Showing 30001 words to 33000 words out of 268471 words

Chapter 11 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

na nan nasan da kansa zai xo ya daukeki idan aka
gama partyn ko karfe sha biyun dare ne, yanxu dole kinga sai mun ajiye ki a nan
after the party in ba dai saurayi kika yi a can ba" Nihad dai ta xuge jakarta ta
fara gyara fuskarta xata yi light make up. Wajen partyn ya hadu iya haduwa kamar
yanda Husnah ta fada ai kam ya yan manya ne suka cika wajen, very dim light ne
kunne a inda suke birthday din, babu abincin da babu da abun sha tun daga ruwa,
lemo, wine, alcoholic drinks, kai komai da akwai a wajen, gasassun rago biyu aka
bankare wajen, ga manya manyan pepper chicken... cake din da budurwarsa tayi masa
ma kadai abun kallo ne... duk hayakin cigarette ya turnike wajen, an sha shagali
iya shagali a birthday din nan, abinda Nihad bata yarda da shi ba shine ta sake ma
maza fuska a wajen, xata dai shige cikin kawayenta mata amma bata xama cikin maza,
ko da kana ta shisshige mata ma banxa xata yi da kai tayi ta danna waya, Husnah ta
kwankwade glass din wani alcoholic wine, glass na biyu kenan ta sha, su Naf da
sauran yan matan wajen su ma duk wine din suke sha, Husnah na kallon Nihad dake
rike da cinyar kaza da wani can drink a gabanta tace "Wllh ki ɗan dana wine din nan
ya fi na wancan ranan dadi sannan shi wannan babu abinda xa ki ji idan kika sha,
wllh soo cool" Nihad tace "Aa baxan sha ba drink din nan ya isheni" Zully tace "Ke
dadina dake kwabsin ki yayi yawa, don Allah ki ɗan kurba idan bai maki ba sai ki
bari kar ki sha, nima kinsan ai ban fiye son wines haka ba, amma tunda kika ga ina
shan wannan ya kamata kisan ba karya" Nan duk suka mata caaa akan cewa ta ɗandana
idan bata ji dadinsa ba sai ta bari, Husnah ta cika mata glass din gabanta tace
"Kiyi sipping first ki ji" Nihad ta dauka ta kai baki ta kurbi kadan, bayan few
seconds ta wara ido tana kallonsu tace "Waow its really nyc, it tastes good" Husnah
ta kyalkyale da dariya tace "Ba na gaya maki ba da kin tsaya kin kwabsawa" Nan
Nihad ta kwankwade wine din, Husnah ta kara cika mata glass nan ma ta shanye, Naff
sai dariya take tana cewa "Wllh ki bar ta haka Husnah tam ni dai na gaya maki"
Husnah tace "Toh meye a ciki ai baya wani bugarwa" Haka dai Nihad ta sha wine tayi
nak, party din da ba a karasa da ita ba kenan tayi ta masu layi a wajen, banda
dariya babu abinda suke mata, Husnah tace "Kaii amma jininta ma bai da karfi wllh,
ɗan wannan wine din shine xai bugar da ita" Nan suka ci gaba da shagulgulansu,
Nihad kuwa ta kife kai a wajen sai bacci, ba a tashi birthday din nan ba sai karfe
dayan dare, Husnah ba irin tashin da bata yi ma Nihad ba amma ta ki tashi, da ta
dagota xata koma ta kife kai, wani abokin celebrant din yace "Na kama daki a nan
why not kawai ku barta ta kwanta ta huta" Husnah tace "Aa nasan halinta tana
farkawa xa mu samu matsala da ita, kawai dai kamata yayi mu ma a kama mana dakin
dama dare yayi ba lallai a bari mu shiga schl ba yanxu, idan ya so duk sai mu kwana
a nan" Ba don ransa ya so ba haka nan ya kama masu dakin, suka ciccibi Nihad sai
dakin suka kwantar da ita saman gado, Husnah dai na ta kaffa kaffa da Iphone din
Nihad a wajen tunda ta san halin wasu daga yan matan dake wajen. Sai kusan biyu
suka kwanta a dakin bayan duk sun yi wanka.
