Showing 27001 words to 30000 words out of 268471 words

Chapter 10 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

khalil da mota, Aminu ya kara bude gate din
Khalil ya shiga compound din da motar sannan yayi parking a parking space Abba dai
ya bisa da kallo, yana sauka daga motar ganin Abba a tsaye, ya nufesa da ledan
pharmacy a hannunsa ya Ι—an risina yace "Ga maganin Alhaji" Abba yace "Wani Magani?"
Khalil ya kallesa yace "Da kace a siyo" Abba yace "Na gaya maka maganin da zaka
siyo min ne?" Khalil ya kalli ledan hannunsa da sauri, kawai sai ya rasa abinda xai
ce, Abba ya amshi ledan ya bude maganin sannan ya bude wayarsa ya shiga message din
da Dr dinsa ya turo masa yaga maganin ne Khalil ya siyo, Abba ya daga kai yana
kallonsa daga sama har kasa, kafin yace komai khalil yayi saurin cewa "Ai ka fada
min sunan maganin, rikewa nayi a kai" Abba dai bai ce komai ba sai kallonsa yake,
Khalil kam ya kasa barin su hada ido, Can Abba yace "Ban gaya maka sunan maganin
fully ba" Da sauri khalil yace "Ka tambayi Habibu a can garinmu akwai wani likita
da ya bude Kemist na siyar da magunguna, na fi shekara takwas ina jire masa shago
yana bani wani abu duk wata, Allah ya bunkasa masa shagon sosai, rasuwa Allah yayi
masa shine yaransa suka rufe shagon bayan sun bada sarin duk magungunan da ya bari,
wannan dalilin ne ma har yasa da Habibu yayi min tayin wannan aikin na taho kano
don ina xaune babu abinda nake, don haka babu wani magani da ban sani ba yanxu haka
sai abinda ba a rasa ba..." Abba yace "Allah ya rufa asiri.... Yau kuma me ya
hadaka da Nihad?" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Bani da masaniyar na mata wani
laifin yau, kawai dai abinda na sani saurayinta ya zo zai bani kudi yau da na kai
ta babban shago xata yi siyayya, sai na nuna baxan amsa ba, shkkn abinda na sani
kenan Alhaji" Abba yace "Kaje xa mu yi magana gobe" Daga haka Abba ya nufi cikin
gida, Khalil ya koma gun mai gadi ya zauna letting out a deep breath. Washegari da
safe Nihad ta leka window ya fi sau goma wai taga ko driver ya fara harhada kayansa
xai bar gidan, amma sai taga ya kai su Sudais da Amina school, kuma da ya dawo taga
ya ci gaba da zama bakin gate, kasa samun sunkuni tayi, ta dau wayarta tayi dialing
number Inna, yana fara ringing ta daga, tace "Ina kwana inna" Inna tace "An tashi
lafiya" Nihad tace "Inna wai jiya ya ku ka yi da Abba da kika xo ne?" Inna
tace "Yace xai yi masa koren kare, ai shi bai san haka yake ba, da kyar ma in ya
kwana a gidan ki bincika ki ga" Nihad tace "Wani bincike bayan ga mutum can a zaune
ina kallonsa" Inna tace "Atoh, Kilan sai yau xai tafi, ai na gaya ma Ibrahim
maganganu masu ta6a xuciya jiya, yace min in sha Allahu xai sallamesa, ina jin sai
yau din xai koresa don jiya kinga ai dare yayi kar ace mutum bai da imani yayi kora
cikin dare" Nihad tace "Sai anjima" Katse wayar tayi ta bude kofar daki ta fito, a
parlor ta hadu da Nihal, Nihal tace "Kinsan in two days time xan koma school" Nihad
ta tsaya ta kalleta tace "Toh ai baki gaya min ba" Nihal tace "Toh yanxu na gaya
maki" Nihad tace "Toh yanxu da Habibu baya nan waye xai kai ki Zaria?" Nihal tace
"Ni ma ban sani ba, sai Abba yayi magana" Nihad tace "Don kinga wannan drivern
sallamarsa xa ayi yau" Nihal dake ta kallonta tace "Okay" Nihad tace "Ko dai har
kinyi shopping din ki?" Nihal tace "Aa probably today or tomorrow, sai yanda Abba
yace" Nihad tace "Okay ki min magana sai mu je har da ni" Nihal tace "Okay, baki da
lectures yau?" Nihad tace "Toh ko ina da lectures ai babu driver da xai kai ni, but
