Showing 207001 words to 210000 words out of 268471 words

Chapter 70 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

shiga, Nihad kadai ce zaune ga abinci a gabanta amma bata taɓa ba, daga sama har
kasa take kallonsa don fararen kaya ne jikinsa sae zuba kamshi yake, sai kuma ta
dauke kai, ya karasa cikin dakin yace "Why are you not eating" Ta hade rai bata dai
ce masa komai ba, ya durkusa gabanta ya bude abincin dake tiriri, plate ya dauka ya
zuba mata abincin with enough meat, ya dau cokali ya deba ya fara kai bakinsa ya ci
kadan sannan ya kai mata baki, dai dai nan Mami ta shigo parlon, makalewa yayi
wajen gashi ya kasa sauke spoon din daga kusa da bakinsa, ita kanta Nihad ji tayi
kamar ta nutse, ta kasa dagowa balle ta kalli Mami, wayarsa dake aljihu ya fara
ring ya ciro da sauri, yaga Abbansa ne ke kiransa, ya ajiye cokalin ya daga ya kai
kunne, Janar na gama fadin abinda zai fada ya katse wayarsa, Khalil ya juya a
hankali yana satan kallon Mami ya ga ankon lafiyayyen lace na su na iyaye take
kirgawa zata fita da shi, mikewa yayi kansa a kasa ya fita daga parlon, bangaren
Abbansa ya tafi, ya zauna saman Kujera yana kallon Janar yace "Good evening sir"
Janar yace "So now, how did my 800M vanish Ibrahim?" Khalil yace "I don't know"
Janar yace "U don't know? Kar ka manta u asked for 300M 2 days before and i refused
giving you, cause i am still yet to see the outcome of wa enda na baka a baya,
bayan kwana biyu kuma my 800M went missing, kai ka shigo min da shi gidan nan ba
wani ba, kai kadai kasan da kudin, ko uwarka da Amina basu sani ba, only you have
the access to my safe in this house, ba kuma wanda ke shigar min that particular
room banda kai, in kudi na baka for joint business sai dai kawai ka salwantar min
da kudadena, anyi hakan yafi a kirga, in dai zan dauraka akan Business tohh that
business will neva go smoothly...." Khalil yayi shiru yana kallonsa, can a hankali
yace "But it's always not my fault, i do use to try my best but ban san meke faruwa
ba" Janar yace "Shi Aliyu kai biyu garesa idan na daurasa kan kasuwancina
kasuwancin ke tafiya smoothly ban taɓa daurasa kan abu nayi asaran ko naira biyar
ba ko in ga ba dai dai ba, kai ko in sha Allahu sai ka salwantar min da kudade, and
now u want me to believe ba kai ka dau min kudina ba?" Khalil bai kuma ce masa
komai ba, Janar yace "Toh me kayi da 800M wanda u still have to end up driving daga
karshe?" Da sauri Khalil yace "Ni ban san komai kan kudinka ba, and ni ba don na
rasa kudi naje driving ba, i can fend for my self for years to come ko da ban yi
driving ba...." Janar dake kallonsa keenly yace "With whose money zaka yi fending
for ur self bayan ur account was frozen then?" Khalil yace "Mami never left me like
that, haka Aunties dina...." Janar ya tabe baki yace "Har gobe bazan daina cewa kai
ka dau min kudina ba...." Khalil dai kallonsa kawai yake, can yace "Toh shikenan,
ina fatan wataran gaskiya ta bayyana ka gane ban dau maka kudinka ba" Janar yace "I
am sending u 20M now, kudin lefen both matan naka..." Khalil na kallonsa yace
"Allah ya kara budi" Janar yace "Are they going to be staying together or
seperately?" Khalil ya sauke kansa yace "Duk yanda Mami ta ce" Janar yace "Oh ohk,
Mamin zata zauna maka da su kenan?" Ya girgiza kai yace "Kawai shawara zan yi da
ita" Janar yace "It's left to you... Zaka iya tafiya" Khalil yace "Nagode" Daga
haka ya mike ya fita daga parlon, direct dakinsa ya koma, yana zaune gefen gado
with different thought running his mind sai ga Alert din 20M daga Janar, shi bai ma
san yaushe ne bikin ba kuma bai san wanda zai tambaya da bazai yi misperceiving
