Showing 96001 words to 99000 words out of 268471 words
"In har a sharadin rabuwar mu har da datse alakata da Umma to
kar mu rabu din, kai xaka wahala ba ni ba" Tana gama fadin haka ta kwace hannunta
daga rikon da yayi mata ta shige dakinta, zaunawa khalil yayi saman kujera deep in
his thought yana sake digesting duk abubuwan da Nihad ta gama fada masa..... Ana
magrib Nihad taji fitar Khalil, tun da rana take kuka duk idanuwanta sun kumbura
saboda ya hana Umma shigowa gidan, tana jin fitarsa ta fito bakin gate din sai taji
ya sa makulli, ji tayi kamar ta kwanta wajen tayi ta birgima, ta dinga rera kuka
kamar ranta xai fita a wajen. Khalil na zaune parlon Abba, ya gaishesa kansa a
kasa, kallonsa kawai Abba yake yana son jin me ke tafe da shi, hoping ba wani abun
Nihad tayi masa ba, Khalil yayi kasa da murya yace "Alhaji dama na zo neman alfarma
ne gun ka" Abba na kallonsa yace "Ina jin ka Ibrahim, fadi koma meye kanka tsaye"
Khalil yace "Ina son xan koma garin mahaifiyata can Zaria tare da ita... Saboda xan
ɗan yi noma a can tunda damuna ya fadi" Abba yace "Yanzu ai karkashin ikon ka take
Ibrahim, ba sai ka tambayeni izini ba don xaka canza wajen zama da ita, iyaka ka
sanar min don in maku fatan alkhairi sannan idan da tallafawan da xan maku sai a
maku" Khalil dai ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Maa sha Allah naji dadin noma da
kace zaka yi, don noma ai shine tushen arziki dama, Allah Ubangiji ya baka nasara
Ibrahim" Khalil yace "Ameen Alhaji, nagode" Abba yace "Yanzu dai ka sa a bincika
maka nawa ake bada hayan gida a garin" Khalil yace "Ina da wani aboki a can na
tambayesa jiya" Abba yace "Nawa yace maka?" Khalil yace "Dubu dari yace min"
Kallonsa Abba yake ba ko kiftawa, can yace "Aa da dai a samo na sama da hakan
Ibrahim, ni ko nawa ne ba matsala bane xan bada" Khalil na kallon Abba yace "Gidan
a kusa da kauyen da
xan yi noman yake, shi sa nace xan amsa" Abba yace "Dubu dari nawa kace?" Khalil
yace "Dubu dari daya" Abba ya kasa cewa komai yana kallonsa, Gaba daya tunaninsa na
kan Nihad duk da haushinta da yake kwana yake tashi da shi a ransa yasan baxai ta6a
son ta zama uncomfortable a rayuwarta ba, deep down him yasan he still love his
daughter" Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Shikenan zan sa maka kudin"
Khalil yayi noticing change a muryar Abba hakan ya sa bai dago kansa ba, Abba yayi
breaking few second silence da ya biyo baya yace "Yaushe xa ku tafi?" Khalil yace
"Ko zuwa satin da xa mu shiga in sha Allah" Abba yace "Ohk to amma ka sa abokin
naka ya ɗan bincika min ko za a samu filaye a nan arean" Khalil ya daga kai ya
kalli Abba yace "Toh Alhaji" Abba yace "Ina sauraronka zuwa gobe da safe" Khalil
yace "Toh in sha Allah" Daga haka yayi ma Abba sallama ya mike ya fita, ɗan
murmushi yayi kawai ya fice daga main parlor. Yana fita parlon Umma ta shigo da
sallama, bayan ta zauna tace "Bako kayi ne halan" Abba ya girgiza kai yace "Ibrahim
ne" Umma tace "Allah sarki, haka dai kawai ka hanani zuwa gun 'ya ta in dinga duba
halin da take ciki, yau kusan sati biyu kenan rabona da ita, wallahi kullum da ita
nake kwana nake tashi a raina, in ji dai suna lafiya?" Abba yace "Lafiya lau, zuwa
yayi min da wani batu" Umma ta gyara zama tace "Wani batu kuma, to Allah ya sa dai
lafiya" Abba yace "Lafiya lau, wai zai je noma garinsu xai tafi da ita" Umma ta
zaro ido tace "Ya tafi da ita ina?? Yaushe Nihad xata wani iya zama a garinsu? To
sai kace masa me Alhaji?" Abba yace "Toh ai a yanzu dai ya fi mu iko da ita, babu