Karfe hudu da rabi Nihad ta farka da wani axababben ciwon kai, da kyar ta mike
xaune tana bin dakin da kallo, sai kuma ta sauka tana layi ta nufi kofar dake dakin
wanda bandaki ne, ta kuma sani tunda sun saba lodging a wajen ita da su Husnah,
tana shiga bayin bayan tayi fitsari taji wani amai ya taho mata, nan ta dinga
kwarara aman tana rike da cikinta dake juya mata, da kyar ta wanke bakinta bayan ya
lafa mata ta fito, bata sake komawa baccin ba sbda ciwon kai me tsanani da ya
takurata, ganin biyar ya kusa ta ta6a Husnah da kyar, ta fi minti goma tana tada
Husnah dake xuba minshari kamar wani kato, kafin ta bude ido cikin magagin bacci
tace "Wai ya aka yi Nihad?" Da kyar Nihad tace "Don Allah wa xai yi dropping dina
gida kafin yan gidanmu suyi noticing bana nan, asuba ya riga yayi" Husnah ta ja
tsaki tace "Tsakar daren nan wa xai wani kai ki gida kowa na bacci, ki bari gobe
kawai" Nihad tace "Ke asuba fa yayi ki duba agogo ki ga, wllh na manta yayanmu na
gida zai iya xuwa bedroom dina yace xai tasheni inyi sallah, idan yana gari duk
yana tashin mu...." Husnah tace "Ohh God Nihad ki barni inyi bacci mana, haba" Daga
haka ta juya ta ci gaba da baccinta, tashi Nihad tayi da kyar ta bude jakarta ta
dau Hijab dinta ta saka sannan ta bude kofar dakin ta fita, babu kowa reception din
hotel din sai tv dake aiki, ta fita haraban wajen, wani mutumi ta gani xaune yana
ta xukar ta6a a waje, ganinta ya kashe ta6ar, ta nufesa tana kallonsa ganin
bahaushe ne tace "Bawan Allah idan babu damuwa ina son taimako wajenka don Allah"
Daga sama har kasa yake kallonta yace "Taimakon me?" Tace "Nasarawa GRA nake son ka
ajiyeni pls, kawayena da muke tare da su bacci suke ni kuma ban xo da motata ba"
Yace "Ohk babu damuwa, bari in dauko makullin motata" Tace "Toh Nagode, nima xan
dauko jakata" Daga haka duk suka koma ciki, ta shiga dakinsu, shi ma ya shiga nasa,
ta tattara komai nata a jakarta, wayarta ne kawai bata gani ba, zaro ido tayi lkci
daya hankalinta ya tashi ta fara tashin Husnah a rikice tace "Husnah ina wayata??"
Da kyar Husnah dake ta snore kamar doki ta bude ido, a fusace tace "Ohh my God
Nihad ki kyaleni mana inyi bacci, me yasa kin fiye takura ne wai" hankali tashe
Nihad tace "Dalla can ina wayata??" Husnah ta ja wani dogon tsaki ta daga pillow
dinta ta zaro wayar ta ajiye mata a gefe sannan ta ci gaba da baccinta, Nihad ta
sauke ajiyar xuciya sannan ta dau jakarta da wayar da sauri ta fita, Tsaye ta gansa
a haraban hotel din yana jiranta jikin motarsa, bayan ta shiga motar shi ma ya
shiga, suna fita daga suite din yace "Ku ne ku ka yi birthday jiya?" Gyada masa kai
tayi kawai, yace "Gaskiya ne, birthday din na manya ne" Duk surutun da yake Nihad
ba tankasa take ba, banda tashi babu abinda xuciyarta yake, she was so
uncomfortable, a haka ta dinga daurewa tana masa kwatance har suka isa dai dai inda
su Husnah suka dauketa daren jiya, yace "Ina gidan naku?" Ta nuna masa wani layi
dake a rufe tace "xan karasa da kafa, kaga gate din a kulle yake" yace "Ohk amma ya
sunanki?" Cike da karfin hali tace "Aysha" yace "Maa sha Allah, Aysha ki bani digit
dinki mana" ta gyada masa kai kawai, ya mika mata wayarsa ta amsa tayi dialing wani
old line dinta dake a kashe tace "Wayar a kashe yake sai na shiga gida na kunna"
yace "Toh shkkn nagode Aysha ni sunana Mustapha" tace "Nagode, sae anjima" daga
