Showing 9001 words to 12000 words out of 268471 words
ayi kenan" Saminu da Shafi'u ne suka fito daga dakunan su, Isiya yace
"Toh ai parlon ma na da girma sai kawai ya maida nan din wajen kwanansa ko" mutumin
ya gyada kai yace "Ohk to shikenan" Isiya yace "Yauwa" Aminu ya kalli su Saminu
yace "Sabon direban gidan ne shi ma kuma nan xai xauna, sunansa Ibrahim kun ga
sunan Alhaji ne...." Saminu yace "To sannun sa da xuwa" Tuni ya juya ya fita daga
parlon ya bar mai gadi, Aminu na ganin haka ya bi bayansa da sauri... Suna tafe mai
gadi yace "Amma kasan da nauyi mu dinga kiran sunan Alhaji gatsau, baka da wani
sunan ko inkiya da xa mu iya dinga kiranka da?" kallonsa yayi yace "Khalil
Mahaifiyata ke kirana" Aminu yace "Allah sarki, to ai mu ma sai mu ce khalil din,
suna me dadi kamar na larabawa wllh" Bayan sun koma mazaunin mai gadi sun zauna,
Mai gadin ya kallesa yace "Yanxu kawai kayayyakin ka xaka je gida ka debo, aikin
naka ma fa ba wani me wahala bane, kaga yan makaranta motar makaranta ce ke xuwa
daukansu da safe, Yan matan nan biyu kuma daya a zaria ma take karatu, dayar ce ke
karatu a nan, ita warce ke karatu a nan din sai ta kai karfe biyu ma bata tafi
makarantar ba, Alhaji kadai xaka ajiye karfe tara gun aikinsa, ban ki ba dae Nihad
don gantali gareta kamar ta ci kafar kare, kuma sae ta fake da makaranta, a takaice
dai kai Alhaji wajen aikinsa da safe shine ainahin aikinka sauran duk masu sauki
ne" Khalil da har ya gaji da surutun Aminu ya gyada masa kai kawai, for the next
30mins Aminu bai yi shiru ba, Khalil har ya daina tanka masa don ya ma yi nisa a
tunanin da yake, dai dai nan Alhaji ya fito, Mai gadi yayi kasa da murya yace "Da
alama yau baxai je motsa jikin ba kenan tunda har gashi sha daya ta yi" Sai kuma ya
mike, Khalil ma ya mike yana kallon Alhajin a bit surprised at who is standing next
to him, Khalil yayi kasa da murya yace "Yan makarantar har sun taso ne?" Mai gadi
ya kalli Khalil da sauri yace "Ka je yana maka magana ne" Khalill ya nufi Alhajin
da hanzari, Alhaji yace "Mu je xaka ajiye mu 3 streets away from this" Khalil yace
"Toh" Motar da yayi parking bayan ya ajiye yan makaranta ya nufa, Abba yace "Wancan
motar ba wannan ba" Khalil ya tafi gun motar da Abba ya nuna masa, Bayan sun fita
gidan Mai gadi ya kulle gate, driving Khalil yake a hankali, lkci lkci yake kallon
Nihad dake zaune bayan mota da Abbanta tana danna wayarta. Ganin Khalil a layin da
Alhajin yace ya ajiye su, Alhaji Ibrahim yayi mamaki sosai, don shi ya ma mance ba
Habibu bane ke jan sa, bai yi masa kwatancen inda xai kai su ba ya dai ce masa 3
streets.... Ganin yayi slow down Alhaji Ibrahim yace "Noo ci gaba da tafiya, gida
na uku xaka tsaya" Dai dai gidan Khalil yayi parking, Alhaji yace "Kayi horn kawai"
yana yin horn mai gadi ya leko ganin motar ya koma ya bude gate din da sauri,
Khalil ya shiga ciki ya samu waje yayi parking , Alhaji Ibrahim yace "Maa sha
Allah, kayi jirana har in fito" Khalil yace "To Alhaji" Nihad ta sauka ta daya side
din wayarta kare a kunnenta, Alhaji Ibrahim ya sauka ya nufi entrance din gidan, Ta
side mirror Khalil ke kallonta amma sai yaga kamar wannan fara ce ai, Nihad dake ta
xagaye da waya a kunnenta da sunan she is making call, whereas she is not kawai
bata son Abba yace su shiga ciki tare ne, tana ganin Abban nata ya shiga gidan ta
turo baki ta tafi can karkashin wani Thatch dake compound din wanda aim dinsa wajen
shan iska, xaunawa tayi a wajen. Khalil ya sauka daga cikin motar ya tafi gun mai
gadin gidan suka gaisa, Mai gadin na kallonsa yace "Ko kai ne madadin Habibu"
Khalil yace "Eh nine" Mai gadin yace "Maa sha Allah" Xaunawa khalil yayi yana bin
compound din da kallo, wanda shi ma yayi haduwan karshe, ya d'an juya ya kalli Side
din da Nihad take, she was so engrossed with what she is doing on her phone....
