Showing 219001 words to 222000 words out of 268471 words
ta
daga kai ta kallesa jin bai amsa gaisuwarta ba, yayi kasa da murya yace "Now tell
me ur problem pls Nadeeyah, is it Nihad? In dai ita ce u need not to bother plss ba
gida daya zaku zauna ba, sai ma ku yi wata da watanni baku ga juna ba i am assuring
you, pls ina son ki kwantar da hankali ki daina duk wani kokwanto a ranki, kuma ki
sa a ranki i owe u a lot saboda halaccin da kika min" Nadeeyah tace "And this is
the fifth time u are saying this to my ears, komai kace saboda halaccin da na maka
ba, ko kuma kace baza ka karya alkawarin auren da ka min ba... so what i want u to
make me understand now is that saboda abun da kake ganin na maka ne kake so ka
aureni so that it wont be like baka min adalci ba, ko kuma saboda alkawarin da kake
ikirarin ka min na aure shine zai sa ka aureni don ka zamo me cika alkawari or
whatt?" Khalil yayi shiru yana kallonta babu ko kiftawa, tayi wani murmushi tce "No
talk to me" Yace "Why are you complicating issues Nadeeyah? Me yasa zaki yi wannan
tunanin?" Ta girgiza kai tace "You are the one complicating issues Kjay, bana
mantawa kwanakin baya na tambayeka me ya kai ka gidansu Nihad driving, a ina kasan
su har kaje gidansu, but u told me that should be a story for another day, kaga sai
yanzu na fahimci cewar saboda ita kaje gidansu ka nemi driving don ka zauna a gidan
har ka aureta" Khalil ya zaro ido yana kallonta yace "Billah ban taɓa ganinta ba
sae da naje gidan, kin ji na rantse, kuma Nadeeyah na gaya maki times without
number mahaifinta ne ya hada aurena da ita, wllh at first bata san ni aka aura mata
ba mw" Nadeeyah ta mike tace "My frnds are waiting for me inside kuma wucewa suke
son za su yi" yayi shiru yana kallonta, can yace "Ohk sae mun yi waya, ki gaida
Mumy" Daga haka ya mike ya nufi motarsa ita kuma tayi wucewarta cikin gidan.
Inna ce zaune saman kujera a dakin Umma, ga Umman kwance saman gado ana kara mata
ruwa sai nishi take Kamila da Nihal na zaune gefenta, Zaune a dakin Mumy ce da
matan yayan Abba duk sun zo duba Umma, Hajiya Turai ma na zaune daga bakin kofar
dakin, Inna tace "Toh ni dai bamu san kan ciwon Sumayya ba gaskiya, abu kamar wasa
karamar magana ya zama babba, daga fasa goshi da targade a hannu, anya ba aljanu
suka shafeta ba kuwa" Babu me cewa komai dai a dakin, sallama aka yi can parlor
Inna tace "Kuma masu shigowa dubiyan nan ma ya kamata a hanasu haka don ba a san
zuciyar wani ba, banda haka ciwo yaki ci yaki cinyewa, ta ina zamu kama hanyar kai
akwati hankali ba a kwance ba, kila ma har sun gaji da jira a can Habujan kada ma
suyi tunanin cinye kudin aka yi" Husnah ce ta makale jikin kofar dakin ganin mutane
da yawa zaune ciki sai wuwwurga ido take, lokaci daya kuma tana sosa gabanta daga
cikin Hijabin jikinta, gaba daya tayi wani zuru zuru da ita kamar ba Husnah ba,
Hajiya Turai ta yamutsa fuska jin wani axababben doyi da ya bugi hancinta, Inna ta
toshe hanci da gyalenta a gigice tace "Wacece wannan kuma? Ba haya tayi a wando ko
me?" Husnah ta ɗan durkusa tana in ina tace "Aa wajen Umma na zo dama... Umma nake
nema" Umma dake fama da kanta ta ɗan bude ido daya tana kallon Husnah, Inna na kara
toshe hancinta a gigice tace "Wacece Umma, me zata maki?" Husnah ta fashe da kuka
tace "Ni dai dama inda zan samu Nihad nake nema, ko ta waya ne don Allah" Inna ta
mike da sauri ta koma can kofar bandaki tace "Wai wannan doyin meye haka yake
gigita ni...." Mumy na kallon Husnah jin abinda tace, tace "Me Nihad din zata maki
kike nemanta?" Umma ta mike zaune da sauri ba tare da ta shirya ba tace "Ke ya zaki
fado ma mutane daki haka kai tsaye?? Daga ina haka?"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son
sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da
xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan
turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba.
Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu
xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da
hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls
guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda
hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls
guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din
da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman
in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800,
6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar
maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰
65
Inna bata ba Husnah chance din magana ba ta daka mata wani tsawa tana kara toshe
hanci tace "Don Allah ki fita ki bamu waje, wacece kuma Nihad, Nihad da ke gidan
mijinta ɗan Janar Jikamshi, meye hadinki da ita" Umma da zuciyarta ke bugawa sosai
tace "Turai don Allah ki fitar mana da ita zuciyata tashi take...." Husnah ta
marairaice tace "Ko number...." Hajiya Turai ta mike da sauri cikin daga murya tace
"Fita ki bamu waje, fita" Juyawa Husnah tayi da sauri ta bar bakin kofar ganin
Turai ta yo kanta gata jibgegegiyar gaske, Nihal ta bi Husnah da kallon mamaki,
Umma ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ta koma da kyar ta kwanta har sannan
gabanta na faduwa, Inna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Da kyar idan ba
wani cutar bane ya kamata, amma wannan doyin gaskiya ba na lafiya bane, a bude mana
window a kara Ac...." Mumy ta ji kamar ta bi bayan Husnah taji neman me take ma
Nihad, tana ta nazarin maganan nata amma ta kasa tashi sai kallon kofar dakin take.
Ana idar da magrib Mami ta shiga dakinta, tun yamma take da baƙi a gidan basu tafi
ba sai dab da magariba, tana kallon Nihad dake kwance saman darduma tace "Me yasa
kika kwanta a kasa?" Cike da karfin hali tace "Sallah nayi" Mami tace "Toh koma
saman gadon" Nihad ta mike ta kwanta kan gadon, tun dazu zazzabin ya dawo mata
sosai amma a haka ta daure ta tashi tayi sallah, Mami ta dauke darduman ta ajiye
inda yake sannan tace "Me kike son za ki ci yanzu?" Nihad ta girgiza mata kai
kawai, Mami ta kashe Ac din dakin ganin kamar sanyi take ji, sannan tace "A kawo
maki Custard za ki sha?" Nan ma Nihad ta girgiza mata kai kawai, Mami ta juya ta
bar dakin, Bilkisu ta kira ta sa ta dama Custard din, ba a dau lokaci ba sai ga ta
ta shigo da shi a cup Mami ta amsa ta kai cikin dakinta tana kallon Nihad ta ajiye
Cup din a kasa tace "Bari ya ɗan huce sai ki tashi ki sha" Daga haka ta tafi ta
gyara curtains din dakin sannan ta rage hasken wutan ta fita.... Bayan minti goma
Mami ta sake komawa dakin, ganinta still a kwance tace "Ai ya huce haka, tashi ki
dauka ki sha" Nihad ta mike zaune, Mami ta dau cup din custard din ta mika mata,
amsa tayi amma tana kallon cikin cup din taji zuciyarta ya fara tashi, ta kauda kai
tace "Bazan iya sha ba" Mami tace "Toh me za ki ci?" Shiru tayi bata ce komai ba,
Mami tace "A kawo shayi?" Nan ma dai girgiza kai tayi, Mami tace "Kin dai san baza
ki kwanta da yunwa ba ko? Think of anything you want to take ayi a kawo maki yanzu"
Hawaye ne ya cika idonta, Mami ta karasa kusa da ita cikin kwantar da murya tace
"Shayin ma baki so?" Ta gyada mata kai, Mami tace "Toh a siyo maki abu a waje zaki
ci?" Nihad ta gyada mata kai, Mami ta juya ta fita daga dakin, wayarta dake parlor
ta dauka tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga tace "Eatry zaka je
yanzu ka siyo abinci ka kawo min" Yace "Abinci? Wani irin abinci?" Mami tace "Idan
an samu pounded yam ko Semovita with vegetable soup" Yace "Ohk" Katse wayar tayi ta
zauna saman kujera. Ba a dau lokaci ba Khalil ya dawo rike da ledan takeaway din
abincin, ya ajiye parlon Mami yana kallonta, tace "Na manta ban ce ka hado da
fruits ba" Yace "Yanzu komawa za ayi a siyo fruits din?" Mami tace "Ehh" Juyawa
yayi a hankali ya fita daga parlon, ta dau abincin ta shiga dakinta da shi, ta kira
Bilkisu ta kawo mata plate, tana gama zuba pounded yam din a plate ta kalli Nihad
tace "Sauko kasa ki ci" Nihad ta mike zaune ta sauko kasa ta zauna kan rug da ta
shimfida mata tana kallon pounded yam din, it looks so enticing kuma bata ji
zuciyarta na tashi ba, Ta kalli ruwan wanke hannu da aka ajiye mata ta wanke
hannunta sannan ta fara cin pounded yam din, Mami tace "Do not rush it, idan kin ci
kadan ki rufe anjima sai ki ci sauran" Nihad ta gyada mata, Mami ta dauko mata
magungunanta ta ajiye gabanta sannan ta juya ta fita, Nihad bata wani ci da yawa ba
kamar yanda Mami tace mata, ta dau maganinta ta sha sannan ta rufe abincin ta tafi
bandaki ta wanke hannunta, ta dauro alwala ta fito tana idar da sallah ta kwanta
bacci ya dauke ta. Wajen karfe sha biyu saura Mami ta shigo dakin ganin idonta biyu
tace "Za ki sha kankana a kawo maki?" Nihad ta girgiza mata kai Mami ta dau abinda
zata dauka ta fita daga dakin.... Da kyar Nihad ta bude ido ta sauko daga saman
gadon Mami ta durkusa saboda daure mata da mararta yayi, Mami dake zaune saman
darduma ta kunna wutan dakin tana kallonta tace "Ya aka yi?" Tana yarfe hannu cike
da karfin hali tace "Cikina ke min ciwo" Mami ta mike da sauri tace "Ciki kuma?"
