Showing 117001 words to 120000 words out of 268471 words

Chapter 40 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

shiga sannan suka rufe gate din, Nihad ta dinga bin makeken compound
din me dauke da wani ubansun mansion da kallo, kai kana ganin gidan nan kawai kasan
ba karya malam, Compound din kuwa yayi ukun nasu ga parking lot kaca kaca, ko wanne
da ride lafiyayye a parke, ita bata ma san ta bayan gidan suka shigo ba, don ta can
ne zata ga ainahin kyan gidan, chalet da aka yi can gefe da ta hango kuwa ya kusa
nasu main building din, tafiya kawai yake tana binsa zuciyarta na bugawa, but how
comes yana ta tafiya kansa tsaye and nobody is even stopping him, taga sun zaga ta
baya ya shiga wani stairs wanda aka shimfida ma carpet grass, shi kansa tsakar
gidan wajen duk malale yake da Carpet grass din, bude wani kofa yayi bayan sun
haura sama sun mike wani babban corridor, ya bude wata kofar duk tana biye da shi a
baya a tsorace, ko nisa bata son yayi mata, gaba daya she is really confused at how
he is just badging in babu shakka ba komai, ita tsoronta kada a kama su ayi masu
dukan tsiya, da ido ta dinga bin parlon da ya shiga tana makale bakin kofa ta kasa
shiga zuciyarta na bugawa, Can taga ya shiga wata kofar da sauri ta bi bayansa ko
kulle kofa bata yi ba, nan taga kofar da ya shiga wani parlon ne wanda ya fi wanda
suka baro haduwa, at this point, she is super confuse, bayan ya isa kofar dakin
Maminsa ya juyo yana kallonta, ya fi second goma yana kallonta wanda hakan ne ya
kara mugun tsoratata, can kuma babu yabo babu fallasa yace "Zauna nan" Ta kasa zama
har taga ya shiga wani kofar, Mami na nan zaune yanda khaleel ya bar ta don ta kasa
samun nutsuwa, gani kawai take shikenan kuma baxai sake dawowa ba, gaba daya
jikinta a sanyaye yake har zuwa yanzu da ya shigo dakin nata, da sauri ta mike
ganinsa with happiness written all over her face ta nufesa kace "U kept to ur
promise son, baka wuce awa dayan ba, i was so worried ina ga kamar tafiya ka kara
yi...." Yayi Murmushi ya kamo hannunta a hankali yace "Amma bana son ki saka rai da
yawa ki sakankance a kan cewar na dawo in zauna Mami, kar ki manta ban san kiran me
Abba ke min ba, he might still not be needing me in his house, kilan idan ya gama
fada min abinda zai fada xai iya cewa in bar masa gidansa and i don't have
choice...." Hawaye ya shiga sakkowa idon Mami tana girgiza kai tace "Baxan yarda da
hakan ba this time around son, sai dai duk abinda zai faru ya faru, shirun da nake
masu ya zo karshe, baxan sake shiru ba in har yace ka bar masa gidansa for the
second time" Shi dai khaleel bai ce komai ba sai kallon mahaifiyar tasa yake cike
da tausayinta, kamar yanda take ganin ya rame, shi ma haka yaga ta rame saboda
damuwa, Can Mami ta share idonta da sauri tace "Where is the young gal?" Ya kalli
kofa yace "She is at the parlor" Mami tace "Ohk" Daga haka ta nufi kofar ta fita ya
bi ta da kallo, zaunawa yayi gefen gado ya rike kansa, yasan ko me zai faru baxai
samu courage din sanar masu ai Nihad yarinya ce da babanta ya aura masa ba, shi
kuma ya amshi auren nata ba don ransa ya so ba sai don ganin girma da mutuncin
mahaifinta sannan baxai iya turning down din offer din mahaifinta ba, yasan baxai
ta6a fara masu wannan bayanin ba, fadawa saman gadon yayi ya kwanta ya lumshe ido
yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mami na fitowa parlor taga Nihad a tsaye
bakin kofa tana shesshekan kuka, tun bayan da taga khaleel ya mata wannan kallon
sannan ga shiga kofar ya kulle tayi saurin komawa bakin kofar fita parlon ta tsaya
zuciyarta na raya mata shikenan babu wani tantama ya kawota ne kawai a gille mata
kai ayi kudi da ita, dama masu kudin nan wasun su kowa yasan ai suna yankan kai, to
kila mai gidan ya ba khaleel contract din samo masa kan da za a gille shi yasa har
ya shigo gidan tare da ita babu wanda ya hanasa, sai ma bude masa kofa da
securities din suka yi har da masu gaishesa, irin dai ya saba shigowa gidan kenan,
sannan gashi taga kansa tsaye ya taho bangaren nan da ita, wato in da za a gille
mata kan kenan, uwa uba tun da suka shigo gidan bata ga ko wani mutumin ba sai
securities, Da mamaki Mami ke kallon Nihad ganin yanda take hawaye tace
"Subhanallah, Baby are you okay? why are you crying?" Kallon matar kawai Nihad take
hawaye na sauka idonta kuma taki ce mata komai, wannan ba ita ce ta gani a hoto
ranan a dakinsa ba? Mami tace "C'mon, come in dear...." Nihad taki karasowa sai
kallonta take, Mami na ganin haka ta juya ta koma dakinta ta shiga tana kallon
Khalil dake kwance saman gadonta da mamaki tace "Khaleel na ganta tsaye bakin kofa
tana kuka, is she okay? Nace ta shigo kuma
ta ki" Mikewa Khalil yayi ya fita parlon Mami ta bi bayansa, yana kallon Nihad, ya
dake yace "Shigo ciki" Mami ta karasa inda take tsaye ta kamo hannunta ta shigo da
