Showing 108001 words to 111000 words out of 268471 words
bata sa ta wai saboda hayaki
da warin gas, duk sanda taje gidan Aunty Jamila ne take girki don dama Aunty Jamila
chef ce, tana gwada mata abubuwa da yawa na girke girke, saving grace din Nihad
kenan da har Allah ya taimaketa ta iya girkin, tana ta zaune parlon sai kuma ta
mike ta tafi dakinsa ta bude tana kallonsa, bata ga alamar yayi sallah ba, ta
karasa ciki ta tsaya side din gadon ta bubbuga pillown da yake a kai tace "Baka yi
sallah ba" Ya bude ido da kyar ya kalleta yace "Ina ruwanki?" Kyabe baki tayi tace
"Toh don ma ka samu ina tashin ka?" Ta wani juya ido ta juya xata fita ya bi ta da
kallo, sai kuma yace "Ina son ruwan zafi" Ta jefa masa wani kallo tace "Toh meye
zaka gaya min? Ko house help dinka ce ni?" Daga haka ta fice daga dakin, lumshe ido
yayi yana son tashi amma ba shi da enough strength din yin hakan, bayan kusan minti
ashirin har wani baccin ya kara daukesa ta shigo dakin rike da kettle din ruwan
zafi, ya bude ido da sauri jin sound din bude kofar, bandaki ta shiga ta dauraye
bucket ta juye masa ruwan zafin a ciki tana fitowa kuma ta fita daga dakin ba tare
da ta kallesa ba, ya yunkura ya mike zaune sannan ya sauka daga saman gadon ya
shiga bandakin. Ko da ya fito yaga abinci ajiye a dakin, ya gama shiryawa yayi
sallahn zuhur, yana ta zaune saman darduma yana kallon warmers din abincin, can ya
jawo karamin warmer din ya bude aroma din miyan ya doki hancinsa, ya bude dayan ya
ga shinkafa ce, kawai zuciyarsa ya basa ai aiko mata da abincin aka yi ya kulle ya
matsar daga kusa da shi. Har aka yi la'asar Nihad bata sake shigowa dakin ba, zuwa
lkcn he is feeling much better, fitowa daga daki yayi ya ganta kwance kan 2 seater
tana bacci, ya karasa cikin parlon, a hankali ya kai hannu ya buga kujeran, ta bude
ido da sauri zata kwala ihu ta gansa, don duk tunaninta aljanin daren ne ita ma ya
zo mata, Ya dauke idonsa daga kallonta yace "Sallah" Tace "Ina ruwanka?" Bai ce
komai ba ya juya ya koma daki, karamar wayarsa ya dauka ya zauna gefen gado yaga
miss calls din Nadeeyah har hudu sai kuma miss calls din Abba biyu, sannan message
na debit din dubu ashirin da biyar bayan debit din drugs da ta siyo masa da safe,
yana ta kallon debit din sai kuma ya mike ya fita daga dakin tana zaune kan kujera
yana kallonta yace "Me kika min da dubu ashirin da biyar?" Ta kyabe baki tace "Toh
kaza naje na siya na dubu goma nayi girki don ni baxan dinga cin abinci lami ba,
bayan nasan Abbana na baka har da kuɗin nama, dubu biyar kuma na siyo spices, dubu
goma kuma na zuba mai a mota, idan ma kudin account din ne suka kare ai sai ka
kirasa kace sun kare" Kallonta ya dinga yi, ta ɗan kallesa ta gefen ido, sai kuma
ta turo baki ta mike ta wuce dakinta ya bi ta da kallo, komawa cikin dakin yayi ya
kara bude abincin da tace tayi yana kallo, har cikin ransa bai yarda ita tayi
girkin ba duk da bai ci ba, can dai ya dau spoon yayi tasting stew din, nan ya kara
tabbatar ma kansa ba ita tayi ba, duk da yunwan da yake ji bai ci abincin ba. Da
magrib bayan ya fito daga masallaci ya ga almajirai biyu ya tsayar da su sannan ya
shiga cikin gidan ya fito da abincin ya juye masu ya koma kitchen ya wanke warmers
din ya fito, daki ya shiga ya dauko makullin mota da atm card dinsa ya bar gidan,
tana jin ya fita ta fito balcony da sauri ko gama goge jikinta bata yi ba don wanka
take taji ya kunna mota ta kwara ruwa kawai ta daura tawul ta fito da gudu, Hijab
dinta da ta fizgo ta saka a kan tawul din, duk a tsorace take da gidan tun da taga
gari ya fara duhu dama hankalinta ya tashi, can saman dakalin da yake zama ta tafi
