Showing 93001 words to 96000 words out of 268471 words
kofa, da sauri tace "Ka kira min Nihal plss" yace "Warce kika kora ko
wacce?" daga haka ya fita dakin, a hankali ta lallaba ta mike ta hau saman gadon ta
kwanta tayi lamo a saman pillow, wato tafiya Nihal tayi upon all her pleas. Kafin
azahar Nihad taji tana iya taka kafar, a hankali take dingishin ta fito daga dakin,
ta shiga nata dakin, kallon katon ledan dake saman gado ta dinga yi, kafin ta
karasa ta bude ledan, abaya ta gani masu ɗan karan tsada sun kusa kala goma, da
mamaki ta dinga kallonsu tana warwaresu, sannan ga undies da cream din shafawa da
turarurruka duk a cikin katon ledan, da sauri ta fito parlor tana kallonsa tace "A
ina ka samu kudi ka siya min abayan nan?" Ya kalleta a takaice yace "Kudin babanki
mana" Nihad tace "To amma wa ya zabo abayan?" Yace "Ni ɗan aike ne, kasuwa kawai
aka aike ni naje na amso" Ta kyabe baki tace "I thought as much" Daga haka ta juya
ya bi ta da kallo har ta shiga daki, wani Murmushi yayi ya maida idonsa kan tv da
yake kallo. Bayan ta yi wanka ta shirya cikin daya daga abayan, sosai yayi mata
kyau ya amshi fatarta, ba laifi haskenta ya fara dawowa amma ramar na nan, ta fito
parlor, kallo daya yayi mata ya dauke idonsa, ta wuce kitchen sauran abincin da
Nihal ta dafa daren jiya ta kara dumamawa ta xuba ta koma daki ta ci, har kusan
la'asar Nihad na ta xuba ido taga ko Umma xata zo yau din ko sai gobe, amma bata zo
ba, wajen karfe biyar ya bude kofar dakinta yace "Ki sameni a mota" Da ido ta bi sa
har ya bar wajen, sai kuma ta mike
ta dau mayafinta ta bi bayansa, duk da yana cikin motar ta ki shiga, she can't
take that risk anymore, tana kallonsa da kyau tace "Ina za mu je?" Yace "Gidanku"
Ta ɗan yi jim, sai kuma dai ta shiga bayan motar ta kulle, suna barin gida taga sun
dau hanyar gida, ta ma rasa ko farin ciki xata yi ko akasin hka, the only good
thing of going to that house is that xata ga Umma bayan nan ita bata marmarin ma
zuwa gidan.... Sai da suka kusa yace "Ki bude kunnuwanki ki saurareni da kyau, zan
kai ki gida ba don komai ba sai don ki gaida mahaifiyarki da bata da lafiya, idan
Abba na nan shi ma ki gaishesa, bayan haka xa mu fito daga gidan..." Da mamaki
Nihad tace "Kana nufin sai in shiga har gidanmu in fito ban je bangaren Umma na
gaidata ba??" Dai dai nan suka shigo layin, yana kallonta da kyau ta madubi yace
"Ba don ki je bangarenta ki gaidata na kawoki gidan ba, a duk inda kika hadu da ita
a nan xaki gaisheta babu xancen xuwa ɓangarenta, idan kuwa kika ce baxa ki bi
umarnina ba, Billah na maki alƙawarin muna fitowa daga gidan xan maida ke garinmu
da zama na har abada" Shiru Nihad tayi bata ce komai ba, bayan yayi parking yace
"Kin ji ko baki ji ba?" Ta hade rai tace "Na ji" Bude motar yayi ya sauka ita ma ta
sauka fuska daure, har sannan dingishi take, Aminu kamar xai goya Khalil tsabar
farin cikin ganinsa, Nihad ta kara tsuke fuska ko kallonsa bata yi ba ta shige
cikin gidan, Aminu yayi kasa da murya yace "Ciwo ta ji a kafar take dingishi?"
