Showing 240001 words to 243000 words out of 268471 words

Chapter 81 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

mum and her Co wife also before
leaving" Khalil yace "Alright sir" Daga haka ya bi bayan Nihad da har ta fita daga
parlon, Aunty Jamila ya samu don har sannan ya kasa facing Mumy, ya sanar mata
Janar zai yi magana da Mumy da Umma, Aunty Jamila tace "Toh bari in mata magana" Ta
tafi inda Mumy ke zaune da duk sisters dinta da Aunts suna amsan gaisuwa, Inna da
idonta yayi bulu bulu tana gefe zaune ita ma da wasu tsofaffin a kusa da ita, Aunty
Jamila ta durkusa kusa da Mumy tace "Baban Khalil na son magana dake da Umma yanzu"
Inna da taji abinda Aunty Jamila tace ta kalleta, a hankali tace "Wacece kuma Umma?
Meye hadinta da Baban khalil din har zata je Jamila?" Sai kuma ta fashe da
matsanancin kuka tana girgiza kai tace "Ban yafe maki ba idan kika je da ita, taje
tayi masa me Jamila? Ina ce matar marigayi aka ce ke kira? Yana da wata matar ne
bayan Maryam? jira fa nake yau da daddare idan kowa ya watse gidan nan Sumayya ta
hada kayanta ta tafi kuma haka, ai na mata kara na bar ta har aka yi uku kuma ban
ce komai ba, taje duk inda zata amma bana son ganinta a gidan nan, Allah ya hada mu
a darussalam" Aunty Jamila dai bata ce komai ba, Inna ta kalli Mumy a hankali tace
"Daure ki tashi ki je Maryam, Allah Ubangiji ya kara mana tawakali" Mikewa Mumy
tayi Aunty Jamila na biye da ita har zuwa parlon Abba, ta nemi gefe ta zauna a
parlon, Janar ya kara mata gaisuwa cikin nutsuwa, nan ya dinga bata baki yanda ya
kamata, ita dai hawaye kawai take kanta a kasa bata cewa komai, daga karshe Janar
yace "Allah Ubangiji ya gafarta masa, ya sa yana kyakkyawan masauki, mu kuma Allah
ya kyautata namu, Allah ya kara maki hakuri da dangana" A hankali Mumy tace "Ameen"
Abokansa ma suka kara mata gaisuwa, Janar ya dau wani fancy leda babba dake gefensa
ya mike ya tafi har gaban Mumy ya ajiye mata yace "Allah ya kara hakuri, we will be
communicating in sha Allah" Aunty Jamila ce tayi masa godiya tace "Allah ya kara
girma, ya saka da Alkhairi" Mumy dai bata iya tace komai ba, Wani abokin Janar ya
tashi shima ya ajiye mata wani ledan a gabanta yace "Allah ya kara hakuri Hajiya"
Sauran frnds din Janar suma suka har hada kudin wajensu waje daya duk suka ajiye ma
Mumy, Aunty Jamila ce ke yi masu godiya ita kam bata iya cewa komai, har suka fita
daga parlon, Janar na kallon Khalil da ya shigo yace "Where are all his children?"
