Showing 216001 words to 219000 words out of 268471 words

Chapter 73 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

bata dinka ba, yawancinsu super ne da
holland, can kasan akwatin ta ciro wani envelope, sojan ya dauki makeken sarka da
dankunnen gwal da zobe sun kusa biyar dake kasan akwatin, Tana zare ido tace
"Takardu fa ku ka ce, kuma ga su" Sojan ya fizge envelope din hannunta ya mika ma
Janar ya amsa ya bude ya ga takardun gida ne har hudu, Ya mayar cikin envelope din
yace "Akwai saura..." Hassana ta fashe da kuka tace "Ni su kenan wllh wllh, ba wani
takardan gida..." Wani naushi sojan kusa da ita ya kai mata a baki, Janar ya mika
masu envelope din yace "Ku mayar ku kulle akwatin ku fitar min da shi" Suka yi
yanda yace, Janar na kallon Hassana yace "Na baki awa daya ki tattara komai naki ku
bar min gidana dake da yaranki gaba daya" Ta fashe da matsanancin kuka ta durkusa
kasa tace "Yaya ka mance tsakanina da kai ne? Kanwarka ce fa ni, Yanzu duk inda
mahaifiyarmu take zata ji dadin wannan walakanci da tijaran da ka min Yaha" Yana
kallon sojojin strictly yace "Awa daya za ku jira ta hada komai nata ta bar min
gidana ita da yaranta, sannan ku yi alerting sojojin anguwan she is no longer
welcome in my house...." Yana gama fadin haka ya juya ya fita, babu bata lokaci
Aunty Hassana ta hau hada kaya tana kuka sosai kamar ranta zai fita, ga gwala-
gwalan nata ma duk suna akwatin, sai ma sun bude wani zip din za su gansu kaca kaca
sun yi na miliyan 40, duka duka account din nata ko dubu dari bakwai bai kai ba, ta
ina zata fara???? cikin minti arba'in ta dau iya abinda zata iya dauka a dakinta,
ta sa su Sajida ma duk suka hada kayansu suna kuka, sojojin suka tasa keyarsu aka
fitar da su daga anguwan gaba daya suka yasar da su bakin titi....




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via

07087865788



Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son
sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da
xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan
turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba.
Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu
xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da
hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls
guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda
hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls
guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din
da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman
in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800,
6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar
maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰

64

Bayan kwana biyu da tafiyar Khalil aka fara shirye shiryen biki a gidan, kai da
ganin irin IV din da aka buga kadai kasan bikin na masu kasar ne, kusan kullum Mami
sai ta fita for the wedding preparation, biki ne na gani na fada ake shirin yi, a
kwana a tashi dae har bikin ya rage saura sati daya, tuni Noor ta koma gidansu
Nadeeyah ta tare a can su ma suna nasu shirin da sauran kawayen Nadeeyah. Yau ma
kamar kullum Mimi ta gama shirin tafiya school ta juya tana kallon Nihad da ba ta
da wani aiki sai kwanciya all this days a daki, a ko da yaushe kuma zaka ganta babu
