Showing 84001 words to 87000 words out of 268471 words
gida, toh gashi yanxu ko kayan da xan
canza gobe bani da shi" Yace "Sae ki maimaita na yau" kuka take sosai, ya juya mata
baya, ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta koma ta kwanta a hankali, bayan kusan
awa daya ya kunna torch dinsa ya haska fuskarta ya ga bacci take.
Can kusan asuba xafin jikinta ya farkar da shi, kamar jiya tana kusa da shi ta
takure waje daya, ya kai hannu jikinta ya ji da xafi....
*Ki biya dari biyar ki karanta hankalinki kwance er uwa*
NIHAAD is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of
payment via👇🏻
07087865788....
27
Yau ma kamar jiya hasken rana ne ya sa Nihad ta farka, da kyar ta mike xaune tana
jin duk jikinta na mata ciwo barin kanta da yayi mata nauyi, sosai hankalinta ya
tashi ganin khalil baya dakin, ta hade kai da gadon karan da take kai tana kuka a
hankali, can dae tayi karfin halin mikewa ganin lokaci na tafiya bata yi sallah ba,
ta nufi yar jakar da ta sa brush dinta da Toothpaste ta dauka ta fita daga bukkar.
Bayan ta idar da sallah tana xaune saman abun da tayi sallan lkci lkci tana share
hawayen dake gangaro mata, rashin ganinsa na kara saka mata damuwa a kan wanda take
ciki, shadow da ta gani bakin kofa ya sa ta daga kai da sauri hoping shi ne ya
dawo, amma sai ta ga ba shi bane, wata budurwa ce warce xa su yi sa'anni da Nihad
din ta shigo dakin, fara ce kal kal don duk hasken Nihad yarinyar ta fi ta, ga ta
kyakkyawa ajin karshe, dogon gashinta da aka kitsa gida biyu manya manya har
ƙafadunta suke tabowa, ga uban wushiryarta a baki, Nihad ta ganeta don jiya kaya
kala biyu ta bata da turare, budurwar na murmushi ta duka gaban Nihad ta ajiye mata
kwanon sha dake hannunta tace "Hannu, yau kamar kin makara ko" Nihad ta kirkiri
murmushin ita ma tace "An tashi lafiya" Yarinyar tace "Lafiya lau, ga farau farau
nan na kawo maki, yanxu xa a dunduma tuwon sae a kawo maki" Sosai gaban Nihad ya
fadi jin kalmar tuwo, ita fa bata ta6a sanin akwai wani kalan tuwo bayan fari ba,
gwara gwara amala ta san baki ne, to da wannan abun da suke kira tuwo ba gwara a
bata amalan ba, ta dai sakar mata wani murmushin karfin halin tace "Toh, nagode"
Yarinyar na wasa da gashinta tace "Ni sunana Furera amma ana kirana Fure ke kuma
fa?" Nihad ta sauke idonta tace "Sunana Nihad" Yarinyar ta zaro ido tace "Sunan yan
birni, ae baxan ma iya kiran sunan ba" Nihad tace "Toh ki kirani Ummi" Fure tace
"Yauwa gwara wannan, amma ae xa ku yi sati a nan ko?" Nihad ta kalleta da sauri ta
girgiza kai tace "Aa yau xa mu tafi" Yarinyar tace "Gwaggo fa tace min xa ku yi
sati" Nihad xata yi magana sai ga Khalil ya shigo bukkar da sallama, lkci daya
kamshinsa ya cika Bukkar, Fure ta koma gefe tana d'an Murmushi, tace "Hamma wai
ashe yau xa ku tafi?" Yanda take maganar kasan a kunyace take da Khalil, Khalil ya
kalleta yace "In ji wa?" Fure ta nuna masa Nihad, yace "Aa xa mu yi sati" Gaban
Nihad yayi mugun faduwa ta gwalo ido tana kallon khalil a ranta ta dinga nanata
satin da yace, meye kuma sati, ba dai sati daya yake nufi ba, cike da murna fure
tace "Yauwa dama haka Gwaggo ta sanar min, ai ko naji dadi sosai, duk xan bi in
xaga da Ummi kauyen mu da wanda ke gaba da namu, a kawo maka farau farau din ne ko
fura da nono xaka sha, nonon ma sabuwa ce jiya aka tatso" Yace "Toh kawo min fura