U can contact me directly via👇🏻
✍🏻
07087865788
4
💖💖 *NIHAAD*💖💖
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
~~~~
Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga manya manyan fans dina irinsu.. Fatima Arebia,
Aisha Abubakar, Maman Shukrah (Banatsapparel and more) Khadijah Dutse, mu'azatu😂,
infact da duk wani member na Khaleesats palace da ban ambato ba a nan ku sani ina
son ku har raina, ina yin ku, ina maku fatan alkhairi Allah ya dafa maku a duk
lamuranku, My respect to many of my fans da suka fara patronizing Nihad without
even waiting for the end of free pages, yawancin ku ba biyan littafin ku ka yi ba
kyauta ce kawai kuke min, kuma ina alfahari da ku, ina maku fatan alkhairi da
Zuri'a dayyiba. Allah ya bar xuminci, ya saka da Alkhairi ya karo maku yalwataccen
arxiki, na kuma sadaukar da page din nan gare ku.
Bayan minti talatin da biyar Nihad ta gaji da jiran Abbanta don har sannan bai fito
daga gidan ba, ga kiran da Husnah ke ta yi mata taki dagawa don bata son tace mata
bata gida tasan baxata jira ta ba, kallon agogon dake makale hannunta tayi ganin
sha biyu har da minti goma ta tashi daga kan kujerar da take ta nufi khalil, Babu
yabo babu fallasa tace "Hey xan koma gida kayi dropping dina yanxu" Sai da ya fara
kallon mai gadi dake gefensa kamar dai da mai gadin take, ta daure fuska tace
"Malam da kai fa nake?" Sai a sannan ya kalleta ya d'an kara kunnensa gaba yace
"Na'am" Rasa ma me zata ce masa tayi saboda bakin ciki, har sannan fuskarta a daure
tace "Ina ga dai kana da matsalar ji, dalla malam ka tashi ka maida ni gida" Yace
"Naga ai Alhajin bai fito ba" Tana masa wani kallo tace "Eh na fi ka sanin bai fito
ba" Yace "To kar ya fito ya tarar bana nan" Ta rike kugu cike da masifa tace "Sai
ka maida ni, idan ka maida ni xaka iya dawowa idan ka ga dama" Ya dauke kai yayi
shiru bai ce komai ba, shi dai mai gadi sai mazurai yake da ido babu damar ya kwaba
ma khalil, shi tsoronsa ma kada wnn ɗan abin ya sa ya rasa aikinsa, yana ga kamar
Khalil bai ta6a aiki gidan masu hannu da shuni bane shi yasa har ya tsaya suna ja
in ja da Hajiya karama banda haka ina shi ina biyeta, ai duk abinda tace haka xa
ayi, tsawar Nihad ne ya dawo da mai gadin reality don sai da ya tsorata, "Dalla
Malam kana bata min lkci, are you even okay, how dare u query my order? Ko dai kana
shaye shaye ne???" Khalil ya ɗan kalleta, sae kuma ya mike ya nufi motar, ta ja
wani dogon tsaki ta bi bayansa kamar xata tashi sama tana harararsa, duk sai taji
ranta yayi mugun baci, bayan mota ta bude ta shiga, tuni mai gadi har ya wangale
gate yana daga mata hannu alamar Allah ya tsare, Khalil yayi reverse ya fita daga
compound din, cikin mintuna kadan ya isa gida da ita, yana parking dai dai gate ta
ja tsaki ta bude motar ta fice without closing the door, da ido ya bi ta har ta
shiga gate din gidan, ya fi minti biyar tsaye da motar, daga bisanni ya sauka ya
