Showing 252001 words to 255000 words out of 268471 words
don girman Allah ka fita" Yace "Ina za ku?" Ta
girgiza kai da sauri tace "Wallahi ban sani ba, Mami ce tace in shirya, don Allah
ka fita Mimi kar ta shigo yanzu" Ya nufota zata koma baya yayi saurin kamota ya
kwance towel din, ta wani hade rai tace "Ni bana son haka, this isn't proper plss,
dakin Mimi ne fa" Yace "Ohk, me kike ce ma Mami dazu?" Ta turo baki tace "Ni dai
nace ka fita don Allah" Yace "Kin yi alkawarin idan na fito za ki shigo dakina ki
gaya min?" Da sauri tace "Ehh" Yace "Ohk" light kiss yayi mata ya juya ya fita,
tana jin ya kulle kofar dakin alamar ya fita, ta ɗan leka cikin dakin taga Mimi
bata nan, ta sauke wani ajiyar zuciya ta fito, ko da Mimi ta dawo dakin ta sameta
tana shiryawa, Mimi ta shiga bandakin don yin wanka ita ma, Nihad na gama shiryawa
ta fito ta tafi bangaren Mami da sauri don bata manta abinda ta gaya mata jiya da
daddare ba.... Mami na dakinta tana shiryawa Khalil ya shigo parlon, Nihad dake
zaune parlor ta sunkuyar da kanta, yayi kasa da murya yace "Ni kika yi ma wayo ko?"
Boye fuskarta tayi taki ce masa komai, sai ga Mami ta fito rike da makullin motarta
yace "Mami zan fita sai na dawo" Mami tace "Alright, mu ma yanxu za mu fita" Yace
"Toh Allah ya kiyaye" Daga haka ya juya ya nufi kofa, Nihad ta bi sa da kallo, Mami
ta koma dakinta don dauko handbag dinta, Nihad ta mike da sauri ta bi bayansa a
second parlor ta gansa har ya bude kofar zai fita, a hankali tace "Ina za ka?" Ya
juya ya kalleta yace "Nima ban sani ba" Tayi shiru tana kallonsa daga sama har kasa
don ba karamin kyau kayan jikinsa suka yi masa ba, lokaci daya mood dinta ya canza,
yace "Ba dai ni kika yi ma wayo ba, zaki shigo hannu ai" Juyawa tayi ta bar wajen
da sauri yace "Wait..." Amma tuni har ta koma first parlor, ya shafa kansa yana
murmushi, sai kuma ya juya ya fita. Gidansu Nadeeyah ya tafi yana zaune compound
din gidan yana jiranta bayan ya kirata a waya, ba a dau lokaci ba sai gata ta fito,
ta ja kujera ta zauna tana kallonsa da murmushi fuskarta tace "Sannu Kjay" Yace
"Sannu kamar wani mara lafiya" Tace "Ohk, weldone KJay..." Yayi mata murmushi yace
"How are you doing" Tace "Alhamdulillah, how is ur wife?" Ya ɗan kalleta, amma sai
bai ce mata komai ba, tace "Naji Mum tana cewa za mu je can gidan ma Anjima" Yace
"Ohk Mum na ciki?" Tace "Yeah, but tana da bakuwa" Yace "Ohk, we will be going to
Yemen on Saturday with my uncle don Abba bashi da lokaci, shine na zo in gaya maki
ki gaya ma Mum don ta sanar masu kafin Saturday din" Nadeeyah dai tayi shiru tana
kallonsa, yace "Ya kika yi shiru Madam?" Ɗan murmushi tayi tace "Kasan a rayuwa
muna namu Allah na nasa ne ko?" Yace "Sure..." Tace "And kasan policy dina a baya
da nake yawan cewa i will never marry someone's else Husband, kuma idan baka manta
ba a lokacin muna Uk da kaje kara karatu ni kuma ina year 1 farkon haduwarmu kenan
nayi wani saurayi me mata da yaro daya da yake zama a Uk, na kuma so sa but na ki
aurensa saboda yana da mata, ka tuna ko?" Ya sauke idonsa bai dai ce komai ba don
truly tana yawan fadin haka a baya, har tsokanarsa ta sha yi kan cewar duk ranan da
zai mata kishiya sai dai fa ita ya saketa yayi aurensa, Jin yayi shiru Nadeeyah
tace "Kayi shiru" ya daga idanuwansa ya kalleta but still bai ce komai ba, murmushi
