Showing 45001 words to 48000 words out of 268471 words

Chapter 16 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

u quiet?" Ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Hoton nan ai
ya dade" Yace "Karya kike, this is a recent pix, jiya da daddare Naf ta daura a
status na gani nayi saving" Nihad tace "Am serious ba kwanan nan muka yi ba, kuma
ai kafin in maka alkawarin daina fita tare da su ne muka yi hoton nan, ka tambayi
Naf din ma" Yace "Nihad!!" Shiru tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, yace "Saboda
ina sonki da aure ya sa ki ka ga har nake hanaki abubuwan nan da kike, banda haka i
have no business with ur life style, quite alright kinsan i have other babes wa
enda muke tare da su har yanxu, but ban ta6a daga kai na hana yarinya yin abinda
tayi niyya ma rayuwarta ba, ban ta6a hanasu holewarsu yanda suke so ba, but ke
saboda intention dina a kanki daban shi yasa nake hanaki duk wannan shiriritar da
kike, Upon how wealthy my parents are, baxa su ta6a yarda in kawo masu mace mara
kamun kai ince xan aura ba, baxa su ta6a amincewa, kuma ya kamata ki kara yarda
yanxu tunda har na tako tun daga Abuja na xo gidanku to da gaske aurenki nake son
yi, i will neva do that for any lady, sai sai idan dama ina da wata sabgar da xanyi
a kano.... Nihad this should be ur last warning!!!" A hankali tace "Toh kayi
hakuri, in sha Allah hakan baxai kara faruwa ba, i am promising u this" Yayi shiru
yana kallonta, tace "Wllh da gaske nake baxan kara ba" Yace "Toh Allah ya sa..." A
hankali tace "Ameen" Yace "Kince min driver din a nan yake zama" Nihad ta gyara
xama tace "Ehh wllh, yanxu haka ma yana nan, ai yana kofar gida sanda ku ka shigo
layin shi ne ya shiga cikin gidan" Aliyu dake ta kallonta yace "Da muka shigo layin
ne ya shiga ciki?" Tace "Aa ai sannan baku karaso ba" Yace "Ohk where is he now?"
Nihad tace "What will happen now, kawai mu fita sai ka xauna a compound ni kuma xan
je in samesa a can boys quarters da yake zama, ince xan je karbo sako ya xo ya kai
ni, daga nan idan ya fito compound xaka gan shi" Aliyu yace "Kamar wasan yara...
But i urgently wants to see him" Nihad tace "Noo, ta haka kadai xai fito compound
har ka gansa, so now let's go outside" Tashi tayi ta dau bowl din apples tace "Bari
in kai maka wannan ka dinga ci" Daga haka ta fita, ya mike ya bi bayanta suka fito
compound din, can karkashin thatch dake dauke da kujeru ta kai masa apples din ta
ajiye saman table, ya xauna yana kallonta yace "Kin yi kyau" Tayi wani blush tace
"Thank you, bari in je in samesa yanxu" Yace "Ohk" Hanyar Chalet ta nufa ya bi ta
da ido har ta bace, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna hudu saura, Nihad na isa
chalet din ta hade rai tana lekan parlor, isiya ta hango yayi dai dai kan kujera
yana ganinta ya mike da sauri ya fito yace "Kaya xa a amsa Hajiya?" Tace "Ina
wannan yaron?" Yace "Wani yaro?" Tace "Halilu" Isiya ya ษ—an gwale ido a ransa yana
kara nanata yaro da tace, can yayi saurin cewa "Yana can daki" Tace "Toh kaje ka
kirasa Mumy ta bada sako a basa" Juyawa yayi yace "Toh Hajiya" Ya fi minti daya
yana kwankwasa kofar dakin da Khalil yake ciki amma bai bude ba, shi dai yasan baya
baccin rana balle yace, to ko kila yana bandaki, bai yi gigin bude kofar ba tun
ranan da Saminu yayi masa haka yayi cutting din masa warning me lafiya, Bude kofar
aka yi khalil na kallonsa yace "Ya aka yi?" Isiya yace "Aa dama mamarsu Sudais ce
ta bada sako wai xa a gaya maka a waje" Khalil yace "Ohk" Fita yayi tun daga cikin
parlor ya hangota, yana fitowa ya tsaya bakin kofa yana kallonta, Tana yatsine
yatsine tace "Yauwa xaka yi dropping dina in amso sako yanxu, kaje ka dauko makulli
ina jira" Juyawa yayi ya koma ciki ba a dau lkci ba ya fito rike da makullin motar,
yana kallonta ya mika mata, ta hade rai tace "Meye kake mika min makulli cewa nayi
ajiye ni xaka je kayi in amso sako ko kai kurma ne" Ya ajiye makullin saman
matakalan chalet din yace "Toh baxan je ba, wanda ya daukeni aikin ma ya daga min
kafan aiki yau...." Ya juya xai koma cikin parlon yace "Shi saurayin naki ya kai ki
ki amso sakon...." Kasa cewa komai Nihad tayi ta bi sa da kallo, ta fi minti daya
tsaye a wajen kafin ta juya ta koma gun Aliyu rai a bace.... Murmushi Aliyu yayi
bayan ta sanar masa yanda suka yi da Drivern yace "Ohk, there is next time, xan
kuma sauke masa girman kan da ke yaudaransa" Nihad tace "Toh wai dama talaka na
irin wannan girman kan? Wllh sai ka xata fa gidan Ubansa ne nan din yanda yake
abubuwansa" Aliyu dai bai ce komai ba, but all his thought is with the driver, he
seriously want them to meet. Sai kusan karfe biyar Aliyu ya bar gidan tare da
Mujahid bayan sun shiga sun ma Mumy da Umma sallama, Dollar dari biyu ya ba Nihad,
yana tafiya dakin Umma ta fara shiga ta nuna mata kudin, Umma ta ja tsaki tace
"Meye haka, ko dubu dari da hamsin bai kai ba, amma ya bani kunya duk wannan girke
girken da ya kwasa?" Nihad tace "Umma fa a ko da yaushe cikin yi min kyauta yake,
wannan ma cewa yayi inje saloon inyi gyaran gashi da shi fa" Umma tace "Toh Allah
na tuba ina laifin ya baki dubu dari biyu da hamsin ma, duk kudin ubansa sannan
kuma shi ma yace min yana business nasan baxai wuce exportation and Importation
yake ba" Nihad bata kuma cewa komai ba, ta bude karamin jakarta dake hannunta ta
saka kudin. Bayan magrib Khalil da Aminu na xaune kofar gida Aminu sai basa labarin
samarin Nihad yake da irin shigar da suka yi, Khalil dai yana ta sauraronsa amma ba
kallonsa yake ba, Aminu yace "Ina gaya maka wllh turarensu har bakin titi, kai kaga
wani rantsattsen takalman da suka saka kuwa, kana ganin yanda suke tafiya kasan 'ya
yan wasu shegu ne a kasar nan, wato barayin kasar nan" sai a nan Khalil ya daga kai
da sauri yana kallonsa, Aminu ya kwashe da dariya yace "Allah kuwa, barayin
gwamnati kenan" Motar da ke tahowa yasa Aminu yayi shiru suna kallon motar gaba
daya don ta hasko su, Khalil ya mike kamar xai shiga gate, sai kuma aka yi kasa da
fitilar motar....