ta zauna hawaye cike idonta, ta fi awa daya wajen zaune ga uban sauro dake ta
cizonta har da guntun gyangyadinta, sai bayan isha ya shigo gidan, bayan yayi
parking ya tafi ya kulle gate ya dawo yana kallonta amma bai ce mata komai ba,
juyawa yayi ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri cikin kuka tace "Ni wallahi
kar ka sake fita ka barni ni kadai cikin gidan nan da daddare, don baka ga abinda
ya faru da Husnah bane har ta bar gidan shi yasa zaka wani tafi ka bar ni kadai
kuma ka tafi da makulli" Ya juya ya kalleta yace "Wacece Husnah?" Ta hade rai tace
"Kawata da ta zo gidan nan ta kwana mana" Yace "Ohhh ta tafi ne?" Nihad tace
"Aljanun dare ne fa suka zaneta fuskarta duk ya kumbura shine ta gudu" Yace "Au
haba?" Ta wani daure fuska tana kallonsa, yace "Toh Allah ya sa kar su dawo kanki
tunda ita ta gudu" Yana fadin haka yayi hanyar dakinsa ta bi sa da gudu ta fashe da
kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me yasa zaka ce min haka? Me nayi
masu ni za su dawo kaina?" Yana shiga dakinsa ita ma ta shige tana kallonsa tana
maida numfashi hawaye cike idonta, duk a mugun tsorace take, yace "Malama kwanciya
xan yi ki tafi dakinki sai da safe" Ta wani gwalo ido tana kallonsa, sai kuma kawai
ta nufi can karshen gadon dakin ta zauna, ya tsaya yana kallonta sai kuma yace
"Ohk, sai in bar maki dakin in koma wancan" Bata san sanda ta fashe da kuka ba tace
"Don girman Allah kar ka barni ni kadai wallahi tsoro nake ji kuma baxan iya kwana
a dakin ni kadai ba" Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana rera kuka, bai kuma ce mata
komai ba ya kulle kofar ya karasa cikin dakin. A hankali ta mike ta shiga bandaki
ta dauro alwala ta fito ta tada sallan isha, yana kwance daya side din gadon waya
kare kunnensa, duk da can kasa kasa yake magana amma lkci daya ta gane da warce
yake wayar, ta ja tsaki ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye ta nufi saman
gadon ta fizge duvet da ke kai ta dau pillow daya ta shimfida duvet din a kasa
sannan ta ajiye pillon ta kwanta, tana ta juye juye kan duvet din can ta kara jan
wani tsaki ta tashi ta tafi ta kashe wutan dakin ta dawo ta kwanta, shi dai bai
daina wayar da yake ba kuma duk maitarta baxata ce ta ji abinda yake cewa a wayar
ba, for almost one hour bai gama wayar ba, ya mike sabida iska da aka fara alamar
hadari, kunna wutan dakin yayi Nihad da tayi lamo a kasa tana jin iskan ita ma ta
mike zaune da sauri ta bi sa da kallo sai kuma ta tashi ta bisa parlon, ya juya ya
kalleta, sai kuma yace "Zan kwanta yanzu kinsan nace maki bani da lafiya, za mu yi
magana gobe" Daga haka ya katse wayar yace "Lafiya kike bi na?" Kin cewa komai tayi
tana kallonsa, haka kawai tayi masa rashin kunya ya ki yarda ta kwana a dakinsa,
shi sa ma taki ce masa komai juyawa yayi ya tafi ya kulle duk windows din gidan,
duk inda ya nufa sai ta bi sa har dakinta sai da ya shiga ya kulle windows sannan
ya fito tana biye da shi suka koma dakin nasa, kulle nasa windows din yayi ya kashe
wutan dakin ya kwanta daya side din, ba a wani dau lokaci ba aka fara yayyafi,
Nihad dai duk a tsorace take a kasa da take kwance, can ta mike zaune a hankali
tana kallon saman gadon, sai kuma ta turo baki ta mike ta dauke pillown da duvet ta
koma saman gadon ta kwanta, yana jin ta bai ce komai ba sai ma juya mata baya da
yayi ya rufe ido, Nihad na jin sauwkan ruwa ta mirgina a hankali ta koma bayansa
tayi lamo, ta dade a hka ta kasa bacci, kamar yanda shi ma ya kasa baccin, da taji
anyi tsawa sae ta kara matsawa gun sa, a haka har bacci ya dauketa daga karshe....
