Showing 150001 words to 153000 words out of 268471 words

Chapter 51 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

accept him Nihad" Nihad dai ta ta6e baki bata ce komai, nasiha sosai
Farooq ya dinga mata kuma yawanci duk sun shigeta kadan ne taji baxata iya abinda
yace ba, bayan khalil ya basu at least 40min ya fito yayi joining dinsu tare da
Mimi, at last dai Driver tare da Noor ne suka maida Nadeeyah gida, Nadeeyan kuma
bata damu ba ganin yana da bako, Mimi sai mamakin Nihad take don bata ta6a tunanin
tana magana har tayi dariya haka ba, shi dai Khalil sai dai ya kalleta ta gefen ido
jefi jefi, sai da aka kira sallah sannan Khalil suka shiga ciki su yi alwala farooq
before going to mosque, Nihad da Mimi suka koma parlon Mami, Bilkisu ta kawo
abincin farooq nan parlon Mami ta ajiye ta fita, Mimi ta kalli Mami tace "Mami
yayanmu yace in kai masa can dakinsa" Mami tace "Toh kai masu can din" Mimi ta mike
tana kallon Nihad tace "I can't take this all alone" Nihad da kamar jira take ta
tashi da sauri, don dama tun da suka shigo ciki jikinta yayi sanyi duk da ya farooq
din ya ce mata ba tafiya zai yi ba amma zuciyarta ya kasa yarda da hakan, Ta dau
wani tray din ta bi bayan Mimi zuwa dakin Khalil, Khalil kadai suka tarar cikin
dakin, Nihad bata yarda sun hada ido ba ta durkusa ta ajiye abincin hannunta a
hankali tana bin dakin da kallo, Mimi tace "Yayanmu ga abincin visitor dinmu"
Khalil yace "Wani visitor?" Mimi ta mike tana kallonsa, Nihad dai ta kasa tashi
daga durkushen da tayi a kasa ita ma tana kallonsa babu ko kiftawa.... a takaice
khalil yace "Ai ya tafi" Nihad bata san sanda ta zauna nan kasan tiles ta fashe da
wani kuka kamar yar yarinya ba, Khalil na kallon Mimi yace "Go and make me coffee"
Mimi ita ma jikinta yayi sanyi, but he should have at least say even a goodbye
mana, juyawa tayi a hankali ta fita daga dakin ta kulle kofar....



Nihad is 500 via 3276052919 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

46

Mikewa Khalil yayi ya tafi har bakin kofa ya tsaya ya rungume hannu yana kallon
yanda take kuka, calmly yace "In da gaske kina son bin sa me yasa tun zuwansa baki
ce masa xaki bi sa ba kika zo nan kina min kukan munafurci, tunda kinsan tafiya zai
yi ba nan zai kwana ba" Nihad ta hadiye kukan da take ta daga kai tana kallonsa
fuska daure, can ta mike tsaye tace "Ina ruwanka da ni? Kaga dai ba ruwana da kai a
gidan nan, don yayana yace in daina kulaka duk abinda xaka min, kuma ni dai naji
maganarsa, don haka kai ma ka fita harkata because bana son inyi disobeying yayana,
idan baxa ka iya cewa inyi hakuri ba dole sai ka min maganan" ta karasa maganar
kamar xata fashe da sabon kuka, kallon bakinta kawai yake, can yace "Ohk yace ki
daina kulani kenan?" Tace "Ehh, kuma ko kana daga min shoulder dinka baxan san kana
yi ba tunda ba ruwana da kai, I will pretend I don't know" Tana kai wa nan ta
nufosa fuska daure tace "Ka matsa min ni in fita" ita haushinta maimakon yace tayi
hakuri shine yake neman tsokanarta kuma, Yace "Aa bari dai a baki kudin mota ki bi
sa kawai, ai yana nan Abuja bai yi nisa ba" Wani kallo ta dinga masa, ya sa hannu
cikin aljihun 3 quarter din jikinsa ya ciro 100 dollar ya mika mata yana kallonta,
ta dinga kallon kudin sai kuma ta kwace ta cukuikuye ta jefar kasa, tana kallonsa