da nonon" Tace "Toh" daga haka ta fita, Nihad ta marairaice tana kallonsa tace
"Amma dai xaka maida ni gida sae kai ka dawo kayi satin a nan?" Ya dauko tabarma ya
xauna kai ba tare da ya kalleta ba yace "Ko kuma ni in tafi bayan sati daya in xo
in dauke ki ba" Bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tace "Don
girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri..." sai a sannan ya daga kai ya
kalleta, ta hade tafin hannunta tana kuka a hankali tace "Don Allah kayi hakuri,
wallahi baxan iya ba, kaji har na rantse" Gyara xama yayi yace "Bukka guda Gwaggo
xa ta bar maki kiyi rayuwarki ke kadai har bayan sati dayan babu me takura ki"
Nihad ta mike da sauri ta nufesa ta durkusa gabansa tana kuka tace "Wallahi xan iya
mutuwa idan ka tafi ka bar ni a nan, kar ka tafi ka bar ni" Kallonta kawai khalil
yake, dai dai nan Fure ta turo kai cikin Bukkar rike da kwaryan nono da fura, Nihad
ta koma gefensa da sauri ta zauna, Fure ta durkusa gabansa ta ajiye fura da nonon
tana kallonsa tace "Kana son sukari?" Khalil yace "Kadan" Mikewa tayi ta nufi kofa
xata fita, khalil ya bi ta da kallo, Nihad ta kallesa, sannan ta kalli yarinyar har
ta fita, Khalil tankwashe kafarsa yana kallon fura da nonon dake cikin kwarya a
gabansa, muryar Nihad ya ji kamar daga sama tace "Kanwarka ce?" Ya ɗan kalleta, sai
kuma yace "Aa, er makotanmu ce, Baabarta ai ta shigo kun gaisa jiya" Sai ga fure ta
shigo rike da sugar a hannunta, durkusawa tayi gaban Khalil tana murmushi ta juye
sugar din a kwaryan nonon, ta ɗan kallesa tace "In dama maka?" Ya gyada mata kai
yace "Ehh" Nihad dake kallonta ta mike tace "Bar shi xan yi" Fure ta kalleta sai
kuma ta mike tace "Toh" Kallonta kawai khalil yake babu yabo babu fallasa ta dawo
gabansa ta durkusa ta dau ludayi ta saka cikin kwaryan, Fure ta mike ta fita, Nihad
na kiciniyar dama fura da nonon kwaryan ya kife duk suka malale a kasa, da mamaki
Khalil da ya koma baya yake kallonta, kana ganinta kasan bata ta6a dama fura da
nono ba, ta turo baki ta mike ta bar wajen ta koma can karshen gadon kara ta zauna
tana kallon mess din da tayi a kasa, khalil yace "Na kara sati daya a kan satin da
nace xa ki yi a nan" da sauri ta mike ta nufosa ta fashe da kuka tace "Wallahi ba
da gangan nayi ba, kwa6ewa yayi a hannuna" Ya hade rai yace "Da baki iya ba me yasa
baki bar warce ta iya ba tayi" Tana goge hawayen idonta tace "Toh meye xata wani zo
tana ma mutane yauki kamar kubewa a nan?" Mikewa khalil yayi yace "Ni dai na gaya
maki, ki shirya kwana sha biyu nan gaba a nan" Nihad na kuka ta riko rigarsa da
sauri ganin xae fita cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri, idan na kara ko
kwana daya a kauyen nan yunwa xae iya kashe ni" Ya janye rigarsa daga hannunsa ya
fice daga bukkar, Nihad ta sulale kan inda ya tashi tana kuka a hankali. Goge
idonta tayi da sauri jin ana sallama, ta kalli matan da suka fara tururuwan xuwa
kofar Bukkar da take don gaisheta, da murmushi take amsa masu gaisuwar tasu cike da
karfin hali don yunwa ba na wasa ba take ji, tunda take bata ta6a jin irin wannan
kalan yunwan da take ji ba, wata mata ta shigo ta kwashe kasar dai dai inda fura da
nono ya xuba ta fita da shi, Nihad ta bi ta da kallo, to ko kiwon dabba ake yi ai a
tunaninta ba a kiwonsa a ordinary sand balle mutum, ko kaji ma ana shimfida masu
