Showing 63001 words to 66000 words out of 268471 words

Chapter 22 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

yace "Ta riga ni shigowa" Nihad kuwa tana shiga gidan dama direct bangaren
Umma ta tafi, Abba ya mike ya fita, a side din Umma ya ga Amina yace "Ina Nihad?"
Amina tace "Tana dakin Umma" Yace "Ki shiga ki kira min ita" Amina ta juya ta koma
ciki, Abba ya koma parlonsa, bayan wasu yan mintuna sai ga Nihad ta shigo parlon
Abbanta kanta a kasa, sallama tayi da muryarta da har ya fara dashewa saboda kuka,
bata yarda ta daga kai ba balle ta kalli Abbanta, ta nemi waje daga opposite din
inda khalil ya zauna ta zauna, Cikin rawar murya tace "Abba ina yini" Abba bai amsa
ba, bai kuma kalleta ba, dai dai nan Umma ta shigo parlon da sallama, kallonta
kawai Abba yake, Khalil ya gaisheta ta amsa ta zauna fuskarta dauke da damuwa tana
kallon Abba, Abba dai ya kalli Khalil yace "Nagode da wannan alfarma da ka min na
auren yarinyar nan Ibrahim, Allah Ubangiji ya baka aljanna" Khalil yayi kasa da kai
a hankali yace "Ameen" Abba yace "Ina kuma fatan Allah Ubangiji ya baka hakuri da
juriyar zama da ita.... In dai da akwai wani abu kar kayi kasa a gwiwan kirana ka
sanar min koma menene shi" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Abba tace
"Abba wallahi bana sonsa kuma baxan ta6a sonsa ba, na tsanesa na tsanesa, ni baxan
ta6a xama da shi a gida daya ba, wallahi i hate him...." Mikewa Abba yayi lokaci
daya ya sauke mata mari me lafiya a fuskarta, ihu ta fasa ta dafe kuncinta, Umma ta
bude baki tana kallon Abba, sai kuma tace "Haba Alhaji, Haba Alhaji...." Dakatar da
ita Abba yayi a fusace yace "Bana son jin komai daga gareki, ki tashi ma ki fita"
Umma ta ja bakinta tayi shiru, cike da bacin rai Abba na kallon Nihad yace "U think
i brought u here to ask for ur opinion? Is that what u think?" Abba ya girgiza kai
cike da takaici yace "You are nothing but a disappointment to me Nihad, i regret
having u as a child...." Kuka kawai Nihad take tana jin kamar a mafarki wai ita
Abba ya mara kuma yake gaya mata wannan maganganun, wanda ko fada bai ta6a mata ba
tunda aka haifeta, Strictly Abba ya ci gaba yace "Kuma in har ba so kike inyi
disowning dinki ba baki da miji da ya wuce Ibrahim, kuma dolenki kiyi masa biyayya
ki bisa, idan ko ba haka ba ki nemi wani uban ba ni ba, sannan idan ba shi ya dauko
ki ya kawo ki gidan nan ba bana son in ga kafarki a nan ko da kuwa xa ayi shekara
ne bai kawo ki ba, ki sa a ranki baki da wani a yanxu banda shi, shine gatanki,
shine komai naki, samun kwanciyar hankalin ki a rayuwa ki bi sa, ko mu da muka
haifeki yanxu bamu da iko da ke sama da shi" Kuka kawai Nihad take xuciyarta na
mata xafi, ita fa she still
can't believe Abbanta ne ke gaya mata wa ennan maganganun, Abba na kallon Khalil
da ya sunkuyar da kansa yace "Kai kuma Ibrahim ina me baka umarni in har Nihad xata
kawo maka iskanci ko raini ka zaneta, ni na baka wannan umarnin ba wani ba" Khalil
dai bai dago kansa ba, Abba yace "Shikenan kiran dama, xa ku iya tafiya" Da kyar
khalil ya iya dago kai yace "Nagode Abba, Allah ya kara girma" Abba yace "Ameen"
mikewa yayi yana kallon Umma yace "Sai anjima" Umma ta dinga harararsa, shi dai ya
nufi kofa, ganin Nihad ta ki tashi sai kuka take kamar ranta xai fita Abba ya daka
mata tsawa yace "Tashi ki bar min gidana, useless girl" Tashi tayi da sauri tana