walwala tare da ita, she look so dull, abincin ma wani lokacin sai Mimi tayi mata
da gaske take dan tsakura, all this while kuma duk kiran da Khalil zai yi ma Mimi
ta bata waya, sai dai ta amshi wayar amma baxata masa magana ba don Mimi na mika
mata wayar take fita daga dakin ta bata space, har ya ma gaji da kiran ya daina,
wayarta kuwa dama ta kashe ta ajiye kusan sati biyu kenan, a daddafe ya iya yin
kwana sha biyu a Jamus don gaba daya hankalinsa yayi gida ba kuma wajen kowa ba
wajen Nihad, rashin maganan da take masa via phone call ya damesa sosai.... Mimi ta
ajiye handbag dinta ta zauna gefen gado tana kallonta tace "Nihad me yasa baki
maganar makarantarki ne yanzu?" Nihad ta daga kai ta kalleta amma bata ce komai ba,
Mimi tace "Soon za ki ji ance exams fa, for almost 2 month now baki shiga lectures
ba, kuma naga ma kamar makarantar ne baki so ko??" Nihad dai bata ce mata komai ba,
Mimi ta mike ta dau jakarta tace "Sai na dawo, zan bar maki breakfast dinki a
parlon Mami ba sai kin je downstairs ba" A hankali Nihad tace "Allah ya tsare" Mimi
na fita ɓangaren Mami ta tafi zata sallameta, Mami na kallonta tace "Breakfast din
fa?" Tace "Ehh xan yi before leaving" Mami tace "Toh ita fa?" Mimi tace "Idan ta
fito zata yi, she is still lying down, zan aiko Bilkisu ta kawo mata nata nan
parlon" Kafin Mimi ta tafi ta sa mai aikin Mami ta kawo breakfast din Nihad nan
parlon Mami ta ajiye, wajen karfe tara Mami ta fita zuwa wajen wata kawarta warce
ita ce tayi assigning lafiyayyun chefs da za su yi girki na bikin, sae kusan karfe
sha biyu ta dawo gida bayan an mata calculation din nawa kudin abincin zai kama
gaba daya kuma ta tura masu, don tuni Janar ya tura mata a account dinta, Babu kowa
gidan yanxu sae ita da su Mimi da Nihad sannan mai aikinta, Hanan kuwa na can gun
uwarta, Janar ma yau kwanansa uku da tafiya India for checkup, the house is so
empty duk da dama can gidan babu hayaniya, Mami na isa ɓangarenta taga breakfast
din Nihad har sannan a ajiye bata shigo ba balle ta dauka, mamaki ne ya cikata ta
fita zuwa dakin Mimi, sae da ta kwankwasa kofar dakin sannan ta bude, kwance ta
sameta saman gado ba kuma bacci take ba, Nihad na ganin Mami ta mike zaune a
hankali, Mami tace "Me yasa baki shigo kinyi breakfast ba?" ta sunkuyar da kanta
bata ce komai ba, Mami tace "Toh tashi ki fito kiyi...." Nihad tace "Toh" Juyawa
Mami tayi ta fita, ta kira Bilkisu ta sa ta fita da Breakfast din tace "Make a new
one immediately" Bilkisu ta amsa da ladabi sannan ta dau abincin ta fita... Ba a
dau lokaci ba Nihad ta shigo parlon Mami tana jan kafa..., Hijab ne har kasa
jikinta, Mami dake zaune parlon tana kallonta tace "Bari ta kawo maki wani yanzu"
Nihad tace "Toh" Zata zauna kasa Mami tace "Zauna saman kujeran" Ba musu ta zauna
kan kujeran ta jinginar da kanta jiki, Mami dae sai kallonta take, can ta ci gaba
da Chatting da sister dinta Hamida da zata taso jibi daga Yemen tare da
mahaifiyarsu da kanninta mata biyu, tana sanar mata abinda zata taho mata da shi
daga Yemen, Nihad na ta zaune har bacci ya É—an fara daukarta Bilkisu ta shigo ta
ajiye tray din hannunta a kusa da ita sannan ta fita, Mami tace "Shiga bedroom za