da kyau tace "Kudin da ba naka ba" Kallonta ya tsaya yi baki bude, can yace "Kinsan
hukunci warce ke ma namiji rashin kunya, namijin ma wanda aka aura mata daga
gidansu?" Ta wani kallesa tace "Ohh dama kai mijina ne? Ai ban san ina da miji ba,
kuma ai shi namiji baya neman tsokanar mace" Jin yayi shiru bai ce mata komai ba ta
dauke kai ta turo baki, a hankali ya kai hannu ya kashe switch din dakin ta juya da
sauri ganin duhu ya gauraye ko ina sai ɗan hasken screen din Iphone dinsa da ya
ajiye saman gado, taji kuma yana sa makulli a kofa, komawa baya tayi a tsorace tana
zaro ido tace "Meye haka kake yi?" Ba abinda ta ji yace mata, Ganin he is advancing
toward her ta fara komawa baya da sauri cikin rikicewa tana cewa "Wayyo don girman
Allah kayi hakuri, duk abinda na fada ba da kai nake ba don Allah kayi hakuri, dama
yayana yace in daina maka rashin kunya kuma na daina tun...." Wani kara tayi a
tsorace jin saura kadan ta fada saman gado don bata san har ta iso wajen gadon ba,
zata tashi da sauri ya mayar da ita ta fada kan gadon, zaro ido tayi a mugun
tsorace ganin he just lied directly on her, cikin rawan murya ko ina na jikinta na
ɓari tace "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi baxan sake maka rashin kunya ba
har abada, kaji na rantse..." Gaba daya ta gigice tana kokarin turasa amma ta kasa,
cause his weight is out of the world, nan kuma ba duk weight din nasa ya sakar mata
ba, ta fashe masa da kuka tana sauke numfashi da kyar ga kamshinsa da ya cika ko
wani breathing dinta, yayi kasa da murya still adjusting on her yace "Baki san kina
da miji ba ko?" Cikin kuka tace "Wallahi na sani, kawai wasa nake maka, don Allah
ka yafe min kayi hakuri baxan kara ba.... Wallahi numfashina zai iya daukewa" a
hankali yace "Ya dauke mana" Bata san sanda tayi wrapping hannunta a bayansa tana
kuka sosai tace "My chest is paining me plss" ai ko ya lumshe ido ya kara sakar
mata weight hakan da tayi masa, as if he is going to sleep, sae kuma yayi placing
forehead dinsa kan nata, joining his nose directly with hers, cike da karfin hali
tace "I am sorry plsss" murda kofar dakin aka yi, yayi brushing lips dinsu ya mike
da sauri ya sauka saman gadon, Nihad ta ja wani numfashin wahala ta mike da sauri,
jikinta na rawa ta silalo kasa hawaye na sauka idonta, ya tafi gun switch din dakin
ya kunna, ya fara dube duben Jallabiyarsa a dakin ya dauka ya daura kan kayan
jikinsa sannan ya tafi ya bude kofar dakin, Mimi dai sai bin su take da ido ya
amshi cup din hannunta da sauri yace "Thank you dear... Zata bi yayanta inda ya
tafi shine na kulle kofar har ki zo, may be u can tell her not to" Nihad dai ta
kasa dago kanta daga inda take durkushe a kasa har sannan bata ji kirjinta ya dawo
dai dai ba, ga wani bugawa da zuciyarta yake alamar ba karamin tsorata tayi ba,
Mimi ta karasa ciki ta durkusa gabanta soothingly tace "Kiyi hakuri, tunda yasan
gidan definitely zai dinga zuwa wajenki ai, so ba sai kince zaki bi sa ba" Nihad
taki yarda ta kalleta kamar munafuka, Khalil dake tsaye bakin kofa yace "Kawai ki
tafi ki kyaleta idan ta gama kukan sai ta fita...." Zumbur Nihad ta mike har sai da
ta ba Mimi tsoro, Mimi ta mike tana kallonta ganin she looks so afraid tace "Are
you alright Neehad?" Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Mimi tace "Toh mu
tafi" Tana makale bayan Mimi suka nufi kofa, taki yarda ta kalli inda yake tsaye,
