Showing 213001 words to 216000 words out of 268471 words
koma ga Allah, to da ko anguwan da nake bazan bari ki karaso
ba balle ki shigo gidana har ki zauna zaman shekara talatin...." Aunty Hassana ta
dinga kallonsa ko kiftawa babu, yace "Ba hauka Ibrahim yake ba da zai raunata Aliyu
haka nan kawai, they must definitely be something, they must be a reason...." Aunty
Hassana na huci tace "Toh ai naga akwai cctv a gidan a duba mana a ga dalilin tunda
goyon bayan ɗan ka kake Abubakar" Janar yace "Cctv din da ku ke kashewa ko wanne
kike nufi a ciki? Hassana yau ba sai gobe ba ki bar min gidana kada in sa sojoji su
fitar min dake, wallahi karfin zumunci kawai nake dubawa nake zaune dake banda haka
a irin makircin da kika hada min a baya ko kusa da inda nake bazan bari ki zo ba"
Wani murmushin takaici tayi tace "Ohk" Daga haka ta juya ta fice daga parlonsa,
direct bangaren Hajiya Amina ta nufa, Hajiya Amina ta taso tace "Ya ake ciki
yanzu?" Hassana tace "Ragowar kudin nan na wajenki zaki turo min yanzu" Hajiya
Amina tace "Kudi kuma? Aa ni babu ko sisi a wajena, ai kudin sun kare" Wani
axababben kallo Aunty Hassana ta jefa mata tace "Me din suka kare?? Miliyan 15 din
nan da yayi saura fa nake nufi" Hajiya Amina tace "Aa, ni fa nace maki babu ko sisi
a tare da ni" Aunty Hassana tayi mici mici da ido tace "Kan uban can, to kuwa zan
maki rashin mutunci, ni zaki ce ma babu ko sisi?" Hajiya Amina tace "Yau ga ikon
Allah, kudin haihuwa suke ne, kwanaki kin san sa na tura ma sadiya miliyan 3, to
dama ai shikenan ya rage a kudin ko bakya lissafi ne??"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son
sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da
xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan
turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba.
Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu
xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da
hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls
guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda
hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls
guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din
da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman
in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800,
6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar
maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰
Ga number da za a tuntuba kamar haka. +2347065525409
63
Mami ta koma ɓangarenta tana hada sauran ankon da zata tura Drivernta ya kai ma
kawayenta da bata tura ma ba Noor ta shigo parlon, hankali tashe tace "Mami Aunty
Hassana da Mumy suna ta fada fa tun daxu" Mami ta mike tsaye tana kallonta da
mamaki tace "Fada kuma?" Noor tace "Wallahi har da dambe" Mami ta zaro ido tace
"Damben lafiya" Noor tace "They are fighting seriously fa a part din Mumy" Mami ta
nufi kofa ta fita da sauri, Noor ta bi bayanta, tun daga Babban parlon gidan take
jin muryoyinsu suna kunduma ma juna zagi kafin ma ta karasa bangaren Hajiya Amina,
tsaye ta ga Janar bakin kofa yana kallonsu, bai kuma yi attempting dakatar da su
