Showing 3001 words to 6000 words out of 268471 words
favor Nihad" tace "Plss
yaya abu na karshe da xa ka iya min a rayuwa shine don Allah kar ka bari Abba su yi
min auren dole, wllh xan iya mutuwa kaga har na gaya maka" Yace "What did ur
boyfriend say about the video?" A hankali ta sunkuyar da kai tayi shiru, ya hade
rai yace "Tambayarki nake" Cikin rawan murya tace "Yayi blocking dina...." Farooq
ya gyada kai yace "Good" ta hade hannunta tace "Don Allah yaya, kasan consequences
din auren dole kar ku bari ayi min, na yarda a min ko wani hukunci amma banda auren
dole, idan ma xa a ce for the rest of my life baxan sake fita waje ba, sannan babu
ni babu karatu har abada i agree but kar ayi min auren dole sbda wannan mistake din
nawa, ka taimaka kayi ma Abba magana" Umma ce ta shigo dakin duk suka daga kai
suna kallonta, tace "So kike ki kara tunxura Abbanki Nihad? Duk shirun da yayi maki
bai isheki ba sai kin tunxurasa, Ba na baki shawaran kar ki ce komai a kan batun
auren nan ba, so kike ki fusatar da Abbanki yayi maki abinda bai ta6a maki ba?"
Faruq yace "Noo wannan ba magana bace Umma, we don't even know da wanda xa a
hadata, ko ma me tayi ai da gatanta and she still have her right, su gani suke
auren shine way out, whereas it's not" Umma tace "Toh tunda kai ka haifesu ai sai
ka gaya masu way out" Ya girgiza kai yace "Umma idan ma auren ne ba sai a bari
komai ya lafa ba, ta yaya abu na xafi xafi a shigo da maganar aure, waye xai
aureta? Noo bata yi deserving wannan auren ba gaskiya" Umma tace "Ko ma wa xai
aureta wannan ba damuwarka bane sai ka xuba ma iyayenka ido, su ai sun san abinda
ya kamata, ko so kake ka nuna masu goyan bayan abinda tayi kake?" Ya dinga kallon
Ummar tasa, Mikewa yayi ya fice daga dakin, ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo,
sai da suka sauka stairs Umma tace "Farooq" ya juyo yana kallonta, tace "Naga kamar
so kake ka ja ma kanka bakin jini gun Kakarku da Engineer, sannan nima hakan ya
shafeni, kawai so kake ka ja min maganan da ba shi da ranan mutuwa gun tsohuwar
nan, don haka kar ka sake tofa komai a kan lamarin nan, ita kanta uwar da ta
haifeta taki cewa komai har yanzu, me magana dama daga ni sai kai, kuma a hakan ma
haushinmu ake, don Usman ma bai tsoma kansa ba balle a ga nasa, to ba Uba daya ba,
ko ciki daya ku ka fito da Nihad ni dai nace ka janye bakinka daga issue din nan
domin a samu masalha, daxu Abban naku ma ya kirani wai ya tafi karkara neman wanda
xai hadata da, to idan ana son asiri ya rufu ai sai dai hakan dama, to wa xai yarda
ya aureta a nan dai cikin gari? don haka nake kara gargadinka, kar ma ka fara cewa
a fasa aure" Faruq yace "Karkara kuma?" Umma tace "Ehh nan fa, ko ka ga alamar
Nihad xata samu miji cikin gari ba karkaran ba nace, da wannan mummunan abin da ta
aikata wa xae yarda nasa ya aureta?" Yace "Ah haba, karkara kuma, noo ba dai
karkara ba, waye ya ba Abba wnn muguwar shawaran? Karkara fa kike ce Umma" Strictly
Umma tace "Farooq" ya daga kai ya kalleta tace "I am giving u this serious warning,
kada ka kuskura ka sake tofa naka a wannan lamarin, kaji abinda nace maka??" Bai ce
mata komai ba, tace "To na dai gaya maka" daga haka ta bar wajen ya bi ta da ido.
