Showing 78001 words to 81000 words out of 268471 words

Chapter 27 - NIHAAD By Khaleesat Haiydar

samu nutsuwa ba sabda walakanta d'an Adam ba shi
daga cikin halina, ba tarbiyar gidanmu bane, ni ban ta6a ba sai ranan, kuma mun yi
hakan ne kawai don mu faranta ma kawar mu kamar yanda ta bukaci mu yi, daga baya na
gane bamu kyauta ba biye mata da muka yi muka ci maka mutunci.... Nayi magana da
sauran kawayena mu zo mu baka hakuri ko ba tare da sanin Nihad din ba amma sun nuna
baxa su iya xuwa ba shine ni na taso da kaina in zo har nan in baka hakuri, don
girman Allah kayi hakuri ka yafe mana gaba daya, ko a jiya ma da ta fito xuwa
makaranta idan ka lura ai da wuri ta dawo, to mu muka sa ta gaba muna nuna mata
illan kin yi ma miji biyayya ko da kuwa baka son shi, dalilin barin ta makaranta
kenan da wuri ta dawo gida, yanxu haka bata san xan xo nan ba, kawai kaina tsaye na
taho...." Khalil yace "A takaice dai me ya kawo ki nan Malama?" Ta sauke idonta a
hankali tace "In baka hakurin abinda muka yi maka ni da kawayena, kuma mu nemi
gafararka" Yace "Toh rike hakurin ki, su ma ki mayar masu da nasu, don ba ku kai ku
min abinda xai bata min rai har ki xo bani hakuri ba" Ta daga kai ta kallesa tace
"Baka dai hakuran ba kenan?" Da wani expression yace "Shine nace kun min wani abu
ne da ya bata min rai har xa ki zo bani hakuri tukunna?" Ta langwabar da kai tace
"By the way, sunana Asma'u, amma kawayena na kirana da Husnah...." Ko rufe baki
bata yi ba ya kulle gate din almost on her face ya juya ya koma cikin gida. Yana
shiga daki ya dau wayarsa dake ring ganin Nadeeyah ce ke kiransa ya daga ya kai
kunne, daga daya bangaren tace "I saw ur calls" Ya d'an yi shiru, da mamaki yace
"My calls?" Tace "Yea, minutes ago" Yace "Ohh, sorry mistake ne" Tace "Ohk, sai
anjima kenan?" Yace "Sure" Katse wayar tayi, ya hau duba call logs dinsa da sauri,
Nadeeyah kawai ya ga ta kira, ya kalli kofar dakin ko kiftawa baya yi. Da yamma
Khalil ya shirya xai tafi can gida saboda kiransa da Abba yayi, Nihad dai na daki
abun duniya duk ya bi ya isheta, da ta gaji da wannan bangaren gadon ta koma daya
bangaren, ko kuma ta sauka kasa ta zauna, ita bata saba xama waje daya kamar
jaririya ba, all through the week ko bata da lectures sai ta shiga school, daga
school kuma su tafi yawonsu da su Husnah, tun goma na safe idan ta fita gida dama
sai magariba take dawowa, sai gashi yanxu wai ita ce daga daki sai bandaki, sannan
babu waya ba komai, ita da 24/7 wayarta na hannunta, tunanin hakan yasa ta rushe da
kuka tana jin kamar ta samu wanda xai harbe mata khalil ta huta, gaba daya ta rasa
me ke mata dadi a duniyar, why is this happening to her, kuka ta dinga rerawa tana
bubbuga kafa. Khalil na isa gida a waje yayi parking Aminu na hangosa ya taso da
sauri yana daddaga hannu sama yana washe hakora yace "Sai kayi oga...." Khalil ya
kashe motar ya sauko, Aminu ya kyalkyale da dariya yace "Shekaranjiya Saminu ya