tayi tace "To be sincere Kjay, after i found out u are married na sanar ma da Mum
dita ni baxan iya aurenka ba na hakura, my Mum tried persuading me inyi hakuri kada
ince haka ko don zumuncin dake tsakaninta da Mami, Mami won't be happy idan nayi
hakan, Few months back ai kaga er uwar Mum dita ta zo daga yemen, she came because
of the issue saboda i was serious nace bazan aureka ba ni na hakura, idan ka lura
har wayarka ai bana dagawa a sannan cause har zuciyata nasan na hakura da kai, amma
Mum dita da sister dinta suka saka ni a gaba for almost a week ana abu daya, har
yau kuma Mami bata sani ba, almost all my maternal relatives sai da suka min magana
a kan issue din nan, and at last babu yanda zanyi haka na janye kudurina na cewa na
fasa auren, but still idan ka lura har yau ni da kai ba kamar yanda muke a da bane,
kuma kai ma ka sha fadan haka...." Yayi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Nadeeyah,
Allah ne ya tsara mana haka" Tayi murmushi tace "Haka ne, daga karshe ya kuma tsara
babu aure dama tsakanina da kai Kjay" Da mamaki yake kallonta, tace "Yeah, we were
not destined to live as husband and wife tun daga farko...." Yace "Why are you
saying this Nadeeyah?" Tace "I am saying this because Nihad is my second cousin,
kuma ni bazan iya auren mijin cousin dita ba duk da ba haramci a auren namu amma
bazan iya ba, Beside even if i should ignore the fact that Nihad is my Second
Cousin, in dai da mutunci Mum dita bazata bari in aureka ba ko don saboda Cousin
dinta warce ita ce Mahaifiyar Nihad" Cike da confusion Khalil ke kallonta don shi
har a lokacin babu wanda ya gaya masa meke faruwa, Yace "Ban gane ba Nadeeyah, u
are getting me confuse, what is happening" Ta mike tace "Ina zuwa..." Yace "Wait
plss ki fahimtar da ni Nadeeyah" Tace "I am coming" Ya bi ta da kallon mamaki har
ta shiga cikin gidan, ba a dau lokaci ba sai ga mai aikin gidan ta fito ta karaso
har inda yake ta sanar masa ance ya shigo ciki, tashi yayi ya bi ta zuwa cikin
gidan, nan ya tarar da Hajiya Safeenah a parlor, ya zauna ya gaisheta ta amsa da
fara'a tana tambayarsa ya ya baro mutanen kano, yace "Alhamdulillah" Tace "Naje har
kanon amma bamu hadu ba har na taho" Da mamaki yace "Wallahi ban sani ba Mum" Tace
"Ehh nasan baka sani ba Khalil" Bai sake cewa komai ba yayi shiru yana
jiran yaji kiran me tayi masa, tace "Kana ji na Khalil" Yace "Ina ji Mum" Tace
"Kasan komai ya faru a rayuwa mukaddari ne daga Allah ko?" Shi dai yayi shiru yana
kallonta, tace "Don haka ina son ka sa a ranka Allah bai kaddara aurenka da
Nadeeyah ba" Da mamaki yace "Mum me yasa kika ce haka?" Tayi shiru tana kallonsa, a
nutse ta shiga yi masa bayanin duk abinda ya faru da kuma alaqarta da Mahaifiyar
Nihad, he was just speechless and at the same time confuse, tace "Duk da aure
tsakaninku bai haramta ba amma sai mu yi masu kara, kuma er uwata ce ta kusa ba ta
nesa ba, daga kai har Nadeeyah ku yi hakuri, kai ka zauna lafiya da matarka ita
kuma Allah ya bata miji na gari, amma bazan iya barin 'ya ta ta auri mijin Nihad ba
albarkacin zumunci, Nayi ma Hajiya Fatima bayanin komai yau kusan sati uku kuma ta
gamsu da duk bayanai na ta kuma min uzuri...." Khalil dai tuni ya fada duniyar
tunani yana ganin abun kamar a mafarki, jin Mum tayi shiru ya kalleta yaga shi take
