Showing 168001 words to 171000 words out of 268471 words

Chapter 57 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

seconds yace "Me ya kawo ki
gidana?" Ta girgiza kai hawaye me zafi na sauka idonta tace "Kayi hakuri Abba" Bai
kuma ce mata komai ba sai dauke kansa da yayi daga kallonta, staring at the Ac in
his parlor, Nihal ta juya ta fita daga parlon hawaye cike idonta, mikewa Nihad tayi
da sauri ta bi bayanta tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Abba ya bi ta da
kallo lokaci daya yaji hawaye ya kawo idonsa, mikewa yayi ya shige bedroom dinsa,
Nihad ta koma bangaren Mumy ta shiga bedroom dinta ta ga Mumy zaune gefen gado
looking so worried, fadawa kan gadon Nihad tayi tana kuka a hankali, Mumy tayi
karfin halin cewa "Me yace maki? Yace ki bar masa gidansa ko?" Nihad ta kasa cewa
komai sai kuka take sosai, Mumy bata san sanda ita ma ta fashe da kukan ba, taji
zuciyarta na mata zafi, Nihad na ganin haka ta mike da sauri ta rungumeta tana kuka
sosai tace "I am sorry i never listened to you mum, kiyi hakuri ki yafe min
plsss..." kasa ci gaba tayi saboda kuka da ya ci karfinta, Mumy tayi karfin halin
cewa "Baki min komai ba Nihad, na yafe maki duniya da lahira, babu abinda kika min,
haka Allah ya tsara maki rayuwarki babu kuma wanda ya isa ya canza hakan" Nihad na
kuka bitterly tace "Amma Mumy baki taɓa ce min Umma ba so na take ba, u never told
me she is misleading me, nobody was there to tell me all this, Umma caused me all
what i am passing through now" Mumy ta dakatar da kukan da take tana sauraronta
babu ko kiftawa, Cikin kuka sosai Nihad tace "Duk abinda nake yi a baya Umma ce
take sa ni inyi, she neva gave me the chance to differentiate what's good or bad,
she is always supporting me in every aspect, i don't know she was just ruining my
life, ta cuci rayuwata, me yasa baki taɓa gaya min bata sona ba, me yasa baki gaya
min ba masoyiyata bace? mumy me nayi mata?" Mumy ta girgiza kai kawai wasu hawayen
na sauka idonta ta kasa ce mata komai, A hankali Nihad na girgiza kai sounding
bitterly tace "Ita ta karfafa min gwiwa wajen yin kawance da su Husnah, she
encourage me to follow them everywhere, ta nuna min duk wani dake aiki a gidanmu
bashi da value i should treat them harshly idan ba haka ba za su raina ni...." Mumy
tayi shiru sai sauraron Nihad take, Nihad tace "Mumy ba wani gidan Aunty Kamila da
naje, duk watanni hudu da nayi bana gidan nan ina hostel tare da su Husnah, i never
went to Auntt Kamila's place Umma planned it for me...." Mumy bata san sanda ta
mike tana kallon Nihad babu ko kiftawa ba, Nihad na share hawayen da yaki tsaya
mata cike da karfin hali tace "Ita tace ma Kamila ta kira Abba tace za mu je kebbi
amma babu wani kebbi da muka je, all those while i am staying in the hostel with my
frnds, duk wani hotel da party da su Husnah za su Umma tasan ina bin su ita ke
encouraging dina in bi su, duk sanda na fita da daddare zuwa party Umma ce ke bude
min kofar parlor babu wanda xai sani, tun da na taso muke haka da Umma....." Tana
kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka me ban tausayi, she is deeply regretting
everything now, tayi da ta sanin abubuwa da yawa da tayi a baya, nobody was there
to tell her Umma ba sonta take ba all that while, wasu abubuwan ma baxata iya gaya
ma Mumy ba amma Umma ta cuceta ta cuceta iya cuta, sannan ta nuna mata da ma duniya
gaba daya babu wanda take so sama da ita, Mumy dai ta kasa cewa komai sae kallonta
take babu ko kiftawa, kana ganinta kasan she is shock, don duk bata san da abubuwan
nan da Nihad ke fadi yanzu ba, ta dai san komin laifin da Nihad xata yi a gidan