ki ga carpet karami ki dauko sai ki zauna a kai, zuwa anjima za a kawo na parlon
nan dazu aka fitar da wanda ke kasa" Nihad ta mike ta nufi bedroom din Mami, juya
mata taga parlon ke yi, tayi baya zata fadi Mami dake kallonta ta mike da sauri,
amma tuni har ta kai kasa, Mami ta nufeta da hanzari ta dagota zaune tana kallon ta
da mamaki tace "Are you okay?" Kasa cewa komai Nihad tayi don har sanan kanta juya
mata yake, Mami ta dagota tsaye tana rike da ita ta kai ta bedroom din dinta, ta
taimaka mata ta zauna gefen gadonta tace "Sannu" Ita dai Nihad bata ce komai ba sai
sauke numfashi take a hankali, Mami ta juya ta fito parlor, shayi me kauri ta hada
mata a mug ruwan zafin ma ba da yawa ta zuba ba tayi diluting da Table water sannan
ta koma dakinta, kwance ta gan Nihad gefen gadon idonta a rufe, Mami ta ajiye mug
din shayin dake hannnunta ta dagota tace "Tashi ki sha shayin, it's already noon"
Nihad ta mike zaune a hankali, Mami ta dau mug din ta mika mata, amsa tayi ta kai
baki ta fara shan shayin. Mami ta juya ta fita daga dakin, ko rabin shayin Nihad
bata sha ba ta ajiye da sauri tana toshe bakinta, bata san sanda ta zabura ta mike
tsaye ba har ta nufi kofa ganin aman ya riga ya taho mata kawai ta dawo ta shige
bandakin Mami, nan ta dinga kwarara amai, Mami dake parlor ta mike da sauri ta koma
dakin don a bude ta bar kofar shi yasa ta juyo kakarin amanta, bandakin ta shiga ta
dafata tana kallonta tace "Sannu" Nihad ta kasa cewa komai, bayan ta wanke bakinta,
Mami ta cire mata Hijab din jikinta sannan ta koma dakin da ita ta zaunar da ita
gefen gado tana mata sannu, Nihad ta kasa ci gaba da zama kawai ta kwanta gefen
gadon, Mami ta koma bandakinta don ta gyara, ko da ta fito bacci ta tadda Nihad
take yi, ta fita parlor ta dau wayarta ta kira Dr Rukayya bayan sun gaisa tace mata
ta zo gida zata duba mara lafiya. Mami na ta zaune parlonta bayan minti talatin da
kiran Dr Rukayya aka bude kofar parlon, ta daga kai tana kallonsa, ya karaso ciki
da sallama, ya zauna saman kujera ya cire face Cap dinsa sannan ya gaisheta, Mami
ta amsa tace "Ya hanya?" Yace "Alhamdulillah, ya gida" Tace "Lafiya lau" Tace "Dama
tafiyar ta sati biyu ce?" Ya É—an shafa kansa yace "Eh" Mami tace "Ohk" Yace "Naga
ba kowa a gidan Mami" Mami tace "Mimi ta tafi makaranta, Noor na gidansu Nadeeyah"
a hankali Khalil yace "Ok...." Mami bata sake ce masa komai ba, bayan few seconds
yace "What about Hanan?" Mami tace "Washegarin ranan da ka tafi ita ma ta tafi
kaduna" Yace "Ohk" Suna ta zaune parlon for almost 5 minutes, bai ce mata komai ba
ita ma haka, Wayarta ne ya fara ring tana dubawa taga Dr Rukayya ce, Mami na dagawa
ta sanar mata tana compound, Mami tace "Ohk, bari Bilkisu ta karaso ciki da ke"
Mami ta katse wayar ta kira Bilkisu, shi dai kallon Mami kawai yake, ya rasa ta ya
zai ce mata ina Nihad, don yana shigowa gidan dakin Mimi ya fara nufa amma yaga ba
kowa ciki, ya koma visitor room dake bangaren Mami nan ma yaga ba kowa ciki, har
Mimin ya kira yaji inda suka je amma tace masa ai ita tana makaranta Nihad kuma na
gida ta bar ta, Mami na gama waya da Bilkisu ta ajiye wayar a gefenta, Jinginar da
kansa yayi jikin kujera yana ta kallonta, Mami ganin kallon da yake mata tace "Toh