kuka sosai ta nufi kofar ita ma, sai kuma ta juyo cikin rawar murya tace "Abba
makaranta na fa?" Abba yace "Sai abinda mijin ki yace, don shi ke da iko dake
yanxu, don in xai dau shawarata ma babu ke babu makaranta har abada, maza bi sa ku
bar min gidana" Khalil dake jin Abba ya fita daga parlon ta bi bayansa tana kuka
sosai, shi dai ko kallonta bai yi ba ya fita xuwa gun mota, Aminu sai wage ido yake
yana jiran fitowar Khalil, yana ganinsa ya fito kuma ya shige mota, Nihad ta bude
bayan motar ta shiga ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tana jin kamar
numfashinta zai dauke, Khalil na isa gate Aminu yace "Ina ta jiranka" Khalil yace
"Xan zo da daddare" Aminu ya washe hakora yace "Toh toh sai ka zo" Da gefen ido ya
dinga lekan Nihad dake bayan mota, khalil ya ja motar suka bar gidan. Sai kusan
karfe shidda suka isa gida, Khalil na parking ya sauka ya tafi ya kulle gate sannan
ya dawo ya kashe motar, har sannan Nihad bata dago kanta da ta kife a bayan motar
tana kuka ba, tana jin ya kashe motar ta bude side dinta ta sauka, gaba daya ta
jike hijab dinta da hawaye har a sannan kuma ba daina kukan tayi ba, ta fara tafiya
towards the building of the house, ji tayi ko ina na juya mata a ido, Rufe motar
khalil yayi da sauri ya nufeta ganin abinda take, amma kafin ya isa inda take tuni
ta kai kasa, ba karamin faduwa tayi a wajen ba, ya zura makullin hannunsa cikin
aljihu da sauri ya durkusa gabanta ya dagota amma tuni tayi pass out, daukarta yayi
ya nufi cikin gidan da ita.

_kiyi subscription ki karanta hankalinki kwance. Nima kuma sai in samu kwarin
gwiwan dinga yi maku double update_
I am soo grateful for the patronage, Allah ya saka maku da Alkhairi ya biya maku
duk wata buƙatar ku ta Alkhairi, Allah ya kara ma iyayenku lafiya.




*Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence via👇🏻
07087865788


21

A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take kwance da kallo, a daki take
saman gado, ta mike xaune da kyar tana jin ko ina na jikinta na mata ciwo ga wani
sanyi da ke shigarta duk da fankan dakin a kashe yake, ta kalli agogon dakin taga
karfe biyu dai dai, window ta kalla ganin duhu yasa ta fahimci biyu na dare ne,
hade kai tayi da gwiwa bayan tayi recalling duk abubuwan da suka faru, she couldn't
stop tears from rolling down her eyes, ta dinga shessheka a hankali, tunawa da tayi
bata yi sallan magrib ba balle Isha'i ya sa ta dago kanta tana goge idonta da ya
kumbura, tayi kokarin sauka daga saman gadon amma taji baxata iya ba, ko ina ciwo
take ji yake mata a jikinta, hakan ya sa ta koma ta kwanta a hankali, Hijab dinta
dake gefenta ta jawo ta lullube da shi ta takure waje daya sbda sanyin da take ji
sosai, amma bai taimaka mata da komai ba sai rawan dari take, bayan kusan minti
talatin ta ji an bude kofar dakin, ita dai tana takure inda take ta rufe har kanta
da Hijab, tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallonta, dama ya zo dubawa ne ya ga ko
ta tashi or she is still unconscious cause he isn't as bad as she is, he have human
conscience in him unlike her, har xai juya ya fita sae kuma ya karasa cikin dakin
ganin kamar she is shivering, ya isa kusa da gadon yana kallonta xai cire Hijab din
da ta rufe fuskarta da shi, ta riko hijab din a fusace cike da tsiwa tace "Baka da
hankali ne?? Uban meye xaka shigo min daki cikin daren nan?" Sake Hijab din yayi ya
juya ya fice daga dakin ta bi sa da harara sai kuma ta ja tsaki ta koma ta kwanta
