Showing 258001 words to 261000 words out of 268471 words

Chapter 87 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

tafiya kawai take amma a tsorace gani
take kamar xata ji ta kume kanta da bango ko ta ci tuntube da wani abu ta fadi, sai
da suka kusa wajen yace "Now, let's stop here baby" Ita dai bata ce masa komai ba,
taga ya zame hannunsa a hankali daga idonta, ta gwale ido tana neman flowers din,
duk da akwai flowers din masu kyau a wajen amma idonta bai sauka kan komai ba sai
kan cages har hudu dake wajen.... Juyawa tayi da sauri ta kallesa, ya wara mata ido
yace "Hope za a janye Allah ya isan yanzu ko?" She was speechless, can kawai ta
karasa inda cages din suke tana kallon kyawawan colourful birds dake ciki, wa enda
ma suka fi nata tsada da kyau, ai kawai sai ta juya ta koma da gudy ta rungumesa
tightly cike da farin ciki tace "Waoww wllh i love them so much, naji dadi sosai,
are they for me pls?" Murya can kasa yace "Kin janye Allah ya isan yanzu?" Ta daga
kai tana kallonsa da sauri kamar me son gano wani abu, zaro ido tayi ta koma baya
hade da dafe kirji tace "Dama kai ne ka sakar min tsuntsaye na a gidanmu??" Ya
karyar da kai yace "Ai ban san naki bane na zata na makota ne" Kawai sai ta fashe
da dariya har da kyakyatawa ta durkusa wajen, ya dinga kallonta yana murmushi har
cikin ransa yaji dadin dariyar nan nata, tayi dariyarta me isarta, ta mike tsaye ya
jawota jikinsa murya can kasa yace "I love u so much dear" Ta kwantar da kanta
kirjinsa tana murmushi ta lumshe ido a hankali tace "I love you more Hubby" Yace
"Kin yafe min yanzu?" Tace "Baka min komai ba my dear, instead ni ce nayi maka" Tun
daga ganin birds din nan Nihad ta dawo lively suka zaga gaba daya gidan da ita tana
gaya masa how beautiful everywhere looks, sun kusa awa daya a compound din sannan
suka shiga ciki shi ma saboda la'asar da ake kira, yayi alwala ya fita xuwa
masallaci ita ma tayi sallan sannan ta shiga kitchen, tunanin abinda zata girka ta
shiga yi, cause she don't want him to be spending money buying food outside, cous
cous tayi deciding ta hada masu with sauce, ko da ya dawo masallaci ya ganta a
kitchen he was so surprise, shi fa kawai ya siya kayan abinci ne saboda ya kamata
ya siya amma ba wai don yasa ran ta iya girki ba balle ta girka masu, bai gama
kwasan mamaki ba sai da ta gama girkin wajen biyar da rabi ta zubo masu a tare, shi
dai yasan da baya gidan bazai taɓa yarda Nihad ce tayi girkin ba ko duk jikinsa
kunnuwa ne, wallahi yayi mamaki sosai, he never expect such taste from her food,
sai yake jin kamar Maminsa ce ma tayi girkin tsabar dadinsa, ita bata wani ci da
yawa ba amma shi kam ya ci har sai da ya kusa cinyewa, ya jawota kusa da shi yayi
mata whisper a kunnenta, turo baki tayi ta rufe fuskarta a jikinsa don maganar tasa
ya bata kunya, Yayi kasa
da murya yace "Amma fa kin fi abincin by far....." Suna ta zaune parlorn har aka
kira magrib ya tafi masallaci ita kuma ta dau plate din abincin ta kai kitchen,
basu taɓa zama su yi hira da Khalil ba sai ranan, they gisted about so many things
har kusan karfe goma da rabi, daga karshe ya sa suka tafi bandaki suka yi wanka a
dakinsa, ta gama shirin kwanciyarta ta kwanta saman gadon tayi lamo, bayan ya
shirya shi ma ya kwanta kusa da ita, banda faduwa babu abinda gabanta yake, ya
rungumeta ya kashe wutan dakin murya can kasa yace "Maran yayi sauki yanzu ko?"