π *Bitter Rivalries*π
And i came really prepared...... π€
Contact me directly viaππ»
βπ»
07087865788
ππ *NIHAAD*ππ
By _Khaleesat Haiydar_βπ»
~~
2
Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat's Palace, my die
hard fansπ₯°π Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya karye amma take ta
bobboye mana, Hajiya Aunty Zahra mai siyar da harawa, Hajiya Nafisa Mom twins, Su
Hajiya Aunty Maryam, Uwar Nabeela, Mrs Jay, Hajiya Inna, Hajiya Deejah, Hajiya
Zeenaru, Nanisa Zero Zero, Hajiya Bilkisu, Hajiya Rabia, Damsel, Uwar Yusrah, Ummu
Zainab, Uwar gidan Barrister wato Khaleesat me siyar da tayoyi, kai duk wanda bai
ga sunansa a nan ba ya biyo ni da sunan xai gansa a next pageπ amma fa ko kun ki ko
kun so sai nayi sharing link dinku, ku tanadar ma sabbin fans ruwa da cin cin ehe.π€
Da daddare Abba na xaune parlonsa tare da Yayansa Alhaji Abubakar.... Alhaji
Abubakar yace "Ae duk ba sai ka sanar masu komai ba, kawai gobe idan an daura auren
kowa ma sai ya sani, i don't think u owe anybody explanation to this" Abba ya
numfasa yace "Toh shikenan" Alhaji Abubakar yace "Yea i think that's okay ba sai
kace ma kowa komai ba for now, a ina kace xa su xauna? I mean which of ur houses
are they staying?" Abba yace "I don't think i can keep her where she will in any
way feel comfy, i wish xai koma can karkarar tasu su xauna in basa enough jari,
idan noma xai yi ma yayi employing workers su yi masa a can ko ni xan dinga biya,
cause i want her to learn a bitter lesson of her life, ina son ta san wata rayuwar
bayan rayuwa cikin daula" Alhaji Abubakar ya girgiza kai yace "No... There is no
need for all that, duk abinda ya kamata kayi kar ka fasa, ka basu inda xa su xauna
comfortably" Bayan Alhaji Abubakar ya bar gidan, Umma ta shigo parlon Abba, ganin
basu ta6a abincin da ta ajiye masu ba tace "Haba yallabai, ko abincin baka ci ba
har yanxu?" Abba yace "Kawai ayi min black tea" Umma tace "Toh shkkn" Tashi tayi ta
dau abincin ta fita, ba a dau lkci da fitarta ba Farooq ya shigo parlon, waya ya
tadda Abbansa ke yi, wanda da jin yanda yake amsa wayar kasan magana ce aka kirasa
a kan Nihad kuma abokinsa ne me kiran nasa, Farooq ya sunkuyar da kansa duk jikinsa
yayi sanyi, har Abba ya gama wayar ya jinginar da kai da kujera bai ce masa komai
ba, a hankali Farooq ya dago yace "Barka da dare Abba" Abba ya amsa, Farooq yace
"Throughout ina ta kiranka but couldn't reach u on phone" Abba yace "Ehh wata er
tafiya nayi, is there any problem?" Farooq yace "Ya gajiyan hanya" Abba yace
"Alhamdulillah" Farooq yayi kasa da murya yace "Abba magana ce dama a kan Nihad?"
Dai dai nan Umma ta shigo da mug din black tea dake ta kamshi, Da hannu Abba yayi
masa alamar ya aka yi, Farooq yayi shiru, Abba yace "Maganar me a kan Nihad Umar?"
