Showing 129001 words to 132000 words out of 268471 words

Chapter 44 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ki ka kai kukanki wajen Allah kika hana kanki bacci a wannan lokacin,
to in sha Allah addu'arki baxata tashi a banza ba, ta yanda baki yi zato ba Allah
xai maki sakayya ya kuma tona asirin koma wanene yayi maki wannan abun" Hawaye ya
dinga sauka idon Nihad ta kasa ce ma Aunty Maryam komai, Aunty Maryam da taji
tausayinta ainun tace "Kiyi hakuri ki daina wannan kukan, tunda kika ambaci Allah
ai an wuce wajen kuma, amma me yasa kika yarda da kawaye har zaki zauna cikinsu
half naked?" Nihad ta girgiza kai cikin rawan murya tace "Wallahi Aunty ni ban taɓa
zama ko a gidanmu haka ba, sannan ni ba a hostel nake ba kawai zuwa nake, lokacin
da xa mu fara exams din first semester level 3 ne na koma hostel kuma ni ko da zani
bana zama cikinsu wallahi" Aunty Maryam na kallonta da mamaki tace "Toh a ina aka
dau video din?" Nihad ta buda hannu tace "Nima wallahi ban sani ba, yanda kowa ya
gansa haka na gansa" Aunty Maryam ta dinga kallonta dumbfounded, can tace "Ban gane
baki san a inda aka maki video din ba" Nihad ta fashe da kuka tace "Wallahi da
gaske Aunty, ni ban san ta yaya aka yi hakan ba, kuma ban ma san ko wani waje ne
ba" Aunty Maryam ta kasa cewa komai don mamaki, can dai tace "Toh kenan ba ke bace
a video din" Nihad na goge idonta tace "Ni ce Aunty, amma ban san ta yaya ba,
because under wears dina ne a jikina" Sosai wannan lamarin ya rikitar da Aunty
Maryam, can dai ta sake cewa "Kuma ba a hostel din bane?" Nihad tace "Ba nan bane
wllh" Aunty Maryam tace "Ba kuma gidanku bane?" Nihad ta girgiza kai tace "Ba
gidanmu bane" Aunty Maryam tace "Ikon Allah, kin tabbata bayan gida baki zuwa wani
wajen ko da kawaye haka?" Shiru Nihad tayi, Aunty Maryam tace "Kin yi shiru" Nihad
ta hadiye abu da kyar amma tana tsoron ce ma Aunty Maryam ai sun kan je hotel da
guess lodge da friends dinta, Aunty Maryam tace "Kina zuwa kenan?" Cikin sanyin
murya tace "Ina bin kawayena duk inda xa su wani lokacin" Aunty Maryam tace "Toh su
suka maki, ki gaya min tsakaninki da Allah baki shan komai?" Nihad ta dago da sauri
tana kallon Aunty Maryam tace "Aunty kamar me" Aunty Maryam tace "Kayan maye, gaya
min tsakaninki da Allah, kar ki min karya don kina min ma zan gwada ki kuma zan
gane, don ni Nurse ce" Nihad na girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Wallahi
Aunty bana shan komai kin ji har na rantse, idan ina shan wani abu Allah shine
shaidata, ki gwada ki ga Aunty" Aunty Maryam tace "Toh kawayen naki fa?" Nan Nihad
ta fara lissafo ma Aunty Maryam abubuwan da su Husnah suke sha Innocently, haka
Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta cause taga babu alamar karya a tare da ita,
iya gaskiyarta kawai take fada, can Aunty Maryam tace "Ikon Allah, to kuma a gida
an san kina bin wa ennan kawayen har ma ki bi su duk inda xa su?" Nihad ta girgiza
kai tace "Stepmom dita ce kawai ta sani, ta ma san gaba dayansu" Buda baki Aunty
Maryam tayi, sai kuma tace "Kuma bata hanaki alaqa da su ba?" Nihad tace "Aa, tace
min in rikesu baxan samu kamarsu ba don suna sona sosai, kuma tana kare ni yanda
yan sauran yan gidan baxa su gane ba, idan na dawo da daddare ita take bude min
kofan parlon mu idan an kulle" Aunty Maryam was really shock jin abinda Nihad tace,
taji zufa na keto mata, tace "Mamarki fa?" Nihad ta girgiza kai a hankali tace
"Bata sani ba ai, dama a bangaren stepmom dina nake, so akwai distance tsakanin