ta yanda xan iya hanasa tafiya da matarsa Sumayya" Umma na girgiza kai tace "Aa
Yallabai wannan ba magana bace, to ko dai ka sallama ma duniya er nan ne bamu da
masaniya? Duk wannan punishment din da kayi mata na aura mata dreba bai isheka ba
sai ka ba dreba goyon bayan tafiya da ita kauyensu da sunan noma? Haba Alhaji ko ba
kai ka haifi er nan ba kaddarar nan ya fada mata ai ka ji tausayinta ka raga mata
balle er cikinka ce kuma masoyiyarka, ina laifin kace ya kawota nan gida ta zauna
har sanda xai gama nomar tasa ya dawo daga kauyen nasu?" Abba yace "Aa, ai mu ba
kananun mutane bane da zance ya bar ta gida Sumayya, tunda har ya girmama ni ya zo
neman izinin tafiya da ita ni kuma baxan yi karanta ba a matsayina na mutum me
kamala a gunsa, yanxu dai nace ya sa a bincika min fili a inda xa su zauna din, ko
nawa ne xan siya, idan ya so ko 3 bedroom flat ne in sa a gina babu bata lkci, don
yana min maganan sun samu gidan dubu dari, dama akwai gidan dubu dari a zamanin
nan?" Shiru Umma tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, Abba ya daga kai ya kalleta
jin tayi shiru, tayi murmushi tace "Maa sha Allah, gida xaka gina ma Nihad din a
can kenan?" Abba yace "Hakan xai fi gaskiya, idan ma babu wuta garin a saka masu
solar 24/7, sannan ayi borehole a gidan, ayi furnishing yanda ya kamata" Umma ta
gyara zama tana Murmushi tace "Hakan yayi kyau kam gaskiya, Allah ya saka maka da
alkhairi ya kara budi, kaga zata zauna comfortably baxata takura ba, har ma ta sake
a gidan ta ji kamar a cikin gari take" Abba yace "Yeah!! So i think duka duka da
filin da ginin ai baxai ci miliyan goma ko sha biyu ba ko?" Umma tace "Ehh to, xai
iya zama hakan tunda ai ba cikin gari bane kila, balle ace filin xai yi tsada
sosai" Abba yace "In sha Allah, ko zuwa gobe aka samu filin xa a daura gini kawai"
Umma na Murmushi tace "Madallah, Allah ya kai mu goben, bari in je in gama abinda
nake a sama" Abba yace "Alright" mikewa tayi ta fita daga parlon. Yau ma kamar jiya
ana kwankwasa gate Nihad da Khalil suka fito a tare, bai ko kalleta ba har ya fita,
ta bi bayansa don wannan karan sai dai duk abinda xa ayi ayi a bakin gate din in
dai Umma ce sai ta bude mata, Ya hade rai ya juya yana kallonta yace "Meye kike bi
na?" Ita ma ta hade rai tace "Kayi tafiyarka inyi tawa mana" ya ci gaba da tafiya
tana bin sa har suka iso gate din, yace "Wanene?" Husnah tace "Assalamu alaikum" Ya
wani hade rai yace "Nace waye?" A hankali tace "Husnah ce" Nihad ta hade tafin
hannunta kamar xata yi kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka bude mata, ni
kenan sai inyi ta zama babu wanda ke xuwa wajena kamar mayya,x kuma ai a sharadinmu
nace baxa ka ki barin kawayena su zo wajena ba kuma ka yarda" Kallonta kawai yake,
nan da nan hawaye ya cika idonta tace "Don Allah fa nace maka" Duk Husnah na jin su
ita kanta addu'a take Allah ya ta6a zuciyar Khalil ya bude mata gate din, Juyawa
khalil yayi ya bar wajen, Nihad ta wara ido cike da farin ciki ta bude gate din,
tayi tsalle ta rungume Husnah tace "Wallahi nayi missing dinki kawata, ina su Naf
da zully?" Husnah tace "Ba su ma san xan zo nan ba wallahi, tun shekaranjiya kike
raina in gaya maki, shine kawai nayi tahowata ban gaya masu ba" Nihad ta kulle gate
din tana Murmushin jin dadi ta kama hannun Husnah da ta bi khalil da kallo har ya
shige parlor, suna isa balcony Husnah tayi kasa da murya tace "Amma dai kawai in
gaida mutumin nan don gobe ma ya barni in shigo, kinsan abun sai da siyasa kawata,