Can cikin bacci ta ji ana ta6a ta, ta bude ido a tsorace, xata bara ihu ya rufe
bakinta da Palm dinsa.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence of payment via 07087865788
Assalamu alaikum manyan mata!!
For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of
jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰
Join my WhatsApp group for beautiful samples. https://wa.me/c/2349090591769
34
Duk a zaton Nihad aljanin daren ne ke tattaba ta cikin Hijab, tunda dama da shi ta
kwanta a rai, a rikice take tattaba jikinsa tana kokarin cire hannunsa daga bakinta
ta kara kwala wani ihu kamar xata shide, bayan ta gano shine ta fada jikinsa da
sauri ta rufe fuskarta a kirjinsa tana kuka sosai tace "Don Allah kace Abba ya
canza mana gidan nan ni baxan iya zama ba wallahi, wayyo Allah na shiga uku" Ya
rike ta very tight shi ma ya daura fuskarsa saman kanta, tana jin yanda yake sauke
numfashi still holding her tightly, kamshin turarensa shi ma ya taimaka wajen kara
kwantar mata da hankali, sun fi minti goma a haka, jin ya ki saketa ta dago a
hankali har lkcn gabanta na faduwa tana kallonsa cikin duhun, a hankali taji ya
saketa ya koma ya kwanta a bit relieved, tana ganin haka tayi saurin kwanciya
bayansa tana kuka a hankali, ko minti biyar bai kara ba bacci me nauyi ya daukesa,
Nihad kuwa bata sake komawa baccin ba, don duk tunaninta kilan shi ma ya ga aljanin
daren ne shine ya ji tsoro ya riketa haka, toh shi ma ya ji tsoro ina ga ita, hakan
ya kara daga mata hankali ta dinga shige masa tana shesshekan kuka ta takure cikin
hijab dinta, raba daren Nihad tayi tana masu gadi, duk motsin da taji sai ta kara
makale masa, sai kusan karfe hudu da rabi bacci barawo ya saceta. A hankali khalil
ya bude ido ta dalilin tada sallah da aka yi, ya mike zaune da kyar ya kunna switch
din dakin dake bangaren da yake ya juya yana kallonta, baccinta kawai take, ya
kalli towel dinta dake can side din sai kuma ya sauka daga kan gadon ya shiga
bandaki, Har ya dawo masallaci Nihad bata farka ba, kallo daya yayi mata ya dauke
kai da sauri, ya dau karamar wayarsa ya fita daga dakin. Sai karfe bakwai saura
Nihad ta bude ido a hankali, bin dakin tayi da kallo sannan ta kalli gefenta towel
dinta ta gani a yashe ta zaro ido ta kalli jikinta da sauri ta mike zaune tana
gyara hijab dinta, kaddai ya ganta haka? Tunanin hakan yasa ta rufe fuskarta da
pillow tana kara rufe jikinta da hijab dinta a kunyace, daga karshe dai ta mike ta
shiga bandaki, bayan ta idar da sallah tana ta zaune saman darduma har gari ya waye
gaba daya sannan ta mike ta fita ta koma dakinta, wanka tayi ta shirya ta fito
parlor, bata gansa a parlon ba sai wayarsa dake saman kujera, ta kalli kofar
kitchen din alamar yana kitchen, ringing wayar ya fara yi ta kalli kofar kitchen
din da sauri, da ta ga kamar bai ji ba tunda bai fito ba tana tafiya a hankali ta
karasa gun wayar ta dauka tana kallon me kiran, Father ta gani a screen din, dai
dai nan ya fito daga kitchen din ta mayar masa da wayar ta ajiye, kamar yanda ta ki