ba, Suhaila da mai aiki na ta rirrike Aunty Hassana warce ke kokarin kara finciko
Hajiya Amina su fara wani sabon damben ga Attachment dinta yashe a kasa Hajiya
Amina ta tuge, Hajiya Amina na huci tace "Ku saketa don Allah ta zo, Banza kawai er
wahala, kafura...." Aunty Hassana na tura su Suhaila da karfi take cewa "Ku bar ni
in illata yar iskar, ni kike kira da er wahala? Ni? Toh wallahi zaki san ni kika ce
ma er wahala" Hajiya Amina na tafe hannu tace "An fada, er wahala, dama ba
wahalalliyar bace?" Cikin daga murya Aunty Hassana tace "Yanda nayi sanadin aka
aureki haka duk abinda zan yi sai nayi an sakeki Amina, wallahi karshenki ya zo a
gidan nan, ke banda na shiga na fita ko a er aikin gidan nan kin isa ki shigo balle
matar gidan? Waye bai san karuwancin da kika yi ba a baya ba?? Waye bai san har
madigo kin yi ba, ke da har London ana booking dinki ki ayi iskanci dake? Banda ni
din ina za ki san Janar ki auresa???" Hajiya Amina tayi wani shewa tace "Riiii, ai
abokin barawo barawo ne, madigo kuma tare muka fara da ke, kuma karuwancin ma duk
tare mu ke yi, gwara ni ba baƙin cikin karuwancin da nake bane ya kashe uwata har
lahira, lafiya lau muka rabu da ita, ke kuwa waye bai san har da bakin cikin
karuwancinki da kike yi tun da aurenki ne ya kashe taki uwar ba? Sannan uwa uba
alhakin mijinki Iliya da kika raba da 'ya yansa yau shekara ashirin kenan, kika
gudo daga kauyen da dangin ubanki suka maki aure da shi sbda shashancin da kike na
karuwanci, kika dawo garin Adamawa garin uwarki kika ci gaba da karuwancinki babu
kama hannun yaro, waye bai san Sajida a titi kika yi cikinta kika haifeta ba??"
Aunty Hassana tayi wani kukan kura tayi watsi da mai aikinta da Suhaila dake
rirriketa, tayi kam Hajiya Amina ta cakumota iya karfinta, nan suka fara sabon
dambe ba ji ba gani, Janar ya nuna ma Suhaila da Mai aikin kofa alamar su fita, sum
sum suka nufi kofar suka fice daga parlon, Mami da hankalinta yyi mugun tashi zata
karasa ciki da nufin rabasu, Janar ya dakatar da ita fuskarsa a murtuke, dambe iya
dambe suka sha har sai da suka kusa yi ma junansu zigidir a parlon, ga jini a bakin
ko waccensu, zuwa yanzu babu Attachment ko daya a kan Aunty Hassana duk Hajiya
Amina ta tugesu, Sai da suka gaji lilis sannan aka ci gaba da zage zage ta uwa ta
uba ana tsine ma juna, Aunty Hassana ta juya tana kallon Janar jini na zuba ta
hancinta tana huci tace "Ita ce ta dauke maka miliyan 800, ka tuhumeta, ba wani ya
dau kudin nan ba ita ce wllh, wallahi ita ce, sannan sai da tabi ta kashe duk cctvn
gidan kafin ta aikata mugun nufinta" Hajiya Amina tayi wani shewa tana tafe hannu
tace "Muka dauke dai tare Hassanaaa, banda kin masu labe shi da ɗan nasa a ina zan
san an shigo da kudi gidan?? Ai kece babban barauniya Hassana, kudi kuma suna
kugunki...." Hajiya Amina na kallon Janar tana huci tana nuna masa Aunty Hassana
tace "Ita ta saka na dauko mata kudin na bata wallahi, idan karya nake Allah ya dau
raina nan take, kuma ko miliyan 5 bata bani ba cikin kudin nan wallahi tallahi,
zuwa yanzu da zaka ji gidaje nawa Hassana ta siya da motoci daga ita har ɗan ta ai