Umma bata barin a mata fada sai ta nuna ai yarinya ce babu abinda ta sani, sannan
ko me take so wajen Abba Umma ke taimaka mata wajen amsa, ko kai maye ne baxaka ce
Umma bata son Nihad da gaske ba, sai ta siya ma Nihad abu sau goma bata siya ma er
ta Nihal ba, wannan ne ma ya sa Mumy ta kara jawo Nihal jikinta sosai.... Nihad ta
zamo kasa muryarta na rawa tace "Don Allah ki yafe min Mumy, amma ban taso na gan
ni a wajenki ba, i never knew u were my mother at first, Mumy me yasa kika bar ma
Umma ni? Why did u hand me over to her?" Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana
kuka sosai, Wani kuka ya taho ma Mumy bayan memory din yanda Umma ta rabata da
Nihad ta karfi da yaji tun tana 5 years ya dawo mata vividly.... Mumy tayi duk iya
kokarinta na ganin Abba bai dauke Nihad daga wajenta ya damka ma Umma ba har hakan
sai da yayi sanadin igiyar aurenta daya a gidan, babu irin bakaken maganganun da
Inna bata gaggaya mata ba a wancan lokacin wai bata da kara bata da kunya akan yar
ta ta fari, ina ruwanta da er ta na fari da har zata zakalkake a kanta tana nuna
tafi kowa iko da ita sae kace ba bafillatana ba, banda zamani ya lalace, su
zamaninsu babu macen da ta isa tayi haka, har inna ke kara tunatar mata cewa Umma
bata rike ɗan ta na fari da na biyu ba bata ma san ta yanda suka girma ba ta kauda
kai a kansu kamar ba ita ta haifesu ba, Ya Farooq da ya Usman basu taso wajenta ba,
tun daga yaye inna ta daukesu suka koma wajenta a Bauchi kuma Umma bata taɓa cewa
don me ba, yawancin rayuwarsu duk a wajen Inna suka yi a lokacin ma kakansu na da
rai, sae ya kasance Kamila ce kawai gaban Umma and she never complained for once,
har dai ta zo ta haifi Nihal, washegari kuma Mumy ta haifi Nihad, wanda sai da Mumy
tayi shekara goma a gidan kafin ta haihu, duk tana gidan aka haifi Usman da Kamila
amma ita Allah bai bata haihuwa ba, dalilin da yasa da ta haifi Nihad Abba ya dau
son duniya ya daura mata gashi fara ce kal kamar zaka latsa ta jini ya fito, ga
masifar kyau kamar er larabawa, dama shi farin yaro da shegan shiga rai yake, ita
kuma Nihal baƙa ce amma suna kama sosai da Nihad, sai ya dau Nihad sau goma bai dau
Nihal sau daya ba don Nihal tana da kiwiya sosai shi sa ma bai bin ta kanta, ba ta
yarda da kowa sai Umma, hakan
yasa yafi shakuwa da Nihad da ko muryarsa taji ta dingi kuka kenan sai ta gansa ya
dauketa, shakuwa me tsanani ya shiga tsakaninsu ya dau soyayya mara iyaka ya daura
mata, har cikin ransa yake jin Nihad, wanda Mumy na lura da Umma kamar hakan baya
mata dadi don bata iya boye hakan a fuska, ga kuma er ta Nihal shegen kiwiya da
kuka, Mumy kan ce ma Abba ya daina bambanta su kar a samu matsala, nuna banbancin
bashi da amfani don duk daya suke a wajensa, amma sai yace mata ai Nihal kiwiya
gareta bata yarda da kowa, haka rayuwa ya ci gaba har aka yayesu, tun Nihad na
shekara uku Umma ta fara nuna tafi damuwa da ita akan Nihal kamar yanda taga Abba
ke yi, ta sha attempting mayar da Nihad dakinta gaba daya amma Mumy taki bada
fuskar hakan, don babu Alkunya take shiga ta dauke er ta ko da kuwa bacci take a
dakin Umma komin dare kuwa, ko hularta bata yarda ta bari a dakin Umma, Umma bata
hakura ba har sai da ta san yanda ta hada makircin da ta hada tare da goyon bayan
Inna Nihad ta dawo wajenta, Wanda har sai da Abba ya saki Mumy akan issue din wai
tana son raba masa kan gida, ga inna ta saka ta gaba da gore gore wai ai ba da ita
ta zo gidan ba sannan ina ruwanta da er ta ta fari idan ba rashin kunya ba, karfi
da yaji dai aka raba Mumy da Nihad, babu yanda Mumy ta iya tana ji tana gani ta
cire hannunta akan wasu lamarin Nihad ta bar ma Umma gaba daya, and that was the
