Showing 18001 words to 21000 words out of 268471 words

Chapter 7 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

ta dauko takeaway daya ta ajiye ma Nihad,
Ayman na kallon Husnah yace "I think bari in kama wani dakin kawai" Husnah tace
"Ohk then" Daga haka ya fita daga dakin, Naf ta ja tsaki tace "Sai shegen girman
kai, wato jira yake in fara masa magana ko" Husnah tace "Ke dai kowa sai kice yana
da girman kai bayan kema kina fama da naki, duk fa Salman ne ya hura maki kunne ki
daina kula kowa sai ki dinga fakewa da ana maki girman kai" Naf tace "Ni fita ma
xan xo in yi yanxu, amma xan dawo later" Husnah tace "Ina xa ki? Baxa ki ci abincin
ba?" Tace "Idan na dawo xan ci" Husnah tace "Kar fa ki ki dawowa Naf, saboda ke
naki gayyato Zully nan fa" Naf tace "Ke wllh xan dawo, wani Alhaji ne ke ta damuna
da kira ya shigo kano, to yayi min alkawarin waya dama, shine xan je" Husnah tace
"Ahh, to maza ki je, Allah ya sa mu ga latest iphone" Naf ta dau figigin gyalenta
tace "Toh Allah ya sa bari in je, Nihad idan na dawo xa mu tsara yanda xa ayi da
ɗan kauyen can shi kuma" Nihad tace "Toh sai kin dawo" Daga haka Naf ta fita daga
dakin, Husnah tace "Tabdi, yau ni naga karfin hali wai barawo da sallama, wannan
idan yayi wata daya a gidan ai sai dai kuma ya koma rayuwa cikin main building ya
bar boys quarters kawai" Nihad tace "Sai yanzu rashin barina in xauna a hostel da
Mumy tayi ke kara damuna sosai, kinsan da na hakura amma tun da aka kawo wannan
drivern damuwan ya dawo sabo" Husnah tace "To ko xaki kara gwada yi ma Abba
magana?" Nihad tace "Babu yanda Umma bata yi da shi ba, amma da yake Mumy da ya
farooq sun hure masa kunne ya ki amincewa, sae dae kawai yayi ta bani hakuri wai
there is time for everything" Husnah tace "Gaskiya in har ba sallaman driver din
nan aka yi ba xaki takura sosai, gashi Abba baxai baki mota ba ko" Nihad tace "Ba
fa ruwan Abba, Mumy ce matsalar gidan nan sae yaya Farooq, amma ae Umma tayi
kokarin ganin an bani motar kwanaki hakan bai yiwu ba" Husnah xata yi magana
wayarta ya fara ring, tana dubawa taga Ayman ne, dagawa tayi tace "Ya? Wani room
number kake?" Yace "102... Pls Nihad ta bani minti goma mu yi magana mana" Husnah
tace "Ohk over there?" Yace "Yeah" katse wayar tayi tana kallon Nihad tace "Ayman
wants to speak to you" Nihad tace "Ohk kin katse wayar kuma" Husnah tace "No, yana
room 102" Nihad tace "Ina ga ya sha kwaya, nice xan bi sa dakin??" Husnah tace
"C'mon, minti nawa xa kiyi ki fito, he said just 10 mins, behave like the big girl
u are mana" Nihad tace "Look, ya bar ni ma inji da damuwata i don't have that
strength to talk" Husnah tace "Don Allah kiyi hakuri ki je Nihad, minti goman nayi
ko bai gama magana ba ki fito kawai, ko albarkacina ya ci mana, yana ganin idan na
gaya maki xaki ji shi yasa ya biyo ta wajena, ki je ki dawo ki ji yanda xa mu yi da
wancan ɗan kauyen shi kuma" Nihad ta d'an kyabe baki, sai kuma ta mike tana gyara
veil din abayanta tace "Wani room ma kika ce?" Husnah ta gaya mata, daga nan ta
fita xuwa dakin. Kwankwasa kofar dakin tayi, sai gashi ya bude yana kallonta da
murmushi fuskarsa yace "Welcome Nihad" gefensa ta bi ta shiga dakin ta xauna saman
one seater dake dakin tana kallonsa har ya dawo ya xauna gefen gado sannan tace "I
am all ears" shiru yayi yana kallonta, ta langwabar da kai tace "Kayi shiru" Ɗan
murmushi yayi yace "Donno where to start from, kinsan kina da wani kwarjini na
daban Nihad" Ta kalli agogon dake wrist dinta, sannan tace "Then just start from d
end" Dariya yayi sannan yace "Ohk, a takaice kawai ina son ki bani dama let date"
Tace "Sorry but i don't double date Ayman" Yace "What's d big deal about double
dating Nihad?" Ta girgiza kai tace "Tsari na kenan, i have my boyfriend, and yana
sona kamar yanda nima nake son sa, so what's d need of dating else where?" Shiru
Ayman yayi, can ya mike ya koma kan kujerar da take ya xauna a hannun kujeran xai
kama hannunta ta fixge ta matsa gefe sannan tace "I am sorry Ayman, ina da
saurayina kuma duk kun sani" Yayi kasa da murya yace "Yeah i know, but pls Nihad...