haka ta bude motar ta sauka, cike da karfin hali take tafiya don jiri ke dibanta,
ta shiga layin da ta nuna masa, sae da ya ga tayi nisa sosai a layin sannan yayi
reverse ya bar wajen, tana waigowa taga ya wuce, ta juya da sauri ta dawo ta fita
daga layin sannan ta dau hanyar nasu layin, gani tayi kamar an idar da sallah bayan
ta iso kusa da gate din gidansu, da sauri ta bude karfen inda aka xagaye da flowers
a kofar gidan nasu ta shige bayan flowers din ta buya tana maida numfashi, don har
an fara fitowa daga masallaci, tana jin aka shiga cikin gida aka kulle gate, Sai
kuma ta sake jin an bude gate din, Muryar Abbanta taji yana amsa gaisuwa nan bakin
kofar gate din, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta, ta kara yin lamo a cikin
flowers din duk da ant da taji suna cizonta bata damu ba, ta fi minti bakwai a haka
bata sake jin motsin kowa ba bakin gate din, hautsinewa cikinta ke yi taji amai na
taho mata, kokarin fitowa take yi daga flower din don ta samu ta shige cikin gida,
kawai taga mutum xaune a dakalin dake kusa da inda take labe, sai da zuciyarta ya
kusa shigewa cikinta don duk xatonta ya Farooq ne don shi ma ya kan xauna a waje
idan aka idar da sallah, ya daga kai jin motsi, sai kuma ya mike tsaye da sauri,
komawa baya yayi yana kallonta with surprise, ita kuwa tsabar tsorata aman da take
rikewa ya taho mata, ta durkusa ta dinga kwarara aman a wajen, kauda kansa yayi
bayan yayi perceiving din aman da take yi, ya sake kallonta this time around da
wani expression a fuskarsa, duk sae da ta amaye sauran liquor din cikinta sannan ta
mike da kyar, ko kallonsa bata yarda tayi ba ta shige gate din gidan, ya bi ta da
kallo babu ko kiftawa, ko second ashirin ba ayi da shigarta ba sae ga mai gadi da
gudu ya fito waje yana kallon Khalil yana zare ido yace "Ina me tabbatar maka bata
kwana gida ba, dawowarta kenan daga duk inda ma taje wllh" Khalil dai bai ce komai
ba, mai gadi ya yamutse fuska yace "Ni warin giya ma nake ji, ko kai baka ji ba don
Allah?" Khalil ya juya ya shiga gate din gidan ya xauna nan saman bench dake gefen
dakin mai gadi with numerous thought running his mind, mai gadin ma ya shigo ya
zauna yace "Ni fa sai nake ganin ma kamar warin giya take ko kai baka ji ba?"
Khalil ya kallesa yace "Amma baka wanke bakin ka ba ko?" Mai gadi ya ɗan zaro ido,
sai kuma yayi yake yace "Ai shi xan wanke ma na fito yanxu..." Tashi yayi da sauri
ya shige dakinsa, Khalil ya kalli hanyar gate din, sai kuma ya mike ya fita,
jakanta da ya hango cikin flowers da ta bari ya dauko ya shige cikin gidan sannan
ya nufi chalet dinsu, A parlor ya tadda Su Saminu sun yi dai dai duk suna bacci, ya
ciro makullin daki a aljihu, ya bude dakin sannan ya shiga ya kulle kofar, xaunawa
yayi gefen gado ya bude jakar, takalma heels ya fara cirowa da kayan kwalliya da
turarruka, sai iphone dinta da ya gani, ya dinga jujjuya wayar don a lock yake, sai
kuma ya ajiye ya ci gaba da ciro sauran kayan jakan, bai san sanda ya bude baki ba
ganin kwalban Codeine, can ya ajiye a gefe, ya bude wani zip dake cikin jakar,
still yayi ya dinga kallon abinda ke wajen babu ko kiftawa, ya kai hannu a hankali
ya cirosu gaba daya yana jujjuyawa, prophylactics ne na maza da na mata, ya ajiye
su a gefen gado ya mike ya nufi window din dakin yana kallon waje babu ko kiftawa.