โœ๐Ÿป
07087865788

Mu hadu after EID in sha Allah, sannan duk ku bi gidan yan uwa da abokan arziki aje
yawon sallah a samo kudin littafin Nihad, don kuwa bayan EID sae dai in baku last
free page inyi mursisi in koma gefe inyi shiru abu na, idan kuma an tattala kudin
yawon sallah an xo an biya littafin Nihad ba wani xancen yin shiru daurawa kawai xa
mu yi abun mu, idan Allah ya ta6a xuciyata ma har page biyu sae mu dinga yi......
๐Ÿ˜๐Ÿ˜œ Amma fa sai na ga kudi kaca kaca๐Ÿ™„
Allah Allah nake in gano wanda Abba ya aura ma Nihad da ja'irar ta suma amma abun
ya ci tura jama'a, to ko dai Aminu ne don shi dama yace zai iya maneji da ita idan
aka hadasa da kudi๐Ÿ˜ฏ


*Shin kina buqatar kayan gyara Wanda zai yi amfani dasu Dan samu nutsuwar ki ke da
oga??*

*To maza Garzaya wurin @Kayanmatan_zuru domin samun mini package me kunshe da
maganin sanyi, maganin niima, maganin Karin dandano, maganin matsi, maganin Kara
kuzari Akan farashi kalilan.....*

_Bugu da Kari akwai kyauta a cikin ko wani package..... Ku tuntube ta a Instagram_
@Kayanmatan_zuru
Ko whatsapp๐Ÿ‘‡๐Ÿป