kallo, A hankali Khalil yace "Amma Mum babu haramci a aurena da Nadeeyah ai" Tace
"Kayi hakuri Khalil, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, Allah ya ma Nadeeyah
zabin alkhairi" Sunkuyar da kansa yayi bai ce komai ba yana ganin kamar dole ma
Allah ya kamasa bayan jiran nan nasa da Nadeeyah tayi at the end ace bai aureta ba,
Mum tace "Bari in je ina da bakuwa khalil" Bai iya yace mata komai ba har ta mike
ta bar parlon, ya Jinginar da kansa jikin kujeran parlon, ba a dau lokaci ba
Nadeeyah ta shigo parlon tana kallonsa tace "Hope ka gane yanxu??" Yace "Ban gane
ba Nadeeyah.... Don ke da Nihad kun kasance Cousins ba wannan yake nufin babu aure
tsakaninmu ba ai" Tace "Toh babu, dama kawai iyayena nake kokarin yi ma biyayya
kuma i am happy things later turnout this way at last, and i pray it's just the
best for me"
*Thanks for the calls and messages to check on me, i am much better*
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
77
Khalil ya girgiza kai yayi kasa da murya yace "Kar ki ce haka pls Nadeeyah, don't
say that plss, it's a promise we made na auren juna, do not allow us break that
promise plss..." Nadeeyah tace "Plss kada mu ja issue din nan Kjay, Allah ya sa
hakan shine mafi alkhairi gareni, sannan kuma gareka, let's close this case forever
and ever, in dai ba ja kake son yi da mahaifiyata ba...." Kallonta kawai yake ya
kasa cewa komai, tayi murmushi tace "So what's up now?" Jinginar da kansa kawai
yayi jikin kujera a hankali yace "Ba wani mahaifiyarki Nadeeyah, dama kin riga kin
sa a ranki ke baza ki auri me mata ba, kuma kin fada just now, baxa ki aureni ba
saboda ina da mata yanzu, i understand u are just using this new issue to cover up"
Tace "I agree with what ever u think Kjay, ko da na aureka bazan samu rest of mind
ba i know, so i love the way things took a new turn, from henceforth u are the
brother i neva had, zan daukeka matsayin babban yayana that will always be there
for me" Shiru kawai yayi yana kallonta lokaci daya duk yanayinsa ya canza, tace
"Let me get u water and some slice of cake" Daga haka ta mike ta nufi cikin gidan
ya bi ta da ido babu ko kiftawa. Bayan la'asar Khalil ya shigo gida bangaren Mami,
gaba daya mood dinsa wasn't good, Parlor ya tadda Mami da Noor xaune suna kallo
tare, ya nemi waje ya zauna yana kallon Mami cikin sanyin murya yace "Ina yini" Ta
kallesa tace "Lafiya lau" Shiru yayi, bayan wani lokaci a hankali yace "Mami me
yasa baki gaya min abinda ke faruwa ba?" Mami tace "Yanxu dai ba ka je ka jiye ma
kunnenka ba Khalil" Jin bai ce mata komai ba ta kallesa, taga kallonta yake alamar
dai he is speechless, tace "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ku baki
daya, Allah ya bata miji na gari ita kuma" Mikewa kawai yayi ya bar parlon Mami ta
bi sa da kallo. Mami na zaune parlon Janar da shigowarsa gidan kenan wajen karfe
biyar na yamma, Apple ne da ta yanka masa a gabansa yake ci, ta ci gaba da maganar
da take masa a hankali tace "Toh yanzu suna son za su dawo maka da kudaden ne" Ya
kalleta da sauri yace "Inyi me da su? No they should keep it, it's okay ba damuwa,
haka Allah ya tsara" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh shikenan, zuwa Anjima
zan kira Hajiya Safeenar in gaya mata, kai kuma Allah ya kara girma" Wayarsa dake