jikinta na rawan sanyi sosai. Har aka yi asuba Nihad ta kasa motsawa daga exact
spot din da take a kan gadon tun cikin dare, she is so sick and weak, tayi yunkurin
tashi ya fi a kirga amma kamar an danneta saman gadon take ji, duk da babu wani
abun da ta ci tun jiya amma haka ta dinga jin amai yana damunta kamar xai taho
mata, ga ciwon kai me tsanani da ya addabeta, wajen karfe takwas taji aman ya taho
mata, bata san sanda wani strength ya xo mata ba ta sauka daga kan gadon tana layi
ta bude kofar bandaki, nan ta durkusa ta dinga kakarin amai amma ba abinda ya fito,
Khalil na kwance parlor yana jin ta amma ko motsawa bai yi ba daga saman kujeran da
yake, a nan tsakar dakin Nihad ta kwanta tana maida numfashi hawaye me xafi na
sauka idonta, tana nan a haka har kusan karfe sha daya na safe, zuwa lkcn kuma
xaxxabin ya ci karfinta, Duk yanda ya so fita harkarta a gidan kasawa yayi, cause
he wasn't raised to be mean, ya kuma san bata ci abinci ba throughout jiya don shi
ya fito da indomie da ta bari a daki bata ta6a ba, karfe sha biyu saura ya mike
yayi hanyar dakin after soothing himself to do so, kwata kwata ba don ranshi ya so
ba ko don tayi deserving ba yayi hakan kawai dai shi din me tausayi ne, yana bude
kofar dakin ya ganta nan tsakiyar dakin a kwance, ya fi minti daya tsaye bakin
kofar yana kallonta kafin ya karasa cikin bedroom din, ya duka a gabanta ya cire
hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta bude idonta da yayi jajir amma babu
strength din rashin kunya ko tsiwa, bai kai hannu jikinta ba but yana jin hucin
zafi a jikinta, ya mike ya fita daga dakin ya dau wayarsa, bayan ya gama kiran da
xai yi ya shiga kitchen, ruwan gora ya juye a kettle ya daura saman gas, bayan
ruwan yayi xafi ya hada shayi a cup ya fito, dakin ya koma ya ajiye mata shayin,
amma ya kasa ce mata ta tashi ta sha, har cikin ransa bai son ko magana ya hada shi
da wannan yarinyar, kawai daga karshe ya fice daga dakin ba tare da ya ce mata
komai ba, bayan kusan awa daya ya fita kofar gida ya shigo da wani likita, wani
asibiti dake home service ya kira suka turo masa likitan, bayan sun gaisa ya kai sa
har dakinta, likitan ya ajiye abubuwan da ya taho da su yana kallon Nihad, Khalil
ya juya ya basu waje yayi zamansa a parlor, bayan likitan ya dubata ya tilastata ta
dan sha shayi, sai da yayi yakin kusan minti sha biyar kafin ya samu da kyar yayi
mata allurai, ya kuma bata magunguna ta sha, da tace masa sanyi take ji ya dauko
wani zanin gado da ya gani a leda ya bude sannan ya bata ta rufa da shi, yace
"Allah ya sauwake, Anjima da daddare xa a dawo yi maki allura" Ita dai bata ce
komai ba don bacci taji yana hauro mata har ya fita daga dakin, yayi ma khalil
sallama sannan ya bar gidan..... Tashi khalil yayi wajajen karfe uku ta dalilin
gate da ake kwankwasawa ya fita zuwa gate din ya bude, Aunty Jamila ya gani bakin
kofar, sosai take kama da Mummy, ya mata sannu da xuwa sannan ya bata hanya ta
shigo gidan, sai da suka shiga parlor ya xauna kasa ya gaisheta ta amsa da fara'a
tace "Ya sabon waje" Yace "Alhmdlh" Tace "Toh madallah, Allah Ubangiji ya baku
zaman lafiya" Bayan few seconds ta sake kallonsa tace "Ina Nihad din?" Ya dan kalli
hanyar daki yace "Tana ciki" Aunty Jamila tace "Toh sanar mata na zo" Mikewa yayi
ya nufi hanyar dakin sai kuma ya dawo yace "Aunty bata jin dadi ne tun jiya daxu