part din stepmom din tawa da na Mum dina...." Aunty Maryam tace "Wa ya ce ki koma
part din stepmom din taki?" Nihad tace "Aa wai tun ina karama ta dawo da ni wajenta
shi ne har na girma" Aunty Maryam tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to ina
jin ki, idan ta bude maki kofar da daddare sai tace maki me??" Nihad tace "Kawai
cewa xata yi inyi sauri in wuce kar a gan ni" Aunty Maryam bata san sanda hawaye ya
kawo idonta ba, nan ta kara tsorata da lamarin kishiya, bata san sanda ta dafe
kanta da yayi mata nauyi ba, can ta dago da kyar tace "Bata da yara ne?" Nihad ta
girgiza kai a hankali tace "Tana da yarinya mate dita, her name is Nihal, ita kuma
tana side din Mumy na, sannan akwai Amina da Aunty Kamila that is married" Aunty
Maryam tace "Kuma duk su ma yaran nata dake gidan suna fita su kai dare ta bude
masu kofa?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Aa babu inda suke zuwa su, ba ma su
da friends" Aunty Maryam tace "Nihad" Nihad ta daga kai ta kalleta, Aunty Maryam
tace "Ku nawa ne wajen mamanki?" Nihad tace "Mu uku ne, ni ce first born" Aunty
Maryam was so heartbroken, tace "Ita kuma fa?" Nihad tace "Babban yayanmu ya Farooq
sai ya Usman, sai Aunty Kamila, Nihal da Amina" Aunty Maryam na girgiza kai tace
"Yanzu a tunaninki duk gidan wa yafi sonki? Yake maki duk abinda kike so?" Nihad ta
sunkuyar da kai a hankali tace "Umma" Aunty Maryam tace "Wacece Umma?" Nihad tace
"My Stepmom" cike da takaici Aunty Maryam na girgiza kai tace "Ta cuci rayuwarki,
ta cuceki, ta cuci mahaifiyarki, ita
kuma salon nata kishin kenan?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, da wannan abun
da ta maki da gwara ta fuskanci mahaifiyarki su xuba kishin yanda ya kamata, bata
maki adalci ba, kuma ko tantama babu da sa hannun wannan matar a video din naki,
Nihad wani masoyinka ne xai dinga supporting dinka kana bad things, kana abubuwan
da basu dace ba? Wani masoyinka ne xai xuba maka ido ka fita ka kai har dare shi
bai maka fada ba kuma ya kareka ta yanda wasu baxa su sani ba balle su maka fada?
Wani masoyinka ne xai ce ka rike yan iska masu shaye shaye a matsayin kawaye har
yana ikirarin baxa ka samu kamar su ba, sannan ya daure maka kugu ka dinga bin su
duk inda xa su? Nihad me yasa ita nata yaran basu da kawaye sannan basa fitan
dare?" Shiru Nihad tayi tana kallon Aunty Maryam ko kiftawa babu, Aunty Maryam tace
"Ba shiru xa kiyi min ba bude baki ki bani amsa yanzun nan?" Tunda Nihad take bata
ta6a zaunawa tayi wannan tunanin ba balle har ta gane komai tayi reasoning a kai,
ita dai Aunty Jamila kawai rabata take da Umma ta karfi da yaji amma bata ta6a
zaunawa ta zayyano mata abubuwan nan da Aunty Maryam ta zayyano mata ba yanzu, to
ai bata ma san abinda take yi da sanin Umman ba balle har ta zayyano mata wannan
abubuwan tunda komanta a boye take yi, Umma ce kawai ta sani... Aunty Maryam bata
yi interrupting Nihad a duniyar tunanin da ta fada ba, kana kallon fuskarta zaka
fahimci she is slowly trying to comprehend duk wani abinda Aunty Maryam ta fada ne,
babu kuma abinda ya fado ran Nihad sai karyan da suka yi ma yan gida wai zata bi
Aunty Kamila kebbi alhalin hostel xata koma da zama, Umma da Aunty Kamilar ne kadai
suka san gaskiyar maganar, kuma har ta gama zamanta hostel din for more than 3
months Umma bata ta6a zuwa inda take ba, har ita Aunty Kamilan, alhalin idan mutum
na hostel kuma iyayensa na garin ko bayan sati uku ne su kan kai masa ziyara.