ya bi ta da ido har suka fita sannan yayi wani murmushi ya kulle kofarsa... Duk
zaman da Nihad tayi part din Mami bayan sun koma da Mimi she is so silent duk da
dama can ba wai tana magana bane amma na yanxu yayi worst, gaba daya ta kasa cire
abinda yayi mata a zuciyarta, abincin ma kasa ci tayi wai ta koshi, Mimi duk
tunaninta ai tafiyar farooq ne ya sa ta zama haka, shi yasa ma bata yi bothering
dinta ba. Wajen karfe tara Khalil ya shigo parlon wearing on his pajamas, sai da
gaban Nihad ya fadi ganinsa da tayi taki yarda kuma su hada ido, yana kallon Mimi
yace "Mami na ciki?" Mimi tace "Aa tana downstairs tun dazu" Yace "Ohk, ni bani da
abinci yau a gidan kenan?" Mimi ta ɗan zaro ido tace "Yayanmu wanda muka kai maka
daki fa?" Yace "I called Noor ta fita da shi ban ci ba, ai wannan yayi yawa sosai"
Mimi tace "Ohk sorry pls, should i get you another one now?" Yace "Yeahh, but ba
nan zaki kawo min ba, and ki ɗan kara hada min irin wannan coffeen da kika yi min"
Sosai gaban Nihad ya fadi da ta lura Mimi fita zata yi daga parlon, sai zazzare ido
take uwa warce tayi ma sarki karya, Mimi ta dau after dress dinta ta daura kan
sleeping dress din jikinta tace "I am coming Nihad" Nihad was shocked and confused
on what to do, haba ai bata san sanda ta mike da sauri xata ce mata tana son bin ta
amma tuni Mimi har ya fita, kamar munafuka ta fara tafiya zuwa kofa, Khalil dake
kallonta yace "Kee" Ta tsaya a tsorace ta kallesa kamar zata yi kuka tace "Ni
rakata zan yi" Bata jira me xai ce ba ta karasa kofar da gudu ta bude ta shige next
parlor amma taga Mimi har ta fice daga nan ma ta kulle kofar, bin bayanta Khalil
yayi tana ganin haka ta kwasa a guje ko kusa da kofar bata kai ba ta take dogon
hijab din dake jikinta na Mimi, sai ga tim a kasa ta zaro ido tana yarfe hannu, dai
dai nan aka bude kofar parlon, Mami ta koma baya tana kallonta tace "Subhanallah,
garin yaya?" Nihad ta mike tsaye da sauri xuciyarta na bugawa tace "Zan tafi in
kwanta ne, shine na fadu" tuni khalil ya koma daya parlon, Mami na kallonta tace
"Toh ki dinga yi a hankali, Hope you are not injured?" Ta gyada mata kai da sauri,
Mami tace "Toh sai da safe" Nihad tayi saurin fita daga parlon, Mami ta bi ta da
kallo, sai kuma ta karasa next parlor din, zaune ta tadda khalil yana waya, the way
he is talking on the phone xaka yi zata ya kai minti talatin yana wayar, Mami tayi
wucewarta cikin bedroom dinta. Sai da Nihad ta shiga dakin da take taji knees dinta
na mata zafi, ta zauna gefen gado tana dubawa taga ba ciwo amma zafi yake mata, da
kyar ta samu ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, ta saka kayan barci bayan ta
shafa turare ta kwanta saman gado tayi lamo, incident din daxu ne ya dinga dawo
mata, but what's the meaning of that?? Lokaci daya ta kawar da tunanin ta jawo
wayarta a hankali tana dubawa, taga miss calls din Ayman har biyu, zata ajiye wayar
sai ga wani kiran nasa, dagawa tayi ta rufe har kanta da duvet, ko minti goma basu
yi da fara wayan ba taji an kwankwasa kofar dakin, da sauri ta mike zaune ta katse
wayar tana kallon kofar, aka sake Knocking sauka tayi a hankali ta tafi gun kofar
tace "Waye?" Mimi tace "It's me" Daga haka Mimi ta bude tana kallonta tace "Mami
said i should ask if u are okay?" Nihad tace "Sure, thank you" Mimi tace "Ohk good