kwali.... Nan ko ga kasa kiri kiri a daki kamar a kofar gida, Gwaggo ce ta shigo
daga karshe rike da kwanon dumamen tuwo ta ajiye mata tace "Hannu Ummi, an tashi
qlau dai ko?" Nihad na Murmushin karfin hali tace "Ina kwana Mama" Gwaggo tace
"Lafiya lau, ga tuwo ki ci kafin kiyi wanka, ko dai kina son yajin daddawa a kawo
maki da man shanu" Da sauri Nihad tace "Aa nagode xan ci haka" Gwaggo tace "Toh,
Don naga jiya ma kamar baki wani ci tuwon ba, wannan na barbada maki me tauraro a
kai, xaki ji dadinsa, kinsan ku yan birni baku amfani da manda a girki" Nihad dai
sai ka rantse tallan close up take yanda take murmushin karfin hali tana kallon
tsohuwar, Gwaggo tace "Ko a damo maki hurar ki hada da tuwon naga faro faron ma
baki sha ba" Nihad ta girgiza kai tace "Aa wannan ya isa mama, nagode" Gwaggwo tace
"Idan kin gama ci sai ki fito an kai maki ruwan wanka" Nihad tace "Toh" Bayan
fitarta da kamar minti sha biyar Nihad ta mike ta fita tsakar gida, haka duk matan
gidan dake shirin surfe suka bi ta da kallo, Gwaggwo ta taso tace "Har kin cinye"
Nihad tace "Ina son xan yi wanka" Gwaggo ta rakata xuwa bandakin ta bude mata kofar
karan tace "Ga ruwan a ciki" Nihad ta saka kai ta shiga ciki, bayan matar ta bar
wajen kawai ta fashe da kuka, yau ita ke ganin rayuwa haka, yanzu a haka xata yi
wankan?? A daddafe ta watsa ruwa tana rike numfashi sbda uban zarnin da wajen ke yi
ta fito da sauri, har ta shiga bukka kallonta matan tsakar gidan suke, ko mai Nihad
bata shafa ba ta saka kayanta ta xauna gefen gadon kara jiki a sanyaye tana bin
kudajen dake ta shawagi a dakin da kallo, Sai kuma ta hade kai da gwiwa ta fara
shesshekar kuka tana jin kamar Ulcer xai iya kamata at anytime. Har rana bata ga
Khalil ba, aka kawo mata gwaza da mai da gishiri, da farko tayi xaton doya ce amma
bayan warce ta kawo mata ta fita, ta dauka tana kare masa kallo kafin ta 6are ta
kai baki a hankali, da sauri ta fito da shi tana yamutse fuska, a haka ta matsar da
kwanon a inda kwanon tuwo da faro faro suke tayi tagumi, cike da tausayin kanta.
Kusan karfe hudu saura Gwaggo ta leko bukkar tace "Ke baki fitowa shan iska Ummi,
ai da xafi dakin..." Nihad ta girgiza kai a hankali tana mata murmushin karfin
hali, alamar bata son ta fitowa, Gwaggo ta kyaleta ta tafi ta ci gaba da abinda
take, duk motsin da xata ji sai ta leka ko Khalil ne amma sai taga ba shi bane, a
haka har ta fita taje tayi alwala ta dawo tayi la'asar, xuwa lkcn jikinta rawa yake
saboda yunwa, she is very very hungry, amma babu abinda xata iya ci cikin abubuwan
da aka kawo mata, kukan ma ta gaji da yin sa yanxu ta daina, tana idar da sallah ta
kwanta saman gadon karan tana juye juye, daga karshe ta mike ta sauko kasa jikinta
na rawa ta bude farau faron dake kulle ta dauka, runtse ido tayi cike da karfin
hali ta kai bakinta kan kwanon ta rike breathing dinta sannan ta hau kwankwada,
ajiye kwanon tayi da sauri bayan ta kwankwadi kusan rabi, saboda wani amai da taji
ya taho mata, ta mike da gudu ta fita daga dakin, gwaggo da matan tsakar gidan dake
surfe suka taso da sauri suna tambayarta lafiya, nan ta dinga kwararar masu aman
abinda ta sha kamar xata shide, Gwaggo da duk ta rude tace "Subhanallahi, me ya
sameki, gashi baya nan" Wata mata ta kawo ruwa da sauri suka ba Nihad dake maida