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and ur evidence via


07087865788...

40

Aunty Maryam ta kai hannunta saman shoulder din Nihad ta dafata a hankali tana
kallonta don har sannan tunane tunane take with shock written all over her, da
sauri Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta hadiye abu
da kyar, cike da karfin hali tana girgiza kai tace "Ni ba wanda ya taba gaya min
abubuwan nan, ni ban sani ba, you are just telling me now" Aunty Maryam tace "And
hope you've realized what i am saying?" Nihad ta gyada kai hawaye na sauka idonta,
sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Aunty Maryam tace "Ni ban san bata so na ba
Aunty, Lokacin wani saurayina yace iyayensa xa su xo gidanmu shine na gaya mata sai
tace min kar in gaya ma kowa har Mumyna, ita da kanta xata je ta gaya ma Abba, na
gaya mata da few days aka saki Video dina a internet shine yayi blocking dina" Buda
baki Aunty Maryam tayi tana kallonta and she was speechless, Nihad na kuka sosai
don sai sannan abubuwan ke dawo mata, sai yanzu ƙwaƙwalwarta ya fahimci abubuwa da
dama, Tana kuka sosai tace "Da Abbana ma ya koreni bata ce komai ba" Aunty Maryam
ta dafata da sauri tana kallonta da mamaki tace "Ya koreki daga ina?" Cikin raunin
murya Nihad tace "Gidanmu, yace baya son ya sake ganina har abada, she was standing
at the door bata ce masa komai ba, and she saw me leaving the house" Sai ta kara
fashe da kuka sosai, she is so pained, bata ta6a kallon Umma from this perspective
ba, ga dai komai vividly a bayyane amma bata ta6a ganewa ba, Aunty Maryam tayi
karfin halin cewa "Kina nufin he sent you away from his house?" Nihad ta gyada mata
kai tana kuka, Aunty Maryam ta kasa rufe baki, can ta kalleta da kyau tace "Dalilin
kawo ki garin nan da Khalil yayi kenan dama?" Sai a sannan Nihad tayi realizing she
just said what she's not suppose to say to her, ta dakatar da kukan da take da
sauri ta hadiye abu da ya tokareta a throat, ta kalli Aunty Maryam, sai kuma ta
fara kame kame "Aa Aunty kawai dama.... Dama, makaranta...." Aunty Maryam da tuni
ta ganota tace "Kar ki min karya" Nihad ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali,
Jikin Aunty Maryam yayi sanyi sosai, wato dalilin kawota Abuja da Khalil yayi
kenan? But ai Mami tace mata Abba ne ya bukaci ya dawo kuma, she became so confuse
at this point, Can ta kalli Nihad tace "Ya isa haka, ki daina wannan kukan, ki tafi
bandaki ki wanke idonki ki kwanta kafin Asuba ya karasa" Nihad ta kasa ce mata
komai, Aunty Maryam tace "Tashi" Tashi tayi da kyar tana jan kafa ta shiga bandakin
ta wanke fuskarta ta fito, Aunty Maryam tace "Ki kwanta, kuma bana son ki sake
wannan kukan kin ji me nace?" Nihad ta gyada mata kai ta kwanta saman gadon, Aunty
Maryam ta mike ta fita daga dakin ta kullo mata kofar. Kwanciyar da Aunty Maryam
bata sake yi ba kenan har gari ya waye, lamarin Nihad ya tsaya mata cak a zuciya,
taji tausayinta da mahaifiyarta ainun, ta kuma ji mata takaicin wannan baƙin taɓon
da aka mata da xai bibiyeta har karshen rayuwarta, this is soo painful, ta kuma
tsine ma Umma ta la'anceta yafi a kirga, ta jima bata ji labarin irin wannan
zaluncin da aka ma Nihad ba, ta kara tabbatar da cewa kishiya bala'i ce kuma masifa
ce. ƙarfe takwas saura ta kira Khalil, yana bedroom dinsa kwance yayi nisa a
tunanin da yake, he is so confused and looking for a way out a kan wannan lamarin,
gaba daya kansa ya daure on what next to do, ko jiya da daddare sai da Mami ta sake
masa magana yayi kokarin ganin Nihad ta amshi admission letter din nata ko gobe ne
kar a shiga weekend, idan yaso idan ta amsa ko ranan sai ta bi jirgi ta koma gida,
ita dai duk ta damu ace Nihad ta tafi gida, ga Abba a jiyan shi ma yayi masa
maganan business din da zai yi a zanzibar, which he will be leaving Nigeria in 2
days time, that is on Sunday, kiran Aunty Maryam ya kara rikita masa lissafi ya
mike zaune da sauri yana kallon wayar, Allah ya sa ba wani maganan Nihad tayi mata
ba dai, sai da wayar ya kusa katsewa ya daga ya kai kunne, yayi composing kansa
yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau, idan baka komai ka taho yanzu ina
jiranka" Nan yaji gabansa ya fadi sosai, Ya dake yace "Hope all is well Aunty?"