Wa.me/+2348033308307


๐Ÿ’–๐Ÿ’– *NIHAAD* ๐Ÿ’–๐Ÿ’–



16

โœ๐Ÿป
By _Khaleesat Haiydar_




Aminu ya kalli Khalil yace "Ni wallahi ca nake saurayin nata ne ya dawo da daddaren
nan kuma, kasan fa sai ya iya xuwa ya dauketa su tafi babu wanda xai sani banda ni
da nake bakin gate din nan" Khalil yace "Saurayin wa?" Aminu bai kai ga basa amsa
ba aka bude Driver seat, Hamid ne ya sauko tare da abokinsa Mujahid, a tare suka
nufo gate din, tuni Aminu ya dinga jera ma Hamid gaisuwa uwa maroki, Hamid ya amsa
yana kallon Khalil, sai kuma ya mika masa hannu, Khalil ya kai nasa hannun suka
gaisa, Mujahid dai sai kallon Khalil yake, kauda kai khalil yayi ya fara tafiya
xuwa gun mai gadin daya gidan dake kusa da su, Bayan sun shiga gate Mujahid na
kallon Hamid yace "Waye wannan gayen?" Hamid yace "I don't know, ni ma yau na fara
ganinsa, probably gidansu na nan layin" Mujahid yace "No, he looks a bit familiar,
amma gaba daya na mance inda na san shi..." Hamid yace "Wait" Juyawa yayi ya koma
bakin gate, Mujahid ya bi bayansa, Hamid na kallon Aminu yace "Aminu" Da sauri
Aminu ya nufi gate din yace "Na'am ranka shi dade" Hamid yace "Wanene mutumin nan
da ku ke tsaye da shi?" Aminu yace "Au.. ai sabon dreba ne, kasan Habibu ya bar
gidan nan, Alhaji ya bude masa tafkeken shago ya koma can, shine ya kawo wannan, ai
ya kwana biyu da fara aikin ma" Hamid dai sai kallon Aminu yake, Mujahid yace
"Driver????" Aminu yace "Ehh dreban gidan ne" Mujahid ya kalli Hamid, Hamid ya juya
ya koma cikin gidan, Mujahid ya bi bayansa yace "Seriously kamar na san shi a UK"
Hamid yayi dariya yace "Kai dai kasan me kama da shi a UK" Mujahid yace "Toh amma
kaman is very obvious, kawai dai i can't recall..." Parlon gidan suka shiga, Nihad
na kwance parlor tana danna wayarta, tana ganinsu ta mike tayi wucewarta sama,
Hamid ya bi ta da wani irin kallo, Mujahid ya saki baki shi ma yana kallonta, can
yace "Yarinyar nan fa na feeling kanta da yawa" Hamid yace "A very spoilt Brat,
right from when she is little bata da manners dama, unlike her half-sister
Nihal..." Hamid ya xauna ya dau wayarsa ya hau kiran Farooq don dama wajensa suka
zo. Washegari Monday Nihad ta gama shiryawa misalin karfe tara da rabi ta fito
parlor, gaida Farooq da ya bi ta da kallo tayi, yace "Amma ba da wannan ษ—an iskan
mayafin xa ki fita ba Nihad?" Ta juyo tana kallonsa ta marairaice tace "Yanxu yaya
me ya samu wannan mayafin? Dubi fa ya sauka har bayana fa" Yace "Wuce ki canxa"
Muryar Umma suka ji tace "Ta canxa a saboda kai ke siya mata mayafan? Ko kuma
sabida a jikinka ta yafa?" Ya juya ya kalli Umma, Umma tace "Sharesa kije kiyi
breakfast din ki, ki kama gabanki" Dinning area ta nufa, Umma ta shigo parlon ta
zauna, Farooq bai sake cewa komai ba, Nihad ta gama shan shayin da ta hada sannan
ta mike, ta gefen ido farooq ke hararanta taki yarda ta kallesa ta nufi bangaren
Mumy, a handle din kofar parlonta ta rataye mayafin sannan ta shiga parlon, zaunawa
tayi saman kujera tana kallon Mumy tace "Ina kwana Mumy" Mumy tace "Wato sai kin
gama duk abinda kike sannan xaki shigo ki gaisheni ko Nihad? Nihal bata ta6a kai wa
karfe bakwai bata shigo nan ta gaisheni ba, amma ke sai sanda kika ga dama" Nihad
tace "Toh Mumy ai saboda Nihal a nan bangaren take kwana shi yasa, ni kuma ai ba