Kallon agogo tayi taga karfe uku saura na dare, ta zagayo side din da take tace
"Sannu, tashi zauna gefen gadon" Mami ta dagota zata zaunar da ita gefen gadon taga
stain din jini a rigar jikinta, cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un" Nihad ta koma ta durkusa saboda murda mata da maran ke yi sosai,
Waya Mami ta dauko da sauri tayi dialing number Khalil, sai da ya kusa katsewa ya
daga, Tace "Ka taho part dina yanzu yanzu" Daga haka ta katse wayar, ta kara dago
Nihad tana mata sannu, duk ta rikice ta rasa abinda zata yi... Khalil na shigowa
dakin ya nufosu da sauri ganinta rike da Nihad yace "Me ya faru Mami?" Mami tace
"Wai cikinta ke ciwo and she is bleeding ko za mu tafi asibiti ne?" Ai bai san
sanda ya amshi Nihad daga hannunta ba hankali tashe yana kallonta yace "When did u
start bleeding?" Ta kasa ce masa komai sai sai hawaye ke sauka idonta, tuni Mami ta
dauko makullin motarta, ganin yanda ya tsaya shi ma ya rasa abun yi duk ya rude, ta
masa tsawa tace "Dallah ni ka fito min da ita mu wuce asibiti" Daga haka ta fice
daga dakin da sauri zata kai ma drivernta makullin mota kafin ya fito da ita,
Asibitin da ya fi ko wanne tsada a Abuja Mami ta sa suka tafi, kuma har suka isa
asibitin bata daina bleeding din ba, duk iya dauriyarta sai da ta fashe da kuka
sosai, likitocin suka shiga da ita emergency, tsabar rudewar da Khalil yayi har
mancewa yayi ashe shima fa likita ne, ya jinginar da kansa jikin bangon asibitin
with throbbing heart, he just cant say why he is bleeding that way, Mami ma ta kasa
zaune ta kasa tsaye a corridor din emergency ward din, she looks so disturbed,
lokaci daya Khalil jikinsa yayi mugun sanyi, he just can't imagine Nihad loosing
the pregnancy, ya kasa ci gaba da tsayuwa ya zauna kan kujeran dake wajen ya rike
kansa zuciyarsa na bugawa, bayan kusan minti arba'in wani baturen likita ya fito,
Mami na ganinsa ta nufesa da sauri, gabanta na faduwa da turanci take tambayarsa ya
ake ciki, yace ta samesa a office, sosai taji gabanta ya fadi, Khalil ya daga kai
yana kallon likitan har ya bar wajen, can ya kalli Emergency ward din, wani
bahaushe ne ya fito, Mami ta kara bin sa, cike da karfin hali tace "Likita ya ake
ciki don Allah??" Ya tsaya yana kallonta yace "Ki kwantar da hankalinki Hajiya, she
will be fine da izinin Allah, mu je office" Bin bayansa tayi zuwa office dinsa,
suna shiga ta zauna saman kujera ya kunna Ac din babban office din nasa ya zauna
yana kallonta kamar yanda ita ma take kallonsa, yace "Ki kwantar da hankalinki,
bleeding din ya tsaya amma there is high chances of her miscarrying the pregnancy
gaskiya" Mami ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, sosai taji hankalinta ya tashi,
tayi karfin halin cewa "Cant anything be done about it pls Dr?? Babu abinda za a
iya yi?" Likitan ya girgiza kai yace "Kawai dai yanzu zan baku shawarwari ne ta
yanda za a tafiyar da cikin nata har Allah ya sa ta wuce stage din nan, she is just
4 weeks pregnant now, and she is having a cervical insufficiency kinga idan ba abi
a hankali ba sannan kuma ba wani iko na Allah ba she is going to loose the
pregnancy at anytime, bazai zauna ba..." Mami tayi shiru tana kallonsa ta ma rasa
abinda zata ce masa, he could see how worried she is, yace "Nan da sati biyu ya
kamata ku yi mata pre natal Ultrasound saboda its likely yan biyu take dauke
da...." Mami ta bude ido sosai tana kallonsa, ya gyada kai yace 'Yeah mun ga alamar
hakan but it's not as if we are 100% sure don at this stage ba a gani, Allah ya