gefensa ya dauka saboda kiransa da ake ya daga ya kai kunne a takaice yace "Basu
wayar kawai in masu magana idan ka iso..." Daga daya bangaren me kiran nasa yace
"Amma kana ji na Abubakar, dama ban maka bayani bane, zancen gaskiya bani kadai
bane, kuma muna isowa suka fara kora mu babu tantama kila ka gaya masu...." Janar
ya katse sa yace "Da kai da waye?" Yace "Da dai ka bugo masu waya kayi masu magana
su bari mu shigo sae kaga ni da wanene" Janar yace "Kaga Yaya ni ba kowa nake
kawowa gidana ba gaskiya, banda kai sai Abdulrazaq babu wanda yasan inda nake, ban
kuma ga dalilin da zaka kawo min wani gidana ba, kai baka ga irin security din
wajen bane" Yace "Kwarai na sani Abubakar amma don Allah kayi hakuri dole ce tasa
na taho ba ni kadai ba, amma...." Janar ya katse wayar kawai, ya dau wayarsa da
sojojin suka san sa da shi ya kira, ya kuma basu umarnin tahowa da Yayan nasa wanda
suke uba daya tare da bakon nasa har zuwa cikin gidansa ba sai anyi ta tsayar da su
a checking point ba, Mami na kallon Janar tace "Amma baka sanar min za kayi baƙi ba
a tanadar masu abu na musamman Janar" Yace "Tun last week yake ta son mu hadu to
kinga i am so busy, saboda shi ne ma nayi canceling tafiyata na yau, banda zuciyar
musulunci ni zan kalli Umaru ma kuwa balle in bar sa ya zo har gidana? Wuyarta dai
Allah ya daga mutum nan xai ga wa enda suka yi ta nufansa da sharri sun fi kowa son
su kasance da shi, ni fa nan da kike ganina na dawo daga rakiyar mutane wllh" Mami
ta girgiza kai cikin kwantar da murya tace "Ka daina kawo abubuwan baya da suka
wuce Janar, sannan yan uwanka ne su kuma hannunka baya taɓa rubewa ka cire ka yar,
ka dubi girma irin ta zumunci kayi hakuri duk ka yafe masu kai ne a gaba, su kuma a
baya, hakurin ka ne ya kai ka har wannan matsayin da su basu samu ko 5% dinsa ba,
don haka eraze all this off ur mind" Janar ya mike ya fita daga parlon zuwa parlon
baƙi don har sun shigo gidan don a mota yayan nasa yake, Mami ta bi sa da kallo sai
kuma ta mike ta bi bayansa, Janar na shiga parlon baƙin yaga Yayan nasa Umaru zaune
saman kujera, Alhaji Umaru yace "Ran babban soja ya dade" Kallonta kawai Janar yake
da mugun mamaki, ita kuwa ta sunkuyar da kai kamar munafuka, Janar ya kalli yayan
nasa rai bace yace "Yaya wacece wannan din ka kawo min gidana? Kuma a kan wani
dalili" lokaci daya ta fashe da kuka sosai tace "Don girman Allah yaya kayi hakuri
ka yafe min duk abinda nayi maka wllh sharrin shaidan ne, na tuba bazan kara ba
yaya, ka dubi girman Allah kayi hakuri, duk inda mahaifiyarmu take bazata ji dadin
wannan abinda ka min ba wallahi" Alhaji Umaru yace "Har gidana ta zo ta sameni tana
kuka Abubakar akan cewar in rakata ta zo ta baka hakuri domin idan taje ita kadai
sojojin koran karya suke mata ga kuma tsallan kwado da za su sa ta tayi ta koma
gida kafa duk a kumbure, dalilin da yasa nayi ta kiranka kenan nace maka lallai
lallai ina son mu hadu...." Janar yace "Amma baka kyauta min ba Umaru, kuma da
nasan da wannan shaidaniyar zaka shigo min gidana wllh bazan bari kai ma ka shigo
ba, wannan ai bai dace ba, ina ruwanka da tsakanina da Hassana?" Alhaji Umaru ya
marairaice yace "Ni fa gyara zan yi Abubakar, naga dai yarinyar nan uwarku daya
kamar yanda muke uba daya da kai, kaga kuwa nima ai er uwata ce kuma baxan ga wata