Farooq ya d'an fara kame kame, sai kuma dai kawai yace "Abba a kan auren nan da aka
ce ne, is it not better a yi hakuri a janye, idan ya so..." Dakatar da shi Abba
yayi yace "Idan wannan maganar ce ta kawo ka, ka je kawai i need rest Umar, kaga
ban dade da shigowa gidan ba" Umma dai na xaune kan one sitter, pleadingly Farooq
yace "Pls ka saurareni Abba" Abba yace "I said i need rest...." Umma tace "ka je
yace xai huta ko kuwa?" Mikewa Farooq yayi ya fice daga parlon, Umma ta kalli Abba
tace "Kayi hakuri Yallabai, xan so ka cire wannan damuwar a ranka, in sha Allah
everything will be alright, kar kaje ka sa ma kanka wani ciwon bayan hawan jinin da
kake fama da" Abba yayi sigh yana girgiza kai yace "A kalla ba a kirani a rana ba
xa a kirani sau goma a kan Nihad, the video is trending day by day.... Me yafi
wannan bakin ciki Sumayyah? A reputable person like me, noo Nihad tayi tarnishing
image din gida na" Da damuwa Umma tace "To ya xa ayi Yallabai haka Allah ya kaddaro
mana, sai dai kawai mu rungumi kaddara, amma akwai wani malami bawan Allah, tun
ranan da abun ya faru Hajiya Sukhaina tace ko shi xa ayi ma magana yayi addu'a
Allah ya kawo karshen trending din abun, shiru xaka ji kamar ba ayi ba wllh, neman
video din ma xa ayi a rasa" Abba ya mata wani kallo yace "Malami? Wani irin
malami?" Umma ta gyara xama tace "Ba boka fa nace ba Alhaji, amma dai shkkn kawai,
ina ce akwai malamai bayin Allah wa enda..." Mikewa Abba yayi bayan ya dau mug din
black tea dinsa ya wuce daki ya kulle kofa. Washegari friday ana sauka sallan
juma'a, Abba ya tafi tare da yayansa da cousins dinsa biyu xuwa garin da aka daura
ma Nihad aure, a kan sadaki dubu hamsin wanda shi ya bayar. Sai kusan la'asar suka
dawo gida, nan kuma ya sanar ma Umma su fara shirye shiryen kai ta, Umma tayi shiru
cike da jimami, sai kuma ta sauke ajiyar xuciya tace "To wani gidan kenan xa a kai
ta yallabai?" Abba yace "Wannan gidan da aka gama na Rijiyar zaki, it's already
furnished" Umma tace "Allah sarki, ina laifin wannan gidan na kusa da mu yallabai,
ai xa su fi sakewa a nan..." Abba yace "Ban yi niyya ba" Umma tace "Rijiyar zakin
ma yayi ai, Allah ya saka da alkhairi" mikewa tayi ta fita don xuwa sanar ma Mum
din Nihad da Yan uwanta dake can bangarenta abinda Abba ya ce, nata side din ta
fara shiga, first daughter dinta Kamila na xaune parlon sai second daughter dinta
Amina, sannan kanninta mata biyu da suka xo daga Jigawa daxu, Umma tace "To duk ku
shirya kai amarya an daura mata auren yau dai" Kamila ta riΖe ha6a tace "Har an
daura?? yanxu Umma Abba bai fada maku da wa aka yi auren ba, ni kawai sai xuciyata
ke bani Hamid ne ko Saif" Umma ta saki baki tace "Hamid? Ita uwar Hamid din karen
hauka ya cijeta xata yarda a hada shi da Nihad? Ko kuma shi Hamid din mahaukaciya
ne da zai amince da auren Nihad, Kai har shi Uban Hamid din da ya kirkiro auren ba
yarda xai yi ayi auren da Ιan sa ba karewa kenan, haka ita ma Innar, wani can dai
Abban naku ya samo a karkara, hakan kuma kadai ne rufin asirinta a dai abin nan da
ya faru" Amina ta mika ma Umma wayarta dake ring, Umma ta amsa ganin autarta ce ke
kira ta daga ta kai kunne da murmushi tace "Hello auta, duk yau kin ji ni shiru ko"
lkci daya ta hade rai tace "Ki zo kiyi me kina karatun ki Nihal? A kan wani dalili
xaki taho kuna tsaka da karatu? To wllh kar ki fara idan ba haka ba yanxun nan in
kira Farooq in gaya masa, me xuwanki xai sa a fasa, bayan har an daura auren ma,
duk sanda ku ka yi hutu idan kin dawo sai kije ki ga dakin er uwar taki ba shikenan