Khalil yace "Zan fito yanxun nan" Daga haka ya bi bayan Nihad, Umma ta fito daga
bangarenta kenan ganin Nihad ta hau tafa hannu tana cewa "Oyoyo oyoyo" Nihad ta ɗan
saci kallon Khalil dake bayanta yana kallonta, ta sunkuyar da kai a hankali tace
"Umma ina yini" Umma tace "Karaso mu shiga ciki daughter" Nihad tayi karfin halin
cewa "Xan shiga wajen Mumy ne tukunna" Umma ta saki baki tana kallonta, tuni khalil
yayi part din Mumy, Nihad ta bi bayansa kamar xata yi kuka, haka Umma ta bi su da
kallon mamaki, kai ko makaranta Nihad ta dawo ba wani lallai taje bangaren Mumy ta
gaidata ba, Umma kuwa dama kafin ta fita sai ta shiga ta gaya mata ga inda xata,
haka kuma idan ta dawo, abinda Nihad tayi yanxu sai yayi mugun daure ma Umma kai.
Nihad ta kasa hada ido da Mahaifiyarta bayan sun shiga parlon, Mumy ta amsa
gaisuwar khalil da fara'a, Yace "Ya karfin jikin?" Tace "Alhamdulillah jiki da
sauki" Nihad na wasa da veil dinta tace "Mumy ya jikin?" Mumy dake kallonta tace
"Alhmdlh" cousin din Mumy ce ta fito daga bedroom suka gaisa da khalil cikin
mutuntawa, Nihad dai sae kallonta take, ganin ta juya ta koma daki ba tare da ta bi
ta kanta ba, Nihad ta mike a sanyaye ta bi bayanta, gaisheta tayi, maimakon ta
amsa sai ta hau ta da fada, tace "Ban kara tabbatar da cewa ke mahaukaciya bace
shashasha sai yanxu, ace uwarki ba lafiya tun da kika bar gidan nan amma kika rasa
inda xaki samu wayar kiranta? nan kuwa a duk sanda matar nan Umma ta shigo sai tace
ai kunyi waya, anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa Nihad? Kullum bawan
Allahn nan sae ya shigo gidan nan gaida uwarki amma sbda ke ba yar halaq bace baki
ta6a cewa xaki biyosa ki duba jikinta ba, to duniya ce dai wanda bai zo ba ma
jiransa take, idan kuma Umma ce tayi nakudarki ta haifeki xa mu ji" Nihad ta zauna
hawaye na sauka idonta tace "Aunty ni tsoro nake ji shi yasa ban kirata ba, kuma
wallahi bai ta6a ce min xai zo nan ba ban biyosa ba" a fusace Aunty Zulai tace "Sai
yace maki xai zo?? Shashasha kawai kin bi kin ja mana abun kunya a duniya wanda har
yanzu kukan wannan mugun abun naki muke, wallahi sai nan gaba xaki yi kukan gaske
da hawayenki a kan wannan video din Nihad, nan gaba xaki san illar da kika ma kanki
a duniya a kan video din nan, kuma yau da ace wannan mijin naki iyayensa da
danginsa yan boko ne ko a cikin gari suke wllh baxa su ta6a bari ya aureki ba ko da
kuwa shi ya ganki yace yana so balle wannan manna masa ke kawai aka yi sbda babanki
ya yaba da hankalinsa, amma da ace ɗan birni ne wllh gori wajen danginsa da yan uwa
ma kawai ya isheki ki hadiye xuciya ki mutu wataran, kina ganin kamar abu ya lafa
ai shkkn an manta, yarinya sai nan gaba xaki gane abinda nake gaya maki ba yanzu
ba, don haka in zaki rungumi mijinki ki bisa ki masa biyayya ki lallaba aurenki, to
gatanki, idan kuwa kin ce ba haka ba kika kuskura kika bari aurenki da bawan Allahn
nan ya samu matsala to idan ba kauyen ubanki xai sake komawa ya samo maki wani
mijin ba ina me tabbatar maki babu wanda xai aureki don ma in gaya maki ki ji da
kyau" kuka kawai Nihad take tana kallonta, Aunty Zulai tace "Shikenan ni abinda xan
gaya maki kenan, tashi ki bani waje" Nihad ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya
mata ta fito parlor kanta a kasa, zaunawa tayi saman Carpet ta dago kai a hankali
ta kalli Mumy taga kallonta take, cikin sanyin murya tace "Mumy ina su Sudais" Mumy
tace "Sun tafi makaranta" Nihad bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes Mumy
tace "Kin ga wancan bawan Allahn dake zaune?" Nihad ta daga kai ta kalli Khalil da
Mumy ke nuna mata bata dai ce komai ba, Mumy tace "In har kina son gamawa da ni
lafiya to ki zauna lafiya tare da shi, idan kuwa kince ba haka ba, ba baki na maki
ba amma baxa ki ta6a ganin daidaituwar lamarinka ba, don haka kika kuskura kika
kashe auren nan naki sae dai ki nemi warce ta haifeki ba ni ba" Nihad ta fashe da
kuka sosai tana kallon Mumy, shi dai Khalil bai iya ya daga kai ya kallesu ba, Mumy
ta kallesa tace "Ku gaida gida Ibrahim.... nagode sosai, xan shiga ciki" Yana
kallonta cikin sanyin murya yace "Allah ya kara lafiya" Ta amsa da Ameen ta mike ta
shiga dakinta, kuka kawai Nihad take kamar ranta xai fita a parlon, bayan few
seconds Khalil ya mike ya fita daga parlon, mikewa ita ma tayi tana kuka ta bi
bayansa.