kulle door din motar, sannan ya shiga yyi reverse ya bar layin ya koma can gidan da
Abba yake. Nihad na shiga gida bangaren Umma ta nufa, jefar da jakarta tayi saman
kujeran parlon tana kallon Umma tace "Umma wani irin driver ne wannan Abba yayi
employing, who even linked them? wllh yaron bai da kunya ko kadan Umma, kinga
abinda yayi min kuwa??" Umma ta ajiye kayan hannunta tana kallonta tace "Me yayi
maki?" Nihad tace "Wllh rashin kunya yayi min, ni babu wani wanda ya ta6a min haka
ma tun da nake, wai yaron ya maida ni gida yaki fa" Umma tace "Aa abu me sauki sae
ayi ma Abban naku magana ya sallamesa, halan d'an kauye ne?" Nihad tace "Toh ae
dama su ne masu wannan tsagerancin da rashin ta idon, wllh Umma wannan idan yayi
wata daya a gidan nan daina kai mu duk inda xa mu xae yi, Allah cewa xai dinga yi
baxae je ba kansa tsaye idan ma bai hada mana da zagi ba, gwara kawai Abba ya dawo
ya sallamesa a samo wani dama ni bai min ba from the start, irinsu ne idan an shigo
da su inuwa su maida mutum rana, wai kinga me yayi min ne, jayayya fa muka tsaya
muna yi da shi" Daga haka ta fice daga parlon ta tafi dakinta don ta shirya xuwa
inda xa su hadu da Husnah, sae dae tana tsaka da shiryawa ta dinga kiran wayar
Husnah ta ji a kashe, lkci daya ranta ya baci, kaddai har tayi tafiyarta, ta zauna
gefen gado tana ta trying din layin amma ya ki connecting. Ana kiran sllhn Azahar
Abba ya fito daga gidan tare da wata tsohuwa, Khalil ya mike tsaye ganinsu, suna
karasowa inda yake Abba yace "Sabon drivern da na dauka kenan Hajiya, yau ya fara
aiki..." Tsohuwar ta kallesa daga sama har kasa tace "To ba laifi, kuma da ganinsa
xae fi Habibu kwazo duba da halittarsa, kawai dae sai mu yi fatan Allah ya sa ya fi
Habibu nutsuwa, don Habibu ni kadai nasan ɗan iska" Khalil yayi kasa da kai tare da
risinawa yace "Ina yini Hajiya" da fara'a tace "Lafiya lau, amma kai buzu ne koh?"
Ya murmusa yana girgiza kai, Tsohuwar tace "Toh a dai kula da dukiyar mutane ka ji,
kai ma sai kaga Allah ya kula da kai, baka ga motar da Habibu ya ajiye kafin ya
tafi ba, duk ta fita hayyacinta daga karshe konden konden aka siyar ma, su ma din
dai a walakance suka siya, ya sunanka?" Yace "Ibrahim" Buda baki tayi tace "Ikon
Allah, Kai ae kawai ka zama d'an gida abun ka daga yau ka ji, babu me raina ka ko
waye shi, kanka tsaye kar ka yarda da hakan, ae sunan Uban gidan naka kenan, kuma
ni na haifesa, Allah yayi maku albarka gaba daya" yana murmushi yace "Ameen" Abba
yace "Toh ki koma haka Hajiya, ni xan tafi" Tace "To Allah ya tsare, idan Habubakar
din ya dawo xan tattauna da shi" Yace "Ba laifi, sae anjima" daga haka ya nufi
motar, Khalil na biye da shi a baya. Yana ajiye Abba a gida, Abba yace "Ka tafi
islamiyya ka dauko yara nasan sun tashi ynxu" Khalil yace "Toh in sha Allah" hanyar
makarantar ya nufa, yana parking bakin gate sae ga Nihal, sannan Fadil da Sudais,
Amina ce karshen fitowa duk suka shige bayan motar, ita kuma ta xauna gaba, ta