Khalil ya juya ya fita, tare ya dawo parlon da Farooq da Usman, Abba ya kara masu
gaisuwa yana kallon Farooq ganin kamar shine babba yace "Kana aiki ai ko?" Farooq
ya gyada masa kai ya sanar masa inda yake aiki a kaduna, Janar yace "That's good"
Ya kalli Usman yace "Kai kuma fa?" Usman ya sauke kansa yace "I had issues with the
place i am working" Janar yace "Ka bani CV dinka kafin in bar gidan nan" Usman yace
"Toh Allah ya saka da Alkhairi" Janar ya mike yace "Bari inyi ma tsohuwa sallama za
mu koma Abuja yau in sha Allah" Har main parlor ya fita ya tafi gaban Inna ya duka
ya kara mata gaisuwa sannan ya sanar mata za su koma Abuja, Ta fashe da kuka sosai
tace "Toh Allah ya saka da Alkhairi, Allah bar zumunci, mun gode, ai ka kyauta ka
ture duk wani aikin tsaro na kasar nan ka jira har aka yi sadakan uku, ina ta
addu'a Allah yasa kada mutanen dajin su lura ba kai su kawo hari cikin gari kai
kuma baka baƙin aiki kaje ka samu matsala da gwamnati" Kuka take sosai tana
maganan, Yace "Kiyi hakuri Baaba, kuma ki rage kukan nan kiyi ta masa addu'a shi
kawai yake bukata daga gareki, kiyi ta masa addu'a" Cikin kuka tace "In sha Allahu"
Dubu dari biyu ya ajiye mata, abokansa ma duk suka karaso suka kara yi mata
gaisuwa, sannan ko wannensu ya ajiye mata dubu dari, ita dai sai kuka take kamar er
yarinya, a haka dai Janar suka bar gidan tare da frnds din nasa don Convoy na waje
tun zuwansu, Khalil ya samu Abbansa da har ya shiga mota, Janar ya juya yana
kallonsa, ya mika masa CV din Usman yayi kasa da murya yace "The first wife, baku
samu kun yi sallama da ita ba...." Janar ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ka bata
500k, i will make the transfer to you" Khalil yace "Alright sir" Janar na kallon
envelope din hannunsa yace "Wannan fa?" Khalil yace "CV din da kace a baka" Janar
yace "Ohh haka ne" Daga nan ya amsa ya mika ma abokinsa dake kusa da shi yace "Kar
in manta wannan pls" Abokin ya amsa, Khalil yace "Allah ya tsare" Daga haka ya juya
ya koma ciki, shi ko don saboda su Farooq bai son a walakanta Umma, ya kamata ta ci
darajarsu, mahaifiyarsu ce kuma uwa uwa ce ko ya take, beside kallo daya zaka yi
mata kaga tsantsan danasani da ladama a tare da ita, duk tayi zuru zuru kamar ita
kadai aka yi ma mutuwa, the thought of this is making him feel so sad. Wajen karfe
shidda Mami tace ma Mumy za su tafi, amma gobe kafin su tafi Abuja zata shigo, tun
ranan da suka zo sai yamma likis suke barin gidan da su Mimi su koma gidansu na nan
Kano, da safe kuma kafin karfe takwas suke isowa gidan, har dai aka yi sadakan uku
yau, cikin sanyin murya Mumy tace "Toh Hajiya, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya
bar zumunci" Mami tace "Ameen, Allah ya kara maki hakuri" Nan tayi ma Inna ma
sallama, sannan ta tafi tayi ma Umma dake can wani lungu a zaune da su Kamila da
kanninta biyu sallama, Mami bata bar gidan ba sai da ta karasa part din Mumy wajen
Nihad, ta sameta zaune tare da Aunty Jamila dake kara kwantar mata da hankali don
ko gajiya da kukan ma bata yi, Mami ta fi 15 minutes a dakin tana bata baki ita ma,
har dai Nihad tayi mata alkawarin bazata sake kuka ba kafin ta bar gidan da su
Mimi. Da daddare Aunty Jamila da sisters din Mumy Suwaiba da Khadija suka dauko
ledan da Janar da abokinsa suka ba Mumy suna dubawa, bundles of note ne masu yawan
gaske yan dubu dubu, kuma kusan kan kudin da abokin Janar ya bada daya ne da na
Janar din, da suka ga ba kudi bane da za su ce zasu iya kirgawa a lokaci kankani
kawai Aunty Jamila ta bude press din Mumy ta ajiye kudaden a ciki. Mumy na kallon
