Showing 243001 words to 246000 words out of 268471 words

Chapter 82 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

Allah
za mu ci gaba da zumunci kawu...." Aunty Jamila ta mike tace "Mu je can parlon
Aunty" Ta mike Mumy ma ta mike duk suka fita parlon tare da bakuwar suka bar kawun
nasu da Mubarak su ci abinci, suka nufi bangaren Mumy.




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah



Ur evidence via 07087865788



*Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun
turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin
kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki
ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin
sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta
dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp
09084473900*

74

Tun da suka shigo parlon Mami ke kallon Hajiya Safeenah da mamaki, ko ba Hajiya
Safeenah bace take gani, ita ko Hajiya Safeenah bata ma lura da Mami ba har ta
zauna a parlon, Aunty Suwaiba ta fita dauko mata ruwa da abinci, Mami tayi karfin
halin cewa "Safeenah??" Hajiya Safeenah ta juya da sauri zuwa direction din da aka
kirata, buda baki tayi ita ma da mugun mamaki tana kallon Mami, Aunty Jamila tace
"Lahh ashe kun ma san juna" Mami tace "Wai dama nan gidan ne za ki zo gaisuwa?"
Hajiya Safeenah ta kasa cewa komai tsabar yanda mamaki ya cikata, Mami tayi er
dariya tace "Ikon Allah, what a coincidence..." Hajiya Safeenah tace "Lallai kam
ikon Allah" a hankali Mumy da ta zauna parlon tana kallonsu tace "Ashe kun san juna
kenan" Mami tace "Kawata ce sosai Safeenah" Mumy tace "Allah sarki, To maa sha
Allah" Babu wanda ya kara cewa komai a cikinsu, ko wacce da tunanin da take a
zuciya, can Mami ta kalli Mumy warce ita ma tayi nisa tunanin da ta fada tace
"Hajiya an kai maki kayan shayi daki, da kin daure kin je kin sha ko ba yawa, ki
daina zama ba cin abinci" cikin sanyin murya Mumy tace "Toh" Daga haka ta mike ta
wuce bedroom dinta, Aunty Jamila ta mike ta bi bayanta don hada mata Shayin, Mami
ta kalli Hajiya Safeenah tace "Toh ya hanya Hajiya?" Hajiya Safeenah ta sauke
ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, sai gashi mun hadu gidan rasuwar" Mami tace
"Wallahi kuwa, amma marigayin kika sani ko uwar gidan tasa?" Hajiya Safeenah tace
"Ita warce ta shiga ciki yanzu ita na zo ma gaisuwa" Cike da confusion Mami tace
"Warce ta shiga ciki? To ai ita ce uwar Nihad, amma kuma i don't understand, a ina
kika santa? And kin saba zuwa gidan nan kenan kuma baki san Nihad ba?" Hajiya
Safeenah ta kalli Mami ta kasa cewa komai da farko, can ta jinjina kai a hankali
tace "My late father and her late father have the same parent amma kuma bamu taɓa
sanin juna ba sai yau ta dalilin rasuwan mai gidanta na zo mata gaisuwa, ni dai
kinga tun bayan rasuwar mahaifina mahaifiyata ta koma kasar Yemen da ni, a can na
girma nayi karatu har nayi aure a can, i never had the privilege of knowing my
paternal relatives gaba dayansu sai babban yayansu wanda muka zo yanzu tare da shi,
shine ma ya kirani ya sanar min rasuwan nan yace min tunda ina Nigeria lallai in
shirya in je gaisuwa don er uwata ce ta kusa amma bamu san juna ba" Mami ta rike
haɓa cike da mamaki tana kallon Hajiya Safeenah, can a hankali tace "You mean
Nihad's mother is ur cousin??" Hajiya Safeenah dai sai kallon Mami take bata ce
komai ba, Mami tace "Ikon Allah" Throughout zaman nasu a parlor babu me cewa komai
cikinsu, Hajiya Safeenah ruwa kawai ta dauka ta sha a abincin da Aunty Suwaiba ta
kawo mata... Mumy ta daure ta sha shayin da Aunty Jamila ta hada mata shi ma don