barin ma shi da yake ɗan kauye gaishesan da xanyi yanxu xa ki ga farin cikin da zai
yi kansa yayi kato, kinsan bakauye akwai son girma" Nihad ta kyabe baki tace "Kar
ki wani gaishesa, meye hadinki da shi ko ina ruwanki da shi bayan ba wajensa kika
zo ba, ni kaina da nake gidan ban ta6a gaishesa ba saboda bai isa ba balle ke"
Nihad na gama fadin haka ta ja hannun Husnah suka shiga parlon, Husnah na hada ido
da shi ta janye hannunta daga na Nihad dake jan ta zuwa daki, ta dan yi murmushin
yake tace "Ina wuninmu?" A fusace Nihad ta ja Husnah fuuu suka wuce daki ta kulle
kofar tace "Amma ba nace kar ki gaishesa ba? Meye amfanin gaishesa yanzu?" Husnah
ta yatsine fuska tace "Ni kaina wllh sai bayan da na gaishesa naga rashin dacewan
hakan, baki ga ma wani shan kamshi da yake shi a dole ya aureki ba, yanzu fa ji
yake shi wani shege ne ya auri er mai kudi" Nihad tace "Ke mu fa mun riga mun ajiye
deal kan cewa xai sakeni, na amince shi ma kuma ya amince ya kuma yarda ni ba class
dinsa bace" Husnah ta zaro ido tace "Haba??" Nihad tace "Wallahi in gaya maki, ai
yaga tsanar da nake masa tayi yawa baxan kuma ta6a raga masa ba shi yasa yaga gwara
mu rabu..." Husnah tace "Yanzu yaushe yace xai sake kin?" Nihad tace "Ku dai kawai
ku zuba ido ku ga ikon Allah" Husnah tace "Kai amma na tayaki murna wallahi, ashe
shegen ya san abinda yake yasan ke ba class dinsa bace cikin ruwan sanyi xai rabu
da ke" Nihad ta tuntsire da dariya tace "Wallahi fa in gaya maki" Husnah ta cire
Hijab din jikinta ta jefar kan gado, Nihad tace "Yaushe kika dinka hijab ke da baki
da ko guda daya" Husnah tace "Wannan ma a hostel na aro shi, ke akwai abinci yunwa
nake ji" Nihad tace "Ehh daxu nayi stew, kawai spaghetti xan yi boiling" Husnah
tace "Toh bari in yi boiling dinsa, akwai a kitchen ai?" Nihad tace "Ehh akwai"
Mikewa Husnah tayi ta bude handbag dinta ta fiddo after dress ta daura a kan riga
da wandon jikinta ta fita, Nihad ta jawo jakarta bayan ta fita ta bude, as usual
kayan maye iri iri ta ga a jakar da Prophylactics dinta, Nihad ta mayar mata da
kayanta ta dau wayarta da ta gani ta bude password don tasan password din nata, har
tayi dialing number Aliyu sai ta tuna ba shi da number Husnah don haka baxata
samesa ba, lkci daya jikinta yayi sanyi, sai dai kawai tayi dialing number Umma,
Umma na jin muryata tace "Daughter, ina ta tunanin ta yanda xanyi waya dake tun
jiya wllh, har cewa Nihal ta kai maki waya gida nayi amma er nan taki, Amina kuma
kinga tunda ana hutu islamiyya take safe da yamma ita ma baxata yarda tayi fashi ba
don in aikota wajenki" Nihad ta marairaice tace "Nima babu ta inda xan kira ki
Umma" Umma tace "Kina ji na?" Nihad tace "Ina ji Umma" Umma tace "Kullum nayi
sallah ina saka wannan tsinannen dreban a addu'a kan cewa Allah Ubangiji ya rabaki
da shi cikin aminci, to sunansa kawai na sani ban san sunan mahaifinsa ba ko
uwarsa" Nihad tayi shiru, sai kuma tace "Nima wallahi ban sani ba Umma" Umma tace
"Yo ai nasan baki sani ba, ke baxa ki iya dubara irin na mace ba ki tambayesa sunan
ya gaya maki, sai kace ba wayayyar Nihad dita ba, ai cikin salo irin na wayayyun
mata zaki bi masa har ya gaya maki" Nihad tayi Murmushi tace "Toh shikenan Umma"
Umma tace "Yauwa zuwa yaushe xan saurareki?" Nihad tace "Gobe" Umma tace "Amma
number waye wannan?" Nihad tace "Na Husnah ne" Umma tace "Au tana can shegen ya bar
ta ta shiga kenan" Nihad tace "Wallahi kuwa Umma" Umma tace "To yaushe xata tafi?"