sai Allah, sannan duk rashin ci gaban da kake gani a kasuwanci da kake daura Khalil
ita ke bin boka da Malamai kudin su tarwatse kar yayi nasara duk don a daura nata
ɗ'an, kuma hakan ne ya faru kusan shekara biyu a gidan nan in ba Aliyu ba baka
daura kowa kan harkokinka ɗan naka ma taje tayi asiri ta sa ka koresa gaba daya,
tunda ai sanda aka nemi kudin aka rasa baka koresa ba, ganin haka yasa ta banka
uban asiri har sai da ka koresa, Hassana bata sonka bata son ɗan ka tana tare da
kai ne kawai saboda abun duniya kuma kam ta tara don a yanzu Hassana ta mallaki
gidajen kanta ya fi takwas duk a kudin da ta saka na dauko mata, Kullum sunanka a
wajen Malamai yake don ta mulkeka son ranta duk abinda zata yi ka kasa yi mata
magana, ai ba a banza ta kori sojojin dake gadin bangarenka da kofar babban parlor
nan ba, a lokacin ta laka masu sharri wai suna kalle yan matan gidan idan sun zo
wucewa duk don ta samu ta ci ma mugun kudurinta, sannan babu me turning off din
Cctv din gidan nan sai ita, duk sanda take shirin yin mugun nufinta abinda take yi
kenan, da kasan da irin zuciyar da Hassana ke tare da kai ko, to ba uwa daya ba, ko
uwa daya uba daya ne wallahi sai ka nisanta kanka da zuri'arka daga Hassana, Matar
da ta hada maka tuggu gun mahaifiyarku an kamata dumu dumu tana zina sai tace ai
kai ka hadata da mutumin wai abokinka ne, alhalin shi abokin naka da ka hadata da
shi ko ta samu ya aureta tunda zawarcin ya ki ci yaki cinyewa sun rabu tun tuni,
amma tayi maka wannan sharrin, ko ka manta ne Janar????" Aunty Hassana ta shige
dakinta da gudu tana dube duben abinda zata dauko ta rotsa ma Hajiya Amina a kai,
Karasawa cikin parlon Janar yayi ya saka ma kofar dakin key ta waje, Hajiya Amina
dai sai huci take, yana kallon Mami da duk jikinta yayi sanyi qlau ta kasa
kwakkwaran motsi a inda take yace "Fita mu je" Mami ta juya ta fita daga parlon,
shi ma ya fito ya saka ma kofar parlon makulli ta waje. Bangarensa ya tafi ya kira
barracks a turo masa sojoji a mota, sannan a hada da mata ciki. Babu bata lokaci
sai ga sojoji sun iso gidan, Janar ya sa sojoji matan suka shiga suka fito da Aunty
Hassana da Hajiya Amina, duk aka kwama masu handcuff, Aunty Hassana na kallon Janar
tace "Yanzu yaya ni zaka sa a saka ma handcuff? Ni? Duk inda mahaifiyarmu take zata
yi alfahari da abun nan da ka min Yaya?" Ko rufe baki bata yi ba ya sauke mata
tagwayen mari wanda sai da taga stars, ya kuma umarci Sojojin da su zane su idan za
su kawo masu taurin kai, Ita dai Hajiya Amina ba abinda tace amma ranta fari kal ta
tona ma Hassana asiri, don shekara kusan 17 kenan Hassana ke amfani da ita a gidan,
don dai ita ma tana da wayo da sai dai ta tashi a tutar babu, Aunty Hassana ta juya
da sauri tana kallon Janar kafin a fita da ita daga parlon tace "Kuma wallahi
wallahi Hanan ba er ka bace, bata da gadonka, boka ne yayi mata cikinta don juya ce
ita bata haihuwaa...." Sojan ta kwada mata mari ta turata suka fita daga
parlon..... Kamar yanda Janar bai yi bacci ba daren ranan nan haka Mami warce ta ma
fi sa girgiza da wannan abu da ya faru, da ya tuna abinda Hassana ta fada na karshe