Tayi shiru bata ce komai ba don tun bayan da ta fara shan maganin bata jin ciwon
kuma, duk iya daurewan da ya so yayi ya kauda kansa daga gareta yayi bacci amma ya
kasa, sai juye juye yake amma bai yi attempting komai ba, can dai ta dago kanta a
hankali tace "Are you okay?" Ya kasa ci gaba da daurewa kamar me rada yace
"Plss.... I..." Sai kuma yayi shiru, rubbing his chest a hankali tace "You what?"
Shkkn ta kara rikita al'amarin, she didn't stop him ta daure duk da condition din
nata, ganin she couldn't hold it anymore daga karshe ta fara masa kuka, amma ya
kasa kyaleta, daga karshe kuma ya dawo yana bata hakuri, bai yi baccin da yake ji
ba sai da ya tabbatar she is okay, ya jira har tayi bacci kafin yayi baccin shi ma
with sweet dreams of her. Tun da ya dawo masallaci sallan asuba basu koma bacci ba,
tana jikinsa yana danna waya a hankali yace "Amma ya kike jin ciwon maran naki
yanzu? Let me see if i should get another medicine for you" Ta girgiza kai tace "Ba
kamar na shekaranjiya bane ciwon" Yace "Na jiya fa?" Tace "It stopped immediately"
Yace "Kuma bai maki cikin dare ba?" Ta gyada masa kai, ya shafa gashinta yace
"Alright love, we will be traveling to Zanzibar hope u will welcome this idea, sai
mu yi like 3 weeks a can...." Nihad ta daga kai ta kallesa, yayi mata murmushi yace
"I promise u will love it there wife" A hankali tace "May be some other time, kaga
Abbana bai yi 40 days ba, sannan kuma ina son inyi settle down a nan so i can rest
and practice my duties as a housewife, i am tired of going from one places to
another, i will love to stay here for sometime..." Cikin sanyin murya yace "Haka
ne, shikenan anytime u feel like wanting to go for holidays u can let me know pls"
A hankali tace "Ohk and one more thing pls" Yana kallonta yace "I am all ears
sweetheart" Bata yarda yaga hawayen da ya taru idonta ba cikin sanyin murya tace "I
know u will be getting married soon, nasan ita budurwar ka ce warce ku ke tare tun
ba yanzu ba, ni kuma Abbana ne yayi mana aure da kai It's not as if i am ur choice
or u had the intention of marrying me, so pls i am begging for Allah's sake, do not
use my past mistakes against me, that might affect me mentally, i have already gone
through a lot in life do not break my heart pls I can't endure it, sannan don Allah
kar kace zaka hada mu gida daya ina rokon ka don Allah, i am saying this because i
know u can afford it...." Bai ce mata komai ba yana jin yanda hawayenta ke sauka a
jikinsa, ya rungumeta ya lumshe ido yana patting bayanta a hankali... Da yammacin
ranan Khalil ya san Nadeeyah zata zo gidan yi ma Nihad gaisuwa but ya rasa ta yanda
zai gaya mata cause shi yanzu da ranta ya baci gwara nasa ya ɓaci sau dubu, har dai
Noor da Nadeeyah suka iso gidan bai sanar mata ba, sai bayan da ya gaisa da su a
parlor sannan ya haura sama zuwa dakinta, kayanta ya sameta take gyarawa a press,
ya zauna gefen gado yace "Su Noor sun zo" Nihad na kallonsa tace "With Mimi?" Ya
girgiza kai kawai, sai kuma dai a hankali yace "With Nadeeyah" Sosai taji gabanta
ya fadi tayi shiru tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Gaisuwa ta zo maki ba