even if it's once a while, i will always provide u with all ur needs, i am not
talking about petty needs" Da mamaki tace "What's that u are talking about?" The
way he was looking at her directly in the eyes yasa ta mike tana kallonsa da kyau
tace "Seems Husnah bata ta6a baka labarina ba ko?? Kawai kana ganin mu tare, duk
inda take xaka gan ni, Ohk get this Ayman, my obstinacy have limit, it hasn't
attain to this extent, sorry" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice
daga dakin ta kullo masa kofar. Tana komawa wajen Husnah, Husnah ta katse wayar da
take ta ajiye, Nihad tace "Baki ta6a gaya ma Ayman wacece ni ba ko?" Husnah bata ce
mata komai ba, Nihad ta nemi waje ta xauna, Husnah tace "Toh wai meye a ciki, kawai
kin bi kin makale ma Aliyu da definitely kinsan yana da yan mata iri iri shi ma, ni
wllh Aliyun nan haushi yake bani, ga shegen ji da kai kamar ɗan jinin sarauta, duk
abinda ya daura ki a kai shi kike yi, ga samari iri iri ko wanne na sonki amma
kince ke sai Aliyu, to Aliyun me" Nan da nan Nihad ta hade rai tana kallon Husnah,
can ta ja tsaki ta dau jakarta ta mike ta nufi kofa, Husnah tace "Tun da an ta6a
numfashin ki ba dole ki nufi kofa ba, to baxa ki tsaya ki ji yanda xa mu yi da
sabon drivern naku ba" Ko sauraronta Nihad bata yi ba har ta fice daga dakin,
Husnah ta ta6e baki tace "Kawai ki makale ma mutumin da yan mata ke rububi a kansa,
ki dauki son duniya ki dora masa, shi kuma yayi ta yin kamar bai san kina yi ba, da
ma yana baki lokacinsa yanda ya kamata ne abun baxai dameni ba" Husnah ta ja tsaki
ta jawo abincin gabanta ta bude.....


Contact me directly via👇🏻

07087865788 WhatsApp only.
7️⃣
💖💖 *NIHAAD*💖💖




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




~~~~~~~


Sai bayan la'asar Nihad ta iso gida, bayan ta fito daga wajen Husnah school kawai
ta wuce tayi attending lectures daya, mai gadi na bude gate ta shiga gidan ba tare
da ta saurari gaisheta da yake ba, tayi parking dai dai inda motar take ta kashe,
sauka tayi ta kulle motar tana kallon inda mai gadin ke xama ko xata ga Khalil, ai
ko yana xaune, ko da wasa bai kalli inda take ba, sai ma danna torchlight phone
dake hannunsa da yake with full concentration, nan da nan taji har ranta ya fara
baci, wai wa yayi ma wannan mutumin hanyar xuwa neman aiki a gidansu? har ta juya
xata wuce ciki sai kuma ta dawo, fuskarta daure ta nufesu, Mai gadi na ganin ta
doso inda suke ya mike daga xaunen da yake yana gaisheta, Babu yabo babu fallasa ta
amsa sannan tace "Aminu kuna canza ma tsuntsaye na abinci da ruwa kuwa??" Yace "Ehh
Hajiya ko daxu da kaina naje wajen na basu abinci da ruwan" Mai gadi ne ke mata
magana amma banda hararan khalil babu abinda take with hatred, how dare him baxai
gaisheta ba ma, wani dogon tsaki ta ja tace "Aminu ka sameni wajen tsuntsayen" Daga
haka ta wuce fuuu xuwa bayan gidan inda cage din birds din nata suke, Aminu ya
kalli khalil sannan ya bi bayanta da sauri, sai a snn Khalil ya daga kai ya bi su
da kallo, suna isa wajen tsuntsayen tace "Aminu in tambayeka mana" Yayi kasa da kai
yace "Toh Hajiya" Tace "Wai waye ya kawo wancan yaron gidan nan da sunan ya nemi