genesis of the whole problem.... Mumy ta kasa ci gaba da zama dakin ta fita kawai
ta koma parlor tana jin xuciyarta na mata zafi, Umma ta cuceta ta cuceta, ita kuwa
bata ma er ta irin rikon da tayi ma Nihad ba, Nihal da kanta ta koma bangaren Mumy
a lokacin ma tayi shekara goma, tana ji tana gani sae Umma ta hana Nihad shigowa
wajenta, babu kusanci kwata kwata tsakaninta da Nihad, to amma ya zata yi, tunda ga
abinda mijinta da uwar mijinta suka ce, kawai sae ta rungume Nihal tana ganinta
kamar yar cikinta. Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta koma saman gadon Mumy ta
kwanta ta rufe idonta a hankali tana jin kanta na ciwo, a haka har bacci ya dauke
ta. Wajen karfe goma da wani abu Nihad ta bude ido a hankali ta dalilin tashinta da
aka yi, ta mike zaune tana kallon Nihal dake zaune gefenta, Nihal tace "Ana kiranki
a parlor" Nihad na murza idonta tace "Waye?" Nihal ta mike tace "Ki fito" Daga haka
ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta mike da kyar ta nufi kofa ta fita Parlon Mumy,
zaune ta gansa duk ya wani birkice yana kallon kofar dakin eagerly, suna hada ido
ta sunkuyar da kai a hankali, Nihal ta juya ta fita ta rufe kofar parlon, sai a
sannan ya mike da sauri, Nihad tayi saurin juyawa zata koma dakin yayi hanzarin bin
ta har ciki ya fizgota, zaro ido tayi tace "Don Allah ka bari kar wani ya shigo"
kin yarda su hada ido tayi taki dago kanta, da taga he is trying to raise her head
up kawai ta kwanta saman kirjinsa tayi lamo, she could feel how fast his heart is
beating, ta lumshe idonta a hankali, ya rungumeta sosai, Underneath his breathe
taji yayi maganan da ita kanta bata ji ba, jin hawayenta a jikinsa ya dago kanta da
sauri yana kallonta, kasa barin su hada ido tayi, cikin rawan murya tace "I am...
Am sorry, i..." sai kuma ta kasa ci gaba ta fashe da kuka, Lokaci daya ya saketa
jin an bude kofar parlor, ta goge idonta da sauri ta fito parlon sai ta ga Nihal ce
ta shigo rike da ruwa da lemo, Khalil ya fito parlon shi ma ya zauna, Nihal dai
bata yarda ta hada ido da su ba. Tashin hankalin da Mami ta shiga ba a cewa komai
da ta shiga dakin Khalil da sassafe taga baya ciki, kuma bata ga alamar ma a dakin
ya kwana ba, tun sannan take kiran duk layinsa taji su a kashe, ta ma rasa
takamaiman abinda zata yi, tun cikin dare take Allah Allah gari ya waye ta samesa
tace masa ko za su je can kano ne gidan iyayenta ko Allah ya sa can ta tafi, sai
gashi ta shigo babu shi a dakin, ta dawo bangarenta cike da damuwa, tana zaune tare
da Mimi a parlon tace "Kuma ko number yayanta baki da shi ko?" Mimi ta girgiza kai
a hankali tace "Bani da shi" Bude kofar parlon aka yi, duk suka daga kai, Mami ta
dinga kallonsa da mamaki don in ba dai tana kwance ba lafiya ba baya shigowa
bangarenta kai tsaye haka, sannan ko minti ashirun bai yi da dawowa gidan ba, kuma
ba ita ce ma da girki ba, Mimi ta mike ita ma tana kallonsa tace "Good morning sir"
Bai amsa mata ba ta nufi kofa ta fita, Mami na ganin yanayinsa ta san ba lafiya, to
me kuma ya faru, ta dai mike cikin dakewa tace "Lafiya kuwa Yallabai? Is everything
alright" Yana huci yace "Stop asking me that, Ina Ibrahim? Provide him now" Mami
sai da gabanta ya fadi, tayi karfin halin cewa "Is everything alright" tsawa ya
daka mata yace "Ina maki tambaya kina amsa min da tambaya?" Ta koma ta zauna bata
sake ce masa komai ba, ya sake jefo mata tambayar ina Ibrahim, a fusace tace "Tunda
dai ba goya Ibrahim nake ba ta ina xan san inda yake da sassafen nan? Ba dai ka san
hanyar dakinsa ba" Yana muzurai yace "Ohh haka kika ce?" Tace "Ya kake son ince?