Tace "Nace dai ina jiranka" Yayi gathering courage yace "Toh" Daga haka ta katse
wayar, duk da sanyin Ac dake dakin ji yayi zufa na keto masa ta ko ina, he just
can't Imagine ace Nihad tace mata ai an daura mata aure da shi, yayi saurin kawar
da tunanin don bai ma son yayi, ya sauka daga saman gadon da kyar ya shiga bandaki
yayi wanka ya fito, cikin few minutes ya gama shiryawa ya dau perfumes dinsa ya
fesa sannan ya dau makullin motar Mami dake wajensa ya fita, ko part dinta bai tafi
ba ya fita zuwa compound, har Khalil ya isa gidan Small mum dinsa ba shi da nutsuwa
babu tunanin da bai zo ransa ba, tunda ya san ba wani saiti gare Nihad ba nan da
nan zaka bugi cikinta ta bude maka komai, yana parking compound din Aunty Maryam ya
kashe motar ya sauka sannan ya nufi parlonta, xuciyarsa na bugawa ya kwankwasa
kofar parlon, mai aikin ta bude, ta gaishesa ko amsawa bai yi ba ya karasa ciki ya
zauna ya jinginar da kansa da kujera, sai ga kiran Aunty Maryam a wayarsa ya daga
ya kai kunne tace masa ya hauro sama, ya mike yana kallon mai aikin yace "Ke ina
bakuwar da take gidan nan?" Da ladabi mai aikin tace "Tana guess room" Direct can
ya nufa da sauri maimakon sama da Aunty Maryam tace ya hau, ya bude kofar dakin ya
shiga, tana zaune gefen gado daure da zanin da Aunty Maryam ta bata bayan ta fito
wanka tana shafa mai, har sannan idanuwanta a kumbure suke don har gari ya waye
bata rintsa ba, Umma tayi mugun tsaya mata a rai, bata ta6a viewing dinta from the
this perspective ba sai yanxu with the help of Aunty Maryam, she wish ana iya maida
hannun agogo baya, wani tsanar Umma kawai taji take ji a ranta idan ta tuna wasu
abubuwan da ta sa ta dinga yi a boye, tunda Nihad ta juya da sauri bayan an bude
kofa suka hada ido da Khalil ta dauke kai ta ci gaba da shafa man da take a
hankali, ya nufota kirjinsa na heaving yace "Kee, me kika gaya ma Aunty Maryam?" Ta
ɗan kallesa, sai kuma ta ci gaba da abinda take taki kulasa, jin bata ce komai ba
ya hade rai yace "Magana nake maki" Tace "Toh ba ga ka a gidan ba kaje ka tambayeta
mana" Sake baki yayi yana kallonta, ganin yanda ya tsaya mata a kai ta mike ta dau
cream dinta xata bar wajen ya fixgota ta dawo dab da shi yana mata wani kallo, ta
zaro ido tace "Ni wallahi ka kyaleni, ai ba ni kadai xaka tambaya ba ita ma sai ka
je ka tambayeta" Khalil ya dinga kallonta sai kuma ya zaunar da ita gefen gadon
strictly yace "Ina me tabbatar maki cewa in har kika gaya mata anything pertaining
to relationship dina da ke, ko kuma dalilin da ya sa muka zo garin nan tare dake, i
have no choice then to divorce you right in front of her, a nan take a gabanta xan
sakeki" Nihad ta wani kyabe baki tace "Toh kayi ta saki na mana, dama ni ai ban san
ina da wani aure a kaina ba, sannan Alhamdulillah tunda duk iskanci na ba a ta6a
ganin ina rungume rungume ba, kawai dama in ka gama sakin nawa ka kai ni tasha ka