dinsa ba, tashi yayi daga karshe ya koma bangaren Mami, ita kadai ya tarar a
parlonta tana waya da Aunty Maryam da ta tafi gun dangin mijinta dazu da yamma,
yana ta zaune har ta gama wayar ta ajiye, kallonta kawai yake ganin bata ko kalli
inda yake ba, can ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Mami Abba ya saka min 10M
yanzu na lefen Nadeeyah, toh ban san ko basu za ayi ba ko a nan za a hada kayan"
Mami tace "Baka da number Nadeeyan ne yanzu?" Yayi shiru yana kallonta, can ya
girgiza kai a hankali yace "No... kawai shawara nake yi da ke ne kafin in mata
magana" Mami tace "Toh kayi magana da ita ni ba maganar da zaka min" Bai kuma ce
mata komai ba, ta dau wayarta da ya fara ring ta daga ta kai kunne, hakan ya sa ya
mike kawai ya fita daga parlon, dakin da Nihad ke zama a gidan ya nufa ya bude
dakin yaga ba kowa ciki, yana ta tsaye yana imagining inda take, to ko tana bedroom
din Mami ne, can dai ya tafi bangaren Mimi to ask her yaushe ne bikin, Knocking
yayi kafin ya bude kofar yana kallon cikin dakin, Bai ga kowa dakin ba amma ga
trolley din kayan Nihad which means she is here, dai dai nan Nihad ta fito daga
bandaki daure da towel tayi wanka, ya karasa shigowa dakin ya kulle kofar, lokaci
daya ta hade rai zata dau Hijab dinta yayi saurin daukewa a wajen ya jawota jikinsa
murya can kasa yace "Kin ci abincin kuwa?" Taki ce masa komai fuskarta a daure, a
hankali yace "Ko an maki wani abu ne?" A takaice tace "Ina ka je da farin kaya
dazu?" A tsakiyar kansa yaji tambayar da ta jefo masa kamar dai ba ita ba, he
wasn't expecting such question from her, ya ɗan buda ido yace "Ba inda naje, i...
I... I met with a long time friend a cikin anguwan nan, ance maki naje wani waje
ne?" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace "Ban yarda ba" Ya rungumeta so that she
won't see the smile on his face, yana murmushi sosai yace "Toh ina zan je bayan
kina cikin gidan nan?" Muryarta na rawa tace "Wajen budurwarka kaje ai na sani" Ya
dago kanta ya wara ido yace "Ina da wata budurwar bayan matar da aka aura min
dama??" Bai jira tace komai ba ya fara kissing dinta passionately, duk ta rikice
tana son kwace kanta ya ki saketa sai ma upgrading da yayi daga kiss din, muryarta
na rawa tace "Don girman Allah kayi hakuri kar Mimi ta shigo, yanzu zaka ga ta
shigo...." kamar me rada yace "Toh za ki bi ni dakina?" Ta marairaice tace "Ai
baxan iya ba, za a ganni" Bai kuma sauraronta ba ya ci gaba da abinda yake mata,
tun tana ce masa kar Mimi ta shigo har dai ita ma ta dauke light ta sakar masa
jiki. Daga ita har shi suka mance a ina ma suke.... kasa hada ido tayi da shi daga
karshe ta rufe fuskarta jikinsa cike da jin kunyarsa, murya can kasa yana rungume
da ita yace "U are the best thing that have ever happened to me, and i now
appreciate the reason i left home, i appreciate my pass...." Ita dai tayi lamo
jikinsa tana jin kamar bacci zai dauketa, Murda kofar dakin aka yi Nihad ta mike
zaune da sauri tana zaro ido, wani ajiyar xuciya ta sauke ba tare da tasan tayi
hakan ba, ashe yasan
ya saka ma kofar makulli shi yasa hankalinsa kwance yayi abinda yake so, ta
marairaice zata sauka daga kan gadon ya jawota yace "She is gone, plss tell me the
name of ur perfume" shiru tayi ta kasa bari su hada ido, ya dago kanta yana kallon
kwayar idonta murya can kasa yace "Tell me" a hankali tace "I will..." Tana fadin
haka ta jawo towel dinta ta sauka daga saman gadon ya bi ta da kallo babu ko
kiftawa har ta shiga bandaki ya sauke wani ajiyar zuciya yana sauke numfashi a
hankali, bai kara minti uku ba a dakin shi ma ya fita ya tafi dakinsa da sauri...
