Showing 135001 words to 138000 words out of 268471 words
jima ba yayi ma Aunty Maryam sallama kan zai je gidansu
Nadeeyah, yana sauka parlor ya ga Nihad a parlon da mai aikin Aunty Maryam dake ta
bata labari, ita dai tayi tagumi tana kallonta don ta gaji da surutunta gashi ko
gane labarin bata yi, tun suna girki a kitchen take bata wannan boring labarin,
wannan yasa ta tuna nasu mai aikin a can gida, warce ko magana bata son ya hadasu
da ita ba kuma ta zama inda take saboda tana ganin ta fi karfin hakan kamar yanda
Umma ta ke yawan sanar mata, and for the first time Nihad felt bad at the way she
treated Hafsah back then, yau dai ga ta ita ma a gidan mutane ba gidansu ba tana
cin arziki.... Khalil ya sauko downstairs yana danna wayarsa, yayi dialing number
Usman, yana fara ring Usman ya daga, ya nufeta ya mika mata wayar, tuni Murja ta
gaishesa ta bar parlon da sauri, Nihad ta amshi wayar ba tare da ta kallesa ba tana
kallon screen din amma bata gane number waye ba, ta kai kunne, jin muryarsa a
hankali tace "Ya Usman" Yace "Ya kike Nihad?" Tace "Lafiya lau, ina yini" yace
"Alhamdulillah, hope you are doing fine, babu matsala dai ko?" Ta sunkuyar da kai
cikin sanyin murya tace "Eh" yace "Ohk are you still using ur account?" Tace "Bani
da atm card ne" yace "Toh ya kaiki banki ki amsa wani" Tace "Toh" Yace "Xan maki
transfer a ciki yanzu" a sanyaye tace "To yaya Nagode" Katse wayar yayi, hawaye ya
cika idonta ta rufe fuskarta jikin kujera hawayen na zubo mata, bata son taji tana
jin haushinsu a rai sbda Umma because she love all of them, basu ta6a nuna mata
ubansu ne kawai daya ba, shi dai Khalil na tsaye don bata basa wayarsa ba, bayan
few minutes ta dago tana goge idonta ta mika masa wayar ba tare da ta kallesa ba,
kallonta yake, zata ajiye masa kan kujera ganin yaki amsa yace "Kee" Sai a sannan
ta kallesa babu yabo babu fallasa, yace "Da xan baki wayar saman kujera na ajiye
maki?" Ita dai bata ce masa komai ba, ya amshi wayar ta mike ta bar wajen, ya bi ta
da kallo har ta bace sannan ya fita daga parlon, washegari kuma ya bar Nigeria for
Zanzibar in the morning. Ranan Talata Mami ta kira Aunty Maryam, bayan sun gaisa
Mami tace "Maryam bakuwar nan ta tafi kuwa?" Aunty Maryam tace "Ehh ta tafi jiya"
Mami tace "Toh maa sha Allah, banda dai yace a gidansu ya zauna ai yarinyar nan bai
kamata a gansu tare ba balle har ya kawota nan gidan" Aunty Maryam dake sauraronta
tace
"Saboda me Mami?" Mami tace "Kika ce saboda me?" Aunty Maryam tace "Au... Toh
Allah dai ya kyauta, Allah ya tsare mana zuri'a" Mami tace "Ameen" Aunty Maryam
tace "Ai ko yan gidansu suna ta godiya" Mami tace "Allah sarki, yanzu hostel din
zasu kama mata ta zauna kenan?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba" Mami tace
"Toh idan ba nan din ba suna da yan uwa a Abuja ne? In basu da kowa ai sai dai
hostel din dama" Aunty Maryam tace "Haka ne" sallama Mami tayi ma Aunty Maryam ta
katse wayar, Aunty Maryam ta fara tunanin ta ina za a fara convincing Mami?? Tun
bayan tafiyar Khalil Zanzibar duk sanda Mami taje gidan Aunty Maryam a daki Aunty
Maryam ke sa Nihad ta zauna har sai Mami ta bar gidan, idan kuma ita ke son xuwa
gidan yayartata ita kadai take xuwa da Mus'ab ta bar Nihad da mai aikinta a gida,
unlike before da har da mai aikinta take zuwa gidan, a cikin wannan kwanakin kuma
mijinta ya sanar mata nan da kwana biyar xa su taho kasar da yake, ta rasa ta inda
xata billo ma yar uwarta a kan Nihad. Ranan friday ta shirya taje can gidan, bayan