baraka in yi shiru ba" Mami ta shigo parlon da sallama don gaisawa da Alhaji
Abubakar, da mamaki ta dinga kallon Hassana warce tayi bakikirin kamar roban wanki,
wanda dama baƙin shine ainahin colour dinta amma man shafawa me shegen tsada da Ac
da ciye ciyen kayan dadi a gidan Janar yasa ta koma jajir kamar baturiya, Mami ta
dai karasa ciki ta zauna ta gaida Alhaji Abubakar sannan ta kalli Aunty Hassana
tace "Sannu Hassana ya kwana biyu?" A dakile Aunty Hassana tace "Lafiya lau" Sae
kuma ta kalli yayan nata cikin rawan murya tace "Wallahi kwayar abincin da za mu ci
babu a gidana Yaya, tun barinmu gidan nan nayi ma Aliyu kira yafi dubu amma wllh
yaki dagawa, ban san inda ya tafi yake rayuwarsa baya son mu rabesa ba ya bar mu
cikin wannan halin da muke ciki da kannensa, ni ba sisi ba, kuma bani da dalilinsa
tunda ba kasuwanci na iya ba, dama dubu dari bakwai ne a account dina bayan bari na
gidan nan, na kama mana hayan dubu dari shidda daki daya da parlor da bandaki a can
cikin gari, dubu dari din na siya mana kayan abinci, to yanzu ko kwayar shinkafa
babu a gidan, tunda muka shigo satin nan a wahale kawai muke wllh yaya, su Sajidah
ma babu kudin motar zuwa makaranta" Janar yace "Ina ubansu da zaki kawo min maganar
banza?" Tace "Ni dai kayi hakuri duk abinda nayi maka yaya, na maka alkawarin hakan
bazai sake faruwa ba, ai mun horu haka kusan wata daya da sati biyu, don Allah kayi
hkuri ka yafe min" Janar ya mata tsawa yace "Me kike nufi yanzu?" Daga ita har
Umarun sai da suka tsorata a parlon, Umarun yayi karfin hali yace "So take kayi
hakuri ka bata dama na karshe ta dawo nan da yaranta su ci gaba da zama Abubakar,
kuma in sha Allahu bazata sake yin abinda tayi ba" Janar ya girgiza kai yace "A
area din da nake ma Hassana bata isa ta zauna ba balle cikin gida na, abu daya zan
iya yi ma Hassana kuma shine na karshe wallahi kun ji na rantse kuma bazan yi
kaffara ba, Sannan bana son ko da wasa ta sake zuwa kusa da inda nake idan kuwa ba
haka ba zan sa sojoji su halbe min ita, Nauyin yaranta kuma ba a kaina yake ba ta
kwashesu ta mayar gun ubansu da ta rabasa da su tun suna yara, ita kuma albarkacin
zumunci zan tura mara miliyan biyar a account dinta taje ta koyi kasuwanci tayi,
iyakar abinda zan iya yi ma Hassana kenan, bayan nan kar ta sake making mistake din
zuwa kusa da inda nake idan ko ba haka ba bazata ji da dadi ba" Umaru yace "Yo ai
hakan ma ta gode, Miliyan biyar a wannan marran, aa wllh ta gode...." Janar ya fice
daga parlon, Mami dai na zaune parlon ta kasa cewa komai, Aunty Hassana ta daga kai
tayi mata wani kallo ta dauke kai, Mikewa Mami tayi ta fita daga parlon, Umaru yayi
kasa da murya tace "Toh yanzu nawa zaki turo min kenan Hassana? Kin ji fa har
miliyan biyar, ke ko kin haye wllh" Ta galla masa wani kallo tace "Ehh lallai amma
baka da tsoron Allah, kai da nace ka tursasa ka dage kayi min kokari wajen ganin ni
da yarana mun dawo gidan da zama, ni ban ma ga amfanin zuwanka ba, ko ni ai zan iya
zuwa ya bani miliyan biyar din ba sai ka rakoni ba Umaru" Umaru da ya bude baki
yace "Amma ke butulu ce Hassana, haka za ki ce min? Ba don ni ba ke kin isa ki zo
kusa da layin nan??" Ko kallonsa bata sake yi ba, Sai ga Janar ya shigo yana
kallonta strictly yace "Na tura maki miliyan biyar, yau ya zama rana