Nihad na fitowa daga wanka aka bude kofar dakin, sae da zuciyarta ya kusa shigewa
cikinta don tsoro, Umma ce ta shigo dakin ta rufe kofar murya can kasa tace "Daga
ina kike Nihad?" Nihad ta daburce tace "Ni Umma?" Umma tace "Aa ban son karya ba
yanxun nan naga giftawarki ba na fito daga parlon Abbanku?" Nihad tayi narai narai
da ido tayi shiru, Umma tace "Gaya min gaskiyan inda kika je" A hankali tace "Wata
kawarmu ce ke birthday Umma" Umma tace "Ki dai nutsu, in ma xaki birthday ae sai ji
gaya min ni baxan hanaki ba, amma baxa je makarantar yau ba bacci xa kiyi ko?" Tace
"Aa xan je" Umma tace "Toh sai kiyi ki shirya karki makara" Daga haka Umma ta juya
ta fita, Nihad ta sauke ajiyar xuciya, sai yanxu da ta sake wani aman da xata yi
wanka taji ta ɗan fara dawowa dai dai, kanta ya daina juya mata, tana gaban madubi
tana shafa mai ta tuna da jakarta, xaro ido tayi ta mike da sauri ta dau hijab
dinta gogagge ta saka sannan ta fito daga dakinta, downstairs ta sauka ganin Farooq
a xaune dining area tace "Yaya ina kwana?" Yace "Kina jin ina Knocking ki ka ki
bude kofa daxu?" Tace "Aa yaya ina bandaki ne, ai na tashi sannan ma" Bai ce komai
ba, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ta bude kofa, yace "Ina xa ki?" Ta
marairaice tace "Xan je in duba ko Allah xai sa tsuntsayen sun dawo" Murmushi kawai
yayi ta juya ta fita, da sauri ta nufi gate, taji dadin ganin mai gadi baya bakin
gate din, sannan khalil ma baya wajen, tana bude gate ta samesu su biyu xaune kofar
gidan, suna hada ido da khalil ta daburce, sai ta hau kame kame, bata amsa gaisuwar
da mai gadi ke mata ba tace "Aminu a layin nan babu inda zan samu katin waya?"
Aminu yace "Inaa, Hajiya ai sai an fita can supermarket" Tace "Ohk" Da gefen ido ta
dinga lekan cikin flowers din dai dai inda ta buya amma bata ga alamar jaka ba, nan
hankalinta ya tashi sbda wayarta na ciki, bata san lkcn da ta karasa wajen ba tana
kara dubawa da kyau, Aminu yace "Wani abu kike nema ne Hajiya?" Wani shegen kallo
tayi masa tace "Toh ina ruwanka?" Khalil dai na ta danna er karamar wayar hannunsa,
ta saci kallonsa.




✍🏻
07087865788
💖💖 *NIHAAD*💖💖




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




11


Juyawa Nihad tayi daga karshe ta koma cikin gidan don ko kallon inda take Khalil
bai yi ba, to wai wa ya dau jakarta? lkci daya jikinta yayi sanyi hankalinta ya
tashi fiye da da, haka nan ta shiga gida jiki ba kwari ta koma dakinta ta shirya,
Hijab har kasa ta saka ko powder bata shafa a fuskar ba, ta fito ta tafi bangaren
Mumy, xaunawa tayi saman kujera ta gaisheta sannan tace "Mumy xan tafi makaranta
ina da lectures karfe takwas" Mumy ta kalli agogo ganin bakwai da rabi tace "Kinyi
breakfast ne?" Tace "Xan yi idan na sauka" Mumy tace "To ko ke fa da kika sa Hijab
yau, kinga yanda yayi maki kyau, amma kullum in ta maki magana daya a kan shegun
mayafan nan da kike sawa ba kya ji" Nihad ta ɗan kirkiri murmushi ta mike tace "Sae
na dawo" Mumy tace "Toh Allah ya tsare, kiyi addu'a kafin ki fita" Nihad ta amsa da
"Toh" sannan ta fita. Gaba daya Nihad neman appetite dinta tayi ta rasa, daga
karshe nan ta bar abincin tayi ma Umma dake parlor sallama ta fita gidan, mai gadi
kadai ta samu xaune bakin gate, ta nufesa tana tsaye dab da shi tace "Aminu don
Allah baka ga min jaka a bakin gate ba? Kamar a nan na yar jiya da daddare, ko da