Aunty jamila a hankali tace "Don Allah ku duba jikin Nihal, ko kuma ki ce nace ta
dawo nan" Aunty Jamila tace "Naga basu dade da dawowa daga asibiti da Kawar Umma da
kanwarta ba ai" Mumy tace "Duk da haka ki duba min ita ko ta samu ta ci abinci,
kuma ta dawo nan" Aunty Jamila ta girgiza kai cike da tausayin Nihal tace "Idan zan
koma Jigawa ki bar ni in tafi da ita Mumy kar yarinyar ta samu matsala a
kwakwalwarta, she is already depressed amma har yanzu babu wanda ya gane hakan"
Mumy dai ta kasa cewa komai, don ita bata ma yi tunanin Nihal will make it har yau
ba, kuma gaskiya Aunty jamila ta fada ita kanta tasan ta shiga depression tun kafin
rasuwan Abba, yanzu kuma duk gani take he died because of her, Aunty Jamila dai ta
juya ta shiga dakin Nihal, duke ta ganta jikin gado kasan dakin duk ta hada zufa,
Aunty Jamila ta nufeta da sauri tace "Lafiya Nihal?" Kasa ce mata komai tayi but
kana ganinta kasan she is in severe pain, Aunty Jamila ta buda ido a tsorace ganin
jini me yasa a kasa, da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai kuma ta
juya da sauri ta koma dakin Mumy hankali tashe ta sanar mata abinda ta gani, Mumy
da sauran sisters dinta da Aunt dinta suka nufi dakin Nihal din da sauri, Mumy na
kallon Aunty Jamila bayan ta dago Nihal tace "Kira min Khalil da sauri" Aunty
Jamila tayi saurin komawa parlor daukan wayarta, makale taga Nihad jikin kofa ta
kasa shiga dakin, Aunty Jamila tayi saurin kiran Khalil.... Karfe sha daya saura na
dare Aunty Jamila ta kira Mumy da ta kasa zaune ta kasa tsaye damuwa kala biyu a
ranta, hawayen ma yanzu babu sai kukan zuci, cikin sanyin murya Mumy tace "Ya ake
ciki Jamila? Ya jikin nata?" Aunty Jamila ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai
tace "Cikin jikinta ya zube, da kyar likitocin suka samo kanta wllh, yanzu Yaya sai
da Turai da kanwar Umma suka san yanda suka bi aka zubar da cikin nan ba tare da
sanin yarinyar ba, to alhaki a kansu wllh, ni dama da suka ce za su kai ta asibiti
dazu sai da na zargi hakan, amma duba da halin da yarinyar ke ciki ai babu wanda
zai kawo abinda za su kai ta su aikata kenan, ba ma ta lafiyanta suke ba, burinsu
kawai ciki ya zube kuma sun zubar sai suje su san abinda za su gaya ma Allah" Mumy
dai ta kasa cewa komai sai hawaye masu zafi ke sauka idonta, she wish basu zubar da
cikin ba ko ita zata rike koma me Nihal zata haifa, ta so anji wasiyyan Abba na
cewa kada wanda yace zai xubar da cikin tun ana saura kwana biyu zai bar duniya,
Aunty Jamila ta sauke ajiyar zuciya tace "Shikenan yaya sai gobe, amma da sassafe
ki ba ko Suwaiba
kayanta ta kawo mana asibiti da ruwan shayi" Cikin sanyin murya Mumy tace "Allah
ya kai mu, ki kula da ita don Allah Jamila" Daga haka ta katse wayar. Washegari da
safe Mami tayi lafiyayyen farfesun kaji ta dafa white rice zata kai ma Nihad ganin
da tayi ko abinci bata ci ko ya za ayi da ita kuwa, ta gama shiryawa Mimi ta kai
mata abincin compound ta saka a mota, Mami ta dau gyalenta da jaka zata fita
wayarta ya fara ring, bude jakar tayi ta ciro wayar ganin Hajiya Safeenah ce ke
kiranta ta daga suka gaisa, Hajiya Safeenah tace "Ya karin hakuri?" Mami tace "Mun
gode Allah" Hajiya Safeenah tace "Toh Allah ya gafarta masa" Mami tace "Ameen,
zuwan naki na nan kuwa?" Hajiya Safeenah tace "In sha Allahu, in dai na gama abinda
ya kai ni zan kiraki... Incase ma baxa mu hadu ba sai ki turo min address kawai in
karasa in masu gaisuwa" Mami tace "Toh ba damuwa, Allah ya tsare" Daga haka suka yi
sallama ta katse wayar, Mimi ta rakata har bakin mota, Noor tun jiya dama ta koma