likita ya zo dubata, ki karasa cikin dakin" Aunty Jamila ta mike ta bi bayansa zuwa
dakin, kofar kawai ya bude mata ya koma gefe, ta shiga dakin da sallama ya juya
yayi komawarsa parlor, don tunda likitan ma ya bar gidan shi bai shiga dakin ba. A
hankali Nihad ta mike xaune tana kallon Aunt dinta, Aunty Jamila ma kallonta kawai
take don ba karamin rama tayi ba, Aunty Jamila ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace
"Ya jikin" kamar jira Nihad take ta fashe mata da kuka tace "Aunty don Allah ku
yafe min, wallahi ban san daga inda video din nan yake ba, ni ban ta6a video haka
ba, kuma ban ta6a bari a min video haka ba, i don't know how everything happened"
Aunty Jamila ta ma rasa abinda xata ce mata, Kuka kawai Nihad take ta hade kanta da
gado, Aunty Jamila ta dagota tace "Ya isa haka, ba kuka na zo ki min ba, abinda ya
faru kuma ya riga ya faru babu me ja da Ubangiji" Nihad dai goge hawayen da ya ki
tsaya mata kawai take, Aunty Jamila ta girgiza kai tace "Da kina jin maganar uwarki
duk haka da bai faru dake ba Nihad, ke ce tara kawaye, ke ce gantali, ke ce shiga
kamar ba yar musulmai ba, kina ganin yanda yar uwarki ke rayuwarta gwanin sha'awa
ita da ma ba gaban iyayenku take karatu ba, kin bata wayonki Nihad, kin kuma yi ma
kanki damage din da baxai ta6a goguwa ba a doron kasa ba, ina ne wannan Video din
naki bai je ba a internet?" Nihad dai kuka take kamar ranta xai fita, Aunty Jamila
tace "Da kika je can kebbi din kinyi kawaye ne?" Nihad ta girgiza mata kai kawai,
Aunty Jamila tace "Ta yaya ma xa ki ce ke baki san daga inda video din nan ya fito
ba? Ba fa daura fuskarki aka yi ba ko wani abu, ke din ce a video din, ko Inner
wear din ma ai ni na siyo maki su a Lagos ba a dade ba" Nihad ta ma rasa abun cewa,
Aunty Jamila tace "Idan kin je makarantar baki zama a hostel ne?" Nihad ta sunkuyar
da kanta, Aunty Jamila tace "Buda baki xa kiyi ki min magana" Cikin rawar murya
tace "Aa" Wani shegen kallo Aunty jamila ta mata tace "Ba kin ce min kawayenki a
hostel su ke ba?" Nihad ta gyada kai tace "Ehh amma a aji muke haduwa da su" Aunty
Jamila tace "Baxa ki daina min karya ba?" Nihad ta hadiye abu da kyar tace "Da
gaske Aunty" Aunty Jamila tace "Toh ke kika sani, ki rike gaskiyarki a ciki, xan ga
ta yanda xa ayi a gano ta ina video din ya fito idan kin ma mutane karya" Nihad dai
tayi shiru gabanta sai faduwa yake, ta yaya ma xata fara ce ma Aunty Jamila babu
wani kebbi da suka je da Aunty Kamila hostel ta koma da zama, cab ai rufeta kawai
xata yi da duka a nan, sannan ko jiya da suka je gida sai da Umma ta bata shawaran
ko da wasa kar ta ce ma wani ai bata je kebbi ba hostel ta koma, ko da xa a cika ta
da tambayoyi, balle ita tasan Husnah da Naf da Zully, enemies dinsu ma basu ma
video ba balle ita, idan ma Zully na video suna daki tunda ita mayyar video ce
Husnah tayi ta masifa kenan tunda su dama sun saba xama daga su sai lingerie, Aunty
Jamila ta katse mata tunaninta tace "Don uwarki wataran da kanki xaki bude baki ki
fadi ta inda video ya fito, dena wani tunane tunane, yanxu dai ki gama nuku nukunki
da karyarki aikin gama ya riga ya gama tunda ga ki a gidan mijin ki" Nihad ta fashe
da matsanancin kuka tace "Wallahi ni ba mijina bane shi Aunty, kuma baxai ta6a xama
mijina ba, shi drivern ne zai zama mijina? Wllh baxan ta6a yarda ba" Aunty Jamila
tace "Gaskiya kam, tunda xa ki iya daukan takarda ki rubuta masa saki ki sake sa...