jiyo mana wannan lamari me ban mamaki daga bakin Hafsah me aiki, yanzu haka aka yi
dama?" Khalil yace "Wani lamari kenan?" Aminu ya washe baki yace "Ahh haba ni ne fa
Aminu, meye kuma xaka boye min banda abun ka" murmushi khalil yayi yace "Ba abinda
xa a boye maka" Aminu ya ja sa har xuwa kan bencinsa yace "Shi kansa bencin nan
yasan ba ka a gidan nan mutumina" Khalil ya shafa kai yace "Toh ya ake ciki?" Aminu
yace "Ana nan dai yanda ka tafi ka bari in gaya maka, har yanzu kasan Alhaji bai
fara fita aiki ba, yanxu haka yana da baki yan zuwa jaje a parlonsa, Ita kuwa uwar
Nihad din na can kwance ba lafiya har da karin ruwa don har gida likitan ke xuwa
dubata, kanwarta me shegen kama da ita din nan ce ke wajenta yanxu haka, Umma kuma
jiya da sassafe ta fita a mota bata dubi halin da abokiyar xamanta ke ciki ba sai
ga ta ta dawo mota duk ya lotse wai tayi dan karamin hatsari a hanya amma babu
abinda ya sameta, ko kwarzane bata yi ba, xancen da nake maka har yanxu Alhaji bai
sani ba, ko mu tace kar mu yi magana, baka ga inda taje tayi parking motar ba don
kar ya gani" Khalil dai bai ce komai ba, amma Mumy da aka ce bata da lafiya ce ta
tsaya masa a rai, Aminu ya tuntsire da dariya yace "Yanxu don Allah yaya zaman naku
da yarinyar nan, ni fa na dauka xa ace ta kashe kanta da taga Alhaji ya aura maka
ita, kiyayya ce fa ta gaske take maka" Khalil yace "Ni ban kashe kaina ba sai ita
xata kashe kanta?" Dariya sosai Aminu yake yace "Gaskiya kam kai aka cuta, anyi
mugun kwararka mutumina, yanxu fa har yara da jikoki sai sun ga wannan videon nata
da yayi yawo a yanar gizo, tabo ne da baxai ta6a goguwa ba har karshen rayuwarta,
kai don ma dai iyayenka ba yan boko bane basa hawa yanar gizo, ai da wallahi baxa
su amince ka auri yarinyar nan ba, ko kai baka kare ma videon kallo bane? Saminu fa
har jawo mana shi yayi kusa kusa yanda xa mu gani da kyau, ita wannan ba ma wani
amfani ta sake yawo da kaya a jikinta bayan duk duniya sun san surarta" Lkci daya
mood din khalil ya sauya, Aminu ya girgiza kai yace "Tirr, amma a gaskiya hada
zuri'a da wannan yarinyar ma bala'i ne, banda kana jin nauyin ubanta me xai kai ka?
Kai da kake da mutunci haka, Sauran titi ce fa, duk ta yasar da darajan nata ta
rarrabar a titi, nan nan nan ranan ni da kai muka ganta da asuba ta dawo daga sheka
ayarta tana
ta rabe rabe bakin gate, kuma ta sha yin hakan tun ma baka xo gidan nan ba ya fi a
kirga, labarinta ma ai sai a bakin Habibu, nasan bai san da wannan hadin ba da ya
zuga ka yace kar ka yarda komin me ubanta xai ce maka, shi ma dai Alhajin ya so
kansa da yawa, bai kuma yi maka adalci ba, ya rasa warce xai aura mata sai Nihad
bayan ga salihar er uwarta Nihal, lalatacciya ce fa babu wanda bai sani ba, ni
wallahi da kudi ma baxan amince in aureta ba balle kyauta...." Mikewa Khalil yyi ya
nufi cikin gidan, Aminu yace "Auu har mun gama hirar? Ko xaka shiga ka fito?"
