Showing 120001 words to 123000 words out of 268471 words

Chapter 41 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

daga part dinta. Karfe tara da rabi Mami ta shigo parlon da
Nihad take tana kallon Nihad tace "Toh ki tashi kiyi wanka don ki ji dadin jikinki
ko?" Nihad ta mike tsaye ba tare da ta bari sun hada ido ba, Mami dai sai kallonta
take, ganin ta nufi kofa tace "Ga bandaki nan a bedroom" Ta girgiza kai tace "Zanyi
a na parlor" Daga haka ta fita daga parlon zuwa daya parlon wanda bandakin ke ciki,
tayi hakan ne sbda la'akari da tayi da Mumynta, bata sharing bathroom din dakinta
da kowa, khalil dake danna waya ya daga kai ya kalleta, tun da ta kalli iphone din
hannunsa bata sake kallon direction din nasa ba, yaga ta shiga bandaki, Mami ta
shigo parlon ta kirasa ya mike ya bi bayanta, suna tsaye parlon farko tace "Toh
yanzu a haka da taki sakin jiki zan kai ta bangarensu Mimi?" Yace "Aa Mami ki yi
mata shimfida kawai a parlor nan ta kwanta" Mami tace "Aa haba dai, ya zata kwana a
parlor, abinda yasa kaga bance zata kwanta nawa bedroom din ba i am leaving it for
you kai ka kwanta, ni zan je in kwanta wani wajen" Yayi Murmushi yace "Aa Mami ba
sai kin bar min gadonki ba, kawai ki kwanta ni zan kwanta parlor, kema kinsan i
prefer sleeping on the couch" Tace "Toh shikenan sai mu kwanta da ita a daki, let
me get her sleeping dress wajensu Mimi...." Daga haka ta fita sai gashi ta dawo da
sabuwar rigar bacci na Noor ta kai dakinta ta ajiye ma Nihad a gefen gado da
tsadaddun spray biyu sannan ta fito, Nihad na fitowa daga wankan taki shiga dakin,
shi dai yana ta danna wayarsa, ta rakube jikin kujera, Mami ta fito parlon zata ma
Khalil shimfida, ganin Nihad a rakube tace "Baby shiga ciki ki shirya, za ki ga
sleeping dress da turare na ajiye maki saman gado" A hankali Nihad tace "Nagode"
Daga haka ta shiga dakin, Shimfida me lafiya Mami tayi ma Khalil a parlor na biyu,
shi dai bin ta kawai yake da kallo, yasan yayi kewar Maminsa fiye da zatonsa, he so
missed all this, har bedroom dinsa Mami kan shiga ta gyara masa back then, tana
gamawa ya mike ya nufeta yayi mata side Hug cikin sanyin murya yace "Thanks Mamina"
Tace "Ai kai ma zaka yi wankan ko?" Yace "Sure" Tace "Let me get u ur pajamas" Daga
haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo, sai kuma yayi murmushi ya shiga dakinta don
shiga banɗakinta yayi wankan, zaro ido Nihad tayi ta rufe jikinta da kayan baccin
da take kokarin sakawa ta durkusa kasa da sauri ta rufe fuskarta, ya sauke idonsa
ya juya ya fita daga dakin, bandakin da tayi wanka ya shiga kawai, Mami ta ajiye
masa pajamas din saman inda tayi masa shimfida bayan ta dawo ta tafi dakinta,
dariya Nihad ta bata ganin yanda ta rakube kasa jikin dressing mirror bayan ta saka
kayan baccin, Mami tace "To tashi ki hau gado ki kwanta" Nihad ta kalleta da sauri