numfashi, amsan ruwan tayi da kyar ta wanke bakinta duk jikinta na rawa, Gwaggo da
hankalinta yayi mugun tashi ta kawo mata kujerar tsugunno tace "Hannu, zauna nan,
zauna" Nihad ta xauna a hankali kan kujeran tana maida numfashi, Gwaggwo tace "Me
ya sameki kike hararwa haka?" Da kyar tace "Bani da lafiya ne dama" Matan gidan
suka dinga yi mata sannu, ganin yanda jikinta ke rawa Gwaggo ta maida ta cikin
Bukkar tana mata sannu ba adadi, wata yarinya da ta aika ta dubo mata Khalil a waje
ta dawo ta shigo Bukkar tace "Gwaggo bamu gansa ba" Gwaggo tace "Toh bari a mata
jike jike tasha ko xaxxabin xai sauka" Daga haka Gwaggo ta fita, kuka Nihad take a
hankali tana juye
juye tana jin kamar kanta xai fashe don ciwo, bayan wani lokaci sai ga gwaggwo da
kwano ta ajiye kasa ta dago Nihad tace "Ga nan jike jiken sassaken itatuwa na maki,
tashi ki sha, ba daci ba bauri, ba hamami" Nihad ta mike tana rawan sanyi Gwaggwo
ta dauko kwanon ta kai mata baki tace "Ungo sha" Cike da karfin hali Nihad dake ta
kallon cikin kwanon ta kurbi ruwan ciki, Gwaggo tace "Kara sha" Nihad ta runtse ido
ta kara kurba ta hadiye tsikar jikinta na tashi, dacin ruwan kuwa ba a cewa komai,
Gwaggo tace "Yauwa, to koma ki kwanta yanxun nan xaki fara xufa, su ararrabi ne da
sabara da tazargade, ga su nan dai" Nihad ta koma ta kwanta Gwaggwo na kokarin
lullubeta Khalil ya shigo Bukkar ya nufo Nihad yana kallonta, Gwaggwo tace "Wallahi
mugun zazzaɓi ne ya rufeta yanxun nan sai hararwa take" Khalil ya duka yana
kallonta ya kai hannu jikinta wanda yayi zafi kamar wuta, cike da damuwa Gwaggwo
tace "Akwai wani karamin asibiti a gidan Darho, kauyen da xaka wuto kafin ka zo
wannan, ko xaka kai ta a dubata a bata magani ɗan nan?" Khalil yace "Toh xa mu je
can" juyawa tayi ta fita daga Bukkar, Hannu ya kai goshinta duk da idonta a kulle
yake yace "Ina ke maki ciwo" Ta fashe da kuka ta tura hannunsa daga goshinta tace
"Ni ka maida ni gidanmu, idan ba haka ba sai Allah ya kama ka" kallonta ya tsaya
yi, can ya gyada kai ya koma gefe yace "Ohkk" tayi karfin halin mikewa cikin kuka
ta kamo hannunsa tace "Don Allah kayi hakuri ba don halina ba ka maida ni gida"
Yace "Toh ina ke maki ciwo?" Tana shessheka tace "Kai na, kuma ina jin yunwa" Ya
mike yace "Sakko" Da sauri ta mike xaune amma ta kasa tashi daga saman gadon duk
yana kallonta, ya mika mata hannunsa ta rike sannan ta mike tsaye a hankali, dukawa
tayi yana rike da hannunta ta dau Hijab jikinta na rawa ta saka, sannan ta dau
handbag dinta, ko bin ta kan atamfarta na karshe da kayan shafe shafenta bata yi
ba, a haka suka fita daga Bukkar, Gwaggwo da matan gidan suka taso, ana mata sannu
in chorus, Gwaggwo tace "Can asibitin ku ka nufa ko?" Yace "Ehh" Nan dai aka dinga
mata Allah ya sauwake, Fure dake tsaye kusa da wani ɗan mariki da aka daure tace
"Gwaggwo in rakasu asibitin" Da sauri Nihad ta kalleta, murya can kasa Nihad ke
girgiza ma Khalil kai tana cewa "Aa baxa mu je da ita ba" Ya ɗan kalleta ta gefen
ido, Gwaggwo tace "Toh ko kama maka ita ai sai fure ta dinga yi a asibitin ko" Da
sauri Nihad na Murmushi tace "Aa mama xan iya ai" Gwaggwo tace "Toh shkkn, Allah ya
baki lafiya sai kun dawo" Nihad dai bata ce komai ba a ranta kuwa tunani take ina
din xa su dawo da take ce masu sai sun dawo? Dalilin ma da yasa bata son Fure ta bi