saka ni a mota in tafi gun dangin mamata tunda ina da su kuma suna so na" Kallonta
ya dinga yi babu ko kiftawa, kawai ji tayi magana da Aunty Maryam ya sa mata
courage da tayi loosing few days ago, taji ta kara samun kwarin gwiwa sosai,
because at least tayi magana da warce ta fahimceta ta yarda da ita, sannan warce ta
ganar da ita abubuwan da duk bata sani ba bata kuma ta6a kawowa a kai ba a baya,
Tashi tayi ta koma can daya bangaren gadon ta zauna tana shafa cream din a kafa,
Wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya kalli screen din sai kuma ya nufi kofa ya
fita daga dakin, direct sama ya haura yaga Aunty Maryam zaune parlornta, ta dinga
kallonsa ya kasa barin su hada ido har ya karaso ya zauna, yace "Ina kwana Aunty?"
Aunty Maryam na kallonsa a hankali tace "Lafiya lau" Sai a sannan yayi karfin halin
daga kai ya kalleta, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Ka gaya min gaskiya
Khalil, dama saboda ka kawo Nihad garin nan ne ka dawo gida ko da gaske kiranka
Abbanka yayi?" Khalil yayi karfin halin cewa "Aunty ai da Abba bai min izinin shiga
gidansa ba kema kinsan babu ta yanda xan shiga, kawai coincidentally ne...." Sai
kuma yayi shiru ya sauke kansa kasa don bai ma san me xai ce mata ba tunda bai san
abubuwan da Nihad ta gaya mata ba, he don't want to say something different, bayan
few minutes yaji Aunty Maryam tace "Me ka fahimta game da kishiyar Mamarta tunda
kace ka zauna a gidansu" Da sauri Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma yayi kasa
da murya yace "A wolf in sheep's clothing, a green snake under the green grass...."
Aunty Maryam ta girgiza kai cike da takaici tace "I was shock at Nihad's story
Khalil, nayi matuƙar girgiza da labarinta, kishiyar Mamarta bata mata adalci ba, ta
cuceta ta gurbata mata rayuwa" Khalil ya lumshe ido ya bude bai dai ce komai ba,
Aunty Maryam tace "Me yasa kace admission letter xata amsa a garin nan bayan ba
haka bane?" Sai da khalil yayi stiff a inda yake zaune, Aunty Maryam tace "She told
me her dad sent her away from his house" Sosai gaban khalil ya fadi jin abinda
Aunty Maryam ta kara cewa, shikenan ya ma san ta riga tace an masa aure da ita
tunda har ta iya buda baki tace an koreta a gida, jin tayi shiru Khalil yayi karfin
halin cewa "Sai me kuma ta gaya maki Aunty?" Aunty Maryam tace "Iya abinda ta sanar
min kenan, sai kuma wanda kai zaka kara min, sannan tace video dinta bata san garin
yaya aka mata ba har ya fita.... Na kuma yarda da ita don babu alamar karya a duk
zantuttukan ta" Khalil dai kallonta kawai yake, can ya sauke wani boyayyen ajiyar
zuciya da ya fahimci iya abinda ta sanar ma Aunty Maryam kenan da gaske, yayi kasa
da murya yace "Haka ne Aunty, but bansan ta ina xan fara gaya ma Mami all this ba,
ni kuma mahaifinta yayi min halaccin da baxan iya kyaleta ta shiga duniya ba bayan
ya koreta gidansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login