karfe tara nake da lectures" Bata jira cewar Nihal ba ta nufi kofar fita parlon ta
fito compound, Backyard din gidan ta nufa kai tsaye gun tsuntsayenta su Saminu na
gaisheta duk tayi kamar bata ji su ba, tsaye tayi bata motsin kirki tana kallon
cages din birds din da duk suke a bude kuma babu birds din a ciki sai roban
abincinsu da ruwa, duk cages din guda hudu a bude suke har na parrot dinta, Dawowa
tayi da gudu cikin gida tana kallon Saminu dake shara Shafi'u na watering flowers
din gidan cikin tashin hankali tace "Saminu ina tsuntsaye na aka kai min?" Saminu
ya mike da sauri haka Shafi'u da yayi dropping watering can din hannunsa, Saminu
yace "Suna can cikin kejinsu Hajiya" Ta gwalo ido tace "Wani cage din??" Duk suka
nufi inda birds din suke, sai ga su sun dawo suna wuri wuri da ido, Saminu na in
ina yace "Wllh Hajiya ko jiya sai da muka xuba masu abinci da ruwa...." Da sauri ta
juya ta bar wajen ta nufi gun mai gadi cikin rawan murya tace "Aminu ina aka kai
min tsuntsaye na?" Aminu yace "Suna can keji Hajiya" Cikin daga murya tace "Wani
Cage din, abinda naje na tarar a bude babu komai ciki" Mai gadi ya mike da sauri
yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, babu komai ciki?" Shi dai Khalil na xaune
yana danne danne da torchlight phone, Aminu ya nufi inda birds din suke da sauri,
Nihad da har kanta ya sara mata ta bi bayansa gabanta na faduwa, can ba a dau lkci
ba sai ga ta ta dawo tsakar compound ta rusa wani uban ihu ta daura hannu a ka uwa
warce aka yi ma mutuwa, Nihal ce ta fara fitowa a guje ta nufota tace "Nihad what
happened?" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Wani yaje ya bude min cage din
birds dina duk sun gudu, wayyo Allah na na shiga uku, wllh har sun saba dani Nihal,
Parrot din har kiran sunana yake yace good morning" Su Aminu da Saminu dai na can
gefe a tsaye sai wuwwurga idanuwa suke, Umma ce ta fito compound din Mumy na biye
da ita a baya, Hankali tashe Umma tace "Lafiya Nihad, me ya faru?" Nihad ta nufeta
tana kuka sosai ta kamo hannunta tace "Umma wani yayi releasing din min birds dina
duk sun gudu babu ko daya" Umma ta saki salati tace "Waye da wannan danyen aikin,
yanxu babu ko daya wa ennan tsadaddun tsuntsayen da Abbanki ya siya maki" Nihad na
gyada kai cikin kuka tace "Wllh duk sun gudu, bude masu cage din aka yi don su
gudu" Mumy dake kallonta tace "Shine xa ki 6ara baki haka ki daga mana hankali
Nihad?" Umma ta kalli Mumy tace "Haba Maryam, ko don ba ke kika bada kudin siyan
tsuntsun ba, kinsan yanda dabba ke da shiga rai kuwa" Mumy tace "Toh waye ya budesu
har suka gudu? Sannan ita me yasa bata xuwa dubasu a kai kai yaushe rabon da taje
inda suke" Cikin kuka Nihad tace "Wllh ina xuwa dubasu ki tambayi Aminu, kullum sai
naje dubasu" Nihal tace "Toh ko da aka basu abinci ne aka mance ba a kulle cage din
ba" Nihad ta durkushe wajen tana kuka kamar ranta xai fita tace "Ni wllh ko ma wa
yayi min haka Allah ya isa ban yafe ba, Allah ya tsine ma koma waye, Allah ya isa,
shi ma sai an nemasa an rasa wataran yanda na rasa tsuntsaye nahhh" Juyawa Mumy
tayi ta wuce cikin gida, Umma ta dagota tace "Ai ba Allah ya isa xa kiyi ba, koma
uban wa yayi wannan aika aikan dole a ganosa a hukuntasa, ki bar komai a hannuna
kawai" Nihad na shessheka tace "Umma wanda yayi mun haka ya tsaneni ne shi sa yayi
haka kuma sai Allah ya tsine masa albarka ya daidaice, Allah ya isana" Nihal tace
"Ki daina cewa haka baki san ko..." A fusace Nihad ta mike ta hankadeta har sai da
ta kusa faduwa, tace "Shut up plss if have nothing good to say" Bude baki Umma