madubi yake kallon Nihal, tace "Barka da rana" xai amsa Sudais da Fadil suka
gaishesa su ma, amsa masu yayi gaba daya sannan ya maida hankalinsa kan driving din
da yake. Nihad na tsaye bakin parlon Abba tana jiran ya amsa sallamar da tayi, yana
amsawa ta shiga, ta karasa parlon ta xauna saman kujera tace "Abba ina yini" yace
"Nihad me yasa kika ki shiga ku gaisa da inna da mutanen gidan?" Ta langwabar da
kai bata ce komai ba, glasses dinsa ya saka yana maida dubansa kan laptop din
gabansa, tace "Abba i came to report this new driver to you" Sake kallonta yayi
yace "What about him?" Tace "Abba kawai don nace ya maida ni gida i am press shine
mutumin nan ya ki, infact yi yayi kamar bai ji abinda nake cewa ba ya bar ni a
tsaye" Abba yace "Is that so?" Tace "Wllh Abba, and it's not as if i was rude to
him, kawai cewa nayi don Allah ka maida ni gida ina son xan koma, kawai sai yayi
min banxa, wllh Sagir mai gadi ne shaidata" Abba dai yayi shiru yana kallonta, bude
kofar parlon Abba aka yi sai ga su Sudais da Fadil sun shigo gaida Abban nasu ganin
motarsa a gida, Nihal ce ta shigo bayansu, Abba yace "Welcome Nihal, tell the
driver to wait me at the balcony...." Juyawa tayi ta fita, ba a wani dau lkci ba
sai ga ta ta dawo tace "Abba na gaya masa" Abba ya ajiye laptop din kafarsa ya mike
ya nufi kofa, Nihad taji wani dadi har cikin ranta dama babu abinda xata ce ma
Abbanta tana so da baya yi, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa Nihal ta bi ta da
kallo, Abba na kallon Khalil bayan ya zauna saman daya daga kujerun dake wajen yace
"Ibrahim me yasa tace ka maido ta gida ka ki?" Khalil ya durkusa kasa yace
"Yallabai ban ki ba, ce mata nayi kar ka fito ka tarar bana nan kace inyi jiranka,
amma daga karshe na daukota na dawo da ita gidan" Nihad dake jikin kofa ta hade rai
jin abinda yace, Abba ya juya ya kalleta yace "Is that so?" Tace "To Abba sae fa da
ya ja min rai, maimakon ina gaya masa kawai ya tashi ya kai ni gida" Abba ya kalli
khalil yace "Je ka" Mikewa Khalil yayi yana kallonta yace "Kiyi hakuri, ban san
haƙan xai bata maki rai ba" Wani shegen kallo tayi masa ta juya tayi wucewarta
ciki. Bangaren Umma Nihad ta koma, Kamar xata fashe da kuka tace "Umma kin ga Abba
bai dauki ko wani action ba dai ko?" Umma tace "Sai yace masa me?" Tace "Ba abinda
yace masa, ni wllh sai dai duk abinda xai faru ya faru, da kaina xan dinga driving
kaina, gashi gobe ina da lectures karfe goma a haka xai kai ni schl din? Nooo i
will prefer to drive my sef" Umma tace "To idan kika tafi da motar da wanne xa a
dauko kannenki daga makaranta?" Tace "Ba ga motar yaya Farooq ba ko yaya Usman"
Bata jira me umma xata ce ba ta fita daga parlon xuwa kitchen, Aminu mai gadi ta
gani a windown kitchen din ta baya, mai aikinsu Hafsah tana xuba wani abinci a
plate, kallonta tayi tace "Abincin waye wannan?" Kafin tayi magana Aminu yace "Na
sabon dreba ne" Buda baki tayi tace "Shi ma din sai an dinga basa abincin a nan?