ita parlon tana kallon Khalil murya can kasa tace "Doesn't she understands
English?" Bai ce komai ba ya juya ya koma dakin, Mami ta zauna gefen Nihad da ta
zaunar edge din kujera kamar me shirin fillawa da gudu, tace "Ya kike yan mata?"
Nihad ta goge idonta tana kallonta a hankali tace "Ina yini" Mami na Murmushi tace
"Alhamdulillah, ya su mamanki?" Nihad ta sauke idonta kasa cikin sanyi tace "Lafiya
lau" Haka kawai Nihad taji hankalinta ya ɗan kwanta ganin Mami, Mami ta kwantar da
murya tace "Ki saki jikinki kinji, nan ma duk gida ne" Nihad ta kasa ce mata komai,
Mami tace "Kin yi sallan magariba?" Nihad ta girgiza mata kai, Mami tace "To ga
banɗaki kije kiyi alwala, bari in kawo maki darduma a bedroom yanzu" Nihad ta mike
ta tafi kofar da Mami ta nuna mata a parlon ta bude a hankali tana kallon ciki,
bandakin ya kusa girman dakinta, ta karanto addu'ar shiga banɗaki a ranta sannan ta
shiga, Mami ta mike ta tafi daki ta ga Khalil ya dauro alwala ya fito, area din da
Mami tayi demarcating a dakin don yin sallah ya nufa, Mami ta dau ma Nihad darduma
daya ta kai parlor ta shimfida mata, sannan ta koma dakin ta shiga bandaki ita ma
ta dauro alwalan, Khalil na zaune saman darduma yana azkar bayan ya idar da sallah,
Mami ta mike bayan ita ma ta idar tana kallon side din da yake tace "Yanzu abincin
xan dauka in kai can parlon, ko ta shigo nan kawai ku ci?" Yace "Ki deba kawai ki
kai mata can parlon Mami" Mami tace "Ai ban san abinda tafi son ci ba, kawai bari
ta shigo ta yi serving kanta ko?" Mami na fadan haka ta fita zuwa parlor tana
kallon Nihad dake saman darduma tayi kuri da ido tace "Baby shigo ki ci abinci"
Nihad ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ganin taki shigowa Mami tace "Shigo
mana" Cikin sanyin murya tayi sallama ta shiga dakin, ta dinga bin abincin dake
jibge a kasa da kallo kamar za ayi party, Mami tace "Ki duba duk abinda kike so ki
diba" Mami na fadan haka ta fita daga dakin, Nihad ta durkusa tana kallon Khalil,
murya can kasa tace "Don Allah ina ne nan ka kawo ni?" Sai a sannan Khalil ya
kalleta tun da ta shigo dakin yace "Inda za a mana alfarma ba tare da an walakanta
mu ko an ci zarafinmu ba, ba kuma tare da an damu da mu talaka ne ko masu arziki
ba" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike ya zauna gefen gadon yace "Debi abinda zaki
deba ki fita" Ita dai ta kasa cewa komai kuma ta kasa bude ko warmer daya balle ta
zuba abincin, Mami ta dawo dakin rike da teapot da cups dinsa biyu a tray, da
mamaki ta ke kallon Nihad bayan ta ajiye tray din hannunta tace "Baki debi abincin
ba" Sai kuma ta kalli khalil kafin tace komai ya kirkiri murmushi yace "Haka take
Mami" Nihad ta daga kai ta kallesa, Mami tace "But why? pls tell her to feel free"
Khalil ya maida idonsa kan tv dake aiki silently bai ce komai ba, Mami ta dau plate
ta debar ma Nihad shinkafa da miya ta ajiye mata, ta debar mata duk wani abu da
xata dibar mata sannan ta mike, Nihad dai bata ta6a jin she is confuse kamar yanda
take ji yanzu ba, gaba daga kanta ya kulle ta kasa fahimtar komai, lkci lkci sai ta
kalli khalil sannan ta kalli Mami, Mami na kallon Khalil a hankali bayan ta gama
zuba ma Nihad abinci tace "When did you say he called you?" Khalil ya kalleta duk
da ya gane wanda take nufi yace "Ke baxa ki ci abincin ba Mami? Ki zuba mana tare
mu ci" Mami tace "Talk to me son, he is back now" Sai da gaban khalil ya fadi ya
mike yace "Really? But hope you didn't...." Sai kuma yayi shiru, ta gefen ido ya
kalli Nihad da ta kafesa da ido babu ko kiftawa, sai kuma ya fice daga dakin, Mami
na kallon Nihad da murmushi fuskarta tace "Ki ci abinci kin ji Baby" Daga haka ta
juya ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo bata kwakkwaran numfashi, bayan kusan
minti sha biyar Khalil ya dawo dakin shi kadai, har sannan Nihad na zaune position
din da take kamar warce ruwa ya cinye, gaba daya jikinta yayi sanyi qlau kana mata
kallo daya zaka gane hakan, Ta bi sa da kallo har ya dau teapot da cup zai fita,
cikin sanyin murya tace "Ka gaya min, wanene kai?" Bai yarda ya kalleta ba yace
"Driver!!" Daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da ido babu ko kiftawa, abinda ya
fada dazu da turanci ne ke kai komo a ƙwaƙwalwarta, lokaci daya ta runtse ido ko
zata samu saukin sara mata da kanta ke yi. Khalil na zaune parlor sai ga Mami ta
shigo tana kallonsa, shi ma kallonta yake, a hankali tace "Kaje wajen Abbanka, yana
kiranka parlonsa" Khalil ya kalleta looking so worried yace "Mami da baki ce masa
na dawo yau ba" Mami ta girgiza kai tace "I never told him, tun daga gate ya
tambaya securities, su suka sanar masa kana gidan nan....." Yayi kasa da murya yace
"But bana son kowa ya san am around Mami" Mami tace "Zaka iya zagawa ta baya ai,
har yanzu babu wanda yasan kana gidan nan" Mikewa yayi ya nufi kofa yana tafiya a
hankali ta bi sa da kallo har ya fita.



Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and ur evidence via👇🏻

07087865788




Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki
kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi
gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai
na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin
keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏


37

Khalil na shiga parlon Abbansa bai bari suka hada ido ba, yana tafiya a hankali ya
zauna saman lallausan Carpet dake kasa, yayi gathering courage yace "Barka da dare
Abba" Shirun da Abban nasa yayi yasa a hankali ya daga kai ya kallesa yaga jaridar
hannunsa kawai yake dubawa, ya sunkuyar da kansa, bayan kusan minti biyu Abba ya
ajiye jaridar hannunsa yana kallonsa a takaice yace "Wani international joint
ventures na wata daya zaka min handling a Zanzibar, and the business isn't new to
you, you know everything about it, so u can chose to stay there in Zanzibar or come
back to Nigeria weekly, bayan kayi min sorting komai zaka iya komawa duk inda ka
fito ka ci gaba da rayuwarka since it's the best for you and you are okay with it,
i will neva beg you to come stay here!!" Yana gama fadin haka ya mike ya shiga
dakinsa Khalil ya bi sa da kallo, sai gashi ya fito da files ya jefa masa nan kasa
yace "Everything u will be needing is there, u can leave my sight now" Khalil ya
dau files din a hankali yace "In sha Allah, Nagode Abba" Daga haka ya mike ya nufi
kofa Abban nasa ya bi sa da kallo har ya fita, yana fita ya juya suna hada ido da
Abba, Abba yayi saurin juyawa ya shiga bedroom dinsa. Har Khalil ya shigo parlon
Mami na tsaye ta kasa zaune sai kai komo take a dakin, she is so disturbed and
worried, Allah ya sa kiran alkhairi yake masa, tana ganin Khalil ya shigo ta nufesa
da sauri tace "What did he say to you??" Khalil ya mika mata files din hannunsa ta
amsa tana dubawa da sauri, can ta kallesa tace "What about this?" Yace "He wants me
to be in charge" Mami ta dinga Kallonsa babu ko kiftawa can tace "He said so?"
Khalil yace "Yea" Murmushi tayi ta rungumesa tana hamdala a zuciyarta amma ta kasa
cewa komai hawaye ya cika idonta, ta sakesa tace "Yanzu yaushe zaka tafi?" Khalil
yace "I need to prepare" Tayi kasa da murya da damuwa tace "Zan so ka shirya first
thing in the morning ka bar gidan nan kafin wani yayi noticing dinka, har yanzu
basu san u are around ba, nasan shi ma bai sanar masu ba" Khalil bai iya yace mata
komai ba, ta goge idonta tace "Shigo ka ci abincin yanzu, i am so happy at this
good news" Ta kama hannunsa suka wuce can bedroom dinta, tsaye tayi bakin kofa da
mamaki tana kallon Nihad da ko motsi bata yi daga inda take ba balle ta ta6a abinda
Mami ta zuba mata a gabanta, Mami ta kalli khalil tayi kasa da murya tace "Are you
sure zata yarda ta kwana nan son? She hasn't taken anything yet, are sure baxaka
duba ko da akwai flight going to kano a yankar mata ticket ba?" Khalil dai sai
kallon Nihad yake, Mami tace "Do so before it's late plss, kasan wasu nature ne
hakan basu sakewa a wani waje ba gida ba, so kar a takurata" Juyawa tayi ta fita
daga dakin, khalil ya duka dab da ita yana kallonta, kin yarda su hada ido tayi,