tayi, sae kuma ta kalli Nihal tace "To wuce ciki" Nihal ta ta6e baki ta juya ta
koma ciki, Umma ta juya ita ma ta bar wajen, Nihad ta hade rai ganin yanda
ma'aikatan gidan ke kallonta, cikin tsawa tace "Uban meye kuke wani kallona
munafukai yan iska, ai har da hadin bakin ku aka sakar min tsuntsaye suka bi
duniya, to ku sani wllh daga yau sbda ku ni xan dinga shiga kitchen sai in ga d'an
iskan da xai xubo maku abinci ya kawo maku, for one week ba ku da abinci wllh a
gidan nan tunda har aka sakar min tsuntsu suka gudu" Tana fadin haka ta juya fuuuu
ta wuce ciki. Da yammacin ranan Farooq ya shigo gidan daga Abuja, Nihad da abun
duniya ya isheta don har sannan Aliyu isn't picking her calls, ga kuma har yanxu
bata ga Driver ya bar gidan ba, kuma babu ma wata alamar da ta nuna xai bari, yana
nan a xaune tare da mai gadi, ko makaranta bata je ba sbda damuwa gashi har test
Husnah tace mata anyi, ta mike daga xaman da take ta yi a parlor ta fito compound
jin motar Farooq, tamke fuska tayi ganin Khalil da Aminu sun nufi Farooq, Khalil ya
fara basa hannu da ladabi, suka gaisa, farooq dai sai kallonsa yake, Aminu dake ta
rawar kafa yana washe baki yace "Ae shine sabon dreban gidan tun bayan tafiyar
Habibu, yau kwanansa biyar ina jin a gidan nan" Farooq ya kara kallon Khalil daga
sama har kasa, sai kuma yace "Driver??" Sai kuma yayi saurin cewa "Ohk maa sha
Allah, ya sunanka?" Khalil yace "Ibrahim" Farooq ya gyada kai yace "Maa sha
Allah...." Tuni Mai gadi ya dau jakar Farooq ya nufi cikin gida da shi, Nihad dake
tsaye balcony ta hade rai tace "Toh ajiye kayi tafiyarka ko ka aikesa ne??" Aminu
ya ajiye jakar ya juya sui sui ya bar wajen, Farooq ya amsa gaisuwan da Nihal ke yi
masa ya nufi Nihad yace "What happened Nihad?" Kamar jira take ta fashe da
matsanancin kuka, yace "Meye haka?" Cikin kuka tace "Ya Farooq wani axxalumin da
baya tsoron Allah ya bude ma tsuntsaye na cage duk sun gudu har parrot din" Bude
baki Farooq yayi yace "Garin yaya?" Ta karasa ta rungumesa tana kuka sosai, ta
gefen ido khalil ya kalleta kafin ya juya ya bar wajen, Farooq ya dago kanta yace
"But how did it happen" Tace "Kawai yau da safe naje basu abinci naga ba komai
cikin cage din" Yace "Ow that's bad, bari anjima sai mu je ki siyo wasu" Ta
marairaice tace "But how will d parrot get to know me just as the old one?" Yace
"Yanda wancan din ya sanki sabon ma haka xai san ki" Daga haka ya kama hannunta
suka shiga gidan tana share idonta. Bayan ta amshi nata tsaraban da farooq ya kawo
mata ta wuce sama xuwa dakinta, wayarta ta dauka ta sake kiran Inna, yana fara ring
Inna ta daga, Nihad tace "Inna har yanxu fa driver din na nan babu inda ya tafi don
ma in gaya maki" A fusace inna tace "Ke raba ni da wani shegen dreba an shigo an
kwashe min yan canjina wai barin gidan da nayi jiya da magariba, kowa sai ce min
yake ba shi bane, to ni na saci abina koko?" Nihad ta tabe baki ta katse wayarta,
sai kuma ta ja tsaki tace "Dama ba a abun arxiki dake..." Da daddare tana dakin
farooq dake kallonta yace "Toh sai in ce masa me idan na kirasa?" A hankali tace
"Kawai hakuri xaka basa a kan abinda driver din yayi masa" Farooq yace "Ba kince
layinsa a kulle yake ba?" Tace "Aa ya ta6a saving numberka a gabana ai, ka tuna
sanda ya kiraka da baka da lafiya?" Yace "Oh, ohk" Daukar wayarsa yayi ta kira masa
number Aliyu yayi dialing, a kashe suka ji wayar, yace "It's switch off" Shiru tayi
bata ce komai ba, yace "Ki je kawai, gobe sai in kirasa" Mikewa tayi tace "To sai
da safe yaya....."