kallonsa shi ma haka bai yarda ya kalleta ba, ya tafi gun wayar ya dauka, kallon
screeen din yake ko kiftawa babu, yana ta kallo har kiran ya katse, ta ga ya zauna
without knowing he did so, still kuma idonsa na kan screen din, he looks a bit
baffled, sake kiransa aka yi, ya daga kai ya kalleta suka hada ido, sai kuma ya
dauke kansa ya mike ya nufi kofar ya fita compound, bayan ya fita still bai daina
kallon wayar ba kuma ya ki dagawa, zaunawa yayi a saman dakalin da ya saba zama ya
daga kiran tare da sallama, he wasn't given the space to even greet or say
anything, ya dai yi shiru yana sauraronsa har ya gama fadin abinda xai fada ya rufe
ido a hankali yace "Gobe in sha Allah" yana fadin haka yaji an katse wayar ya kalli
screen din, sai kuma ya jinginar da kansa da bango, and he sat there for more than
an hour ya kasa shiga cikin gidan, Nihad dake ta zaune parlor ta mike ta shiga
kitchen din taga shayin da ya hada a mug har ya huce. Har Nihad ta iso inda yake
bai sani ba, shadow dinta da ya gani ya sa ya daga kai, ta jingina da bango tace
"Me yasa ka bar shayin a kitchen a bude kuma?" Bai ce mata komai ba, ta tsaya for
almost 2 mins, can ta juya ta koma ciki, dafe kansa yayi, a karo na farko yayi
regretting barin wayarsa a kunne, yawanci sai xai yi waya yake kunna wayar yana
gamawa kuma zai kashe but for almost 3 months now ya daina kashe wayar. Tashi yayi
daga karshe ya shiga cikin gidan, tana zaune saman kujera ta bi sa da kallo kamar
ya sani ya juyo ya kalleta, ta dan turo baki ta ci gaba da kallon tv da take, har
bayan azahar khalil na daki, Nihad ta ji ana kwankwasa gate, ganin bata ga alamar
zai fito ya bude ba ta mike ta tafi dakinsa, murda kofar tayi ta shiga ciki, a rufe
taga idonsa, ta karasa inda ya ajiye makullin ta dauka ta fita, tana bude gate din
gidan taga Naf da zully a tsaye, ta ɗan buda ido cike da fara'a tace "Lahhh, sannun
ku da zuwa" Naf tace "Nihad, yaushe Husnah ta bar gidan ki?" Nihad da gabanta yayi
mugun faduwa don suna cewa Husnah aljanun daren da ta manta ne suka fado mata, cike
da karfin hali tace "Jiya da safe" Naf ta kalli Zully, sai kuma ta kalli Nihad tace
"Toh lafiya qlau ta bar gidan ki?" Nihad ta marairaice tace "Ni dai da safe na
ganta jikinta wani iri kamar an zaneta, fuskarta duk ya kumbura haka ma bakinta da
idonta shine tace min wai aljanun dare ne suka mata haka" Naf da zully suka kwashe
da wani dariya barin Naf da sai da ta kai kasa sbda dariya, Naf ta dago bayan tayi
dariyarta me isarta tace "Halan ku biyu kadai ne a gidan?" Nihad ta girgiza kai
tace "Aa shi ma yana nan ai" Zully tace "Ke kuma kina ina sanda aljanun daren yayi
mata haka?" Nihad tace "Ni dai bacci nake, kuma ai kun san anyi ruwan sama, kawai
na tashi da safe na ganta a kitchen duk an zaneta, tace in miko mata jakarta da
wayarta" Dariya kawai su Zully suke har da kyakyatawa, Nihad dai sai kallonsu take
with confusion, Naf tace "Toh sai ku daure ku zo dubata a asibiti don tana can rai