Naga dai ba nan yake kwana ba da ka zo nemansa a nan, za ka wani zo ka isheni ina
Ibrahim" Ya fi second ashirin yana kallonta yana gyada kai, kafin ya juya ya fice
daga parlon almost ripping the door off, tagumi tayi tana tunanin to me kuma yaron
nan yayi? Wannan wani irin fitina ne ita kam, Noor ce ta shigo parlon tana kallon
Mami a sanyaye tace "Mami kin san me Yayanmu yayi?" Mami da taji gabanta na faduwa
sosai tace "Me yayi Noor?" Noor ta zauna cikin sanyin murya tace "He broke into
Abba's room and collected all what Abba seized from him, lalata makullin dakin ma
fa yayi" Buda baki Mami tayi ta kasa cewa komai zuciyarta na bugawa, Noor tace "Ina
jin cikin dare kowa na bacci yayi haƙan, he scattered everywhere in the room" Mami
ta saki salati ta rafka uban tagumi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai
ga Aunty Hassana ta shigo parlon babu ko sallama cike da rashin mutunci tace "Ke
kam fatima kin haifar mana fitina a gidan nan, don Khalil fitina ne wallahi...."
Mami ta dakatar da ita tace "Ban haifi fitina ba sai in ke kika haifi fitina
wallahi"


*Thanks for being patient with Khaleesat*

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788


53

Mami bata tsaya ta kara sauraran Aunty Hassana ba ta mike ta shige dakinta ta
shirya ta fice ta bar masu gidan daga ita har yayan nata zuwa gidan Hajiya
Safeenah. Tana zaune parlon Hajiya Safeenah abun duniya ya isheta, Hajiya Safeenah
tace "Na fa ce ki kwantar da hankalinki Hajiya Fatima, yarinyar da har nude video
dinta yayi yawo a gari ai kinsan dama can idonta a bude yake kome aka ce ta aikata
to zata iya aikatawa, ke dai kawai Allah ya shirya mana zuri'a, kuma babu tantama
kila gidan nasu ta koma, ke kuma kina nan duk kin bi kin daga hankali" Mami dake ta
kallonta tace "You have a point, sai yanzu da kika yi maganan nan na tuna wacece
yarinyar, duk yaron da idonsa yayi budewar da nata yayi koma meye zai iya aikatawa
gaskiya kika fada, ni fa wallahi bani da yanda xanyi ne amma ni ba wai son zamanta
nake a gidana ba, haka kawai taje ta kara aikata wani abun da ba shikenan ba, gashi
baka gane gabanta balle bayanta, nukurcinta yayi yawa, sannan kwana biyun nan ina
ta lura da yanda Khalil din ke shige mata, sam bana son haka...." Hajiya Safeenah
ta rike haɓa tace "Au, ashe kema dai kin lura, jiya bayan mun dawo gida zancen da
Nadeeyah ta kawo min kenan...." Mami tayi shiru da tunani iri iri a ranta, can ta
sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi abun ya dameni, to yace mana wajen iyayenta ya
zauna a kano ya zanyi masa, ga Maryam me goyan bayansa, tukunna ma dai wasu irin
iyaye ne xasu hada yar su da gandameme kamar Khalil wai su taho Abuja tare sannan
ya bar ta a gidansu wai zata yi karatu? A ina aka taɓa haka kamar dai garin gaɓa
gaɓa aka taso? Idan ma haka ne ai kamata yayi uwar ko uban wani ya biyota sai a