Saura how many page free pages ya kare???

✍🏻
07087865788


πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻




10......

Khalil na xaune yana waya a bakin gate mai gadi ya karaso wajen daga boys quarters,
Khalil ya saka wayar a aljihunsa bayan ya gama, Aminu da har ya xauna ya mike yace
"Aa bari in baka waje ka ci gaba da wayarka...." Khalil yace "Na gama" Aminu ya
dawo ya xauna yana kallonsa yace "Na lura baka son kayi waya a gaban mutane saboda
hayaniya ko?" khalil yace "Haka ne" Aminu yace "Ina can tare da su Saminu muna ta
jajanta lamarin tsuntsayen nan da suka gudu, abun da mamaki da al'ajabi, sun kusa
shekara daya da rabi fa a wajen ba a ta6a nemansu an rasa ba sai yau" Khalil yace
"Ai gwara da suka gudu kar xunubanta ya dinga shafarsu su ma" Aminu ya kyalkyale da
dariya yace "Wllh baka da dama, ni tashin hankalina abincin da tace xa a hanamu, in
an hanamu abinci ya xa mu yi? Ba fa kanta kenan, duk da nasan uwarta baxata yarda
da hakan ba, amma makira ce tana iya biyomu ta kwace idan an kawo mana" Khalil yayi
murmushi kawai, Aminu yace "Amma fa kana bani tsoro da mamaki yanda kake nuna mata
baka shakkarta, akwai wani littafi da na ta6a saurara a shafa labari, kaga yanda ta
sa ka gaba haka? To haka ita ma yarinyar littafin ta sa mutumin gaba yana aiki a
kampanin babanta ita kuma ita ce manaja a kampanin, tayi ta masa walakanci da
rashin mutunci daga baya ta xurma sonsa in gaya maka, To sai...." Dakatar da shi
khalil yayi yace "Me kake nufi?" Aminu ya gyara xama yana washe baki yace "Toh wa
ya sani ko hakan xai iya faruwa wataran, barin taga sambalele me dogon hanci, ka fa
san matan nan ba alkibla garesu ba...." Khalil yace "Ta wahala.... banda abun ka
ina ita ina talaka? Sai dai kuma bata san wani talakan ma ko da kudi aka hadasa
bazai saurareta ba, in dai kamar ni talakan yake wllh ko kallonta baxai yi ba"
Aminu ya gwale ido, sai kuma ya tuntsire da dariya yace "Yanxu kana nufi misali yau
ace maka gata nan ka aura baxa ka aura ba?" Khalil yace "Misalinka ba me yiwuwa
bane har duniya ta nade, don kuwa da in aureta gwara na aura Krista, ko kuma in
dauwama ba auren, kai kasan darajan da Allah yayi ma Ι—an Adam kuwa? To bari kaji ko
da kudi wannan yarinyar baxata tsaya inda budurwata take ba, ga ta dai yar talakawa
kamar ni amma ita wannan fitsararriyar baxata tsaya inda xata tsaya ba wllh...."