aikin driving?" Aminu yace "Hajiya Habibu ne ya kawosa ae" Da mamaki tace
"Habibu??? Habibu dai?" Aminu yace "Kwarai Hajiya" Juyawa tayi ta wuce ta bar sa
tsaye a wajen, gida ta shige, Aminu ya dawo bakin gate ya xauna yana kallon khalil
dake kallonsa shi ma, yayi kasa da murya yace "Wai tambaya take wa ya kawoka, to
ban san ko na kwabsa ba da nace Habibu, kasan fa Habibu mutuminta ne, har makudan
kudi tana basa, to duk inda xata kai tsaye yake kai ta har ya jirata, ya sha gaya
min maganganu amma yace kar in gaya ma kowa" Khalil yace "Wani magana?" Aminu ya
gyara xama yace "Ae otal daddaya ne a garin nan da wajen shakatawa irin ta manya
bai ta6a ajiyeta ba... Kai duk dai wani otal dake kano da ya amsa sunansa otal xuwa
take, wani lkcn tun safe sae dare xae je ya daukota, Khalil dake ta kallonsa da
mamaki yace "Hotel?? Me ke kai ta can?" Aminu yace "Ahaf ka ji ka da wani xance, me
ake zuwa yi otal, kuma kaf babu wanda ya sani a gidan nan sae Habibu sae kuma ni da
yake gaya ma, kai wani lkcn har Habuja tana xuwa kuma ta dawo a ranan, kasan
sha'anin jirgi, peee ta tafi peee ta dawo ita da kawayenta, babu wanda xae sani,
duk kowa tunaninsa tana makaranta, ita ce Kaduna, Ita ce legas, patacot.....kai
manyan garuruwan kasar nan dai da ka sani babu inda yarinyar nan bata xuwa, babu
abinda Habibu bai sani ba game da ita ai, ina ga shi yasa taji haushin barin dreba
da yayi" Khalil dai yayi shiru, Mai gadi yace "Atoh ni kallonta kawai nake kyar"
Khalil yace "Allah ya kiyaye" Mai gadi yace "Ameen dae" Nihad na shiga bedroom
dinta ta ajiye jakarta da mayafi ta dau wayarta tayi dialing number Habibu, yana
fara ringing ta nemi gefen gado ta xauna babu bata lkci ya daga hade da sallama
yace "Hajjaju Hajjaju ina yini" Tace "Lafiya lau Habibu" Yace "Ya kwana biyu kuma?"
Tace "Lafiya lau, Kana ji na?" Yace "Ina ji Hajiya" Tace "Wannan drivern da ka kawo
ma Abba, a ina ka san sa?" Habibu yace "Wani abu ya faru ne Hajiya?" Tace
"Tambayarka nake kana tambayata" Yace "Ehh Hajiya na san sa, d'an uwa na ne,
garinmu daya" Nihad tace "Bana son karya ta ina ya xama ɗan uwanka kana baƙi yana
fari??" Habibu yace "Ayya Hajiya ai in dai ka fito kauye daya da mutum ku ka shigo
maraya dan uwanka xaka kirasa, haka abun yake ki tambayi kowa ma" Ta kyabe baki
tace "Toh abu daya nake so da kai yanxu" Yace "Toh ina ji Hajiya" Tace "Ko nawa
kake so xan baka Habibu, in dai kudi ne kar ka ji komai" Shi dai yayi shiru, tace
"Kana ji na?" Yace "Ehh ina ji Hajiya" Tace "So nake ka kira Abba ka 6ata sa a
wajensa, ka kirkiro wani babban laifi kace yayi a garin naku ashe dalilin da ya sa
ya bar garin kenan, kai baka sani ba sai yanxu wani ɗan garin naku ke sanar maka"
Jin shirun da Habibu yayi tace "Kayi min shiru?" Da sauri yace "Ehh ina jin ki
Hajiya, ina sauraronki" Nihad tace "Good, yaushe xan saurareka?" Yace "Xuwa gobe in
sha Allah" Tace "Ohkk" daga haka ta katse wayar ta mike ta nufi window tana jin
wani relieve a ranta. Khalil na shigowa parlon chalet din da suke ciki dab da
magrib ya dinga bin parlon da kallo, tun safe da ya fito bai sake shigowa ba sai