damka mana ita a hannu ace gata nan don Allah zata yi karatu a sa mata ido, to wai
sai aka hadata daga ita sai khalil ya kawo mana ita, ko marasu addini baxa su yi
haka ba, ni wallahi na rasa yanda zanyi ne, i have a big question mark on this
issue, ga Maryam tayi ɓake ɓake kan lamarin sai goyan bayansa take wai sai an
riketa tunda iyayenta suka rike shi, to shi ba namiji bane ko da da kafafuwansa
yaje gidan nasu shi kadai, ita kuwa ai sai cikin iyayen wani ya rakota saboda halin
rayuwa, komai fa na son tsari a rayuwar nan, amma sam wannan lamarin ba tsari, a
hada baligi da baliga wa enda ba muharraman juna ba" Hajiya Safeenah tace "Gaskiya
abun dubawa ne wannan, kuma kika ce kwanaki yayanta yaje gidan ko?" Mami tace "Ehh
yaje kam, amma ko da iyayen ma baxa su biyota ba ai sai su ba yayan nata ya kawota
ba Khalil ba, it's making no sense to me now, tun farko ya kamata inyi masa wannan
tuhumar amma hankalina bai je ba, sannan ban taɓa jin an kirata daga can gidan nasu
ba ko kuma ita ta kirasu" Hajiya Safeenah tace "Toh dai ki kara kiran layukan
Khalil din ko xaki samu, aji in gidan ta koma kin ga hankalin kowa sai ya kwanta,
sai kuma a koma next issue that's on ground" Mami ta sake dialing number Khalil,
luckily ya fara ring, gyara zama tayi ta sa handsfree tana jiran ya daga, sai da ya
kusa katsewa sannan ya dauka, tace "Khalil me ya kai ka dakin Abbanka?" Khalil ya
ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ajiyata na dauka Mami" Mami ta bude baki tana kallon
Hajiya Safeenah, can tace "Ajiyarka? Wato khalil duk yanda zaka daga min hankali
shi kake nema a rayuwarka ko? Ba nace ka fita batun abubuwanka da ke hannun Abbanka
ba? Me yasa baka jin magana ta ne fisabilillah" Khalil yayi kasa da murya yace
"Mami i did nothing wrong, bayan takarduna babu wani abu da na taɓa masa a dakinsa,
i seriously need them Mami, tunda ke baxa ki iya dauko min ba shine fa na dauka da
kaina Mami...." Mami ta buda baki, ta ma rasa abinda xata ce masa, can tayi karfin
hali tace "Duk inda kake ka dawo ina nemanka immediately, sannan kada kayi making
mistake din zuwa gida ka zo nan gidan Hajiya Safeenah ka sameni" Ya ɗan yi shiru,
sai kuma yace "Toh" Mami zata katse wayar, Hajiya Safeenah tace "To baki tambayesa
batun yarinyar ba" Mami da har ta manta tace "Ohh, Sannan ita kuma yarinyar can ina
fatan gidansu ta tafi?" Khalil yayi shiru kamar baxai ce mata komai ba, sai kuma
yace "Eh" Mami tace "Toh madallah, sai ka gaya ma iyayen nata taki zama Abujan,
it's better kawai su nema mata transfer ta koma Kanon da karatu ya fi" Khalil dai
bai ce mata komai ba, tace "Baka ji na ne?" A hankali yace "Ina ji" Tace "Then do
as i say, kai kuma immediately ka taho gidan Hajiya Safeenah ina jiranka" Yace "Ni
bana Abuja yanzu" Buda baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login