ba, amma ki wani ce xaki kamo hanya kamar ana yaki" a kufule Umma da ta gama
sauraronta tace "To wai uban meye na wannan kukan da kike, so kike ki ja ma kanki
wani ciwo ne ko ko? Bata da waya yanxu a hannu, idan na fita yanxu xan bata sai ku
yi magana, amma ta ina xaki baro Zaria da yamman nan ba hutu ku ka yi ba, kuma dama
kin ta6a dawowa gida ke kadai ne banda gulma da daura ma kai wahala Nihal?? Ni dai
sai anjima ban san shashanci" Katse wayar Umma tayi, Aunty Laraba tace "Wai tahowa
xata yi daga Zarian?" Umma tace "Ehh wai, kinji wata gulma dai, ko uban me xata xo
tayi oho" Aunty Laraba tace "To wai ita tace ma Abban nasu bata son Maryam Abatcan
da er uwar ke xuwa ne?" Umma tayi murmushi tace "Aa haka dai yayi niyya ita ya
turata federal dai dai ita, ita kuma Nihad dama Private ne dai dai da ita inji
uban, wato Maryam Abatcha, option ma ya bata ta xabi Private uni da take so shine
ta xabi Maryam Abatcha" Aunty Maimuna tace "Ai ko ga Maryam Abatcha ana ta gani a
soshiyal media" Umma dai bata ce komai ba, sai kuma tace "Allah dai ya shirya mana
zuri'a kawai" daga haka ta fita xuwa bangaren mum din Nihad, a corridor ta hadu da
matan Alhaji Abubakar su biyu sun shigo gidan, suka gaisa da fara'a ana kara
jajanta lamarin da ya faru, Hajiya fatima tace "Daxu Abbansu Hamid ya dawo gida
yake sanar mana ai har an daura aure, nace shine babu labari ko daga gare ku
Hajiya" Umma tace "Wllh abun ne ya xo a haka Hajajju, kinsan muna ta tunanin xa su
hakura a fasa auren a nemo wani solution, to kin san halin mazan namu da kafiya,
wllh sun ki, kawai fatan Allah ya basu xaman lafiya da ko ma waye mijin" Hajiya
Zuwaira tace "Shikenan addu'ar, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a gareta,
Allah kuma ya duba yan baya" Duk suka amsa da Ameen, Umma tace "Mu je dama bangaren
Maryam din xan je" a tare suka tafi part din Mumy, bayan an gaisa an kara
jajantawa, Mumy dai bin su kawai take da kallo bata cewa komai, Umma ta sanar mata
abinda Abba yace sannan ta fita daga dakin. Bayan magrib xa a kai Nihad, kafin
Magrib din Abba ya tara gaba daya matan nasa da 'ya yansa, Usman, Farooq, Kamila,
Amina, Nihal ce kawai bata nan a yaran Umma, yaran Mumy kuwa Nihad da kanninta biyu
wa enda duk maza ne, daya me shekara tara da kuma me shekara shidda duk basa
parlon, Bayan duk sun hallara a parlon Abba ya nisa yace "Ina fatan duk kun ga
abinda ya faru da yar uwarku Nihad, Nihad is nothing but a disappointment to the
family, kar ku ga Nihad tayi wannan mummunan laifin na bada ita ga wanda nayi niyya
without bothering ko ya cancanceta ko bai yi ba, to wllh wllh if anything of such
should happen again in my family infact ko wanda bai yi kusa da hakan ba idan ya
faru a family dina wllh i will prefer to shoot that person" Umma ta sauke ajiyar
xuciya tace "Allah Ubangiji ya tsare, ya kare mana zuri'a Alhaji" Abba ya kalli
Mumy da bata cewa komai tun faruwan abun, amma kana ganinta kasan she is
heartbroken, her first child, habaa ko bacci bata iya yi tunda wannan lamari ya
faru, da tasan Nihad xata girma ta yi irin wnn rashin jin da Allah bai raya mata
ita ba, tun faruwan hakan ita ma ta kashe wayarta sbda kiran yan uwa da abokan
arziki da suka san Nihad, Abba yayi gyaran murya yace "Ban ga laifinki ba Maryam
don ni nasan kinyi iya bakin kokarin ki na ganin kin ba ma Nihad tarbiya yanda ya
kamata, u tried ur best, matsalar kawai u didn't make Nihad ur frnd aside mothering
her, amma dai babu komai, kawai dai kafin Nihad ta dauko mana abinda xuciyarmu xai