Ko da Mimi ta dawo dakin Nihad na kwance ta rufe har kanta da duvet, gani take
kamar Mimi zata gane wani abu, Mimi dai bata ce mata komai ba don dakin banda
kamshin turaren yayan nata babu abinda yake, ta koma daya side din gadon ganin
agogonsa a kasa ta dauka ta ajiye a hankali kan bedside drawer sannan tayi
Kwanciyarta ta kashe wutan dakin, Nihad ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya jin
bata mata magana ba, don da tayi ma bazata kulata ba she will pretend she is
sleeping. Washegari da safe Khalil ya shigo bangaren Mami don gaisheta, Bayan ya
gaida Mami ya kalli Aunty Maryam dake kallonsa, sunkuyar da kai yayi ya gaisheta
ita ma, ta taɓe baki ta mike tace "Mu koma dakin naka dama yanzu nake son in bi ka
can" Ya mike ya bi bayanta suka koma dakinsa, Ta zauna gefen gado tace "Kai yanzu
ka kyauta abinda kayi Khalil? Me zai kai ka kayi abu kanka tsaye?" Zai yi magana ta
dakatar da shi tace "Daga baya kenan Khalil, ba wani abinda zaka fada da zai yi
justifying foolishness dinka, ka riga dai kayi abun ka kai tsaye, ur father is
supporting you because he is a Man, kuma dama ku maza mentality dinku daya" A
hankali yace "Ku yi hakuri Aunty" Tace "Aa ni dama nayi, duk da yanda daga kai har
Nihad din kuka mayar da ni yar iska har nake hadata da wani saurayin su yi waya, to
laifi akan ku, don Allah ya gani ban sani ba" Khalil bai san sanda yayi murmushi
ba, Aunty Maryam ta jefa masa wani kallo, ya zauna gefenta a hankali yace "Wallahi
Aunty ban san ta yanda zan ce ma Mahaifinta a'a ba a sanda ya bani aurenta, kema
kinsan da nauyi, kuma kinga ai baxan ce zan kawosa gidanmu ba ga issue that is on
ground..." Aunty Maryam ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh Allah ya baku zaman
lafiya, Mami kuma sai kayi ta lallabata har ta hakura gaba daya, kasan fushin uwa
bala'i ne babba, don haka kayi ta bin ta har dai ta sauko, sannan kudin da Janar ya
tura maka na lefen Nadeeyah kawai ka tura masu su siya duk abinda suke so, yanzu
haka ake yi gaskiya" Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace "Aunty har da na
Nihad ya bada amma ban gaya ma Mami bane kawai" Aunty Maryam ta kallesa tace
"Nawa?" Yace "Ita ma 10M" Aunty Maryam tace "Maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai,
ita ma ka tura ma iyayenta su yi mata lefen, ba sai ka sanar ma Mami ba may be daga
baya zaka iya gaya mata, but for now don't say anything to her" Yace "Toh Aunty,
and Abba yayi min magana ko hadasu zan yi nace sai nayi shawara da Mami" Aunty
Maryam tace "Aa gaskiya baza ka hadasu ba, noo it's not even possible, ita Nihad ka
bar ta a gidanka, Nadeeyah kuma ka nemi gida ka kama mata kawai, bikin ma ai an
kara 2 weeks dazu Mami ke gaya min" Yace "Ohk i don't know about it" Aunty Maryam
tace "How will u know dama bayan wannan gurmin da ka hada" Murmushi kawai yayi,
Aunty Maryam ta mike tace "Bari in je, za mu fita ne da Mami yanzu" Yace "Toh Allah
ya tsare" Tace "Ameen, sai ka kira iyayen nata ka tura masu kudin yanzu" Yace "In
sha Allah" Bayan Aunty Maryam ta fita daga dakin Khalil yayi dialing number Aunty
Jamila, Aunty Jamila dake zaune parlon Umma tare da Mumy ta shigo yi ma Umma
sallama zata koma Jigawa, Inna ma zuwanta kenan ta zo duba Umma da er ayabarta
kwaya uku da lemu daya, Jamila ta ciro wayarta ganin Khalil ke kiranta ta daga hade
da sallama, bayan sun gaisa Khalil ya sanar mata dalilin kiran nasa, Aunty Jamila
ta buda ido speechless at first, sai kuma tayi saurin cewa "Ahhh to maa sha Allah,
maa sha Allah, Allah ya kara arziki, zan tura maka account din Mumy" Daga haka suka
yi sallama ta katse wayar ta kalli Mumy cike da mamaki tace "Aunty Khalil ne ya
kirani yanzu, wai Babansa ya bada miliyan goma a hada ma Nihad lefe, shine zai turo
mu hada a nan" Umma tayi kuri tana kallon Aunty Jamila babu ko kiftawa, dama tunda
suka shigo ko um bata cewa balle um um, duk ta zama wani iri kamar warce ta dade
tana jinya, kana ganinta kasan hankalinta baya tare da ita, tana cikin tsananin
damuwa, hatta Mumy har lokacin Abba bai kai ga sanar mata babu aure tsakaninsa da
Umma ba don ita ce da girki banda yau da zata ajiye Umma ta dauka, kuma yau din ma
sai dare yake da intention din sanar mata, Inna ta mike tana kallon Aunty Jamila
tace "Waye Khalil?" Aunty jamila na murmushi tace "Mijin Nihad, wai babansa ya bada
miliyan goma a hada mata lefe shine zai turo mana mu hada a nan" Inna ta fashe da