Khalil na isa balcony ya kira Abba ya sanar masa yana gidan, Abba yace ya basa few
minutes yana da baki, Khalil ya amsa masa da to sannan ya xauna saman kujeran dake
wajen, har wani sarawa yaji kansa ke yi da maganganun Aminu, yana ta xaune balcony
din sai ga Aunty Jamila ta fito xata kwaso kayan shanya da tayi a baya, mikewa yayi
, ganinsa tace "Aa kai ne a nan..." Gaisheta yayi, ta amsa tace "Ya gida?" Yace
"Alhamdulillah" Tace "Toh ka shiga ciki mana" kawai murmushi yayi bai ce komai ba,
tace "Ka karasa Sudais ya kai ka ka duba Mumy kasan bata ji dadi ba" yace
"Subhanallah, amma da sauki ko?" Tace "Alhmdlh" yace "Toh Allah ya bata lafiya"
Tace "Ameen" tana barin wajen ya shiga parlon kansa a kasa, Sudais na ganinsa ya
taho da gudu ya rungumesa yace "Uncle mun daina ganinka" Ya shafa kansa yace "Gani
na zo ai, ina fadil?" Yace "Yana wajen Mumynmu bata da lafiya" Khalil yace "Toh kai
ni in gaisheta" Har part din Mumy Sudais ya kai sa, yayi sallama bakin kofar
parlon, Wata frnd din Mumy ta amsa, shiga parlon yayi kansa a kasa ya nemi saman
carpet ya xauna ya gaishesu, duk suka amsa, Mumy dake xaune parlon an cire mata
last drip dai kallonsa kawai take, Bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace
"Ya jikin Mumy?" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah Ibrahim, ya gida?" Ya sauke
kansa yace "Lafiya lau, Allah Ubangiji ya kara Lafiya" Tace "Ameen Nagode" Bai kuma
cewa komai ba, Hajiya Zara ta mike ta fita daga parlon, bayan few minutes Mumy tace
"Kayi hakuri Ibrahim, an cuceka an hadaka aure da warce bata cacanceka ba, nasan
baka da yanda xaka yi ne kuma baxa ka iya k'in amsan tayinta da mahaifinta yayi
maka ba...." Da sauri yace "Aa Mumy, Allah ne ya tsara haka, kuma muna fatan Allahn
yasa hakan shine mafi alkhairi" Hawaye na sauka idon Mumy tace "Ni kam bani da
abinda xan ce maka sai dai in baka hakuri akan abinda Alhaji ya maka, sannan ni
baxan ce kayi hakuri da Nihad ba, idan kaga baxa ka iya ba ko xaka cutu ina me goya
maka bayan ka saketa kawai ta dawo gida...." Cike da karfin hali Khalil yace "In
sha Allah baxa ayi haka ba Mumy" Mumy ta share idonta bata kuma cewa komai ba, Wani
duniyar tunani khalil ya fada gaba daya jikinsa yayi sanyi, he couldn't even think
straight, kiran sallahn magrib da ake ne yasa ya dago kai ya kalli Mumy ya ga
kallonsa take, a hankali yace "Xan je masallaci Mumy, Allah ya kara lafiya" Tace
"Ameen Ibrahim nagode" Tashi yayi a hankali ya fita daga parlon, Umma ya tarar a
main parlor ta masa wani kallo sai kuma ta ja tsaki tayi hanyar kitchen, ya bi ta
da ido kawai. Bayan an idar da sallan magrib tare suka shigo gidan da Abba har xuwa
parlonsa, Khalil ya xauna ya gaida Abba da ladabi, Abba ya amsa yace "Ya gidan?"
Yace "Alhamdulillah" Abba yace "Ya kamata xuwa gobe ku shirya ka tafi da ita can
garinku ta gaida iyayenka, bayan kwana biyu sai ku dawo" Khalil ya ɗan yi jim, sai
kuma ya dago ya kalli Abba yace "Toh in sha Allah Alhaji, Allah ya kai mu goben"
Abba yace "Ameen, farooq ya zo min da wani batu jiya amma sai kun dawo dai" Khalil
yace "Toh Alhaji, nagode" Abba ya ciro dubu dari ya mika masa yace "Ka yi full
tank, sannan kayi ma iyayenka tsaraba da sauran" Khalil ya sa hannu biyu ya amsa
yace "Toh Allah ya saka da alkhairi Alhaji" Abba yace "Ameen, Allah ya maka
albarka" Khalil ya amsa da "Ameen" a tare suka fito main parlor da Abba, Umma ta
fito daga kitchen kenan ganinsa da Abba tace "Aa Ibrahim har xa ka tafi, bari to ga
abinci ka kai ma Nihad tunda an gama" Ya kalleta yace "Toh" Komawa kitchen tayi da
sauri, Abba dai ya zauna parlon har sannan kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa,