yanxu, kuma kafin ya fita tass ya share ko ina, amma yanxu parlon wani sai yace
yara kanana sun shiga sun yi wasa da rana, beside that every where is so untidy,
nan kayan wanki, can kayan guga da Isiya ke yi, ga plate din abinci da cups a
tsakar parlon, kofar ma a wangale ake barinsa sauro su shiga yanda suka ga dama, Ya
dinga kallon Saminu, Isiya da Shafi'u da ke parlon, Kafin ya ce komai Shafi'u yace
"Ana ta kiran wayarka tun daxu fa" Kallon direction din da jakarsa yake yayi, sai
kuma ya kallesu yace "Amma nace ku yi hakuri ku bar barin kofa a bude sbda sauro,
tunda a parlor nake kwanciya ko" Isiya yace "Baka ga fankar ya lalace jiya ba, AC
dama tun da ka xo ai baya yi, shhkn sbda sauro sai mu ki bude kofa iska ya shigo"
Khalil ya dinga kallonsa, Saminu yace "Haba kai tun da ka zo sai kayi ta abu isa
isa da gadara don kaga muna maka shiru, mu kafin ka zo haka muka saba barin kofa
gaskiya" Khalil bai kuma ce masu komai ba ya nufi gun kayansa, ya dau jakarsa da
blanket, sai tsintsiya da parker da yake shara, hanyar dakuna uku dake chalet din
ya nufa, duk suka bi sa da ido har da waigawa, sai da ya bude ko wani daki sannan
daga karshe ya shiga na dama, ajiye jakarsa da blanket yayi, duk wani ghana must go
da jaka da ya gani a dakin sai da ya cilla sa waje, sannan ya cire dukunannen zanin
gadon dake kan gadon shi ma ya cilla masu waje, tas ya share dakin, sannan ya shiga
bandaki nan ma ya wanke, ya fito ya bude jakarsa da makulli ya dauko Harpic da hypo
ya koma bandakin, bayan ko ina ya dawo yanda yake son ganinsa, yayi wanka ya dauro
alwala ya fito, har xai kulle jakarsa sai ya tuna wayarsa ya dauko ya ga miss calls
din Habibu kusan 7, ya gama kare ma number kallo sannan ya ajiye wayar ya mike ya
fita daga dakin ya sa makulli, ya zira makullin a aljihun jallabiyan jikinsa, babu
yabo babu fallasa ya fito parlon ya nufi kofa duk suka bi sa da kallo babu wanda ya
iya cewa komai har ya fita. Bayan khalil yayi sallah yana xaune gefen mai gadi sai
ga Hafsah ta kawo ma mai gadin abinci, Mai gadi na kallonta yace "Shi ma ki kawo
masa tasa abincin nan kawai" Tace "Toh" sannan ta juya ta koma ciki, Khalil ya mike
yace "Xan dau wayata da ka sa a caji" Daga haka ya shiga dakin mai gadin ya dauko
wayar ya dawo ya xauna, yayi dialing number Habibu ya kai kunne, ba a dauki lokaci
ba Habibu ya daga yace "Ranka shi dade" Khalil ya gyara xama yace "Ya kake" Habibu
yace "Lafiya qlau wllh, ya aikin?" Khalil yace "Alhamdulillah" Habibu yace "To
madallah, kana ji na" Khalil yace "Ina ji" Habibu yace "Wani abun ya hadaku da
wannan yarinyar Nihad ne?" Khalil yace "Wani abu kamar me?" Habibu yace "Aa wai ko
sa'insa, ko dai makamancin hakan" Khalil yace "Ko daya" Habibu yace "Tohh, akwai fa
matsala" Khalil yace "Ta me kenan" nan Habibu ya sanar masa yanda suka yi da Nihad
daxu, Khalil yace "xan kiraka anjima" Daga haka ya katse wayar ya amshi abincin da
Hafsah ta kawo masa yace "Nagode" Nihad ta fito daga wanka kenan da daddare Mumy ta
shigo dakinta, sunkuyar da kai tayi tana goge jikinta tace "Ina yini" Mumy tace "Wa
ya baki makullin motar Farooq daxu?" Nihad ta kalleta da sauri, sai kuma ta