nan nake ba" Mumy tace "Toh yayi kyau ki ci gaba, nan gaba ma ki daina shigowa
gaisheni kawai xai fi maki alkhairi" Nihad tayi shiru sai kuma tace "Kiyi hakuri"
Mumy na kallon kayan jikinta tace "Wannan ษ—an iskan dinkin kika yi da tsadadden
atamfar nan kenan?" Nihad tace "Mumy gown ne fa" Sai kuma ta mike tace "Mumy na
makara, yau muna da test" Mumy tace "Ki tabbatar Hijab xa ki sa Nihad" Tace "Toh,
sai na dawo" Daga haka ta fita daga parlon, zare mayafinta tayi ta bar wajen da
sauri sai da ta tafi dakinta ta dau jakarta sannan ta dawo parlor, lekan parlon ta
dinga yi ta ga har lokacin Farooq na xaune, Umma ma na parlon, tana kallon Umma
tace "Umma sai na dawo" Umma na Murmushi tace "Toh Allah ya tsare daughter" Ta saci
kallon farooq tace "Yaya sai na dawo" Banza yayi da ita, bata ko kallesa ba ta
fita, tana isa gate ko kallon Mai gadi da Khalil dake wajen bata yi ba tayi
ficewarta daga gate din tana tafiya cike da isa, ta riga ta dau vow daga yanxu, da
dai Khalil ya sake jan ta a mota gwara taje ta hau adaidaita, tayi canceling ta hau
mota yayi driving dinta. Mai gadi na mata Allah ya tsare ko kallonsa bata yi ba
balle ta amsa masa, kamar yanda bata kalli Khalil ba shi ma haka ba kalli inda ta
bi ba, Mai gadi yace "Ikon Allah, yau kuma da kafa xa a makarantar" Khalil yayi
murmushi kawai bai ce komai ba. Nihad na isa makaranta har wajen karfe sha daya
basu da niyyar shiga lectures da su Husnah suna xauna Cafeteria suna ta hira
abunsu, kaf Clique din sun canxa xuwa latest iphone da ya fito ko wata daya ba ayi
ba amma banda Nihad, kuma kaf dinsu babu warce iyayenta suka siya ma, sun dai yi
kame kamensu sun samu waya, Naf tace "Amma nayi mamaki kice ke baki da just 250k da
xaki cika ki canxa waya, to shi wannan saurayin naki Aliyu meye amfaninsa?" Nihad
tace "Aa ni dai baxan tambayesa ba, kuma dama ni bana tambayarsa komai" Sai kuma ta
dau wayarta tayi dialing number Abba ta saka handsfree tayi masu alama su yi shiru,
yana fara ring Abba ya daga yace "Hello dear" Shessheka ta fara yi tace "Abbaa"
Daga daya bangaren Abba yace "What happened?? Me ya sameki?" A hankali tace "Abba
ina shigowa makaranta xan sauka daga mota wayata ta fadi screen din ya fashe gaba
daya" Abba yace "Subhanallah" Nihad tace "Yanxu ga shi wayar ya dauke" Abba yace
"Hasbunallah, baya yi yanxu wayar kenan?" Tace "Ehh baya yi" Abba yace "Toh abinda
xai faru idan kin koma gida ki ba wannan driver din ya je inda ake gyaran waya a
gyara ko nawa ne ma sai ya kirani ya sanar min" A hankali Nihad tace "Toh" Abba
yace "Shikenan, Allah ya tsare gaba" Nihad tace "Ameen, Nagode Abba, sai anjima"
Daga haka ta katse wayar tana kallonsu Naf dake sauraron Abba gaba dayansu, suka
kyalkyale da dariya suka ce "Gaskiya ne er daddy" Nihad tace "Toh amma me yasa xai
hadani da wannan fitsararren yaron, this plan isn't going to work idan da shi fa"
Husnah ta cije yatsa tace "Kashh, yau ga ranan Habibu, to wai shi wannan din dama
har yanxu ba a koresa bane?" Nihad ta tabe baki tace "Toh mayen xai tafi ne?
Wallahi duk abubuwan da nake masa ya ki tafiya sai ma gyara xama da yake yi a gidan
yanda ku ka san gidan ubansa, yau ma fa wani gaye ne ya kawo ni schl don nace baxan
sake shiga mota daya da drivern nan ba, ina tsaye busstop din anguwanmu sai ga benz
din gayen, shine ya rage min hanya har cikin makarantar nan, amma da da adaidaita