sai hankalinsa ya tashi, wai Hanan ba er sa bace, then there is need for a DNA
test.... Mami na idar da sallah da asuba Aunty Maryam ta fara kira don bata mance
furucinta a jiya da yamma kafin ta tafi airport ba, sai gashi hakan har ya faru,
amma bata sameta a waya ba, can ta mike a hankali ta fita daga bangarenta, dakin
Aliyu ta fara zuwa don duba kafarsa, amma taga dakin wayam kuma bata ma ga alamar
ya kwana a dakin ba, juyawa tayi ta fita ta karasa bangaren Janar, ta samesa zaune
saman kujera still pondering, bata taba ganinsa a yanayin nan da yake ciki ba sai
many years ago, kana ganinsa kasan abun ya tsaya masa a rai, ta gaishesa cikin
sanyin murya, ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Ta kwantar da murya tace "Plss kar
ka sama kanka damuwa Yallabai, this isn't proper for ur health, sannan ina rokon ka
ka dubi albarkacin zumunci ka kyale Hassana, sai kaga Allah ya maka sakayya ta inda
baka zato...." Janar ya kalleta da sauri kuma a fusace yace "Amma ina ga baki da
hankali ko Fatima??" Mami dai tayi shiru, yace "Then if u have nothing good to say
ki bar min parlona kada ki kara bata min rai don Allah" Mami ta sauke ajiyar zuciya
bata dai sake cewa komai ba, Khalil ne ya shigo parlon da sallama, shi fa duk
abinda ya faru jiya a gidan bai sani ba don yana barin bangaren Aunty Hassana dama
gidansu Nadeeyah ya tafi kuma bai dawo ba sai kusan karfe goma saura, Ya zauna
saman kujera ya gaida Janar, Janar ya amsa without looking at him, he felt guilty
duk abubuwan da ya ma ɗan nasa a baya, Khalil ya gaida Mami ita ma ta amsa, bayan
few seconds Janar yace "When are you leaving?" khalil ya daga kai ya kallesa yace
"Later in the day in sha Allah" Janar yace "Da matar taka zaka tafi can din?"
Khalil ya ɗan yi shiru, he felt unhappy da bazai iya tafiya da ita ba, ya so ace da
ita zai yi tafiyar but it's not going to be possible in ba dai daga tafiyar zai yi
ba, a hankali yace "Ai bata da passport" Janar yace "Ohk, sai ayi kokari tayi, it's
important...." Khalil yace "Is the trip urgent sir?" Janar yace "It is, tun 5 days
ago ya kamata" Khalil yace "Ohk" Daga haka ya mike ya basu waje ya fita daga
parlon. Karfe takwas Janar ya shirya da escort dinsa suka tafi barikin da aka kai
Aunty Hassana da Hajiya Amina, ai ko ya tarar sojojin sun ci ubansu dai dai
gwargwado, tun karfe hudun asuba suke tsaye har zuwa yanzu da Janar ya zo, ga
tsallen kwadon da suka yi daren jiya na kusan awa biyu, banda azaba babu abinda
cinyoyinsu ke masu, ga sauro da zafi a inda aka ajiyesu, duk sun yi duhu kamar basu
taɓa shan Ac ba, Janar na kallon Hajiya Amina bayan ya shiga har inda suke ya ajiye
mata farin takarda a gabanta, Hajiya Amina taki daukan takardan, yace "Na sake ki,
saki daya, biyu, har uku, Hanan kuma zan kai ta ayi DNA test, if i should find out
that she isn't my daughter, you are to go with her" Yana gama fadin haka ya juya ya
fita ya shigo tare da sojoji murdaddu har biyar yana kallonsu ya nuna masu Aunty
Hassana yace "Ku bi duk hanyar da za ku bi sai ta furta maku inda takardun gidajen
da take siya da motoci suke" Suka ce
"Yes Sir...." Juyawa yayi ya fice daga babban guardroom din.