cause she never expect it, can tace "Aa zan kwanta a kasa" Mami tace "Common hau
gado kiyi kwanciyar ki Baby" Shiru Nihad tayi sai kuma ta mike a hankali ta tafi ta
hau saman babban bed din wanda furnitures dinsa kadai ma abun kallo ne, Mami ta
dago mata duvet ta mika mata ta amsa ta rufe jikinta ɗon dakin yayi sanyi ta
dalilin Ac dake kunne. Har kusan karfe dayan dare Nihad bata ga bacci ba, tuni Mami
tayi bacci, da ta tuna wasu abubuwan sai taji hawaye me zafi ta gefen idonta na
zuba, she wish she could rewind everything from the scratch, she wish many things
didn't happen, daga karshe da taga she needs to cry out ko zata samu saukin abinda
take ji a ranta, cike da karfin hali ta mike zaune tana kallon Mami cikin duhu, a
hankali ta lallaba ta sauka daga kan gadon ta tafi bakin kofar, nan ma ta tsaya
tana tsoron kada kofar yayi kara idan ta bude har ya farkar da Mami, can dai ta
runtse ido ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude, bata ji yayi
kara ko kadan ba, ta fita ta kullo mata kofar, yana kwance parlon nan ma wutan a
kashe yake, a hankali tana tafiya making sure she isn't making any sound ta tafi ta
bude dayan kofar ta shiga daya parlon, can wani corner ta tafi ta zauna tana
shesshekan kuka cike da tausayin rayuwarta, hawaye kawai take wani na bin wani, tun
da ta fito daga
dakin Khalil da shi ma bai yi baccin ba ya bi ta da ido cikin duhun har ta tafi
daya parlon, he can't say why he is still awake may be over excitement ne na cewar
yau gashi a gida da Maminsa after some years, bayan kusan minti 7 ya mike a
hankali, shi ma bai kunna wutan ba ya nufi kofar ya bude gently ya fita, ta
direction da yake jin shesshekan kukanta ya nufa, kawai gani tayi wani abu da yayi
mata kama da statue tsaye a kanta, er kara tayi a mugun tsorace ta mike xata gudu
ya rikota, sai a sannan ta ji kamshin turarensa ta rufe fuskarta da sauri a jikinsa
tana kuka a hankali, bayan few seconds yace "Saboda kiyi kuka kika fito nan?" Ita
dai bata ce komai ba sai shesshekan kuka take tana Girgiza masa kai kawai, ya
janyeta jikinsa yace "Zauna nan" ta tattaba bayanta taji kujera, hakan ya sa ta
zauna a hankali, yana tsaye inda yake yace "Ki saurari duk abinda zan ce maki yanxu
cause it's for ur benefit" ita dae tayi shiru tana jin sa gabanta na faduwa, yayi
kasa da murya yace "On no condition xa ki gaya ma wani a gidan nan relationship
dinmu, that should be s secret between us har zuwa sanda xa mu cika ma juna
alkawarin da muka dauka a baya" Nihad dai kanta na kasa, yace "Nace ma yan gidan
admission letter kika zo amsa garin nan, so duk abinda zaki ji na gaya masu gobe ya
zama hakan kema a wajenki" Nihad ta share idonta ta gyada masa kai kawai, ya kunna
wutan parlon yana kallonta yace "Sai da safe" Bata yarda sun hada ido ba ta mike ta
nufi kofar shiga second parlon Mami ya jira har ta shiga sannan ya bi bayanta.