Aunty Jamila ta tsareta ne a dakin, Nihad na zaune gefen gado ta tashi daga baccin
da take, Mumy ta juya ta kalleta, sai kuma ta hada mata shayin a cup din da ta sha
ta dauka ta mika mata tace "Ki sha, ki tafi parlor ku gaisa da bakuwa..." Nihad ta
amshi shayin ta ajiye kan bedside drawer, a hankali ta sauko daga saman gadon ta
nufi bandaki don wanke bakinta, Aunty Jamila tace "Ga abinci nan Maman Khalil ta
kawo maki, sai ki hada da shayin" To kawai Nihad tace ta shiga bandakin. Bata tadda
su Mumy da Aunty Jamila a dakin ba bayan ta fito, ta dau shayin amma ta kasa don
bata da appetite gaba daya, it's now completely dawning on her cewar da gaske ta
rasa beloved Abbanta har duniya ta nade, ta goge hawayen da ya taru idonta ta tashi
daga kan gadon ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fito parlon Mumy, a kan Hajiya
Safeenah ta fara sauke ido a parlon, ta sunkuyar da kanta ta karasa ta durkusa
saman Carpet tace "Ina wuni?" Cikin sanyin murya Hajiya Safeenah tace "Lafiya lau,
ya hakuri??" Nihad tace "Alhamdulillah" Hajiya Safeenah tace "Toh Allah ya ji kansa
ya gafarta masa" Nihad tace "Ameen" Mami dai sai kallon Nihad take, kamar yanda
Hajiya Safeenah ma ke kallonta, Aunty Jamila da Aunty Suwaiba sai wata frnd din
Mumy kadai ne a parlon, Mami tace "Kin ci abinci?" Nihad tace "Yanzu zan ci" Mami
tace "To tashi ki je ki ci" Ta shi tayi ta koma dakin ta kwanta gefen gado, bata
san sanda wani baccin ya sake dauketa ba alamar alluran bai gama sakinta ba. Karfe
biyu saura Mami ta bar gidan bayan an mayar da flight dinsu zuwa karfe uku, Hajiya
Safeenah kuwa dama sai gobe zata koma Abuja, Mami bata samu yin sallama da Nihad ba
don har ta bar gidan bacci take. Wajen karfe biyar Nihad ta fito kofar gida ta
dalilin kiranta da Khalil yayi ta wayar Aunty Jamila, tun da ta fito gate din yake
kallonta, tana tafiya a hankali ta karaso gun motarsa, ya bude mata front seat ta
shiga ta kulle motar, A hankali yace "When did u wake up?" Ba tare da ta kallesa ba
tace "30 minutes ago" Ya juyo da ita yana kallonta ita ma tana kallonsa, ya kama
hannunta murya can kasa yace "Nasan baki ci abinci ba ko?" Bata son yaga hawayen
idonta saboda alkawarin da tayi masa, ya tada motar ya bar layin, wani tsadadden
eatry ya kai ta, ya dau menu din wajen dake saman table bayan sun zauna ya mika
mata yace "Zabar mana abinda za mu ci, kiyi mana order" Ta ɗan kallesa, sai kuma
tace "Sai wa zai biya?" A hankali yace "Hajiyata" Murmushi kawai tayi, ya kira mata
server din wajen, ta nuna masa abubuwan da zai kawo masu, Khalil dai sai kallonta
yake har server din ya bar wajen, ta daga kai ta kallesa, ya kashe mata ido yace
"Naga abinci me tsada kika yi ordering hope aljihunki da nauyi?" Tace "Idan ma ba
nauyi u can wash dishes...." Murmurshi kawai yake bai ce mata komai ba, aka kawo
masu abincin cikin some minutes, haka ya dinga distracting dinta da zance suna cin
abincin, and he love the way she ate much, suna nan zaune Mami ta kirasa don tun
dazu ya kira yaji ko sun isa gida lafiya, bayan sun gaisa tace "Don Allah ka ɗan
dinga sa mata ido ta dinga cin abinci" Yace "Alright in sha Allah, ga ta nan ku
gaisa" Ya mika ma Nihad wayar, bayan ta gaida Mami tace "Kun isa gida lafiya" Mami
tace "Alhamdulillah, ki daure ki dinga cin abinci kin ji" Nihad tace "In sha Allah
zan ci Mami" Sallama suka yi ta mika masa wayar. Sai dab da magrib suka bar wajen
bayan ya biya bills din, yana parking dai dai kofar gida yace "Bari in shiga
Masallaci" Tace "Toh" Ta bude motar ta sauka ya dau ledan takeaway da suka yi ya