wani abu ba, don Allah idan kin fito kar ki nuna mata komai Baby, Nadeeyah is a
very nice gal, bata da matsala and kinga sai Allah ya kaddara cousin dinki ce ma,
nasan kinsan haka pls behave maturedly Wife" Nihad dai bata ce masa komai ba, ya
mike yace "Kar ki bata lokaci ki fito pls" Daga haka ya juya ya fita, Hijab kawai
Nihad ta dauka ta saka don skimpy dress ne a jikinta, har ta sauko kasa gabanta
faduwa yake, bata dai yarda sun hada ido ba ta karaso cikin parlon ta xauna, Noor
tace "Good evening sis" Nihad ta kalleta tayi murmushin karfin hali tace "Sannunku
da zuwa" Nadeeyah tace "Ya karin hakuri?" Ba tare da Nihad ta kalleta ba tace
"Alhamdulillah mun gode Allah" Nadeeyah tace "Allah ya ji kansa, Allah ya gafarta
masa" Nihad tace "Ameen" Mikewa tayi at first Khalil ya zata sama zata wuce, ya bi
ta da kallon mamaki, sai kuma ya ga hanyar kitchen ta nufa, ta dauko masu ruwa da
lemo ta kawo ta ajiye masu sannan ta tafi ta debo abincin da ta girka dazu shi ma
ta ajiye masu, ya ji dadin hakan da tayi, Drinks din kawai suka sha su ma kuma basu
wani dade a gidan ba suka tafi don driver na jiransu a waje, Khalil ya bi ta har
kitchen bayan taje ajiye tray din drinks din a hankali yace "Thank you Wife" Ita
dai bata juyo ba balle tace masa komai amma Allah kadai yasan abinda take ji a
ranta, and she is trying her best not to cry.

A satin Nihad hudu a gidan Khalil ya fahimci abubuwa da yawa game da ita wanda a da
idan aka gaya masa bazai taɓa yarda ba, babban abinda ya burgesa ya kara narkar
masa zuciya game da ita shine tsaftarta, she is neat in all aspects ba kuma na
ganin ido ba, she is just neat in nature, sannan ko kaɗan bata da son jiki don
kullum take gyaran babban gidan duk da su kadai ne a ciki, bayan ta gyara dakinta
ta wanke bandaki sannan ta shiga nasa ma tayi hakan, ga kuma parlon kasa da
kitchen, a ko da yaushe cikin kamshi me kwantar da hankali da zuciya zaka samu
gidan, ya zata kawai na kwana biyu zata yi ta gaji ta watsar but sai yaga ba haka
bane ways dinta ne tsaftace waje, bata son kazanta da gaske, another sweet thing is
that she can cook varieties, tun daga abincin gargajiya, na zamani, snacks, infact
all, ba kuma wajen kowa ta koya ba sai wajen Aunty Jamila, iya girkinta na kashesa
da mamaki, he never knew she had all this qualities a baya, hakan ya kara masa
sonta sosai ba kadan ba, ganin kansa yake the luckiest on earth da Allah ya mallaka
masa ita a matsayin matarsa, he just love her dearly, wannan yasa a ko da yaushe
duk sallan da zai yi yake saka Abbanta a addu'a don he gave him a gift that he
could never have found else where, yana alfahari da ita a matsayin matarsa, duk
bayan 3 days yake zuwa gida ya gaida Mami, idan Janar na nan shi ma su gaisa, kuma
baya wuce awa daya a gidan kamar ana mintsilinsa, ko da wasa bai taɓa attempting
din kai Nihad gidan ba don yana ganin Mami zata iya rike masa ita, shi ko a yanda
yake ji yanzu yasan bazai iya rayuwa without Nihad ba, har tunani yake ta inda zai
fara adjusting idan yayi resuming aiki. A yau Inna da Aunty Jamila da daya matar