da su Janar, Mami tace "Sai na dawo, kafin in dawo kuma you make sure our boxes are
ready don Flight dinmu na komawa Abuja karfe daya ne" Mimi tace "Toh Allah ya kai
mu, ki gaida Nihad" Mami tace "In sha Allah" Daga haka Mimi ta juya ta koma cikin
gidan. Mumy na bedroom dinta tare da Inna dake rusa kuka kamar ranta zai fita tace
"Har hakura nayi na kai zuciyata nesa fa na bari aka yi uku Maryam, hakan da nayi
ban kyauta ba kenan?? idan ina ganin matan nan a gidan nan kin san me nake ji a
zuciyata kuwa? Wallahi kallon warce ta kashe min ɗa nake mata, akan me zaki dinga
bani hakuri haka Maryam? Kinsan zafin rasa ɗa kuwa? Har abada fa bazan sake ganinsa
ba ya tafi kenan" sai ta kuma rushewa da matsanancin kuka tace "Allah Ubangiji yayi
maka rahama Ibrahim, Halinka na gari ya bi ka, tun da muke bai taɓa saɓa min ba,
kullum cikin yi min biyayya da kyautata min yake, idan ma ya taɓa min laifi na yafe
masa duniya da lahira, Allah yayi masa Rahama, Allah Ubangiji ya basa sa'a" Mumy
dake zaune gefen gado ita ma hawayen kawai take ta ma rasa me zata ce ma Inna, tun
dazu take kokarin ganar da ita rashin amfanin ce ma Umma sai ta bar gidan, Cike da
karfin hali tace "Albarkacin yaranta za ki duba Inna, ko don su Farooq kar kiyi
haka don girman Allah, har yanzu ba wai mutane sun san me ke faruwa bane, ba wanda
yasan abinda ya faru, kuma kinga akwai sauran yan uwa da abokan arziki da basu tafi
ba, idan kika ce sai ta bar gidan nan yau ai kinga za su so sanin abinda ke faruwa,
ki rufa mana asiri tunda Allah bai tona mana ba don Allah inna" Kuka Mumy take yi
sosai, Inna na shessheka tace "Maryam ganinta na daga min hankali ne, idan ba dai
zama zan yi a dakinki in ki fita har sai duk an gama watsewa ba sannan in sa ta
tattara komai nata ta bar gidan nan ita ma" Mumy na girgiza kai tace "Nace ki dubi
su farooq kar kiyi haka Inna, ki bar su su ji da daya" Inna tace "Da can bata duba
su Farooq din ba tayi duk abinda tayi, ni dai wallahi don kin hanani ne Maryam
banda haka Sumayya bazata kwana a gidan nan nima in kwana ba yau" Mumy bata sake
cewa komai ba tana share hawayen da yaki yanke mata yau kwana hudu kenan, a kwanaki
hudun nan ba karamin rama tayi ba, kana ganinta kasan karfin hali kawai take amma
tana cikin tashin hankali da shock, Inna dake kallonta tana shesshekan kuka tace
"Ki daure ko ɗan ruwan shayi ne ki dinga sha Maryam, kar kije wani ciwon ya kama ki
kuma" Mumy dai bata ce komai ba, Aunty Jamila ta shigo dakin da sallama tana kallon
Mumy tace "Kawu Salisu sun iso Yaya" Mumy ta kalleta tana share hawayen idonta,
jikin Aunty Jamila yayi sanyi, bata son ganin yayartata a haka, hankalinta tashi
yake sosai, Karasowa cikin dakin tayi cikin sanyin murya tace "Plss i need u to be
strong Aunty, i know it's hard, it's painful but for the sake of ur little kids be
strong plss" Lokaci daya ita ma ta fara hawayen, Mumy dai ta rike kanta bata ce
komai ba hawaye na sauka idonta, Inna kuwa na can ta fada duniyar tunaninta tana
hawayen ita ma, Aunty Jamila ta goge idonta tace "Na kai su can parlon tun da akwai
mutane a naki, ki taso yaya" Kai kawai Mumy ta gyada mata, Aunty Jamila ta mike ta
fita daga dakin, Mumy ta kalli Nihad dake bacci tun wayewar gari, tun bayan rasuwan
Abban nata sai yau tayi bacci na kusan awa uku, amma yanda take ganin rana haka
take ganin dare, yau din ma alluran bacci Khalil yayi mata bayan da ya kirata ta
samesa a mota a waje, Mumy na kallon Inna a hankali tace "Bari in je inna, yayan
babanmu ne ya zo" To kawai Inna tace mata, Mumy ta fita daga parlon tana tafiya a