lkci daya yaga hawaye ya ciko idonta, still looking at her yayi kasa da murya yace
"Where u offended in anyway?" Ta kallesa sai kawai ta fashe da kuka sosai, cikin
karfin hali tana magana da kyar tace "Don Allah... Kayi hakuri ko a motor park ne
ka kai ni ka sa ni a motar Jigawa in tafi wajen Aunty Jamila, don Allah kayi min
wannan last alfarman" Tana kuka me ban tausayi ta fadi hakan, sai kuma ta hade
kanta da gwiwa, yana ta kallonta kafin yace "An maki wani abu ne a nan din da za ki
tafi jigawa?" Ta daga idanuwanta da hawaye ke zuba tana girgiza kai tace "Ni bance
an min komai ba" ya dau duk abincin da Mami ta sa mata a plate ya kai parlor sannan
ya dawo yace "Fito ki ci" Tace "Ni na koshi" Yace "Fito nace" Mikewa tayi trying
hard not to burst into new cry ta fito daga dakin ta tafi ta zauna inda ya ajiye
abincin, ta hadiye wani abu da ya tokare mata throat da kyar, Yana kallonta yace
"Now eat" Bata san sanda kukan ya subuce mata ba tana girgiza masa kai, ya hade rai
yace "Kee" ta daga ido da sauri ta kallesa, ya durkusa yana kallonta, sai kuma ya
ciro handkerchief ya mika mata, Da sauri ta sunkuyar da kanta, ganin har sannan
mika mata handkerchief din yake ta kai hannu a hankali ta amsa, ta goge hawayen da
ke zuba idonta da shi shi dai kallonta kawai yake, bayan ta gama goge idon ta daga
kai a hankali tana kallonsa, ya sauke idonsa ya matsar da plate din abincin
gabanta, ta kalli cokalin dake cikin abincin ta dauka ta diba ta kai baki a hankali
ta fara ci, mikewa yayi ta bi sa da kallo har ya fita zuwa next parlor din, gaba
daya taji baxata iya cin abincin ba, she has clearly run out of appetite, this is
the third shock of her life so far, but this particular one is so strong and it's
about giving her heart attack, of all the shock, this made her felt bata da sauran
hope a duniya, this made her loose all hope, she now believe she is now all by her
self a duniyan, kwakkwaran wata daya ba ayi ba ta girgiza da lamari har kala uku,
yanda take ji a ranta ta kara tabbatar da bata da wani sauran gata kuma a duniya,
ganin komai take kamar mafarki amma ita dai tasan ba mafarki take ba, this is
nothing but reality, bata ta6a jin ta tsani kanta duk abubuwan dake faruwa ba sae
yau, she hate herself for everything so far, ta daure ta tashi da kyar ta mayar da
duk abincin cikin warmer dinsu ta fito don tasan baxata ta6a iya ci ba, ta zauna
kasa ta jingina da kujera, ko sanin hawaye na zuba idonta bata yi ba. Khalil na
zaune first parlor da Maminsa dake waya da sister dinta, she is happily telling her
that he is back, daga nan kuma ta kira aminiyarta warce kasar su daya and she is
always there for her at all time, shi dai khalil kallonta kawai yake har ta katse
wayar, Mami ta mike tace "An samu jirgin kuwa son?" Ya girgiza kai yace "Aa Mami"
Tace "Toh gobe first thing sai kayi mata booking ticket kafin ka tafi koh?" Khalil
bai ce komai ba, Mami ta koma can ciki, ba a dau lokaci ba sai gata da plate din
abinci ta zubo masu, tare suka ci abincin, ya ci peppered chicken din kawai a
maimakon pepper soup yace mata ya koshi, Mami ta kira Bilkisu ta kwashe duk
abubuwan ta fita da su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login