sai ka tashi kaje kayi wanka ka nemi abinda zaka ci ka bani waje ko??" A hankali
yace "I am okay" Mami tace "Toh ka bani waje za a shigo min da bakuwa yanzu" Cike
da karfin hali yace "Mami tare suka fita da Mimi ne?" Mami tace "Wa?" Sai kuma ya
kasa cewa komai, Mami tace "Baka da number Mimin ne?" Yayi shiru yana kallonta,
bata sake kallon inda yake ba har Bilkisu ta shigo da Dr Rukayya, Khalil ya dinga
kallonta, Ta gaida Mami da ladabi, Mami tace "Sannu da zuwa Dr" Dr Rukayya ta kalli
Khalil murmushi kwance fuskarta tace "Barka da rana ranka shi dade" Yace "Longest
time Dr" Tace "Ai kam ka buya" Mami ta mike tace "Mu je ciki Dr" Dr Rukayya ta bi
bayanta zuwa bedroom dinta, Khalil ya bi su da kallo har suka shiga, kasa daurewa
yayi ya mike ya bi bayansu, Tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallon Nihad dake
bacci saman gadon Mami, Dr Rukayya dake duke dab da ita tana kallonta ta kai
hannunta a hankali goshinta to feel her temperature, sosai taji jikinta yayi zafi,
Dr Rukayya ta mike tana kallon Mami tace "Tun yaushe ne bata da lafiyan?" Mami tace
"I just noticed today, da yake ba bangaren nan take ba tana dakin Mimi ne" Dr
Rukayya ta gyada kai tana kallon Nihad da ta bude ido a hankali tana kallonsu, Mami
na kallonta tace "Ya jikin?" Kai kawai ta iya gyada mata, Mami tace "Toh ki dubata
Dr bari in baku waje" Tana fadin haka ta juya ta bar wajen, Khalil bai bari sun
hada ido da Mami ba ya juya da sauri shi ma ya bar bakin kofar dakin, ko da ta
shigo parlon bata gansa ba ya koma can first parlor, Dr Rukayya ta duka tana kallon
idon Nihad da kyau, ta dago hannunta tana kallon fingers dinta, calmly tace "When
last did u see ur period?" Nihad tayi shiru, sai kuma ta buda hannu alamar bata
sani ba, Dr Rukayya tace "Akwai abu a bakin ki ne da baki son bude bakin kiyi
magana Dear" Nihad ta girgiza kai cike da karfin hali tace "Aa" Dr Rukayya tace
"Good, now tell me how you r feeling?" Nihad ta jingina da gadon cikin sanyin murya
tace "Ina jin jiri idan na tashi, sannan in na ci abu sai in fara jin amai, i am
feeling dizzy..." Shiru tayi daga haka, Dr Rukayya tace "Tun yaushe kika fara jin
hakan?" Ta É—an yi shiru sai kuma tace "Not too long" Dr Rukayya tace "Good, koma ki
kwanta" Nihad ta kwanta a hankali, Dr Rukayya ta juya ta fita daga dakin zuwa
parlor, zaune ta tadda Mami ita kadai a parlon, ta zauna saman kujeran dake kusa da
Mami tace "Hajiya ina mijinta kuwa?" Mami tace "Shi kika tarar dazu ai da kika
shigo" Ta É—an buda ido da mamaki tace "Wai Dr Khalil?" Mami tace "Eh" Dr Rukayya
tace "Maa sha Allah, ashe surkarki ce wallahi da na ganta fara na zata ko yarinyar
er uwarki ce, maa sha Allah that's nice, ashe Khalil yayi aure ba labari" Mami dai
kawai ta É—an yi murmushi, Dr Rukayya na dariya tace "Yana matsayin likita amma
baxai duba matarsa ba sai an kira mata likita daga waje, ko rudewa yake... Kinsan
haka wasu likitocin suke" Mami tace "Toh yanzu dai me ke damunta?" Dr Rukayya na
murmushi sosai tace "Congratulations
Hajiya, u are going to be a grandmum soon, duk da na so sai anyi test kafin in
sanar maki but duk wani symptoms na ciki na gani a jikinta, ur in-law is pregnant"
Mami ta dinga kallonta ko kiftawa babu, can ta sauke idonta a hankali tace "Toh