a hannun Allah an bata gado, mu kuma ce mana tayi bata kwana a gidanki ba hatsari
tayi xata tafi kaduna jiya da daddare an kirata mamarta ba lafiya" Nihad ta gwalo
ido tana kallonsu, Naf tace "Ai kam dai tana asibitin da aka ta6a kwantar da kawar
zully nasan kin gane asibitin" A hankali Nihad tace "Na gane" Naf tace "Sai ki gaya
masa ya kawo ki ku dubata, don da aiki ma ake da niyyar mata a idonta daya daga
baya kuma idon ya ɗan bude kadan" Nihad tace "Toh xan gaya masa" Naf tace "Mu yanzu
akwai inda za mu, amma xa mu hade a asibitin anjima in ya kai ki kenan" Nihad tace
"Toh" Daga haka suka koma motar Naf ta bi su da kallo, sai da suka bar layin sannan
ta juya ta koma cikin gidan, tsaye ta gansa bakin kofar parlor, tana karasawa
balcony ya hade rai yace "Wa ye ya Kwankwasa gate din?" Babu yabo babu fallasa Tace
"kawayena ne, sun zo su ce min Husnah tana asibiti bata da lafiya wai har xa ayi
mata aiki a idonta daya, ni dai wllh ka kai ni in dubata tunda a nan gidan aljanun
daren suka mata haka" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dinga kallonta, can ya
juya ya koma ciki. Bayan la'asar taga ya shirya yana rike da mukullin mota ta mike
da sauri kafin tace komai yace "In kin shirya ina jiranki idan kuma baki shirya ba
inyi tafiyata" Da sauri ta tafi daki ta dauko hijab din ta ta saka, bayan sun bar
gidan taga sun hau saman titi tace "Asibitin xa mu je?" Yace "Ohk" Nan ta gaya masa
asibitin, tana ganin sun kusa asibitin tace "Baxa mu siya mata wani abu ba?" Yace
"Ohk za ki siya mata wani abu kenan?" Tace "Ehh" Yace "Me zaki siya mata?" Tace "Ga
wasu masu fruits can kawai ka tsaya mu siya mata" Parking yayi dai dai wajen ta
bude motar ta tafi tace su hada variety of fruits na 10k, suna hadawa ta shigo
motar tana kallonsa tace "Dubu goma ne" Yace "Ohk, ki basu" Tace "Toh ina atm card
din?" Yace "Atm din wa?" Ta wani kallesa tace "Naka mana?" Yace "Ni nace maki ina
da kudin siyan fruits?" Ta marairaice tace "Toh amma ba sai da na tambayeka ba?"
Yace "Bani da kudin biyan fruit din kawarki" Kamar zata yi kuka tace "Na shiga uku,
bayan kasa nace su hada fruits din, ni yanzu ya zan ce masu?" yace "Ke ina atm card
din ki?" Tayi narai narai da ido tace "Bama ni da shi ni, kuma wllh babu ko sisi
account dina tunda Abba ya dai a bani kudi" Yace "Sauka kice masu su mayar da
fruits dinsu kin fasa siya" Ta gefen ido take kallon alamar atm card din nasa dake
aljihun rigarsa, can ta zura hannu da sauri ta cafki atm din, rike aljihun yayi
yace "Keee" Ta hade rai tace "Idan baka sake ba zan karya wallahi" sai kuma ya cire
hannunsa a hankali, ta turo baki ta zare atm card din ta sauka daga motar ya bi ta
da kallo, ta basu suka cire kudinsu ta koma mota da fruits din ta saka atm card din
a handbag dinta ta kulle, bayan few seconds kawai ya tada motar suka bar wajen.
Suna isa asibitin Nihad bata taba tunanin zai shiga dakin ba, amma sai kawai ta ga
ya shiga, Husnah na hada ido da shi sai da ta firgita, Su Naf da Zully da wasu
frnds dinsu biyu dake dakin suka mike ganin irin