sun gaisa da Mami a bedroom dinta, it took her like five minutes kafin ta samu
kwarin gwiwan yi ma yayartata magana, Mami tace "Wani magana kuma ke tafe da ke? To
Allah ya sa lafiya, ina jin ki" Aunty Maryam tace "Mami dama iyayen yarinyar nan ne
suka kira jiya, suna neman alfarman ta zauna wajenmu don basu son xamanta a hostel,
and i think lectures will be commencing in 2 weeks time" Mami dai kallon Aunty
Maryam kawai take, Aunty Maryam tace "Toh ni kuma gashi nan da kwana biyar xa mu yi
tafiya" Mami tace "Ikon Allah, to Maryam ke ko da ba tafiya xa kiyi ba ina ke ina
rike yarinyar nan dama? Kuma ma da suka gaya maki haka ai sai kice barin kasar ma
xa ki yi, sannan ni kuma da kika zo nan kika gaya min me kike son ince maki? Meye
nawa a ciki?" Aunty Maryam tace "Amma Mami ke kam ba me mance alkhairi bace, bansan
ki da manta alkhairi ba komin kankantarsa, ko albarkacin xama da suka yarda Khalil
yayi a gidansu har na shekara daya ai bakya ce haka ba" Mami tace "Yanzu ya kike
son ayi Maryam, ni dai kinsan baxai ta6a yiwuwa ince yarinyar nan ta zo gidan nan
ta zauna ba, tsangwama da hantaran yan gidan ma kadai ya isheta balle aje ga shi
matsalar da Khalil din xai shiga in har Abbansa ya samu labarin shi ya kawota gidan
nan, a ina ya santa da har xai kawota gidansa, ku na lura yin abu ku ke kanku tsaye
duk wani abun magana bakwa gudunsa, ke kinga da sararin zamanta nan gidan, kwana
daya kadai da tayi kina ganin abinda ya faru" Aunty Maryam tace "Ni wallahi idan
kina nuna shakkan matsiyatan gidan nan a fili abun kona min rai yake yaya, ita
tsinanniyar Hasanar kike tsoro ko kuma Aminar? Haba Mami ko sau daya ke baxa ki
kwatar ma kanki yanci ba, ke kenan baki son fitina ke kenan gudun abun magana, A
haka rayuwar xai ci gaba? Yo Abun magana na nawa? Dubi tuggun da suka hada ma danki
suka sa ya bar gidan nan kina ji kina gani baki iya buda baki kin tsaya kinyi
defending dinsa ba shi da gidan ubansa, nima kika hanani magana a sannan, wannan
wace irin rayuwace? Toh wallahi mu ba butulu bane, kuma ba mu mance alkhairi komin
kankantarsa, in sha Allahu yarinyar nan bata da wajen zama tayi karatunta da ya
wuce nan gidan, kuma wajenki tunda har iyayenta suka nuna mu ma sun yarda damu,
sannan da iyayen nata basu rike shi khalil din ba Allah kadai yasan depression din
da xai fada a lokacin, kana ji kana gani a kwace duk wani abu naka da ka mallaka, a
amshe takardunka akan laifin da baka aikata ba, a toshe duk wani hanyar samun
kudinka, sannan ace ka bar gidanku ba a son ganinka, infact garin ma gaba daya kada
a samu information din kana ciki, ka tafi duk inda xaka tafi, me kike tunanin zai
samu mutumin da aka ma hakan idan bai fada hannun na gari ba? Ni nasan zamansa
gidansu really contributed wajen rage masa damuwarsa banda haka da baki gansa a
yanda kika gansa ba yanzu, ai Allah ya tsine ma Hasana da Amina, ya walakanta su
dai dai gwargwado, wato tunda ta kashe aurenta yau shekara kusan ashirin to bari
naki ma ta kashe maki, ga agololinta ta cika gida da su suna ta baza mulki son
ransu, wani abun ma sae ayi masu ba ayi ma naki yaran ba, to ai ni da xata burgeni
ta auri Janar din kawai mana mu ga, for 20 good years kina daukan cin kashin matan
nan kin kasa ta6uka komai, don dai kawai ni xamana ba steady bane a Nigeria amma
wani abun da ba ayi ba wallahi, to gaskiya it's high time kema ki kwaci kanki ki
daina shirun nan Mami, yarinya kuma duk shegiyar da tace Khalil ne ya kawota gidan
nan kice karya take, bai santa ba bai ma ta6a ganinta ba, babu sa hannunsa a