dake xuciyarsa kawai yake yana ma Nihad wasu abubuwan as form of punishment amma
shi yasan sonta a jininsa yake, but he can't help it, tayi disappointing dinsa
sannan ta xubar masa da mutunci a idon duniya, Umma ta cika warmer da abinci,
sannan ga wani warmer din daban na kaza ta fito parlor, sai da ta bubbude warmer
din tana kallon khalil cike da damuwa tace "Don Allah idan ka je ka lallabata ta ci
abincin nan, duk ta rame ta lalace wallahi, Shekaranjiya da naje ma da ya na samu
ta ci abincin, yanxu kam ban san halin da take ciki ba baiwar Allah, wa yasani ma
ko bata cin komai" Shi dai Abba bai ce komai ba, khalil kuwa banda kallonta babu
abinda yake, Abba ya mike yace "Ka jirani Ibrahim" Khalil yace "Toh Abba" Ba a dau
lkci ba sai ga shi ya dawo da dubu talatin ya mika ma Khalil yace "Ka siya mata
carton din maltina da na madaran gwangwani" Ta gefen ido Umma ke ta kallon Abba,
Khalil ya amsa yace "Toh In sha Allah Abba" Abba yace "Sai da safe, Allah ya tsare"
Juyawa Umma tayi ta shige kitchen ta tsaya jikin cabinet kamar me nazari. Khalil na
isa gida sai da yayi isha a masallacin dake layin sannan ya shiga gida da motar
yayi parking, bayan ya kulle gate din ya dawo ya fiddo abincin daga cikin mota ya
kai parlor ya sake fitowa ya kai maltina da madara parlon ya ajiye sannan ya kulle
gidan, xaunawa yayi saman kujera ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, da
yasan haka abubuwa xa su kasance masa da bai yarda ya fara shigowa garin kano ba,
where will he even start this amendment from?? Babu warce ta tsaya masa a rai sai
Mahaifiyarsa, this seriously isn't going to be easy, Mikewa yayi daga karshe ya
nufi dakinsa yana tafiya a hankali, har ya bude kofar sai kuma ya fasa shiga, ya
dawo ya bude dakinta, zaune ya ganta a kasa idonta yayi bulu bulu alamar tayi kukan
gaske yau, ya tabe baki ya kulle kofar ya koma parlor kawai yayi xamansa, tashi
Nihad tayi ta bi bayansa, ta tsaya bayan kujera tana shesshekar kuka..., ya ɗan
daga kai ya kalleta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Da bashi ne?" Wani bakin
ciki ya rufeta a fusace tace "Ban sani ba, ka zata kai ka isa ka dinga punishing
dina? Waya biyu aka kawo min gidan nan ka salwantar min da su, toh wallahi zaka sha
mamakin abinda xai faru idan baka bani wayata ba" Mikewa yayi ya bar mata parlon ya
shige dakinsa ya kulle, kuka kawai take kamar ranta xai fita, babban tashin
hankalinta shine Aliyu da xai yi ta kiranta ya ji a kashe, yanxu babu ta inda xata
yi ta iya kiransa, da ma baya kulle gate ne ko makota ita sai ta shiga don ta kira
Aliyu, amma ko daxu da xai fita kulleta yayi ta ciki, ko bin ta kan warmers din
abincin dake parlon bata yi ba ta koma daki ta dinga kuka kamar ranta zai fita, har
kusan karfe biyun dare Nihad bata yi bacci ba, abun duniya ya taru yayi mata yawa,
last week fa warhaka tana baccinta peacefully a saman gadonta, tashi tayi a hankali
ta goge idonta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar dakin nata ta fito, taga ya
kashe duk wutan gidan, ko ina yayi duhu, tana lalubawa ta tafi hanyar dakinsa ta
kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude ta shiga dakin, nan ma dai ya
kashe fitilar, sai da ta fara tattaba socket din dakin cikin duhun ko xata ga
karamar wayarsa a jiki taga babu, cikin sanda ta nufi gadon dakin ta durkusa, hannu
ta kai xata laluba kan gadon taji hannunta saman broad haired chest dinsa, zaro ido
tayi a mugun tsorace xata mike ta gudu ya fixgota ta fado saman gadon daga gefensa,
yayi kneeling dai dai inda take har tana jiyo respiration dinsa, yana kallonta
cikin duhun kafin yace komai jikinta na rawa tace "Wayyo na shiga uku, wallahi
torchlight nake nema xan je in sha ruwa a kitchen...."