Waye yace haka?" Daga mai aiki har mai gadin suka yi shiru, tace "Ohh kawai ku kuka
tsara hakan sbda ku ke siyan kayan abinci?? To Abba bai ce haka ba, ni ma kuma
bance ba, saboda haka ajiye abincin nan dake hannunki baxa a kai ba, kai kuma Aminu
ka kama gabanka, ba shi da portion din abinci a gidan nan" juyawa Aminu yayi ya bar
wajen a sanyaye, Hafsah ta nemi plate ta rufe abincin ita ma a sanyaye, tsaki Nihad
tayi ta dau plate ta debi abinda xata deba ta cika nama sannan ta fita, tana fita
Nihal ta shigo kitchen din ita ma xata xuba abinci, ganin wanda Hafsah ta rufe tace
"Hafsah wannan wa ya ci ya rage?" Hafsah dake wanke wanke tace "Aa ban dade da
xubawa ba, Aminu ne ya xo amsar ma sabon dreba abinci Aunty Nihad ta hana" Nihal
tayi shiru da mamaki, can tace "To saboda me?" Hafsah tace "Nima ban sani ba wllh"
Nihal ta buɗe abincin tana kallo, can ta rufe ta kalli Hafsah tace "Ki kai masa"
Hafsah ta xaro ido tace "Ta fa hana Aunty Nihal" Nihal bata kuma cewa komai ba ta
dau spoon ta daura saman abincin ta fita daga kitchen, xaune ta tadda Khalil bakin
gate da mai gadin, mai gadin ya dauko masa wani guntun bread dake ta ajiye dakinsa
da pure water ya basa, kallonta suke gaba daya, shi dai Khalil yana kokarin gane
wacece, don kamarsu ta ɓaci da Nihad, sai da ta karaso ya gane ba Nihad bace don
Nihad ta fi ta haske har ma da tsayin hanci, amma both suna da dimple, ta mika masa
abincin tace "Ga abincin" Amsa yayi ya d'an yi murmushi wanda iyakarsa Lips yace
"Nagode" Juyawa tayi ta koma ciki, Mai gadi yace "Kaga er albarka, muna ganin
abubuwan al'ajabi fa a gidan nan, halaye iri iri in gaya maka, kaga Nihal din nan
da kake gani, ko kadan bata yi halin uwarta Hajiya ba, yarinya ce nutsatssiya ga
sanin ya kamata, uwa uba ga girmama d'an adam ko da kuwa almajiri ne, ba dai ka
ganta da kawaye ba kuma, uwarta kuwa ban ta6a ganin mace mara kirki mara mutunci
irinta ba duk nan hakuri muke da ita, gashi bata da aiki sai shige ma matan manya
manyan kasar nan, sannan
ita kadai ce bata yarda Habibu ya ja ta a mota ba, duk sanda xata fita sai ta bari
Alhaji ya fita sannan ta ja mota ita ma, bata dawowa kuma sai dab da magariba motar
nan kaga duk yayi butu butu da laka malam, tana dawowa kuma xata sa Habibu ya wanke
motar, ita kuma wancan Ja'irar da ta hanaka abinci ban ta6a ganin me kirki irin
uwarta ba, wato matar Alhaji ta biyu kenan, ga dai ita ce ta fari gun uwarta,
tsakaninsu da Nihal kwana daya tak, shi sa xaka gansu kamar yan biyu, sai kuma
Allah ya basu kama daya, komai nasu iri daya ne, to wllh Hajiya Mumy uwar Nihad
mace ce me mutunta mutum babu ruwan baiwar Allahn nan da duniya, sai gashi Allah ya
hadata da shaidaniyar yarinya, bata da aiki sai na bitar kawaye da rashin daraja
ɗan adam, to haka Allah yayi ikonsa a gidan nan, kyansa ace Nihad uwarta Umma, ita
kuma Nihal uwarta Mumy kaga dai dai kenan, amma Allah bai tsara hakan ba, ni fa da
rana daya aka haifesu sai muce canja su aka yi a asibiti, amma Nihal aka fara haifa
er baka da ita washegari aka haifi Nihad ita kuma fara tass, kaga ko ai ba ayi
canje ba" Khalil dake kallonsa yana sauraronsa attentively yace "Ita Umman yaranta
nawa?" Mai gadi ya gyara xama irin abun nema ya samu din nan, yana kirga su da
yatsa yace "Kaga Farouq shine ɗan ta na fari, a Habuja yake aiki, ya kan yi wata
biyu ma bai leko gidan nan ba, ba laifi yana da kirki da faram faram da jama'a, shi
ma kuma bai yo halin uwarsa ba gaskiya, sai Usman shi kuma kadaran kadahan, shi ba
a ma gane alkibilarsa, yana da kirki oho, bashi da kirki oho, atoh a haka na san sa
gaskiya, sai Kamila warce tayi aure shekara biyu kenan, wani shegen mai kudi Umman
tasan yanda tayi ta hadata da ta aura, sai Nihal sannan autarsu Amina, amma fa ta
fi ji da Nihal din don ita ma auta take kiranta, ita wannan Aminar ma mara kunya ce
gaskiya amma fa akwai son karatun addini, tana ajin karshe na sakandari, Nihal kuma
ABU Zaria take, ita