su kenan don in sun tafi da ita ai dole su dawo da ita kauyen, ita kuwa bata fatan
abinda xai sake dawowa da ita kauyen nan, suna isa inda Khalil ya ajiye mota ya
saketa ya zaga daya side din, a hankali ta bude front seat din ta shiga, bayan yayi
warming motar ya ja motar, matan gidan da suka taru bakin kofar shiga gidan har da
masu daurin kirji, ga yaransu duk ba wando a tsattsaye su ma, sai daga masu hannu
suke kana ganinsu dai kaga yan kauyen kayau, haka ma sauran makota da suka fiffito
jin karar mota, Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya, at long last!!! har taji
xaxxabin ya tafi sai kuma bakar yunwan da take ji, tafiyar minti talatin suka yi ta
ga alamar sun fara shigowa gari, farin ciki gunta ba a cewa komai, bata ta6a
tunanin xata fito daga kauyen can da ranta ba, ta zata sai buzunta, so truly akwai
mutane irin haka a rayuwar nan, akwai mutane dake rayuwarsu cikin kauye haka? lkci
daya jikinta yayi sanyi, and they are leaving happily abunsu babu wani damuwa, ko
pole din wuta ita bata gani a garin ba balle a je ga an ja masu wuta, parking ta ga
khalil yayi dai dai wani pharmacy, duk da bata san inda suke ba amma tasan sun
shigo cikin gari gaba daya, ya kashe motar ya sauka yana kallonta yace "Sauko
malama" A hankali ta bude motar ta sauko ta bi bayansa tana jan kafa saboda jiri da
take gani, suka shiga pharmacy din, bayan sun gaisa da me Pharmacy din ya koma gefe
ya tsaya yana kallon Nihad da ta jingina da kofar pharmacy din bata shigo ba, har
ta rame tayi wani uban duhu kamar ba Nihad ba, Ya kalli me Pharmacy din yace "Ita
ce bata da lafiya" Me Pharmacy din yace "Sannu Hajiya karaso" Tana jan kafa ta tafi
gaban table dinsa ta xauna, Tunda aka haifeta ba a taba kawo su pharmacy idan basu
da lafiya ba, sai dai asibiti, amma wai yau ita ce a pharmacy xa a mata treatment
bata da lafiya instead of hospital, muryar Pharmacist din ne ya dawo da ita duniyar
tunanin da ta tafi, ta sauke idonta kasa a hankali tace "Zazzaɓi nake ji da ciwon
kai" Yace "Kina amai ne?" Ta gyada masa kai tace "Ehh nayi daxu" Yace "Ohk" Kallon
khalil yayi yace "Xa a maganunguna da allurai...." Khalil ya rungume hannunsa yace
"Sai dai magungunan kadai, don kauyen da muke akwai nisa, baxai yiwu mu dinga xuwa
muna komawa ba kullum" Da mugun shock Nihad ta kallesa, bata san sanda ta fashe da
matsanancin kuka tace "Don girman Allah ka rufa min asiri kar ka maida ni garin
nan" Khalil ya danne dariyarsa ya hade rai, Me Pharmacy ya tuntsire da dariya yana
kallon Nihad da duk ta gama rikicewa, Khalil yace "Shi garin namu kike ce ma garin
nan" Ta hade hannunta cikin kuka tace "Ka rufa min asiri mu wuce gida don Allah"
Khalil ya kalli me pharmacy yace "Malam ba mu maganin kawai, hanyar kauyen ba shi
da dadin tafiya da daddare, kaga magariba ya kusa" Kuka kawai Nihad take hankali
tashe tana kallon khalil, me pharmacy dai ya basu magunguna ya sa a leda ya mika ma
khalil yace "Duk prescriptions din na jiki" Khalil ya amsa yace "Nawa ne?" Me
pharmacy din ya gaya masa ya zaro kudin a aljihu ya mika masa, Yana kallon Nihad ya
daure fuska yace "Tashi mu je" Ta mike tana kuka tace "Kayi min rai kar ka sake
maida ni garin nan wallahi baxan iya xama ba kilan ma in mutu" Khalil yace "Fita mu
je" Fita tayi daga pharmacy din ya bi bayanta, tayi mugun ba me pharmacy din dariya
don sai kallonta yake,