*Nihad* is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence via👇🏻
07087865788
Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki
da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai
maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da
boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*
Domin karin bayani ki tuntubi wannan number 👇🏻
✍🏻
+2347057607751
30
*Masu forwarding min novels daga nayi posting to other groups su sani hakkina bazai
ta6a barinsu ba don good 4 hours nake using wajen ganin na hada just 1 page, babu
ruwana da wai mutum daya ya siya a group sai ya tura ma saura tunda ni ba er iska
bace ban yarda da wnn iskancin ba, duk me yin hakan taje ita da Allah, kuma Allah
zai saka min, dama ɗ'an abinda mutum ke rainawa yake maida shi ba komai ba bai san
shine doom dinsa ba a rayuwa, wani ba wai bai da 500 din biya ba, kawai kyashi ne
baxai barsa ba amma ya iya karatu ya ji dadi, sannan masu min posting a facebook
suma su da ALLAH!!!* Na gaji da zuba maku ido kuma haka.
Suna fitowa parlor Nihad na kallon khalil cikin kuka tace "Don Allah ni ka barni in
je in gaida Umma" Juyowa yayi yana kallonta yace "Akwai wata Umma bayan warce kike
gaida da muka shigo daxu?" Muryarta na rawa tace "Toh kawai a parlor xan gaisheta?"
Yace "Eh" Kuka kawai take tana kallonsa ta wuce sa kamar xata tashi sama ta nufi
kofar fita parlon, bin bayanta yayi ya sameta jikin mota tana kuka kamar ranta xai
fita, ya zaga driver seat ya bude ya shiga, bude bayan motar tayi ta shiga don ita
har yanzu Drivern gidansu ne shi, Aminu ya marairaice bayan Khalil ya fito da mota
waje yace "Ina ta rokon Saminu ya jira min gate in kawo maka ziyara amma ya ki..."