Kinga karshen rashin yarda kenan" Nihad ta kara rushewa da kukan takaici, ita fa da
taji ance khalil mijinta sai taji kamar an dau duniyar gaba daya an aza mata a kai,
da dai a dinga furta mata wannan kalmar gwara a nuna mata bindiga kawai a harbeta,
Aunty Jamila bata damu da kukanta ba ta bude cup din da ta gani a rufe ta ga shayi
ne a ciki, tace "Me kika ci yau?" Ta girgiza mata kai hawaye caba caba a fuskarta
tace "Ban ci komai ba" Aunty Jamila ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta fada kan
gado tana rera kuka, Khalil na ganin Aunty Jamila ya mike yace "Za a dauko maki
wani abun ne Aunty?" Aunty Jamila tace "Aa, so nake ko shinkafa da miya ne a samu a
dafa, inji akwai kayan miya a gidan?" Yace "Aa xan fita in siyo yanxu" Aunty jamila
tace "Toh shkkn" Daga haka ta shiga kitchen don daura ruwan shinkafa, Nihad ta
hadiye kukan da take ta jawo jakar Aunty Jamila ta zuge zip din, Wayarta ta ciro
tayi dialing number din Nihal, sai ga number ya fito da suna, aika kiran tayi ta
kai kunne, Nihal na dagawa tayi sallama hade da cewa "Ina yini Aunty?" Nihad ta
wani kyabe baki tace "To ni ce nan ba ita ba" bata jira Nihal ta saurari Nihal ba
tace "Kin ga Number Husnah xa ki turo min ta nan yanxun nan ba wani magana na kira
ki min ba" Nihal tace "Ke me xa ki yi da number Husnar nan ne?" Nihad tace "Wannan
bai shafe ki ba, kawai ki turo min abinda na tambaye ki" Magana Nihal take amma
Nihad ta katse wayar kawai, ba a wani dau lkci ba sai ga number Husnah ya shigo
wayar Aunty Jamila, Nihad ta mike da sauri ta tafi gun jakarta ta bude ta dauko
biro da jotter, A hankali ta dawo ta zauna sbda har sannan bata gama dawowa
dai dai ba tana dan jin jiri, bayan ta kwashe number ta tura takardan cikin pillow
case dinta, sannan tayi dialing number Husnah, yana fara ring Husnah ta daga, Nihad
tace "Ni ce Husnah" Husnah dake cikin kasuwa ta nemi wani shago ta shiga da sauri
ta zauna tace "Nihad ina ta kiran wancan layin da kika kirani da shi jiya naji
kamar anyi blocking, line busy kawai yake sa min, har dare ina trying wllh, to ni
kuma na rasa ta inda xan sameki" Nihad tace "Ai wayar wancan wawan yaron ne, wato
blocking din ki yayi ko?" Husnah tace "Wallahi kuwa, wai yanxu kina nufin daga ke
sai shi a gida daya?" Nihad ta fashe da kuka tace "Wallahi the thought of this na
sa inji kamar in kashe kaina Husnah" Husnah tace "Ki kashe kanki a kan wa?? Aa
wallahi turo min address din gidan yanxu" Nihad tace "Toh ai ban san ko ina ne nan
din ba, amma bari in kira Umma in tambayeta" Husnah tace "Toh maza kirata ko ki
turo min numberta ni in kira" Nihad tace "Toh" Katse wayar tayi ta hau kiran Umma,
yana fara ring Umma ta daga, Nihad tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Jamilan na can
kenan yau?" Nihad tace "Ehh" Umma tace "Toh anjima Amina na nan xuwa maki da wayar
anyi rijistan layin"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login