mika mata, ta amsa tace "Thank you" Ya sakar mata murmushi yace "You are welcome
love" Sauke idonta tayi ta juya ta nufi cikin gate, ya kashe motar ya sauka. Mamaki
ya cika Nihad ganin Hajiya Safeenah a parlon Mumy tare da Inna, ta gaishesu ta
shiga cikin daki tana kallon Mumy dake zaune tare da Aunty Jamila, sa mamaki tace
"Mumy bakuwar Mami bata tafi ba? Naga Mami ta tafi ita ai" A hankali Mumy tace "Ba
bakuwa bace, gwaggwonki ce, she is my sister...." Nihad ta dinga kallon Mumy cike
da confusion tace "I don't understand ur sister, frnd din Mami ce fa, she is also
staying in Abuja, and ta zo nan saboda Mami ne" Mumy bata sake cewa Nihad komai ba
don ko magana me tsayi bata so, Aunty Jamila tayi murmushi tace "She is our cousin
sister Nihad, ke may be kin santa a Abuja saboda Maman Khalil, mu kuma er uwarmu ce
ta kusa ma kuwa" Nihad ta karasa kusa da su kana ganinta kasan ta rikice sosai tace
"Ban gane ba Aunty" Aunty Jamila tace "Zauna ki ji yanda mu ke da ita" Nihad ta
zauna gefen gadon tana kallonta, nan Aunty Jamila tayi mata bayanin relationship
dinsu da Hajiya Safeenah, Nihad dinga kallonta babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa,
What?? Does it mean Nadeeyah second Cousin dinta ce kenan?? Duk a zuciyarta take
wannan tunanin, Da yake su Mumy basu san komai kan auren da Khalil zai yi ba shi
yasa basu fahimci abinda yasa Nihad ta daburce haka ba, Aunty Jamila tace "Ita ma
Maman khalil din yanda kika yi mamakin ganinta a gidan nan haka tayi, ke a
tunaninki saboda Maman Khalil ta zo gidan nan ko?" Nihad ta gyada mata kai a
hankali amma ta kasa cewa komai don she is speechless, Aunty Jamila tace "Toh ba
saboda ita bace, er uwarmu ce ta kusa sosai, kasancewar uwarta er yemen yasa bamu
taɓa saninta ba, don a can suke da zama bana jin sun jima da dawowa kasar nan"
Nihad dai ta ma rasa abinda zata ce masu, gaba daya jikinta yayi mugun sanyi, Aunty
Jamila tace "She said tana da yarinya kuma tare suke a Abuja, kin san yarinyar ko?"
Nihad ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Aunty Jamila tayi kasa da murya ganin
reaction din Nihad is weird tace "Ko dai wani abu ya taɓa hadaki da ita a Abujan
ne?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Aa, kawai nayi mamaki ne" Mumy dai
kallonsu kawai take bata cewa komai don abinda ya dameta daban, Nihad ta mike ta
fita daga dakin still in shock, tana fitowa parlor suka hada ido da Hajiya Safeenah
warce ita ma tunani iri iri sun addabeta a zuciya tun bayan da ta san irin alaqarta
da Nihad, Nihad ta sunkuyar da kanta ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta fita,
dakin Nihal ta shiga ta sameta tana bacci, zaunawa tayi gefen gadon dakin ta
jinginar da kanta a hankali jikin gadon. Washegari karfe goma Hajiya Safeenah ta
bar gidansu Nihad zuwa Abuja don ta kagu ta koma don ta hadu da Mami, kuma tun da
ta zo har ta koma bata hadu da khalil a gidan ba, infact bai ma san ta zo ba don ba
a gidan yake kwana ba. A kwana a tashi har Abba ya cika kwana ashirin da tara da
rasuwa, zuwa lokacin kuma duk Allah ya sa ma family dinsa wani dangana na daban,
sun amshi kaddaran rasa shi hannu bibbiyu, yan uwa da suka zo daga garurruka daban
daban duk sun koma garinsu, gidan ya rage daga su sai su kawai, sai Inna da har
sannan taki komawa gidan babban ɗan ta wanda kullum da daddare shi ma zai zo gidan
shi ma, Aunty Jamila ma dai bata koma ba tana wajen yayarta sauran kannin Mumy ne
suka koma gidajensu, Har a lokacin Umma na gidan amma zaman daki kawai take, ko nan
da parlonta bata lekowa, a ko da yaushe ka shiga dakin nata zaka ganta zaune at the