Alhamdulillah" Dr Rukayya tace "Yanzu zan dauko Pt test strip a motata, don dake
tabbatar da hakan" Mami tace "Toh" Daga haka ta nufi kofa ta fita, ba a wani dau
lokaci ba sai ga ta da Urine specimen container da pt test stip, ta shiga dakin
Mami ta gaya ma Nihad yanda zata yi amfani da shi sannan ta kama hannunta zuwa
bandakin don ta kasa tsayawa sbda jiri, Dr Rukayya na ta jiranta a dakin bayan
minti shidda ta bi ta zuwa cikin bandakin, murmushi tayi ganin test din was
positive, bayan sun fito ta fita tayi discarding strip din da container, ta dawo
parlor ta sake congratulating Mami da ke zaune looking speechless. Bayan fitar Dr
Rukayya ta siyo drugs da alluran da zata ma Nihad, Mami dai na ta zaune parlor ta
kasa ma shiga ciki ta duba Nihad din, can dai ta mike daga karshe ta shiga cikin
dakin.... After Zuhur Khalil ya sake dawowa bangaren Mami, zuwa lokacin Dr Rukayya
tayi ma Nihad duk abinda ya kamata ta wuce, Babu kowa cikin parlon amma ya kasa
karasawa cikin bedroom din don bai san ko Mami na ciki ba, ya tsaya for almost 2
minutes contemplating kafin ya karasa ya tura kofar a hankali, Nihad ce kawai
kwance dakin tana bacci restlessly, ya sauke wani ajiyar zuciya ganin Mami bata
ciki ya karasa da sauri, ya zauna gefen gadon ya kai hannu forehead dinta yana kare
mata kallo keenly, he sat there looking at her for almost 2 minutes, sai kuma yayi
wani murmushi dai dai nan ta bude ido a hankali don baccin yin sa kawai take don
dole, All her body is just weak, gashi ko tunanin abinci tayi sai taji zuciyarta na
tashi amai na taho mata, Daure fuska tayi ganinsa, yayi kasa da murya yace "How are
you feeling?" Ta kara hade rai zata juya masa baya ya dagota zaune, yayi kasa da
murya cike da damuwa yace "To me na maki kike ignoring magana da ni for two weeks
now?" A fusace tace "Ni ka kyaleni don Allah" Yace "Ki gaya min laifin me nayi?"
Tace "Toh ai ba dole sai da ni kawai zaka yi waya ba tunda kana da warce ita ma
zaka iya waya da ita" Kallonta yake yi da mamaki, ta fizge hannunta zata juya masa
baya ya jawota ya rungumeta jikinsa yace "But ai ke kadai ce matata, ko da wacece
zanyi waya ai ba matata bace tunda ba aure tsakaninmu" A hankali ta sakar masa kuka
ya lumshe ido thinking of what to say to her don sarai ya gama gano ta, dai dai nan
aka bude kofar dakin kafin yayi saurin saketa har Mami ta shigo, Nihad taji kamar
kasa ya bude ta shige kawai ta huta, Ya mike da sauri ya kasa dago kai balle su
hada ido da Mami, sai kuma ya nufi kofa, Mami ta bi sa da wani kalloz a takaice
tace "Go back and take her to ur room" Tana fada masa haka ta juya ta bar dakin,
sai a sannan ya dago kansa yana sosa keya, can kuma ya koma wajen Nihad yace "Tashi
mu tafi" Wani kallo tayi masa tace "Wallahi baxan je ba ai ni ba fitsararriya bace"
Ya wara ido yace "Ni ne fitsararre?" Komawa tayi ta kwanta ta juya masa baya, yayi
murmushi ya juya ya fita daga dakin. Sanin Mami is watching his move ya sa ya
shirya bayan la'asar ya tafi gidansu Nadeeyah... Yana ta zaune compound din gidan
sai ga ta ta fito, shi dai ya ma rasa gane kanta for almost 3 weeks now, ta zauna
saman kujera without looking at him tace "Ina wuni" yayi shiru yana kallonta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login