*Littafin Nihad dari biyar ne, ki fita hakkina kafin ki karanta min littafi
hankalinki kwance*

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence via👇🏻


07087865788

26

Kunna wutan dakin Khalil yayi ya koma gefen gadon ya zauna fuskarsa daure yace
"Ohk, dauki torchlight din ki fita" Har sannan gabanta bai daina faduwa ba, a
hankali ta dawo edge din gadon tana satan kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace
"Dauki ki fita nace" Ta sauke ƙafafuwanta kasa a hankali tana kallon karamar
wayarsa da ta hango gefen pillow, Ya jefa mata wani mugun kallo yace "Ko bayan shi
da wani abun da kike so ne?" Ta ɗan turo baki tace "Ga can torchlight din da xan
ara" Ya kalli inda take nuna masa, sai kuma yace "Ohk" dauko wayar tasa yayi ya
mika mata yana kallonta, a hankali ta kai hannu xata amsa, da karfi ya buge mata
hannu da wayar, da sauri ta janye hannunta ta bude baki tana kallonsa tana yarfe
hannun, ya mike ya dau shirt dinsa ya saka sannan ya nufi kofa ya bude mata da
kyau, fuska daure yace "Zo ki fita" Ta fashe da kuka tace "Shine har sai ka kwala
min waya a hannuna? Sai kace kai baka shigo min daki idan ina bacci" Cikin
kakkausar murya yace "Zo ki fita nace" ganin babu alamar wasa tattare da shi ta
mike ta nufi kofar hawaye cike idonta, tana fita ta juyo ta kallesa tace "Ban yafe
buge min hannu da kayi da shegen wayarka ba, don ma ka samu xa a ari torchlight din
shegen wayar" Yi yayi kamar xai bi ta, ta ruga ta shige dakinta ta kulle kofar da
sauri tana maida numfashi. Washegari da yamma bayan Khalil ya gama shiryawa yanda
xai je ya sanar ma Nihad ta shirya xa su yi tafiya ne babban aiki a wajensa, tun
safe ya fice gidan don kawai ya daina ganinta, ko awa daya bai yi da dawowa ba kuma
bai ji motsinta ba bai kuma duba dakin nata ba, daga karshe kawai yayi dialing
number Nihal tana dagawa ta gaishesa ya amsa yace "Ya makaranta?" Tace
"Alhamdulillah" Yace "Kin dawo ne?" Tace "Aa ya farooq yace min yana hanya" Khalil
yace "Toh Allah ya kawo ku lafiya" Tace "Ameen" Shafa kansa yayi yace "Dama so nake
ki sanar ma er uwarki ta shirya kayanta kala uku xa mu je can gida, kawai haka xa
ki ce mata" A hankali Nihal tace "Baxa ka iya gaya mata ba kai kenan?" A takaice
yace "Ehh" Tace "Toh Shkkn, ka bata wayar" yace "Zan kai mata yanzu" Nihal tace
"Ohk" mikewa yayi ya tafi dakin Nihad ya bude kofar dakin, tana tsaye jikin window
abun duniya ya tarar mata, har ta gaji da kuka, tun da garin Allah ya waye ruwa
kawai take ta sha don ta gaji da cin indomie gashi babu kayan miya a gidan, yunwa
take ji sosai, jin ya bude mata kofa ta juya a fusace tace "Malam ka daina shigo
min daki kanka tsaye kamar wata matarka, idan ma wani abun ne baxa ka kwankwasa ka
jira in fito ba?? Balle ma ni bana son kana min magana a gidan nan har abada"
Kallonta kawai yake, ta murguda baki ta ci gaba da kallon tsuntsayen da take kallo
ta window, khalil ya sa handsfree a wayar hannunsa yana daga inda yake tsaye yace
"Gashi ki gaya mata" Nihal tace "Hello Nihad" Nihad ta wani tamke fuska tace
"Menene??" Nihal tace "Abba yace ki shirya kayanki xa ku je can gidan" Nihad ta
buda ido sosai tace "Don Allah da gaske?" Nihal tace "Ehh" Wani farin ciki ne ya
rufeta, cike da murna tace "Ai kayana a hade suke ban ciro su a akwatin ba" Khalil
bai bari Nihal tace komai ba ya katse wayar ya juya ya fita, kan kace me Nihad ta
gama rurrufe akwatunanta ta ja su ta kai parlor gaba daya, ji take kamar mafarki
wai xata koma gida, she sooo happy, da ido Khalil

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login