Washegari Nihad na tashi taga ita kadai ce dakin Mami, tana kokarin gyara gadon sai
ga Bilkisu ta shigo, Bilkisu na murmushi tace "Ina kwana" Nihad ta sauke idonta
tace "Mun tashi lafiya" Bilkisu tace "Ai da kin bar shi ma xan shigo in gyara,
aikina ne" Nihad dai bata ce mata komai ba ta shigo ta fara abinda zata yi, Nihad
ta fita parlor, tana bude kofar first parlor taga Mami da khalil a zaune parlon, Ta
gaida Mami da ladabi Mami ta amsa mata da fara'a, ta kalli Khalil suka hada ido, ta
kasa barin wajen bata gaishesa ba saboda Mami dake zaune, bata yarda ta kallesa ba
tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya, ga breakfast din ki" Mami tace "Bari a kai mata can
parlon so that she will be comfortable" Yace "Aa za ta yi a nan" Nihad dai bata ce
komai ba, can ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, ya nuna mata breakfast
din dake saman tray, ta dauka ya nuna mata inda xata zauna, Mami dai sai bin ta da
kallo take because she is so cute and meek, Mami ta kallesa tace "Amma 'yar mai
gidan da kake ce min kana zama wani lokacin a gidansa ce ko?" Khalil zai yi magana
aka bude kofar parlon, Mimi da Noor ne suka shigo, suka yi wani ihu a tare ganinsa,
daga inda yake zaune duk suka tafi da gudu suka rungumesa so happy seeing him, sai
ga wasu set din Yan matan biyu Hanan da Farhana, su ma duk suka rungumesa so so
happy seeing him, he couldn't help it but smile don shi ma yayi kewansu sosai, Mami
dai sai murmushi take, Mimi ta kalli Mami ta fashe da kuka tace "Mami mene ya sa
zaki boye mana yayanmu ya dawo, Abba yace he's been around since yesternight" Sai
kuma ta fashe da kuka, Khalil ya jawota gefensa yana kallonta yana murmushi yace
"Is there any diff between now and the yesternight" Tace "Yes of course, wallahi da
nasan kana nan nima a nan zan kwana jiya, i soo miss you yayanmu" Tana fadin haka
ta kara rungumesa tana hawaye, Nihad dai sai bin su take da kallo kana ganinsu
kasan su ne ainahin rich kids din, duk Mimi ta fi kama da shi, Noor ma fara ce
Farhana da Hanan ne kadai haskensu bai kai nasu Mimi ba, Farhana sai kallon Nihad
take keenly, can ta kalli Mami tace "Mami who is she?" Mami tace "Our visitor"
Tambayarta ne ya ja hankalin sauran yan matan suka kallo inda Nihad ke zaune, Noor
ta ɗan juya ido tace "Ohh She looks familiar" Hanan dai kallonta take babu ko
kiftawa kamar me son gano wani abu, can ta ja Noor suka fita daga parlon tana zare
ido tace "Kin tuna wata yarinya da video dinta ya tafi viral weeks ago?" Noor ta
zaro ido bayan tayi recalling video din tace "Ohh yess!! exactly, wallahi suna kama
sosai, i think baxan rasa video din a thrash bin dina ba" Tun da Khalil yaga
sisters din nasa duk sun yi concentrating kan Nihad, yace "Ohk, ohk now, i need
rest za mu hadu anjima a main parlor..." Mimi tace "Yayammu who is she, nima kamar
na santa" Mami tayi dariya tace "A ina kika santa, banda karya Mimi" Mimi ta juya
ta sake kallon Nihad da ta sunkuyar da kai gabanta na mugun faduwa don banda nude
video dinta babu abinda ya fado ranta, mikewa Khalil yayi yace "Mimi za mu hadu
anjima a main parlor, i said i need rest, ku fita" Sai ga Noor da Farhana sun shigo
da gudu parlon, Hanan ta biyosu da sauri, Noor ta nufi Mami har tana tuntube tana
mika mata wayarta tace "Mami u remember this???" Mami ta amshi wayar ganin video
din da take nuna mata tace "Wai ba nace ki goge video din nan ba Noor? What is it
still doing a wayarki?" Noor na zaro idanuwanta kamar za su fito tana nuna Nihad
tace "Ba ita bace warcan" Mami ta kalli Nihad da sauri, sai kuma ta amshi wayar
tana kallo, Kasa cewa komai Khalil yayi, Nihad da jikinta yayi sanyi kamar warce
aka kwara ma ruwan sanyi ta kasa kwakkwaran motsi inda take zaune ta dinga bin su
da kallo kamar warce tayi ma sarki karya, sai kuma ta sunkuyar da kanta with tears
in her eyes, Mami ta kalli Khalil da sauri, sai kuma ta kara kallon Nihad, tuni
Farhana ta tafi ta kirawo wasu set din yan mata biyu duk suka tsaya bakin kofa ko
warce da wayarta a hannu, da ta kalli videon sai ta leko ta kalli Nihad baki bude,
Mami da ita kanta jikinta yayi sanyi qlau ta kara kallon Khalil that is saying