kuka ta koma ta zauna, sai kuma ta saki kabbara da karfi tace "Allah mun gode maka,
Allah mun gode maka" Mumy na kallon Aunty Jamila tace "Jamila maimakon su hada
kawai a can har sai an turo kudi nan, ina ga ba gwara kice kawai su yi a can
ba...." Inna ta saki baki tana kallonta, can a fusace tace "Ke dai har yau baki da
wayewa Maryam, ai yanzu iyayen mace ake ba kudi su hada mata kaya, salon a bar masu
miliyan goma su cuceta su ki siya mata abinda ya kamata saboda bakin ciki? Yo ko
wannan figaggiyar baƙar shegiyar ta isa ta raba kudin biyu ta boye rabi, wannan din
nan da suka ce uwarsu ce kawai daya da Janar din, su turo kawai nan duk za mu siya
mata kaya na gani na fada na kece raini, wanda babu wanda zai ce Ibrahim ne ya
haifeta, ai tunda Allah ya tsameta daga cikinmu ya mayar da ita cikin masu
fitinannen kudi ita ma shiga zata dinga yi kamar yar sarki, in sha Allahu kayan da
za mu siya mata sai ya girgiza su wllh, yanda babu wanda zai raina min jikata a
gidan, ana gama hada kayan kuma a hadani da dreba in kai har Abujan, nima zan kara
dubu goma ta akan kudin a hada da miliyan goman duk a mata siyayya, da kyar idan ba
sai mun siye kwari ba" Aunty jamila tace "Kwarai kuwa Inna, kaya sai wanda bamu
gani ba a kasuwa ne baza mu siya mata ba, in sha Allah zamu hada mata kaya na gani
na fada...." Aunty jamila na fadin haka ta tura ma Khalil account din Mumy, babu
bata lokaci kuwa ya sako masu 10M din, Umma dai ta zama er kallo a parlon sai bin
su kawai take da ido ba bakin magana, a zaune take amma dishi dishi take gani.....
Wajen karfe sha daya khalil ya koma bangaren Mami, he still wants to tell her he is
sorry, fushin nan da take da shi ya sa ya kasa samun nutsuwa, ita kadai ya samu
bedroom dinta ya duka kasa ta juya tana kallonsa tace "Lafiya??" Ya marairaice mata
yace "Don Allah Mami kiyi hakuri ki yafe min, wallahi bazan samu nutsuwa ba idan
kika ci gaba da fushi da ni" Mami tace "Inyi fushi da kai a saboda me, a'a ni ba
fushi nake da kai ba, abinda kake so ne fa kayi, don haka bani da wata matsala da
wannan, kawai dai abinda na sani gida da Maryam tace maka zaka raba masu babu
wannan zancen, ban amince da haka ba, daƙuna biyar ne a gidanka banda biyu da ke
downstairs, don haka babu wani gida da zaka kama, they will be staying in the same
house...." Khalil ya daga kai yana kallonta ya kasa cewa komai.




*Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*


Ur evidence via 07087865788
Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son
sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da
xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan
turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba.
Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu
xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da
hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls
guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda
hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls
guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din
da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman
in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800,
6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar
maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰


62

Nihad na zaune dakin Mimi bayan azahar tana danna sabuwar wayar da Khalil ya siya
mata, har ta kira Mumy da ya farooq da wayar don ya saka mata layi da credit a
ciki, Mimi ta shigo dakin rike da ankonsu ita da Hanan ta diresu gefen gado, laces
biyu ne sai super uku uku, Nihad dai sai kallon kayan take, Mimi tayi wani sigh
tace "Ankon mu ne wannan.... Idan an siyo wani zan cire maki naki, Suhaila ma ba a
kawo nata ba" Nihad tace "Ankon mene?" Mimi ta kalleta zata yi magana amma kamar
warce ta tuna wani abu sai tayi shiru tana kallon Nihad din, can ta juya kawai ta
harhada ankon ta saka a press dinta ta nufi kofa, Nihad ta bi ta da kallo har ta
fita, Nihad ta ajiye wayar hannunta tana sake maimaita kalmar ankon da Mimi tace
mata a zuciya, a hankali ta koma saman gadon ta kwanta. Khalil na zaune first
parlor din Mami tare da Aunty Maryam, Mami kuma tana other parlon din nata tare da
bakuwarta, Aunty Maryam tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace "Komai tace maka
kar ka mata musu kayi ta bin ta da toh, amma gaskiya baza ka hadasu gida daya ba"
Khalil dai yayi shiru bai ce komai ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login