Khalil na kallonsa yace "Wataran ma baxa kayi gadin ba gaba daya, sannan matsayinka
xai dawo dai dai da na kowa a duniya" Aminu ya daga hannu biyu sama yace "Allah
Ubangiji ya amsa bakinka, Allah ya dubemu yanda ya dubeka lkci daya, wannan
gagarumin ci gaban da ka samu Allah ya sa mu a danshinka, wayyo wa yaga Aminu ya
daina gadi, duk basur ya cinye ni sbda zama kan benchi daga safe har dare, na ma ji
Alhaji yace xa a dubo sabon driver tunda kai yanxu ai ba batun tuki kuma" Murmushi
kawai khalil yayi ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika masa yace "Ga
wannan ka sha kankana" Aminu ya karba hannu bibbiyu yana cewa "Allah ya taimakeka
oga" Wani shegen kallo Nihad ke ma daga Khalil din har Aminu tana jin kamar ta
hadiye zuciya don takaici, nan ta kara jin wani sabon tsanar Khalil ya dirar mata,
wato fafa yake yi sbda Abba ya aura masa ita, ji yake babu ya shi a duniya, Bayan
sun bar layin tana kallonsa ta madubi tace "Kai yanzu kawai jin kanka kake saboda
Abbana ya daukeni ya aura maka ko? Gani kake ka fi kowa sa'a a duniya tunda yanxu
kudin da Abbana ke baka ya ninku linkin ba linkin har da su kyautar dubu daya,
shkkn xaka dinga amfani da ni kana cin kudin Abbana" Khalil yayi wani murmushi bai
tanka ta ba, ta murguda baki tace "Ai shi dama talaka bai iya samun waje ba, nasan
yanxu alfahari kake yau gani matarka ko?" Yace "Ohk" Ta kara murguda baki bata kuma
ce masa komai ba har suka isa gida, sauka tayi daga motar bayan ya bude gate tayi
shigewarta ciki kamar xata tashi ciki, yayi wani murmushi kawai ya motar ya shigar
da shi compound din. Bayan Nihad ta idar da magrib ta fito parlor ta samesa kwance
saman dogon kujera yana waya, ganin bai lura da fitowarta ba duka a hankali ta
rarrafa har bayan kujeran ta kasa kunne tana sauraron wayar da yake yi, A hankali
taji yace "Nan da wata daya in sha Allah xan dawo, idan kuma na dawo baxan sake
fita ba sai bayan aurenmu" Yana fadin haka babu sunan da ya fado ran Nihad sai
Nadeeyah don har ta haddace sunan nata a xuciyarta, ta ɗan kyabe baki tana tsugunne
bayan kujeran tana kara kasa kunne, Taji yace "Aa, akwai dalilin da ya sa na dade
wannan karan Nadeeyah, ba wai da son raina bane, amma in sha Allah na kusa gama
abinda nake yi, ni kaina na gaji da USA haka" Buda baki Nihad tayi hangangan jin
sunan kasar da ya kira, Tunda aka haifeta bata ta6a ganin me lafta karya kamar
wannan mutumin ba, wato USA?? Mutumin da ko ruwa ta kasa sha a garinsu balle ta ci
abinci shine yake karyan yana USA, ya ma san full meaning din USA din kuwa?? Taji
yayi dariya ya mike zaune yace "Wai da gaske??" Magana yake amma bin parlon kawai
yake da idanuwansa don banda kamshin Nihad babu abinda yake ji a parlon, amma kuma
bai ga alamarta ba, don haka ya koma ya kwanta a hankali yace "Ke ce farko kece
karshe Nadeeyah, in sha Allah baxan hada ki da kowace mace ba, don kin min hallacin
da baxan manta ba, in dai kuma ba baturiya kike son in auro mu dawo Naija tare in
hada ku gida daya ku zauna ba, kinga ai nasan baxa kiyi kishiya da ita ba" bayan
few seconds yayi murmushi yace "Ya na ji kin yi shiru?" Mikewa Nihad tayi tana tafe
hannu tace "Ni wallahi ban ta6a ganin inda babba yake karya ba sai kai..." tuni
Khalil ya katse wayar, ya mike tsaye yana kallonta, da mamaki Nihad tace "Kasan
ma'anar USA kuwa? Kasan ina ne Usa? Me yasa baka tsoron yin karya a rayuwarka?"