kasa dauka nan gaba tun wuri ni da yayana da yan uwana mun mikata, kusan xance na
bada sadakarta" Abba na fadin haka ya ciro sadakinta dake aljihunsa ya mika ma Umma
yace "Sai ki damka mata ku da xa ku kai ta" Umma ta amsa cikin sanyin murya tace
"Yanxu Yallabai mun yi deserving a bada er mu ba tare da mun san wanda aka ba ma
ba? Ai hankalinmu baxai taba kwanciya ba, tun jiya nake bin ka kaki gaya min, ai
yana da kyau a sanar mana mu sani don muna da hakkin sani, idan ma ni bani da
hakkin in sani mahaifiyarta fa?" Abba ya Ιan yi shiru, sai kuma ya dau wayarsa yayi
dialing number snn ya kai kunne, ana dagawa yace "Ka shigo nan parlor ka sameni
yanzu" daga haka ya katse wayar, duk kowa yayi shiru ya xuba ido ya ga wanda xai
shigo parlon barin Farooq da Umma. Da sallama ya bude kofar parlon, ganin su Umma
ya dakata daga bakin kofar bai shigo ba, Abba na kallonsa yace "Karaso" ya karasa
shiga cikin parlon kansa a kasa, duk occupant din parlon
kallonsa suke with full shock, Abba ya nunasa yace "Shi na ba auren Nihad, shine
mijinta" Mikewa Farooq yayi yana kallon Abba baki bude, Mumy ta hadiyi wani kullutu
da taji ya tokareta a makogwaro, Umma kuwa sae kallonsa take daga sama har kasa
babu ko kiftawa, ta ma rasa yanayin da take ciki ita, Kowa na parlon ya kasa cewa
komai, tsabar silence din parlon da allura xai fadi xa a ji karar faduwarsa, shi
kam dai yana ta tsaye ya sunkui da kai har sannan, Abba yayi breaking silent din
yace "Je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon, Usman ya kalli Abba yace "Haba Dad?
Yanxu shi ka aura ma Nihad?" Farooq yace "No Abba, u should have given her a
choice, bata yi deserving ayi mata dole ba sbda wannan kaddarar tata, but Abba...."
Kasa cewa komai yayi ya koma ya xauna, shi ma ya rasa yanayin da yake ciki, but he
don't think it's still bad after all, just dat.... Girgiza kai kawai yayi, Umma
tace "Haba Alhaji...." Abba ya mike yana bin kowa da kallo yace "No one have the
right to query my authority" Yana fadin haka ya bar masu parlon ya shiga bedroom
dinsa, suka dinga kallon kallo a tsakaninsu a parlon, Usman ne ya fara mikewa ya
fice daga parlon, Mumy ta mike ta bi bayansa ita ma tana share idonta, Umma ta
sauke ajiyar xuciya tana kallon Farooq, ita gaba daya ma kanta fa ya kulle, Abba
really took them unaware, jinginar da kanta tayi da kujera Farooq ya mike ya fice
daga parlon shi ma. Ana idar da magrib yan kai amarya suka fara shirye shiryen kai
ta, Nihad bata ta6a shiga irin tashin hankalin da take ciki ba a wannan moment din,
ko video dinta bai tada hankalinta kamar yanxu ba, gashi nobody is there to console
her, Nihal na schl, Husnah kuma taki xuwa gidan sbda Farooq, gashi bata da numberta
a kai balle ta amshi wayar wani ta kirata, su kamila da Amina tamkar ma farin ciki
da abinda ya sameta suke don uban kwalliya suka ci har da kashe dauri Hajiya
Zuwaira ce ta kai ta gun Mumy tayi mata fada ta sa mata albarka, sbda takaici da
bakin ciki Mumy ta ki cewa komai daga karshe da aka tilastata sae cewa tayi Allah
ya tsare, Alhaji Abubakar ne kawai yayi mata fada, Abba kuwa tun da aka idar da
magrib ya ki shigowa gidan dama, a haka dai aka tattara ta da akwatunan kayanta uku
wanda Umma da Kamila suka hada mata wasu kayayyakinta a ciki, kuka take kamar xata
shide, har addu'a ta dinga yi Allah ya dau ranta kafin a karasa da ita gidan, tana
ganin an shiga gidan ta kara sautin kukan da take a haka har aka shigar da ita
daki, gida ne bungalow madaidaici me dakuna uku, ko wani