hankali, Mami dake zaune parlon tare da Aunt din Mumy ta bi Mumy da kallo tace
"Amma da kin samu ko shayi ne ki sha Hajiya" Mumy tace "Ehh nayi baki ne yanzu zan
dawo sai in sha" Mami tace "Toh je ki dawo" Aunt din Mumy ta sauke ajiyar zuciya
tace "Bata cin abinci kwata kwata, wannan kadai ma ya isa ya sa mata ciwo ai" can
parlon Abba Mumy ta tafi don can Aunty jamila ta sauke baƙin, Dattijo ne sosai don
zai yi shekara 87, sai kuma wani wanda bazai wuce 58 ba, da wata mata dake tare da
su, sauran sisters din Mumy da suka sun shigo parlon yi masu sannu da zuwa su ma,
Mumy ta zauna saman Carpet tana kallon dattijon a hankali tace "Sannu da zuwa Kawu"
Cike da alhini Dattijon na Girgiza kai yace "Sannu Maryam, sannu, Allah ya baki
hakuri, ashe Ibrahim sa'i yayi, toh Allah ya gafarta masa yayi masa Rahama, Allah
ya kara maki hakuri" A hankali Mumy tace "Ameen kawu, fatan kun zo lafiya" Yace
"Lafiya lau, saukan mu kenan, tun jiya muka so zuwa Mubarak muka jira ya iso
Abujan" Aunty Jamila ta shigo parlon da tray din ruwa da lemo, wata kawar Mumy na
biye da ita da warmer din abinci da plates, ta ajiye masu, matar ta juya ta fita
bayan sun gaisa, Aunty Jamila ta nemi waje ita ma ta zauna tana kara masu sannu da
zuwa, mutumin dake gefen Dattijon yayi ma Mumy gaisuwa shi ma, haka ma matar dake
zaune a parlon, Mumy tace "Ameen, Allah ya bada lada" Dattijon na nuna mutumin dake
gefensa yace "Baku san wannan ba ko?" Duk suka dinga kallon Mutumin da ya nuna
masu, Dattijon yayi murmushi yace "Xumunci yayi wuya yanzu, yaran yanzu bakwa
zumunci wai ku yan boko, to ɗan uwanku ne Mubarak, shine ɗa na na biyu" Aunty
Suwaiba tace "Allah sarki, zumunci kam yayi wuya kawu, wai ɗan uwanmu amma da za mu
hadu a hanya sai dai ya wuce mu ce" Dattijon yace "Toh dai kuyi ma kanku fada,
shikenan don iyayenku sun rasu sai aka ce a yanke zumunci, to Allah ya ji kansu ya
gafarta masu" Duk suka amsa da "Ameen kawu, kai kuma Allah ya kara maka lafiya, in
sha Allah za a gyara" Ya nuna masu matar dake zaune yace "Wannan ma ba sai na bata
bakina ba nasan baku santa ba...." Duk dai suka yi shiru suna kallonta, yayi
murmushi yana girgiza kai yace "Babanku Ahmadu bai taɓa baku labarin Kawunku
Abudurrahman ba? Wanda ya rasu shekaru kusan 30 da suka wuce yanzu" Aunty Jamila
tace "Lahh kawu Abudurrahman din ne bamu sani ba Kawu? Kawai dai muna yara ne
lokacin" Yace "Toh er sa ce wannan...." Duk suka dinga kallonta, Mumy tace "Allah
sarki, sannu da zuwa Hajiya" tayi murmushi tace "Sannu, zumuncin ne yayi wuya
yanzu, gashi duk bamu san juna ba...." Alhaji Mubarak yace "Kun ga cousin dinku ce
ta kut da kut amma duk ba a san juna ba" Aunty Jamila tace "Gaskiya kam, rayuwa
kenan, Allah ya ji kan kawu Abudurrahman, tunda Allah ya hada mu yau in sha Allah
za a ci gaba da zumunci yanda ya kamata, naji dadin haduwar mu da ita, muna da
labarinta amma bamu santa ba" Dattijon yace "Toh ga ta yau... Dama mu hudu ne kacal
gun iyayenmu duk kun sani, ni ne babbansu sai Abudurrahman Allah yayi masa gafara,
Sannan Ahmadu mahaifinku shi ma Allah ya ji kansa, Autarmu Asiya wajen haihuwar
fari ta rasu, Allah ya gafarta mata, to don haka ga yar uwarku ku ci gaba da
zumunci don Allah, dama Allah bai yi mu da yawa ba, kun ga ita kadai ce gare
Abudurrahman har ya koma ga mahaliccinsa, ni dama Mubarak ne sai Salaha da Asiya,
Ku kuma Maryam, Jamila, Suwaiba sannan Khadijah, ɗan autanku ya rasu, don haka
Allah ya ji kansu da rahama" Duk suka ce "Allah ya gafarta masu, kuma in sha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login