very far end a kan darduma da carbi a hannunta, Kamila kuwa kamar kar Abba ya rasu
ta dawo hankalinta duk sabbin halayen da ta tsiro
ta daina tunda dama ba bin jikinta yayi ba, Nihal ce kadai har yanzu bata daina
kukan Abbanta ba safe, rana, da dare, ita kadai ce taki hakura, kullum zaka ganta
babu walwala sai kuka, gwara Nihad ita cikin dare take nata kukan, duk don Nihal ta
kwantar da hankalinta Mumy har cewa tayi Abba ya bar mata wasiyyan ya yafe mata
duniya da lahira kawai Allah bai yi za su gana bane, amma Nihal taki yarda da
hakan, ga Umma ko magana bata son mata a gidan, su ya farooq ma sama sama suke
kulata, sai tayi kwana da kwanaki bata ga yayyin nata ba tunda yanzu dakin Mumy ta
dawo gaba daya take Rayuwarta, result din su na final exams ma da ya fito sai da ta
samu spill a almost duk courses din da ta dauka a semester din, ita da ko carry
over bata taɓa samu ba a makarantar, wajen Mumy da Aunty Jamila kadai take samun
relief a gidan, sae Nihad dake jan ta jiki ynzu, Aunty Maryam ta kira Mumy tun
sanda aka yi rasuwan yayi sau hudu yanzu, kuma duk sanda ta kira zata sa Mumy ta ba
Nihad su gaisa. Mumy ce zaune kan darduma da Hijab dinta har kasa hannunta rike da
carbi, Aunty Jamila da Nihad ma suna dakin sai Nihal dake kwance idonta a rufe
amma ba bacci take ba, Mumy ta kalli Aunty Jamila cikin sanyin murya tace "Ya
kamata kuma ta tattara haka ta bi mijinta su tafi gida ko Jamila?" Nihad ta daga
kai ta kalli Mumy da sauri sanin da ita take, Aunty Jamila tace "Gaskiya kam, tunda
anyi sati hudu har da kwana biyu yau, kuma nasan saboda ita ne ma bai bar garin nan
ba har yanzu, kar rashin hankalin namu yayi yawa" Nihad ta marairaice tace "Mumy ba
sai anyi 40 days ba?" Mumy ta ɗan kalleta tace "Me za kiyi har 40 days a nan din?"
Aunty Jamila tace "A duk inda kike kika ma Abbanki addu'a zai samesa ba sai lallai
gidan nan ba Nihad, kinga Allah ya baki miji wanda ba ko wace mace ke samun irinsa
ba a rayuwar nan, uwa uba ga danginsa mutanen kirki mutanen arziki, duk da
matsayinsu amma kowa nasu ne babu girman kai ba komai, to kada mu zama kananun
mutane mu yi ta ajiyeki a nan, gashi yau har sati hudu, don haka ki shirya gobe ya
daukeki ku koma..." Nihad ta dinga kallonsu har hawaye ya cika idonta, tsoronta kar
ta koma Abuja damuwar rasuwan Abbanta ya dawo mata sabo, don idan tana ganin Mumy
da yan uwanta tana jin relieve sosai, Ta goge hawayen idonta cikin sanyin murya
tace "Then can i go together with Nihal?" Aunty Jamila tace "Sai abinda mijinki
yace" Nihal ta buda ido tana kallonta, a hankali tace "I will come but not now"
Nihad bata sake cewa komai ba, haka Aunty Jamila ta sata gaba ta fara hada kayanta
a akwati, Usman yayi sallama kofar dakin, Mumy da Aunty Jamila suka amsa masa ya
shiga, bayan ya gaishesu yace "Mumy dama na shigo in gaya maki Abban Khalil ya
samar min aiki a Nnpc na garin kaduna" Mumy da Aunty Jamila suka hada baki wajen
cewa "Alhamdulillah" sosai suka taya sa murna, Mumy tayi masa addu'a sosai tayi
masa fatan alkhairi, Yace "Nagode Mumy, Allah ya kara girma" Mumy tace "Yaushe zaka
yi resuming aikin kenan?" Yace "Gobe lahadi za mu tafi kadunan tare da Farooq don
shi ma zai koma aiki, on monday in sha Allah zan fara aikin" Mumy tace "Toh Allah
ya bada sa'a, Allah ya tsare" yace "Ameen" Daga haka ya mike ya fita daga dakin,
Aunty Jamila tace "Allah sarki, na taya sa murna sosai, Allah ya saka ma General da
alkhairi" Tun da aka tura ma Usman offer din yaje ya nuna ma Umma a dakinta, ko
gani bata yi ba bayan ta masa addu'a ta tasa ya je ya nuna ma Mumy a bangarenta.