Alhaji Abubakar tare da Kamila suka iso garin Abuja da kayan lefen Nihad, Khalil
bai sanar mata zuwansu ba kuma shine yayi masu jagora har zuwa gidan Janar, Mota
uku suka taho da, daya na Farooq, sai Jeep din Alhaji Abubakar, da kuma na haya da
suka yi chattering daga motor park, duk ukun kuma kayan lefen Nihad na ciki don
akwatuna sha biyu ne, sai uban turaren wuta da Humra da Mumy tayi mata, Aunty
Jamila kuma ta taho mata da products din KMZ, Inna sai salati take a zuciyarta
ganin lafiyayyen anguwan da suka shigo duk sojoji ta ko ina, har dai suka isa gidan
Janar, Inna ta kalli Aunty Jamila tana wuri wuri da ido tace "Nan din ma duk a
cikin Najeriya yake Jamila?" Aunty Jamila tayi murmushi tace "Haba tun yaushe muka
baro Najeriya Inna" Inna tace "Ko da naji, dama tun da muka sauka kan wani rubabben
titi kafin Halilu ya isko mu nasan mun bar Najeriya na dai yi shiru ne kawai" Sosai
Mami da Hajiya Safeenah, da wata kawar Mami suka yi welcoming dinsu dama an hada
masu abinci iri iri da drinks, Sojojin suka dinga shigowa da akwatunan zuwa babban
parlon gidan, bayan an gama gaisawa an cika masu gabansu da kayan ciye ciye su Mami
suka bar parlon, Inna ta kalli Aunty Jamila tace "Sai da nace ku bari ko kala
shidda ne in saka a akwatina aka ki aka ce sai dai kala biyu, to yanxu ga irinta
nan, kun dai ga gidan nan ba irin gidan da mutum zai sa kaya daya ya wuni da shi
bane, minti nawa ne kaya ya fara tsami a jikin mutum? Ni dai wallahi Habubakar bai
kyauta min ba, kafin dare ma sai in sanye kala biyun da na taho da shi ai" Hajiya
Hauwa dai sai murmushi take, Aunty Jamila taki ce ma Inna komai, babu abinda Inna
bata taɓa a abincin da aka ajiye masu ba, wani da ta ji taste din ba irin nata bane
sai tayi maza ta mayar cikin warmer din tana gwaggwale ido, Mami ce ta shigo parlon
bayan kusan awa daya, Inna ta mike tace "Hajiya a ina zan yi wanka in canza kayan
haka kuma" Aunty Jamila ta kalli Hajiya Hauwa da ta saki baki tana kallon Inna da
mamaki, Mami na Murmushi tace "Mu je sama Baaba" Inna tace "Naga ma an tafi da
akwatin nawa can sama" Mami tace "Ehh yana can dakina" Inna aka bi bayan Mami ana
daga shoulder sai kuma ta juya da sauri tana kallo Aunty Jamila tace "Ke jamila kin
saka min sarkata da dankunne a cikin akwatin kuwa?" Aunty Jamila da tayi tagumi
tace "An sa" Da sauri ta bi bayan Mami, Kamila ta tabe baki tace "Dama ai sai da
Baffa yace kar a taho da ita, yanzu ai ga irinta nan" Khalil na ajiye su Aunty
Jamila dama gida ya koma don tun safe ya baro gidan, hankalinsa duk ya koma can,
yana shiga parlon kamshin turaren da ya doki hancinsa sai da ya sa shi zaunawa a
parlon for some minutes yana bin ko ina da kallo, can ya mike jin alamar tana
kitchen, ya shiga kitchen din miyar vegetable ya sameta ta gama hadawa, tuwon ma ta
gama, rungumeta yayi ta baya yace "Baby wannan wani irin turaren wuta ne kika sa
haka a gidan nan? Yafi ko wanne dadin kamshi" Tayi murmushi tace "Tohm tunda shi ma
turaren wutan sai kayi santinsa to wata neighbor dinmu ce ta shigo ta kawo min
dazu, tace min ordering dinsa tayi...." Ya wara ido yace "I bet from dubai, or...
