, bude motar tayi ta sauka ta nufi
inda Aliyu yake, shi dai Khalil bai daina kallon Aliyu ba kamar ya ga wani halitta
na daban, tana
karasawa gun motar Aliyu dake ta kallonta underneath his breathe yace "Waow, baby
kin kara kyau fa, tell me what is d secret" Tayi masa murmushi wanda har dimple
dinta sai da ya lotsa, sauke idonsa yayi kasa, can ya zaro dollar 100 a aljihunsa
yace "In bashi wannan ya jira mu a nan?" Tana kallon kudin tace "Toh kasan dai ba
wai mun saba da shi bane, snn bashi da kirki fa wllh" Aliyu yace "Kudi ne baki fara
basa ba shi yasa baku saba ba, yana ganin wannan yanxu xaki ga kun dawo kun dai
daita kun saba" Bude motar yayi ya fito, walking majestically ya nufi motar, Nihad
ta bi sa da kallo, Waige waige khalil ya fara yi da sauri, as if looking for an
alternative kafin Aliyu ya karaso gun motar, lokaci daya kawai yayi locking motar
kafin ya iso, Aliyu na karasowa ya bude motar yaji a kulle, kwankwasa glass din
motar yayi, Khalil ya kauda kai duk da Aliyun ba ganinsa yake ba, Sau biyu Aliyu na
kwankwasawa kafin ya daga kai ya kalli Nihad, ta buda masa hannu alamar i told u
dama, mamaki ne ya cika Aliyu ya dinga kallon motar, can ya sake Kwankwasa glass
din, tace "Dear just leave him ka bar wajen kawai, ba nace maka ɗan iskan yaro
bane" Aliyu da ransa ya gama baci yace "Who did he