nothing, can ta hadiye wani abu tace "No, no may be resemblance ne kawai, ai akwai
resemblance" Noor da Farhana suka wani gwalo ido har suna hada baki suka ce "Mami
wallahi ita ce, the video is so clear fa ba wai yayi dishi dishi bane, ki duba mana
ki ga, ita ce wllh" Da sauri Hanan ta tafi tana mika ma Mami waya wai don ta kara
gani da kyau, Mami ta ki amsar wayar bata kuma sake cewa komai ba, Sajida tace
"Ikon Allah, then who brought her to this house? Ance yar Maryam Abatcha American
University ce fa" Mimi dake tsaye gefen Khalil ta kallesa a hankali tace "Yayanmu
who is she?" Bai ce mata komai ba yana bin sisters din nasa da kallo ya nuna masu
kofa yace "Ku fita" Farhana ta kyabe baki haka ma Hanan duk suka juya, Noor ma tayi
ficewarta, Mimi ta dinga kallon Nihad dake ta hawaye, Ita ma ta fita daga parlon,
Mami dai mutuwar zaune tayi a inda take. Daga karshe ta mike ta shiga dakinta ta
zauna side din gado duk jikinta a sanyaye, a ina Khalil ya samo yarinyar nan har
zai shigo da ita gidan nan? Bilkisu ta fito daga bandaki tana kallon Mami ganin
yanayinta tace "Mami are you okay?" Mami tayi karfin halin cewa "Sure, ki tafi idan
ina bukatarki zan kira ki Bilkisu" Tace "Toh Mami" Daga haka ta fita daga dakin,
Har sannan Khalil na tsaye ya rasa abun yi, Nihad dai ta hade kai da gwiwa tana
shesshekar kuka, Bayan Bilkisu ta fita ya juya ya tafi dakin Maminsa, yana shigowa
dakin ya kulle Mami ta mike tana kallonsa cike da tuhuma tace "Khalil wacece warcan
yarinyar ka kawo mana gidan nan? Who is she? Menene alaqarku?" Yayi gathering
courage yace "Mami calm down pls, yarinyar mai gidan da nace maki nakan zauna
wajensa a kano ce, kuma ai na gaya maki dalilin da ya sa muka taho tare, Banda
wannan babu wani dalilin Mami" Mami tace "Toh zan tura maka kudin jirgi ka siya
mata ticket ta koma, ai ta gama abinda take ko?" Ya rasa abinda xai ce, Mami ta
hade rai tace "Ko baka ji abinda nace bane?" Yayi kasa da murya yace "Mami bata
gama ba, bata samu amsan admission letter din ba ma" Mami tace "Toh me kake nufi?
Ka gaya min me kake nufi Khalil?" Ya marairaice yace "Mami karki manta gidan
babanta fa nake all this while, bai san ni ba ya yarda da ni, yayi accomodating
dina na zauna cikinsu for almost 10 months now" Mami tace "Yanxu ya kake son ayi
khalil? Me kake son in fada a wannan issue din? Sai kace baka san mutanen gidan nan
ba ko mance halinsu ne? wait first... Wai ma ita ce a video din nan ko ba ita
bace?" Ya sauke idonsa kasa bai iya yace komai ba, Mami tayi masa tsawa tace "Baka
ji na ne?" Cike da karfin hali yace "Ita ce" Mami tace "Nawa ne kudin jirgin, zan
tura maka yanzu" Yana girgiza kai hankali tashe yace "Mami mun yi magana da
mahaifinta kan cewa ta zauna nan gunki har ta karbi admission letter din tunda bai
fito ba, Mami we can't repay him this way, he is one of the nicest person i have
met in life, kawai ka haifi yaro ne baka haifi halinsa ba, but her mother and
father are down to earth, sun min abinda baxan mance su a rayuwa ba, sannan Mami
duk yaran gidan mahaddatan qur'ani ne, kawai dai ita...." Sai kuma ya kasa ci gaba
don ya rasa me xai ce, Mami ta fashe da kuka tace "Magana kake son ja min yanzu
fisabilillah Khalil? A ina kake son in ajiyeta har ta zauna a gidan nan bayan kana
gani duk yan matan sun shaida ita ce a videon nan kuma sun je su idar, sannan har
shi Abbanku sae da ya tofa nasa a lokacin da ya ga video din nan kwanaki, he was so
disappointed yayi ta addu'an Allah ya shirya mana zuri'a, sai kawai yau a ganta a
gidan nan ba kuma kowa ya kawota ba kai?? Kai da kake da ta6o ta ko ina a gidan nan
shine zaka kara shafa ma kanka kashin kaji? Check this out khalil, yaushe har Abban
naka ya bukaci ka dawo da har zaka dawo tare da wannan issue din? Kayi min gata
kayi ma kanka gata ka fitar da ita daga gidan nan kafin wani ya kara noticing dinta
bayan kanninka, Plss take her out of this house Khalil"


Masu jira ina turawa su yi fowarding a dinga yi ana tunawa da hakki, ku kuma masu
karantawa a bati amma fa a duniya yake bati, duk na gaisheku kyauta ya damuna??