night" Nihad ta dan mata murmushi ta gyada kai kawai, daga haka Mimi ta juya ta bar
wajen Nihad ta kulle kofarta ta koma ta kwanta. Washegari Khalil na tare da Mami a
parlonta Aunty Hassana ta shigo da sallama, Khalil na jin muryarta yayi saurin kara
waya a kunne yana maganan da babu shi, Mami dai bata ce komai ba, har Aunty Hassana
ta karaso, shi kuma ya mike ya fice daga parlon still making fake call, Mami tace
"Mun tashi lafiya Hajiya Hassana" Aunty Hassana da ta bi sa da kallon gefen ido
tayi saurin cewa "Lafiya lau, ya yaran?" Mami tace "Alhamdulillah, ya su Sajidah"
Aunty Hassana tace "Toh ni naji kin min shiru, baki ce ga abinda ake ciki ba, don
last week naji Abbansu yace xa a kai kudin auren yaron nan, to mu ba wani shirye
shiryen da xa muyi a nan ne?" Mami tace "Ai gobe ne idan Allah ya kai mu" Aunty
Hassana tayi shiru tana kallonta da mamaki, can tace "Gobe goben nan amma ba
labari?" Mami tace "Ni ai na zata Amina ta gaya maki don muna tare da ita a parlon
Yallabai ya saka lokacin, and that was last week" Aunty Hassana ta hade rai tace
"Saboda Amina ce tafi kusanci da ni ko me?" Mami tace "Ba dai ta yanda xa ayi kice
baki ji daga bakinta ba Hassana, ko ita bata gaya maki ba ai yaci yayan naki ya
gaya maki, yaushe rabon mu hadu dake cikin gidan nan balle maganar ya hadu mu? Ai
mun kwana biyu bamu hadu ba" Aunty Hassana tace "Gaskiya ne, kya yaɓa min magana
son ranki ai, ba laifin ki bane" Bude baki Mami tayi tana kallonta tace "Meye abun
ɓacin rai a zancena Hassana?" Tuni Daga Hassana ta mike fuuu ta fice, tana komawa
bangarenta ta dau waya ta hau kiran kawarta Chamo, ta yaya za ace gobe xa akai kudi
ita da ta zata Mami zata ce mata an daga lokacin kai kudin, Chamo na dagawa Aunty
Hassana tace "Ke gobe fa naji ana cewa xa a kai kudin auren, yaya haka?" Chamo tace
"Toh in kai kudin aure sai aka yi yaya? Baki ta6a ganin inda aka fasa aure ranan
daurin auren bayan an tara jama'a ba?" Aunty Hassana tace "Haka ne, to amma idan
kuma
hakan bata kasance ba fa? Ai risk ne wannan Chamo, kamata yayi ko kudin ma kar a
kai balle a saida rana" Chamo tace "Ke dadina dake gajen hakuri wallahi, sai kace
yau aka saba maki aiki kiga aikin ya ci Hassana?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar
xuciya tace "Aa ba haka bane Chamo, ni dai kawai ina ga ba sai an wani je ga ranan
daurin aure a fasa ba, kawai tun ba aje ko ina ba a fasa gaskiya hankali na zai fi
kwanciya" Chamo tace "Toh ai abinda baki sani Malam yace min dole ne xa a kai kudin
amma a banza tunda ba auren za ayi ba, daga sanda aka kai kudin matsaloli xa su
dinga billowa daga both part har aure ya ruguje daga karshe" Aunty Hassana dai tayi
shiru don ita fa bata gamsu ba, tasan karkari aka kai kudin nan a sa wata daya in
dai yayanta ne, can tace "Toh daga ina ne xa su bukaci a fasa auren Chamo?" Chamo
tace "Shi da kansa Khalil din xai ce ya fasa, ke ni bari kiji wllh malamin ma ce
min yayi bai ga auren ba kwata kwata, xa dai ayi ta kashe kashen kudi, a siya
wancan a siya wannan na biki amma fa ba auren" Aunty Hassana tace "Toh yanzu
Sajidar ce ko farhana?" Aunty Hassana tace "Toh ai kya bari maganar auren ya ruguje
tukunna ki kawo wannan ko?" Aunty Hassana tace "Toh shikenan, sannan abu na karshe
kinsan ɗan iskan yaron nan ko gaisheni ya daina yi a gidan nan?? Wallahi tun da ya
dawo ga maciji bai hadani da shi balle yarana, iyaka yayi da kanninsa ko Hanan"