bamu ikon gano hakan ne base on experience and how good we are" Yana murmushi ya
kare maganar, Mami dai ta kasa ce masa komai, Cikin kwantar da murya yace "In sha
Allah everything will be fine Hajiya, kar ki wani daga hankalinki, but nan dai da
sati biyu ayi Ultrasound din don tabbatarwa, by then she is 6 weeks pregnant" a
hankali Mami tace "Amma babu abinda ya samu cikin yanzu ko Dr?" Yace "Cikinta na
nan har yanzu, kawai dai yanzu zan baki measures da za a bi don gudun miscarrying
cikin, sannan we will keep her here for some days, Da farko well balanced meal,
kuma duk wani abu da zai dameta ya daga mata hankali da fargaba a gujesa gaskiya,
sannan she should be on bedrest, shi yasa nace za mu yi admitting dinta a nan na
yan kwanaki..." Sosai Mami ta basa attention dinta tana sauraronsa har ya kai
karshe, Bayan ya gama Mami tace "Idan aka bi duk abubuwan nan da ka fada ai
shikenan babu wani abu da zai samu cikin kuma ko Dr?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma
yace "Hajiya to be sincere to u... the chances of keeping this pregnancy, and the
chances of loosing it is just 50/50, that's just the plain truth" Mami ta kasa ce
masa komai, can ta mike tace "Muna bukatar sallama zuwa da safe Dr" Ya daga kafada
yace "Alright then, Allah ya kai mu goben" Tace "Zan iya shiga in ganta yanzu?"
Yace "Sure, ai an maidata ward yanzu haka" Tace "Nagode" Daga haka ta fita daga
office din, wani likita ta tambaya ya gaya mata ward din da aka kai Nihad, tana isa
kusa da ward din ta tsaya ta ciro wayarta a jaka tayi dialing number Janar, hoping
he is going to pickup, yana fara ring kuwa ya daga, daga bangaren yace "Why are you
awake by this time??" Tace "Fatima ce bata da lafiya" Har Janar zai tambayeta
wacece Fatima kawai sai ya tuna warce take nufi wato Nihad, yace "Hasbunallah
what's wrong with her?" Mami tace "Na kira Dr Rukayya ta zo jiya ta dubata da na
fahimci bata da lafiya, bayan ta dubata ta tabbatar min tana dauke da ciki"
Janar ya ɗan yi shiru, can yace "Maa sha Allah, that's a good news, Allah ya bata
lafiya, maa sha Allah" Mami tace "Toh dazu Ina sallah wajejen karfe uku ta fara
bleeding, cause she is in my room" Janar yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,
kuna ina yanzu?" Tace "Muna asibiti, and they are telling me nonsense, that there
is high chances of her loosing the pregnancy, sannan cikin ma na yan biyu ne" Janar
yace "Take her away from that hospital immediately, i will make some calls now zuwa
gobe za ki fita da ita America....." Mami tace "Shi yasa dama na kiraka" Janar yace
"Ina khalil din?" Tace "Tare muka zo asibitin da shi, amma ni ban ga amfanin ma
zuwa da shi ba, yanzu na fito office din likitan wanda nake tunanin bai san abinda
yake ba gaskiya, har yana bani assurance akwai high chances of loosing the babies
who does that, i dont think he is okay" Janar yace "Ku koma gida ku fara shiri
kawai" Mami tace "Shikenan sai anjima" Daga haka ta katse wayar ta shiga ward din,
Khalil na zaune kusa da Nihad yana rike da hannunta yana kallonta, ita kuma tana
bacci, gaba daya ya zama wani iri kamar shi ne babu lafiyan, yana ganin Mami ya
juya yana kallonta, he doesn't look himself at all, gaba daya a sanyaye yake, Mami
ta nufi gadon tana kallonta ita ma, a hankali ya mike ya fita daga ward din zai je
gun likitan don jira yake ta fito dama. Da asuba Mami ta bar masu asibitinsu tare
da Nihad bayan ta biya bills din, dama sojan da ya kawota da motar soja guda daya
da ya biyosu suna cikin asibitin giving dem security tun a jiyan, gari ya fara
haske suka isa gida, Mami