safe nan don Allah baka gani ba??" Yace "Subhanallahi jaka Hajiya? ae ko wllh tllh
ban gani ba, kema kin san da na gani ae xan adana maki" Nihad ta rasa abun cewa
tayi shiru, iphone dinta fa na jakar yanxu ta ina xata fara? Wani xufa ta ji na
keto mata, can ta dake tace "Ina driver din?" Aminu yace "Ya tafi yayi wanka" Tace
"Sae kaje kace masa ya fito ya kai ni makaranta ni dai" Aminu ya mike da sauri yace
"Toh Hajiya" daga nan ya nufi chalet din. Bayan Aminu ya shiga har dakin da khalil
ke ciki ya sanar masa abinda Nihad tace, khalil dake zaune gefen gado yana combing
kansa yace "Ta saba xuwa makaranta karfe bakwai da rabi dama?" Aminu yace "Atoh
dae, nima ban ta6a ganin ta fita da safe xuwa makaranta ba wai kuma ran asabar,
amma kai dai kawai ka fito kaje ka kai ta kar ta kara maka wani fitsarar" Khalil ya
kallesa bai dae ce komai ba yana ci gaba da combing din kansa, Aminu ya bi dakin da
kallo yace "Wai!!! amma kana kokarin gyara dakin nan, dubi fa dakin kamar a can
daya bangaren, ba dauda ba wari ba tarkace, wannan ai idan na kwanta a nan sai in
makara al-qur'an...." Khalil ya mike yace "Mu je..." Aminu ya kasa kunne yace "Ba
waya bace ke wannan rurin?" Khalil yace "Mu dai je" Aminu ya mike ya fita dakin,
Khalil ya bi sa da kallo kafin ya dage duvet din da ya lullube jakar Nihad da shi a
saman gado sannan ya bude jakar ya ciro wayarta dake ta vibrate alamar kira, Husnah
ya kara gani for the fourth time a jikin screen din wayar, tun daxu take kira,
nannade wayar yayi da duvet don baxae iya silencing dinsa ba sbda security dake
jiki, ya dau makullin mota ya fita daga dakin ya kulle sannan ya fita compound.
Yanda xaka san abun duniya ya taran ma Nihad xama tayi a kan bench da mai gadi da
Khalil ke xama, ita dai tana da yakinin dole Khalil xai hango jakar a bayan flowers
kuma ai a bude ma ta bar karfen wajen, wai to don bashi da kunya sai kawai ya kama
ya dau mata jaka, yaushe ta sake masa har xai kai hannunsa kan jakarta, wato yanxu
jira yake sai ta tambayesa kenan? Cabdi... tana hangosu tayi maza ta mike ta sha
kunu, Khalil dai ko kallon direction dinta bai yi ba ya tafi gun motar ya bude ya
shiga, bayan yayi warming mai gadi ya bude masa gate, Sai da ya fita compound
sannan Nihad ta fita ita ma tana tafiya a hankali ta bude back seat ta shiga ta
xauna, Aminu ya dinga daga mata hannu alamar a dawo lafiya, ko kallonsa bata yi ba,
Khalil ya ja motar suka bar layin, tunani take to yanxu dai tambayarsa jakarta xata
yi? Cab gaskiya baxata yi hakan ba, m ta saci kallonsa ta madubi suka yi ido hudu,
da sauri ta dauke kanta ta wani daure fuska ta zuge zip din wani jakar da ta dauko
ta fiddo chewing gum ta bude ta jefa baki, shi dai driving kawai yake, sai da suka
kusa makarantar tayi gyaran murya tace "Malam ka bude min Ac xafi ya dameni...." A
takaice yace "Ke kika san meye shi" Tayi masa wani kallo tace "kace me??" Bai tanka
ta ba, ta masa wani shegen harara ta ja tsaki kasa kasa ta ci gaba da taunar
chewing gum dinta, suna isa makarantar dai dai department din nasu yayi parking,
tana ta sauraron ta ji ko xai yi maganar jakar amma shiru, gabansa kawai yake
kallo, ganin bata sauka ba, kuma kamar bata da niyyar saukan yace "Ko yau ma xa a
bar maki makullin ne?" Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login