Nihad tace "Kamar fa kwana xata yi naga kaya kala biyu a jakarta" Umma tace
"Madallah dai dai kenan, kinga gobe sai ki kirani kawai ta wayar nata" Nihad tace
"Toh Umma" Daga haka Umma tayi mata sallama Nihad ta katse wayar, dai dai nan taji
Husnah tayi wani kara, ta mike da sauri ta fice daga dakinta, Tana fita parlor
Khalil na shiga kitchen din, ita ma ta nufi kitchen din da sauri.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah,
ki fita hakkina ki karanta cikin salama er uwa
Ur evidence via👇🏻
07087865788
Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki
da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai
maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da
boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*
Domin karin bayani ki tuntubi wannan number 👇🏻
✍🏻
+2347057607751
31
Husnah ce tayi zaman dirshan a kitchen din dake malale da ruwa, gaba daya ta jike
jagab daga saman cikinta har xuwa ƙafafuwanta, ta wawwara hannu ta runtse ido cikin
daga murya tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Wayyoo na shiga uku na
lalace, gaba daya na kone a jiki... Don Allah a kawo min agajin gaggawa" daga
gefenta tukunya ce dauke da ruwan zafi a ajiye, Khalil ya shiga kitchen din da
sauri yace "Me ya faru haka?" Ta bude ido ta fashe da matsanancin kuka tana
kallonsa tace "Don Allah ka taimakeni wallahi, ruwa me uban zafi ne ya kwaro min
gaba daya tun daga cikina har kafa, taliya naje zan zuba ruwan ya kifo min, don
Allah ka kawo min agaji kar jikina ya toye" Da mamaki Khalil ke kallonta, kuka
kawai take tana jijjige kafarta da hannu tana cewa "Wayyo Allah na, wllh ruwan ya
tafasa sosai, don Allah a taimakeni duk radadi jikina yake min" Khalil yayi ma
kofar kitchen din kallon kasa kasa jin kamshin Nihad, ya ganta tsaye bakin kofar,
bai yarda ya kalli fuskarta ba, ya kashe gas din ya karasa kusa da Husnah ya mika
mata hannu yace "Taso" Karaf ta cafke hannunsa ya dagota ta mike tana kara sautin
ihunta tana cewa "Wayyoo mamata, Wayyoo zafi, na shiga uku me za a shafa min ya
daina min wannan radadin da nake ji..m" Hanyar kofar kitchen din ya nufa da ita
still ya ki kallon Nihad, ita kanta Husnah bata kalli Nihad ba sai gunjin kuka take
tana jijjiga kai tana yi tana runtse ido, ganin Nihad ta ki matsawa daga kofar
kitchen din Khalil ya daga kai a karo na farko ya kalleta, rungume hannu tayi tana
kallon su, yace "Matsa a hanya" Ta zabga masa wani ta juya da sauri ta bar wajen ta
wuce dakinta, Husnah ta bi Nihad da kallon gefen ido tana cewa "Don Allah a
taimakeni kar jikina ya kwaile in ma asibiti ne mu je" sai kuma ta zame hannunta
daga nasa tayi dai dai a kasa ta kwanta tana birgima tana kuka, dakinsa ya nufa ta
bi sa da kallo, sai ga shi ya fito da makullin mota yana kallonta yace "Mu tafi
asibitin" tana girgiza kai cikin kuka tace "Wallahi baxan iya tashi ba" Yace "Toh
kira kawarki" Daga haka ya fita ya je parking space ya tada mota, Mikewa Husnah
tayi tana gunjin kuka ta tattale hannu ta bi bayansa, tuni ta isa gun motar tana