Saudi??" Dariya Nihad tayi tace "Aa fa a nan ne, A *Albaita-Al-sahal* tace min tayi
ordering turaren" Yace "Then we will order ours too" Ta kashe gas din tace "Sure"
Juyo da ita yayi yana kallonta yace "Guess what baby?" Tayi shiru tana kallonsa
tace "What?" Yace "Da farko dai Abdallah yana hannun hukuma yanzu haka, after
beaten blue black by soldiers.... That's my papa's handwork, and since he is
involve in sha Allah nasan dole za a hukuntasa yanda ya kamata" Nihad da farin ciki
ya cikata tace "Alhamdulillah, am so happy to hear this, maa sha Allah" For just a
week now aka fara neman Abdallah bayan Khalil ya buda ma Janar abinda yayi, at
first ya ki gaya ma Janar cause bai san ta yanda zai yi viewing issue din ba, kada
ace duk gidan kuma basu da kamun kai ne, but sanin Janar na saka baki duk inda
Abdallah yake dole sai an lalubosa a kasar, shine kawai dai yayi shahada ya sanar
masa duk abinda ya faru though yasan Abbansa baya tunani negatively, Janar yaji
tausayin Nihal sosai kuma yayi alkawarin za a hukunta Abdallah yanda ya kamata, ko
sati daya bai yi da gaya ma Janar ba sai ga Abdallah a garin gombe an kamosa har
zuwa garin Abuja bayan ya ci duka a hannun sojoji, Khalil yace "Ko da yake bazan
gaya maki na biyun ba, zaki gani ne kawai da idonki" Bai jira cewarta ba ya ja ta
suka bar kitchen din ya tafi sama da ita yace "I am pressed Baby" Nan da nan ta
hade rai ta wani turo baki.....




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788




*Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun
turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin
kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki
ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin
sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta
dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp
09084473900*

79

Karfe hudu saura Khalil ya gama shiryawa ya fito dakinsa ya shiga na Nihad, kwance
ya sameta kan gado yanda ya bar ta amma idonta a rufe, ya zauna gefenta yana
kallonta, a hankali ya kamo hannunta ta bude idonta tana kallonsa, yace "How are
you feeling now?" Tace "Da sauki" Yace "Ya daina gaba daya?" Ta gyada masa kai,
yace "Anjima da magrib za mu je asibiti" Ta mike zaune tace "Ya fa daina, kuma ai
ba ko da yaushe yake min ciwon ba" Yace "No sweetheart, we need to go to the
hospital to know the cause of the pain" Shiru tayi bata ce komai ba, ya kai hannu
lower abdomen dinta, for almost 1 minutes bai cire hannunsa a wajen ba as if
feeling something, ita dai kallonsa kawai take, can ya daga kai ya kalleta, a
hankali tace "Ai ya daina ciwon gaba daya yanzu" Bai ce mata komai ba, bayan some
minutes ya mike yace "Anjima da daddare za mu je asibiti" Tace "Fita zaka yi
yanzu?" Yace "Yeah, amma bazan dade ba zan dawo" Ta mike zaune zata sauka daga kan
gadon tace "Toh bari in kawo maka abinci" Yace "Sai na dawo zan ci" Tace "Toh amma
baka ci komai ba fa" Ya ɗan kalleta sai kuma murya can kasa yace "Bayan na dazu?"
Ta ɗan buda ido tana kallonsa, sai kuma tayi murmushi a hankali tace "Allah ya
tsare Dear" Yayi pecking lips dinta yace "Ameen Baby" Sauka tayi daga saman gadon
ta rakasa har parking space, sai da ya bar gidan sannan ta koma ciki. Nihad na
zaune parlon sama tana waya da Nihal wanda sun fi 40 minutes suna wayan, kuma duk
labarin Ayman take bata, kwana daddaya ne basa waya kuma Nihal bata boye ma er uwar
tata komai akan relationship dinta da Ayman, tun bayan dawowar Nihad Abuja take
amfani da wayarta frequently bata kuma sake kashewa ba saboda Mumy da Nihal sai
yaya Farooq da suke yawan waya shi ma, babu ranan da zai wuce bata kira Mumy sau
biyu ko sau uku ba, ko yau ma sun yi waya da Mumyn amma bata sanar mata su Aunty
Jamila na Abuja ba, Jin shigowar motar Khalil tayi ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login