Sahu xa ku gan ni ae" Zully tace "Aa to baki yi masa yanda xai bar gidan bane, da
nice tuni xan masa check out wllh, wannan ai karamin kwari ne" Nihad tace "Kai
Zully wasu fa mayu ne, shi wannan a maitan ma yayi nisa, gaba daya na lura bai son
barin gidan ne, tunda yana cin me kyau ya sha me kyau" Husnah tace "Kawai shiryawa
xa mu yi mu je har gidan mu ci maki ubansa mu masa tijara" Nihad ta kyalkyale da
dariya tace "Yauwa don Allah ku shirya ku zo dama 24/7 yana xaune bakin gate da mai
gadi, amma fa you girls should dress decently kun san halin Mumy" Husnah tace
"Wannan ba matsala bane duk xa mu sa Hijab a jaka, xuwa Thursday xa mu zo don ranan
ne muke da time, gobe akwai club da xa mu je, Wednesday kuma xa mu je wani picnic,
yauwa ki shirya mu je na ranan Wednesday din nan ba da daddare bane da yamma za
ayi" Nihad tace "Ohk drop location" Throughout ranan babu wanda ya je kusa da dept
balle ya shiga lectures, daga karshe ma fita suka yi xuwa wani babban eatry
saurayin Zully xae siya masu abinci. Da yamma bayan la'asar Khalil na tsaye bakin
gate yana sauraron Aminu dake basa labarin wani abokinsa da suka taso tare, lkci
daya yayi mahaukacin kudi ya guji kowa daga karshe aka gano ashe kidnapping yake,
Aminu dake ta kumfar baki yace "Har yau xancen da nake maka Inusa na dogon gida,
yau kuma shekara uku kenan...." Bude gate aka yi duk suka juya, Inna ce ta shigo
gidan da sallama tana rike da jakarta me kyau, Aminu ya mike da sauri yana washe
hakora yace "Barka da zuwa Hajjaju" Inna ta ษ—an kalli Khalil ta tsaya daga bakin
gate din tace "Yauwa Aminu, yan gidan basa nan ne, naji ko ina shiru?" Khalil ya
karasa ya gaisheta da ladabi ta kallesa tace "Auu, ni ai ban ganka ba Aminu kadai
na hango, sannu ya kake" Khalil yace "Lafiya lau, Ya gida Hajiya?" Tace "Toh
Alhamdulillah, yanxu Hamid ya ajiye ni a mota ko gama sauka ban yi ba ya juya yayi
wucewarsa, gashi a can bakin titi in gaya maka naga wani apple me kyau ana siyarwa
amma ya ki tsayawa in taya balle in siya, mun baro wajen can farkon shigowa anguwar
nan wallahi" Khalil yace "Toh bari a dubo maki" Inna tace "Yauwa maza kaje kaji
nawa nawa ne ka dawo ka gaya min" Fita gate din yayi, Inna ta bi sa da kallo, sai
kuma tayi kasa da murya tace "Wai dama har yanzu basamuden nan na gidan nan Aminu?"
Aminu na danne dariyarsa yace "Yana nan Hajiya" Inna tace "Toh saboda me? Shi
Ibrahim din ne ya bar sa ya ci gaba da zama a gidan ko ko? Yau naga fitina" Aminu
yace "Ae ba shi da matsala fa Hajiya, kowa a gidan ya shaida, kullum nan muke yini
tare da shi" Inna tace "Aa rufe min baki Aminu, wllh in nice a gidan nan da ido
daya zan dinga bacci" Tayi kasa da murya tace "Irinsu ne fa ke aikata mugayen
abubuwa a duniya yanxu Aminu, ko kai baka ga siffarsa ba, wannan idan cacan baki ya
hadaka da shi sai dai ya daga ka ya nana shege da kasa, to bai cuceka ba? Da nayi
niyyar kwana amma gaskiya baxan iya ba da wannan mutumi a gidan nan, ina dalili"
Dariya kawai Aminu yake, Inna tace "Bari in shiga mu gaisa da su kawai inyi
fitowata in wuce" Daga haka ta wuce cikin gidan, tana zaune parlor da Mumy dake ta
sauraronta Khalil yayi sallama bakin kofar, Inna tayi kasa da murya tace "Kaddai
shi ne? Har nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login