Aunty Jamila da Nihal na zaune parlon Mumy suna kallon wani movie Khalil ya kirata,
ta daga wayar bayan ya gaisheta yace "Aunty dama zan zo da wani bako ne yanzu zai
ma Mumy gaisuwa" Aunty Jamila tace "Toh sai kun zo" Nihad na can daki tare da Mumy
da tun yanzu har ta fara mata nasiha ta yi hkuri ta zauna lafiya da mijinta kar ta
basu kunya, gaba daya sun sa ta hada kayanta duk da dai basu ce ma khalil din gobe
ya dauketa su tafi ba, tana son gaya ma Mumy auren da zai yi amma ta kasa don
that's her only nightmare ynzu, Aunty Jamila ta shigo dakin tace "Yaya ki fito za a
maki gaisuwa" Mumy tace "Toh" daga haka ta mike ta nufi kofa, Nihad ta bi ta da
kallo, lokaci daya hawaye ya cika Idonta, Mumy na shigowa parlon ta zauna tana
kallon balaraben dake zaune, ya gaisheta da turanci ta amsa da fara'a, nan yayi
mata gaisuwa, ya kuma yi ma Abba addu'a sosai, cikin sanyin murya tace "Ameen,
thank you very much" Khalil ya gaida Mumy don duk ranan bai shigo gidan ba, Aunty
Jamila ta tafi main parlor dauko ma baƙon ruwa don in dai Nihal ce ba tashi zata yi
ba in ka bibiya ma hankalinta baya tare da ita, don a ko da yaushe zaka sameta
absentminded barin idan ana kallo, Baƙon ya daga kai yana kallonta yace "Hi Nihad,
i am so sorry for ur lost, may Allah SWT grant him aljannatul firdauss" Khalil ya
ɗan yi murmushi ya kallesa da turanci yace masa ba Nihad bace sister dinta ce, Mumy
ta tabo Nihal da bata ma san ana mata magana ba, Da sauri ta dawo duniyar tunanin
da ta tafi, Khalil yace "Yana maki gaisuwa...." Ta kallesa duk da bata san abinda
yace ba tace "Ameen nagode" Nihad ta fito daki don sarai ta dau muryarsa, ya daga
kai yana kallonta bayan ta fito, tana Murmushi tace "Hi Ayman" Da Fara'a ya amsa
mata, ta karaso ta zauna a parlon, nan suka gaisa yayi mata gaisuwa ta amsa ta masa
godiya, yana nuna mata Nihal da mamaki yace "The resemblance is obvious, just
complexion difference" Tana Murmushi tace "Yeah, she is my blood, her name is
Nihal" Ya sake kallon Nihal yace "Nihal" Nihal ta kirkiri murmushi bata ce komai ba
Yace "It's nyc meeting with you Nihal" Ta gyada masa kai kawai, don bata son magana
yanzu, Ayman bai wani dade a parlon ba, bayan ya sha ruwan da Aunty Jamila ta ajiye
masa, yayi ma Mumy sallama ya ajiye mata dollar dari biyar, Mumy da Aunty Jamila
suka yi masa godiya sosai, ya fita parlon tare da Khalil, Mumy na kallon Nihad da
mamaki ganin yawan kudin da ya ajiye mata tace "Who is he?" Nihad tayi murmurshi
tace "Sister din Mami namesake dinki ce ta hadani da shi farkon zuwana Abuja" Aunty
Jamila ta buda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login