Yace "Kin karya daya daga sharadinmu don haka nima dole xan karya daya...." Yana
gama fadin haka ya bar parlon ta marairaice ta bi sa da kallo har ya shige dakinsa,
ta fi minti biyar tsaye parlon can dai ta bi bayansa, a hankali ta murda kofar
dakinsa, tsaye ta gansa yana unbuttoning shirt dinsa, ta turo baki tace "Toh kayi
hakuri" Ya juyo ya jefa mata wani kallo yace "Baxan yi" Ta marairaice tace "Don
Allah mana" Bai sake kulata ba ya shige bandaki, ta ɗan kyabe baki, sai kuma ta
dinga kallon wayar tasa dake gefen gado, tana tafiya a hankali kamar munafuka ta
karasa gadon ta dau wayar, number Nadeeyah ta shiga tana kallon number tana ta6e
baki, wai ba ma tayi blocking din number nan ba, wato unblocking yayi, tana dai ta
kallon number, can ta ja tsaki kasa kasa ta kara blocking number tayi deleting ta
ajiye wayar ta fita da sauri. Fitowa Nihad tayi dai dai sanda Khalil ma ya fito
daga dakinsa, ta 6ata fuska tace "To ai cikin deal dinmu baka ce idan ana kwankwasa
gate kai kadai ne xaka dinga xuwa budewa ba, nima xan iya fita in bude tunda ba kai
kadai bane cikin gidan" Ba abinda yace mata ya nufi kofar parlor xai je bude gate
din da ake ta bubbugawa kamar xa a cire, Nihad ta tafi jikin window dake parlon
tana kallonsa har ya isa gate din, Yana tsaye bakin gate din yace "Waye?" A mugun
fusace Umma tace "Uban me tambaya, nace uban me tambaya, halan gidan na ubanka ne
idan ka ji an kwankwasa gate sai ka tambayi waye sannan ka bude?" Kawar Umma dake
gefenta tace "Wai kaddai Dreban ne ke maki wannan tambayar?" Umma tace "Atoh ba
matsiyaci bane? Kuma kin mance matsiyata basu iya samun waje ba?" Hajiya Turai tace
"Aa ga alama" Umma tace "Ai kinsan gidan Ardo ko Nenne dake kauye ne shi yasa yake
tambayar waye" Hajiya Turai ta kwashe da dariya tace "Sai dai haka kam" A mugun
fusace Umma tace "Au, baxa ka bude min gate din ba??" Khalil yace "Me gyara yana
hanya don tun jiya gate din ya samu matsala, mu ma bamu samu fita ba duk yau, don
haka sai ku jira" Buda baki Umma da kawarta suka yi jin abinda yace, shi kam yana
gama fadin haka ya juya ya bar bakin gate din ya koma ciki, Nihad na masa wani
kallo tace "Waye a gate din da kaki budewa?" Yana kallonta da kyau yace "Warce kika
yaudari kanki kika bai ma matsayin mahaifiyarki" Nihad ta zaro ido tace "Umma??
Shine kaki bude mata gate din?" Bata tsaya jin abinda xai ce ba a fusace ta taho
xata fita daga parlon ta je ta bude ya fixgota, tana tsaye dab da shi yana kallonta
da kyau yace "In har kina son mu rabu cikin salama ba tare da iyayenki sun yi fushi
da ke ba ko an ga laifinki to kar ki tsallake umarnina ko daya, datse alqarki da
warce kike kira da Umma yana daga cikin umarnina gare ki, bayan mun rabu xaki iya
ci gaba da mu'amala da ita wannan ba matsalata bace, amma muddin muna tare babu ke
babu ita" Nihad was shocked and lost of words at first, can dai tana girgiza tace
"Amma kasan abinda kake cewa kuwa? Kasan warce kake cewa xaka datse alaqata da
ita?? Kasan wacece Umma kuwa ko dai duk zamanka gidanmu baka san matsayinta ba?
Matar Abbana ce fa? First wife din Abbana ce, She is my step mother, kuma duk
duniya babu wanda ke sona baya ga ita, ban san dai ko Mumy da ta haifeni ba ba
tunda ita bata ta6a nuna min son da take min a fili ba na Umma kawai na sani, Umma
tun tasowata ban ta6a cewa ga abinda nake so a duniya an hanani a gidanmu ba, kome
nake so shi nake samu, yanda Umma taga Abbana ke ji da ni haka ita ma tafi sa ji da
ni, kuma bata ta6a hanani yin duk abinda nake so in yi ba tunda a ɓangarenta ma na
taso, she is 100% in support of me always, ta daukeni kamar er da ta haifa a
cikinta, dai dai da second daya bata ta6a banbanta ni da Nihal ba, don sai taki
goyon bayan Nihal amma ni ta goyi bayana, ba kuma ta son bacin rai na ko na second
daya, yanda na shaku da Umma ko Mahaifiyata ban shaku da ita haka ba wllh, don dama
tun ina karama ta maidoni dakinta, ita ce komai na, amma shine yau xaka bude baki
kace min xaka datse alakata da Umma?? Kana da hankali ma kuwa?" Kallon cikin ido
kawai khalil ke mata, bai kuma ta6a jin tausayin rayuwarta ba sai a wannan lokacin,
Ta fashe da kuka tace