Masu posting on Facebook, Hassan Basiru majia, Aminu Arthur and the rest, Hmm an
dai ce prevention is better than cure, i warned first.

Nihaad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence via👇🏻

07087865788......
*Wato duk me son sanin wani turare Nihaad ke sakawa da ke sa Khalil jiyo kamshinta
da ta gifta waje upon the hatred ya biyoni pc don abun sirri ne, nima shi nake sa
wa Barrister ke jiyo kamshina tun daga gate, joke apart..., kuma saboda wannan
kamshin ya min alkawarin daga ni ba kari* 🤓🥰


_SCENTMANIA_💯


38

Khalil bai kuma ce ma Mami komai ba sai kallonta kawai yake lokaci daya duk jikinsa
yayi sanyi, juyawa Mami tayi ta fice daga dakin ta zauna second parlonta, a hankali
Khalil ya zauna kan kujeran dake dakin yana jin kansa na mugun sara masa, gaba daya
he is confuse, dafe kansa yayi thinking of where to start from, where will he begin
now? Damuwar Mami ya ninka wanda shi ya ji ya shiga a lkcn, daga karshe taji ta
kasa zaman ɓangaren nata, she just can't imagine Khalil ya sake barin gida for the
second time saboda wannan issue din, tafi kowa sanin halin mahaifinsa, this time
around also he won't take it likely with him, tashi tayi tana jin wani sabon
tashin hankali ta fita daga parlon, Nihad na nan zaune yanda take a first parlor
din, Mami bata yarda ta kalleta ba amma jin yanda take kuka sai ta kasa fita daga
parlon duk da ta bude kofa, kulle kofar tayi gently ta juya ta kalleta, sai kuma ta
nufeta walking slowly tace "Kina ji na, ki daina wannan kukan ya isa haka, ga
breakfast dinki ki tashi kiyi" Nihad bata iya ta ce mata komai sai kuka take kamar
ranta zai fita, sai a yanzu maganganun Aunty Jamila ke dawo mata and it seems this
is just the beginning of what she's talking about.... Mami tayi karfin halin cewa
"Taso muje can parlon ki karya, kuma nace ki daina wannan kukan haka nan" Daga haka
Mami ta daukar mata abubuwan karin ta kai other parlor dinta ta ajiye, bayan ta
dawo parlon tana kallon Nihad tace "Baxa ki bar kukan nan haka ba? Taso mu je can
parlon" Sai a sannan Nihad ta mike da kyar, har sannan kuma ta kasa daina kukan da
take, Mami ta rike hannunta har zuwa daya parlon ta zaunar da ita tace "Eat now"
Zaunawa kawai Nihad tayi, her heart is so heavy, and she is now beginning to feel
useless, juyawa Mami tayi ta fita daga parlon, Visitor room dake bangaren nata ta
shiga kawai ta zauna cike da damuwa. Khalil ya mike daga karshe jin kukan da Nihad
take ya fito parlon don Mami a bude ta bar kofar bedroom din nata da ta fita,
Zaunawa yayi kan kujeran dake kusa da inda take zaune, he is speechless at first,
after few seconds ya kalleta, a hankali yace "It's okay, and...." Sai kuma yayi
shiru, Can yace "Kiyi hakuri" Ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, yace "Baki ji
me nace ba" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login