zuwanta gidan, dama ai kowa ya sanki da taimako to wannan ma duk cikin taimakon da
kika saba yi ne, amma babu ta inda khalil ya santa, kawai haka za ki ce masu,
sannan hantara da tsangwama da kika ce baxa ma su ganta ba balle su yi mata, dakin
baki na nan bangaren xata zauna, da safe ta tashi ta tafi makarantar ta, ta dawo da
yamma to a ina za su ganta? Duk sanda na shigo Nigeria yin wani abu ta dawo wajena
har sanda xan koma, ba shikenan ba?" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take ta
kasa cewa komai, sallama aka yi a parlon duk suka daga kai.
*Not too okay, ayi manage pls*
wa enda suka yi payment ban masu reply ba har yanzu su yi hakuri xan yi kokari inyi
pls, those that checked on me i do really appreciate, Allah ya bar zumunci.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via
07087865788
42
*This pages is dedicated to Safiyya Usuman uwar Sultan, sauran kuma duk su ci kansu
kandas ba mai ba yaji* 🤓
Umma tace "Ayya inna ai suna can garinsu da ita" a tsorace Inna tace "Garinsu? Ina
ne garin nasu? Buzu ne fa, ba shi da wani gari da ya wuce Nijar, Nijar din ya
kinkimi jikata ya kai kuna gani baku hanasa ba? ta ina zata fara da zafin saharar
su, ga shi ance mana ana ta juye juyen mulki a can yau kwana da kwanaki, ni da
Abubakar muna ta jimami" Umma tace "Aa Inna, garin zaria ya tafi da ita" Inna ta
saki baki, can tace "Kan uba, ku ka bar sa ya tafi da ita wannan garin, ai duk É—an
kano yafi karfin zama a can, Sannan da xai kai ta can din wani shegen ya bi su a
cikinku??" Umma tace "Haba Inna, ai sun je sun dawo ya fi a kirga, Nihad fa ta sake
fiye da yanda kike tunani Inna" Inna tace "Kai nima dai wallahi da na tsaya nake
biye maki kamar wata er wiwi, maganina ma kenan, matsa ki ban waje wajen Ibrahim na
zo ba wajenki ba, kai kuma Ibrahim wajenka na zo ba wajen Sumayya ba" Abba yace
"Toh ya kike son ince Hajiya? Dama ana zuwa cigiyar wanda kulawarsa da komai nasa
ya fita daga hannun iyayensa? Ai ni tuni na mikata garesa, alaqarsa da ita ya fi
namu yanzu, don haka duk inda ma ya kai ta dai dai ne, ba ruwana, ba ruwanki, ba
ruwan kowa" Inna da ta saki baki tana kallonsa tace "Yau ba lafiya, kace ba ruwanka
Ibrahim?" Yace "Toh hanasa tafiya da ita xan yi?" Umma na murmushi tace "Banda
abunki Inna mata da mijinta ki zo cigiyarta a gidansu, ita da gidan nan kuma ai sai
dai ta kawo mana ziyara, idan aka ganta gidan nan yanzu ai ba lafiya kenan, kuma
wallahi ko sati ba ayi ba sun zo gidan nan da shi sun mana sallama kafin su tafi
Zarian wai garin mamarsa ce, kawai dai ba ku da rabon ganawa ne, amma yace ba
jimawa xa su yi ba za su dawo, suna dawowa kuma da kaina xan je can gidan in dauke
ki in kaiki gidan nasu" Inna tace "Toh wai ni shikenan nuna masa ku ka yi bani da
matsayi ne da tun da aka aura masa ita daga shi har itan babu wanda ya taka yaje
inda nake yace min ci kanki? duk da dai naje Bauchi kwanan nan na dawo" Umma tace
"Au ashe dai kinyi tafiyar dai, to ki dai yi hakuri Inna, sun je ne baki nan, ki
tambayi yan gidan kilan basu gaya maki bane da kika dawo" Inna tace "Kai Ibrahim
fito za mu yi magana" Daga haka ta juya ta nufi kofa tace "Don ban ga xan iya
magana gaban kwaɓeɓiyar nan ba" Abba ya mike ya bi bayanta suka fita, Umma ta bi ta
da harara, can ta ja tsaki tace "A haka dai"
Ranan alhamis Aunty Maryam suka fara shirye shiryen barin Nigeria tare da mai
aikinta da yaranta mata biyu da ke wani boarding school a nan Abuja, duk sai jikin