marairaice tace "Umma ce ta bani" Mumy tace "Ke yanxu Nihad duk wata hanyar da xaki
bi ki sani magana shi kike nema a rayuwarki ko?? Kwata kwata baki daukeni bakin
komai ba, duk abinda xai 6ata min rai shi kike rawan jiki kiyi, ki kama ki dau mota
ki kama hanyar makaranta without i and ur dad knowing ko Nihad" Nihad ta fara
shessheka tace "Mumy u don't want to be considering me, ni baxan iya shiga mota
daya da wancan sabon driver din ba shi yasa na amshi makullin motar ya Farooq gun
Umma" Mumy tace "A saboda meye baxa ki shiga mota daya da shi ba? Saboda shi ba
mutum bane? Kawai don bai baki makullin mota kin tafi gantali ba shine kika dau
karan tsana kika daura ma mutumi? He is only trying to protect his job don ai ba a
basa umarnin ya baki makulli ba ko" Kuka Nihad take sosai tace "Ko me nace Mumy
baki supporting dina, wllh yaron ba shi da kunya, ya raina ni kawai" Mumy tace
"Wato yaro ne ma?? Me yasa ita Nihal bata complain a kansa, ina ce shi ke dropping
dinta a islamiyya kullum, i even ask her ko taga yana da matsala tace min he is so
friendly, me yasa ke baxa ki sauke kanki yanda er uwarki ke yi ba" Nihad ta hade
rai tace "Wannan wawiyar me ta sani, ko bai mata magana ba ma ai washe masa hakora
xata yi ita tayi masa, baxa ma ta jira ya gaisheta ba ita xata fara gaishesa sbda
bata da hankali, pls mumy ki daina sa Nihal a cikin mutane" Mumy tace "Ki bi duniya
a sannu Nihad, babban matashi irin wannan sbda yana aiki karkashin Abbanki kice
baxa ki gaishesa ba sai dai ke ya gaisheki, me yasa baxa kiyi koyi da Nihal ba, me
yasa kika dau duniya da xafi haka" Nihad tace "Ni dai Mumy kiyi hakuri ki bani
makullin motar ki yau wllh ina da lectures karfe goma, Ni kuma baxan juri shiga
mota daya da shi ba" Mumy tace "Toh xa mu gani kuwa, kuma wllh kika sake xuwa gun
Hajiya kika amshi makulli sai na 6abbalaki a gidan nan" Nihad tace "Shikenan ni
baxan je makarantar ba kawai" Mumy tace "Ohk ni kike gaya ma wannan ko" Ta fashe da
kuka sosai tace "Toh Mumy ya kike son inyi, ni naga kamar ma kin fi son driver din
nan a kaina kawai" Mumy tace "Ehh na fi sonsa a kanki, kuma wllh kar ki kuskura ki
bari karfe goma yayi maki a gidan nan, sannan shi din xai kai ki, idan kuwa ba haka
ba xaki sha mamakin abinda xan maki, tunda ke kin dau girman kan duniya kin daura
ma kanki" Daga haka Mumy
ta fice daga dakin, Nihad tayi kukanta ma'ishi, taji ta tsani wannan bawan Allah,
ta tsanesa... Babu yanda ta iya haka ta tashi ta shirya, karfe goma saura minti
biyar ta fito compound, atamfa ce jikinta da wata mitsitsiyar mayafi da ta rataya a
wuya, hannunta rike da laptop dinta da jaka, fuskarta a daura ta nufi can inda ta
hango Driver din a xaune da Aminu, tana masa wani matsiyacin kallo, cike da isa da
gadara tace "Tasowa xaka yi kayi dropping dina a school idan ka ga dama, kai kuma
Aminu sai ka gaya masa makarantar tamu" Daga haka ta juya ta bar wajen ta tafi can
gun motar, murya can kasa kasa Aminu yace "Iko sai Allah" Mikewa Khalil yayi ya
nufi motar, Har xata bude back seat sae kuma ta fasa ta xaga ta bude seat din gaba
ta shiga, yanda ta hade

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login