Aminu yace "Aa dole xaka ji haushinta wllh, nima kuma ina taya ka jin haushinta
kullum, ji tijaran fa da tayi maka daxu, banda yanayin rayuwa a ina xata ganka har
ta cakume kwalar rigarka tana dungure kanka tana maka munanan xagi, a Ζ™alla ai xaka
bata kusan shekara goma na sani, amma ta maka wnn cin mutunci da tijara gaban Nihal
da kawarta, ba ma wannan ba ji yanda ta dau bahon ruwa gaba daya ta juye maka a
cikin jama'a" Khalil yayi wani Murmushi bai dai ce komai ba, Aminu yace "Ni dai yau
ace min ga ta in aura xan yarda in aureta ko don kudin babanta da kuma halaccinsa,
sai kuma in saita mata xama...." Daga sama har kasa khalil ya kalli Aminu, bai san
sanda yayi dariya ba yace "Kai ta kudin kake kenan" Aminu ya washe hakora, Khalil
ya girgiza kai yana Murmushi, Aminu yace "Wllh ni fa naji dadin bude kejin nan da
aka yi tsuntsayen suka gudu, Allah ne ya bi min hakki na abinda ta min jiya a kan
su" Khalil yace "Ku kuka bar mata tsuntsayen suka kai har warhaka a gidan ai" Daga
haka ya mike ya bar Aminu a wajen xai je yayi alwala kafin a kira isha'i. Nihad na
komawa dakinta taga missed calls din Husnah da yawa, ta xauna gefen gado ta kirata,
yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad ta dinga jin hayaniya tace "Kina ina haka?"
Husnah tace "Mozida suite" Nihad tace "Me ake yi a nan?" Husnah tace "Wllh na manta
ban gaya maki ba shekaranjiya a schl, Abokin saurayin Naf ne ke birthday, nayi ta
kiranki tun daxu baki daga ba dama wai in gaya maki" Nihad tace "Toh ai tun jiya ya
kamata ku gaya min, kuma yanxu kinga dare yayi" Husnah tace "Kashhh, kinga ke
matsalarki kenan Nihad, karfe takwas din ne dare?" Nihad tace "Toh ta yaya ma xa
ayi in taho babu me kai ni, kinsan wawan nan har yanzu Abbanmu bai koresa ba wa
yasani ma ko asiri yayi ma yan gidan duk suke supporting dinsa, Umma ce kadai ke
bayana a ko da yaushe, throughout na xuba ido yau in ga ko xai tafi ban ga ya tafi
ba" Husnah tace "Kinsan abinda zai faru?" Nihad tace "Aa" Husnah tace "Yanxu xa mu
fita mu karo wasu wine, kawai ki san duk yanda xa ayi ki fito mu hadu a wannan
katon supermarket din na anguwarku" Nihad tace "Kar fa ku bar ni inyi ta jira
Husnah" Husnah tace "Haba wani jira, bayan gashi nan yanxu ni da Naff da Sumy za mu
fito" Nihad tace "Okay, bari a shiga masallaci sbda yan sa ido, sai in fito" Husnah
tace "Sai mun hade, kar kuma kice ban gaya maki ba, A abokan celebrant din har da
'ya yan gwamnoni, shiga ce ta kece raini xa ki yi, duk da nasan ki ba wasa" daga
haka Husnah ta katse wayar. Nihad ta mike ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje jin
ana kiran isha'i, ta dauro alwala ta fito da sauri, tada sallah tayi bayan ta idar
ta fito da wani ubansun gown dinta ja wanda Aliyu ne ya siyo mata daga kasar waje
ta saka, ko make up bata yi ba duk ta harhada kayan make up din da turarruka a wani
babban jakarta da xae iya daukan hijab da takalmi da tarkace da yawa, tana jin an
tada sllh sae da ta jira aka yi raka'a daya snn ta fita da sauri bayan ta sa ma
dakinta makulli, tayi surveying parlor don tabbatar da babu kowa a ciki, ko wa na
dakinsa, dama kuma gidan ana magrib kowa ke shigewa daki babu me shiga privacy din
wani, sai kuma washegari idan an hadu wajen breakfast, yawanci da yake a bangaren
Umma dakinta yake, Umma kan shigo taga ko tana waya kuma da wa take wayar, to dai
ta sa ma dakin makulli ko taje xata shiga xata ji sa a kulle, da sauri da sauri ta
fito compound nan ma ta ci sa'a babu kowa, duk suna masallaci, kan kace me ta bar
compound din ta kama hanyar inda supermarket din da Husnah tace ta jirasu yake,
tana isa wajen ko minti biyar ba ayi ba sai ga motarsu Husnah suka dauketa suka
wuce, Husnah tace "Yanxu da Habibu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login