Nihad yayi sanyi, the present of Aunty Maryam use to make her feel strong, it's
making her move on with life, tana kara samun kwarin gwiwa har ta mance duk wata
damuwar da take ciki and now she is leaving her, Aunty Maryam na lura da sanyin da
Nihad tayi, and she felt really sorry for her, she wish she could do something
about it, she wish xata iya tafiya da ita inda xa ta, daren Thursday Aunty Maryam
ta idar da sallahn da take a sama ta sauko kasa ta karasa sauran kintse kintsen da
bata yi ba a gidan don ranan Asabar za su tafi, har xata koma sama sai kuma ta tafi
ta bude dakin Nihad duk da taga jiya bata yi tashin daren ba da ta leka ta, zaune
ta ganta kan darduma ta hade kai da gwiwa, ta dago kai jin an bude kofar dakin,
Aunty Maryam ta shigo dakin ganin idonta tace "Kukan me kuma kike Nihad?" Wasu
sabbin hawayen suka ciko idonta ta kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Talk to me,
why are you crying?" cikin rawar murya Nihad tace "Aunty you are leaving me... idan
kika tafi kika bar ni i don't have anybody here" tana fadin haka ta fashe da kuka,
Lokaci daya jikin Aunty Maryam yayi sanyi ta dagota ta zaunar da ita gefen gado
tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ke da zaki fara makaranta Nihad, sannan
wajen yayata fa za ki zauna, she is also nice, you will like her so much, and
Khalil is also there for you always" kuka kawai Nihad take don tasan idan Aunty
Maryam ta tafi shikenan she might go back to her former self, there will be no one
to encourage her anymore, har ranta bata son gidansu Khalil, she don't think she
can cope staying there, ganin yanda take kuka Aunty Maryam ta jawota jikinta cike
da tausayinta tace "Kiyi hakuri Nihad, bana son kina wannan kukan, ni ma ina son mu
zauna dake kawai bani da yanda xan yi ne, but even with my absence baxa kiyi
lacking komai ba" Kai kawai Nihad ta daga mata hawaye na sauka idonta, Aunty Maryam
tace "Je ki wanke fuskarki ki zo ki kwanta" Tashi tayi a hankali ta tafi bandaki ta
wanke fuskarta ta fito ta hau saman gadon amma wasu hawayen ne ke zuba idonta,
mikewa Aunty Maryam tayi jikinta a sanyaye ta fita daga dakin, ita kanta tasan in
dai ba khalil na gidan ba zaman gidan ba lallai yayi ma Nihad sauki ba, duk excuses
da Mami ta kawo a kan dalilin da baxata riketa ba gaskiya ne, amma saboda babu wani
option yasa Aunty Maryam duk tayi shunning excuses din. Washegari friday tana
dakinta tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga bayan sun gaisa tace
"Baxa ka dawo weekend ba?" Yace "Ina airport yanzu haka, in sha Allah yau xan dawo"
Aunty Maryam tace "Toh kana sauka ka daure ka fara biyowa ta nan gidana" Yace "Ohk,
hope all is well?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Yaushe ne tafiyar Aunty?" Tace "Gobe
in sha Allah" Yace "Ohk, sai na dawo in sha Allah" Sallama suka yi ta katse wayar,
gaba daya ta kasa sauka gun Nihad don har ranta bata son ganin kukanta. Wajen karfe
biyu zeenah ta shigo wajenta a daki tace "Ummi why is ur visitor crying since
morning?" Aunty Maryam ta kalleta tace "Go and mind ur business please dear" Ta
zaro ido tace "No i was only trying to show concern" Aunty Maryam tace "Je ki kira
min ita" juyawa tayi ta fita daga dakin, Bayan wani lokaci sai ga Nihad ta shigo
parlon Aunty Maryam tana tafiya a sanyaye, bata yarda sun hada ido ba ta zauna
kasan Carpet, Aunty Maryam ta dinga kallon idanuwanta da suka kumbura, can ta sauke
ajiyar zuciya tayi kasa da murya tace "Wajen yayata ne baki son zama Nihad?"