Inna ce tsaye tsakar parlon tayi mitsi mitsi da ido tana bin duk masu kallon
akwatunan kayan Nihad da kallo kada ko tag a nema a rasa cikin kayan, akwatuna 12
ne tsadaddu, 6 iri daya sauran shiddan ma irinsu daya, kayan ciki kuwa sai son
barka, Aunty Jamila da kawarta da wata kawar Mumy basu siya mata kayan banza ba,
kaya ne na gani na fada masu tsada, matan yayan Abba ne da yan uwa da abokan arziki
cike a parlon ana ganin kaya kowa sai sa albarka yake, Umma dai na zaune one sitter
sai bin kowa da ido take bata cewa komai, gaba daya tayi bakikirin kamar ba ita ba,
ita fa har yanzu gani take zata farka taga duk wannan abun mafarki take, da ko anyi
mummunan mafarki in haka ne, amma dae shiru shiru bata ga ta farka ba, gashi duk
dare da kyar take rintsawa saboda sai taji kamar an soka mata mashi a zuciyarta, ta
dingi juye juye kenan tana numfashi da kyar, Kamila ma na tsaye bayan kujera duk ta
rame saboda damuwa, sai bin akwatunan take da kallo, wanda ko rabin kayan ciki ita
bata samu ba, Inna na daga hannu tace "Toh a gaskiya idan ba ganin haramun ku ke
son yi ma kayan nan ba kuma ae ya isa haka, ganin kaya kusan minti ashirin yanzu
kamar wa enda aka ajiye ma kwari, ai yawansu bazae sa ma a gama ganinsu ba don ma
ku ji, kai wllh baza ma a sake bude kayan ba koma wa zai zo, iyaka ya ga akwati mu
ce masa kayan miliyan goma da dubu goma ne a ciki ya juya yayi tafiyarsa, idan ana
yawan bude akwatin ma ai sai su samu matsala mu shiga uku su ce sakwan muka
siyo...." Aunty jamila dake kan kujera tace "Gaskiya kam Inna" Inna tace "Toh kun
gani, ae ba ayi ma lefe kallon haramun haka, idan anyi saisa saisa sae a tashi
kuma" Wata er uwar Mumy dake zaune parlon tace "Toh yanzu yaushe za a kai kayan
Hajiya?" Inna tace "Aa wannan sai sanda Ibrahim ya sa mana lokaci, muna isa Habujan
dama sai ayi waya da Halilun ya sanar a gida ga fa mu nan zuwa da kaya niki niki,
kun ga ai kafin mu karasa sun mana girki irin tasu ko? tunda ance Abujan ma tana da
girma" Matar tace "Toh mutane nawa ne za su je kai kayan idan lokacin yayi?" Inna
ta kalleta daga sama har kasa, ta sake kallonta da kyau, can dai tace "Sirara ma za
a tafi da saboda matsi a cikin mota, dama daga ni sai Jamila da wannan da aurenta
ya mutu wato Kamila za mu je, kinga ai duk bamu da jiki, Ita Sumayya an barta ta ji
da jinyar goshinta da hannu kar a fama mata a hanya, amma dama ai ba gayya za ayi
ba" Matar bata sake cewa komai ba, bude kofar parlon aka yi Nihal ta shigo da
trolley dinta, Inna tace "Oyoyo yan makaranta"
Khalil bai ji dadin rashin ganin Nihad ba sanda zai tafi wajen karfe sha daya da
rabi na safe, wai Mami tace su tafi su yi gyaran gashi da Mimi, he don't know how
to ask Mami wani saloon din suka tafi, don yayi ta kiran layin Nihad din a kashe,
Mimi kuma bata picking, sai yayi tunanin ko Mimi bata tafi da wayarta ba, Har ya
isa airport mood dinsa was so dull.... Da yammacin ranan sojoji suka shigo da
Hassana gidan tana dingishi da kyar, kana ganinta kasan ta ci baƙar azaba hannunsu,
dama basu shigo gidan ba sai da suka Sanar ma Janar zuwansu, yana tsaye babban
parlor kuma suka shigo, har bangarenta ta kai su suna biye da ita babu rahama a
fuskarsu, Janar ya bi bayansu, tsabar yanda hannunta ke ciwo ta kasa daga wani
babban akwatinta dake dakin, wani soja ya sauke mata akwatin ta bude lock din ta
hau ciro atamfofi kusan kala talatin wanda