cewa "Don girman Allah mu yi mu tafi asibitin kar na mutu, ko ina zugi yake min" Ya
bude mata back seat ta shige ciki, Tun da ya tada motar Nihad ta fito parlor ta
tsaya jikin window tana kallon su, sai da ya bude gate ta ga ya dawo zai shiga
motar kawai ta fito ta nufi front seat ta shiga ta kulle, ya bude gefen mazaunin
driver yana kallonta da kyau yace "Ina za ki?" Ba tare da ta kallesa ba tace
"Asibitin da za ku" Ya kalleta daga sama har kasa yace "Ohk, haka za ki je asibitin
kenan" Fuska daure tace "Sai ka jira ni in dauko mayafina" Daga haka ta fice daga
motar da Husnah ta cika da ihu kamar warce ake gunduwa gunduwa da namanta, tana
ganin Nihad ta sauka tace "Don ya Rasulullahi ka ja motar mu tafi kar a rasa fatar
jikina, wllh jin jikin nake kamar ba nawa ba, kar fatana ya karasa zagwanyewa" Bai
ce mata komai ba ya shiga motar, amma bai ja motar ba, sai ga Nihad sanye da Hijab
ta shige gaban motar, ya ja motar suka fita gidan ya sauka ya kulle gate. Wani
asibiti da babu nisa daga anguwansu ya kai ta, duk nurses suka tattaso da sauri
saboda tun daga Gate ihun Husnah ya cika asibitin, Nurse daya na kallon Khalil tace
"Me ya sameta?" Khalil da ya koma gefe ya tsaya yace "Wai konewa tayi" Nan aka
shiga da ita emergency aka dau scissors za a fara barke riga da wandon jikinta,
Nihad dai na reception din hospital din ta zauna, babu wanda zai ce tare suke,
Khalil kuma na kofar shiga reception din ya jingina da bango ya rungume hannunsa,
wani ihu Husnah ta sakar ma nurses da Dr din tace "Don Allah a kira min yayana ya
zo kila mutuwa zan yi, a kirasa ya zo kusa da ni" Wata Nurse ta fita ta kira
Khalil, yana kallonta yace "Me xan yi a can din?" Rai bace Nurse din tace "Haba
bawan Allah ko da baka santa ba ta bukaci ka je ai ko don saboda condition da take
ciki zaka je, wai ko ba matarka bace?" Daga haka ta juya ta koma emergency ward
din, Khalil ya bi ta da kallo kafin ya shiga asibitin ya bi bayanta, Nihad ta bi sa
da wani kallo, bai ma san tana yi ba, yana tsaye bakin kofar ward din Husnah ta
hangosa ta dinga miko masa hannu wai ya zo ya ceceta kar ta mutu, likitan da Nurse
dai sun gama 6arke kayanta da scissors suna neman inda ta kone, Can likitan ya
kalli Khalil da ya ki karasawa ciki yace "Wani irin ruwa ne ya zubar mata?" Khalil
ya buda ido yace "Ban sani ba fa, ko kafin na fito ruwan ya gama kwararewa a
jikinta" Nurse din na kallonta tace "Ruwan zafi ne ko dai ruwan dumi" Husnah ta
hade rai tace "Ban gane ruwan dumi ba, sharrin zan ma kaina ince ruwa zafi ya zubar
min a jiki bai zuba ba, kawai dai dama fata iri iri ce, amma Allah kadai yasan zugi
da radadi da nake ji yanxu haka, har cikin raina nake jin wannan axaban wallahi"
Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, likitan ya cire safan hannunsa yace
"Nurse ki basu magunguna" Yana kai wa nan ya fice daga ward din, nan nurse ta fito
reception ta harhada magungunan ta dawo ta mika ma Khalil Bill din dubu sha biyar,
amsa yayi ya fiddo Atm card dinsa ya mika ma nurse din, daga baya ta sake dawowa ta
bukaci pin dinsa sannan ta juya, Husnah dai sai