Chamo tace "Shi khalil din??" Aunty Hassana tace "Wallahi nake gaya maki" Chamo
tace "Wannan ai abu ne me sauki, xan kira malamin in gaya masa xa a san yanda xa
ayi...." Aunty Hassana tace "Toh Nagode, za mu yi magana zuwa anjima" Daga haka ta
katse wayar tana ta tunane tunane, ita wallahi ko kudin auren ma bata son ya shiga
hannunsu, don tasan ba amsa xa ayi ba idan aka fasa auren ai, ga kudi ba na wasa ba
xa a kai ta sani. Throughout ranan Nihad taki fito dakinta don ko by mistake bata
son haduwa da Khalil, wani sabon tsoronsa take ji har cikin zuciyarta, saboda yanda
ta sa abinda yayi mata jiya da daddare a ranta sai da tayi mafarkinsa cikin dare,
wajen karfe shidda na yamma Mami ta shigo dakin nata tana tsaye bakin kofa tace
"Why are you inside throughout?" Nihad ta ɗan yi yake tace "Aa ina kallo a waya ne"
Mami tace "Ohk, ga can takalmi Noor ta siya har da ke" Nihad ta dinga kallon Mami
jin wai Noor, ko dai Mimi take son cewa, da sauri tace "Toh Mami, xan fito yanzu"
Mami ta juya ta fita, a hankali Nihad ta mike ta dau mayafinta sannan ta fito daga
dakin. Tana shiga parlon Mami taga Mimi zaune tana operating laptop dinta, Mimi
tace "Kinyi scarce yau fa, hope you know you are having lectures tomorrow" Nihad ta
ɗan yi murmushi kawai ta zauna ta gyada mata kai, Mimi ta dau takalmi ta mika ma
Nihad tace "Noor got this for us all, same color same design" Nihad ta amsa tana
kallon takalmin tace "I appreciate it" bude kofar parlon aka yi Khalil ya shigo,
Mimi tace "Awnn Yayanmu you look good daga wajen Sis Nadeeyah kake ko?" Yace "Yeah,
ina Mami?" Tace "She went in not too long" Ya ɗan kalli Nihad suka hada ido, ta ɗan
daburce tace "erm... Good evening" Yace "Evening" Daga haka ya nufi dakin Mami
yana murmushi, Mimi ta wara ido tace "That's sweet of u Nihad, kuma naji dadi da
kika ji maganata" Nihad dai bata ce komai ba, can kuma dai ta dau takalminta tace
"Zan je inyi sallah, it's almost magrib" Mimi tace "Ohk" Daga haka Nihad ta mike ta
fice daga parlon don bata ma son ya fito ya sameta. Tare Khalil da Mami suka tafi
bangaren Abba ta dalilin kiranta da Abban ya aika khalil yayi, Mami ta gaishesa
bayan sun samesa a parlor tare da Aunty Hassana, Mami tace "How was the trip?" Yace
"Alhamdulillah" Mami tace "I was thinking ba sai ka dawo ba, representative dinka
kawai zaka aika goben" Abban ya ajiye takardun hannunsa yace "Ni ba saboda shi na
dawo ba ai, kuma i think gobe xan yi tafiya portharcourt..." Mami tace "Allah ya
kai mu" Shi dai khalil na zaune nesa da su yana danna wayarsa, Abba na kallon Mami
yace "Dama i want to confirm if ke ce ke aikosa ya zo nan yayi min rashin da'a"
Aunty Hassana ta sauke wani ajiyar xuciya, Mami ta kalli khalil da sauri, Khalil ya
ajiye wayarsa yace "But i see nothing wrong don na tambayi hakkina Abba, i am
asking you for my property, i seriously need them" Abba ya mike yace "Toh daga yau
ka sake shigo min nan da wannan maganar i am promising u i won't take it likely
with you..... Nace baxan bayar ba kuma i mean it" da mamaki Khalil yace "But why? I
have all right to ask Abba" cike da damuwa Mami tace "Me yasa idan na maka magana
baka ji Khalil? Me yasa kake daukan maganata for granted pls" Khalil ya mike yana
jin ransa na ɓaci yace "Mami to saboda me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login