Girgiza mata kai kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Toh ki gaya
min inda kike son zama" cikin sanyin murya Nihad na wasa da gefen gyalen jikinta
tace "Bani da inda zan zauna" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonta cike da
tausayinta, irin wannan yarinya karama haka ace wai an koreta daga gida, why? to
yanxu da ba don Khalil din ya taho da ita ba da ya zata yi kenan, sai da ta shiga
duniya kenan tunda gashi wai dangin mamarta basa nan, what a cruel world we are in,
how comfortable is this her step mum now da tasa aka kori yar teenager haka daga
gida saboda selfish interest dinta, lallai duniya abun tsoro, bayan few seconds
Aunty Maryam tace "Je ki zuba abinci ki ci" Tashi Nihad tayi ta nufi kofa ta fita
daga parlon. Karfe hudu saura Khalil ya shigo gidan ya tarar da Aunty Maryam dake
parlonta a zaune, tayi welcoming dinsa ya zauna sannan ya gaisheta tace "Ya hanya?"
Yace "Alhamdulillah" Kallonta kawai yake yana jiran ya ji kiran da take masa, Ta
sauke ajiyar zuciya tace "Kjay, ina tunanin halin da Nihad xata shiga idan na tafi
na bar ta a kasar nan, she's been crying since 2 days ago, i feel really sorry for,
she is too young to be passing through all this, tana bukatar tausayawa da soyayya
irin ta uwa, ban san yanda xan yi ba...." Kallonta kawai khalil yake, can a hankali
yace "Aunty ba wajen Mami za ki bar ta ba?" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Kai
ma kasan mun banbanta da Mami ta ɓangarori daban-daban, yanda na jawota jiki har ta
sake ta buda min cikinta Mami baxata yi haka ba, sanyinta baxai bari tayi hakan ba,
ko me xa ayi mata a gidan kuma nasan iyaka Mami tace tayi hakuri, toh da wanda ya
dameta zata ji ko da na yan gidanku KJay?" Khalil dake ta sauraronta yace "Toh meye
shawararki Aunty?" Aunty Maryam tace "I am thinking of telling Abu Zeenah sai mu
tafi tare da ita ƙasar da za mu" Khalil was speechless at first, can yayi karfin
halin cewa "Aunty karatun nata fa?" Aunty Maryam tace "Sai a samar mata a can ta
fara" Yayi kasa da murya yace "But i have paid all the fees, kuma kinga ai na kashe
kudi da yawa, ni kuma baxan wani iya bin processes din refund ba" Aunty Maryam tayi
shiru tana kallonsa, ya kwantar da murya yace "Kar ki damu Aunty in sha Allah she
won't be uncomfortable as you are thinking, beside Mimi na gidan, nasan baxata bari
ana ci mata fuska ba, sannan nima next week zan gama abinda nake a can in dawo
Nigeria gaba daya" Aunty Maryam still ta kasa cewa komai but deep down her tausayin
Nihad kawai take ji kawai tana jin da kawai ya bari sun tafi da ita, shi dai
kallonta kawai yake hoping she is convinced, daga karshe tace "Shikenan, Allah yayi
mana me kyau, Allah ya bata ikon kwantar da hankalinta